0% found this document useful (0 votes)
1K views146 pages

Kibiyar Kishi 1to End

Copyright
© © All Rights Reserved
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
Download as txt, pdf, or txt
0% found this document useful (0 votes)
1K views146 pages

Kibiyar Kishi 1to End

Copyright
© © All Rights Reserved
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
Download as txt, pdf, or txt
Download as txt, pdf, or txt
You are on page 1/ 146

KIBIYAR KISHI

NA
✍🏻
MARYAM ANOUR

Bismillahi rahamani rahim

Page 1

"Assalamualaikum!
Assalamu alaikum!!
Walaikum salam!!!

Ahh,Aisha ku ne haka?ku shigo mana ya kuka tsaya a waje kamar wasu Baki.

wata tatijuwar mata wace baza ta haura shakara arbain ba tayi maganar,tare da
shinfida musu taburma."Antashe lfy baba Mariya mun same ku lafiya? Lafiya
alhamdulilah da fatan kuma kuna lafiya,ya mai gidan ki shima fatan yana lafiya?

Lafiyan shi kalau alhamdulilah.

Mashallah haka muke son je ,daga haka ta tashe ta nufi kitchen.ganin haka ne husnah
da suke tare da Aisha binta kitchen din.

Baba ya banga su Kausar ba.

Sun je gidan auntyn ku Maryam.gaskiya nayi kewar su Wallahi,yaushe zasu dawo?

Gobe inshallah. tohm Allah ya kaimu.

Daga haka ta juya da nufin fita baba ta tsayar da ita ta hanyar cewa tsaya ki tafi
da wanan,sai tayi kasa da muryar,inna fatan kinye abinda nasaki?Eh naye kuma bata
gane ba yanzu ma yana cikin kayana anjuma zaki gani.Yauwa yar gari.

Yanzu mu tafi Kar tace mun barta itta kade anjuma mayi maganar.Daga haka suka fita
suka same ta,tana waya kuma daga gani mai mahimmanci ne. bayan tagama ne suka kara
gaisawa. ya naga baki sha ruwan?

Na sha fa.daga haka suka fara hira jefi jefi.

Baba Mariya ce tace "kwasam kuka ji kira ko,to Wallahi dangin mahaifin ta ne suka
matsa wai lallai su aure zasu mata.nayi kokarin fahimtar dasu Amma firr sunki
ganewa wa,wai yarenya takai munzalin aure Dan haka su sun mata miji,zasu aurar da
ita.

Na fahimta baba,ni dama naso tayi

karatu ta samu koda degree ne,duba da yanda ilimin ya mace yake da anfani a zamanin
mu na yanzu.amma tunda miji ya fito kam tayi auren,in yaso ko a gidan tane sai
tacigaba da karatun in mijin ya yarda."cewar Aisha

Ehh nima haka nace tunda miji ya fito kam gwara ayi auren kawai in yaso ta cigaba
da karatun daga baya inda rabon ta cigaban din.

To amma Baba anan Kano zai aje ta ko inna?Eh da de yace zai kaita Abuja can wajan
aikinsa kenan,to daga baya kuma ya canja Ra'ayi.anan zata zauna.

Zai hada su da abokiyar zaman ta.

Ok dama yana da mata ne?"Eh yana da mata.To Allah ya basu zaman lafiya.
Daga haka suka cigaba da hira,

Can Aisha tace Baba nikam zan wuce.da wure haka?

Ehh inna son leka su ummi ne kafin in wuce gida.

To shi kenan ki gaishe min da ita kice nima inna hanya zan shigo wajan ta gobe in
Allah ya kaimu. Toh zata ji. Baba yau gidan ki shuru banga yaran ba.

Na aike su ne wallahi shiyasa kika ji gidan shuru haka.Toh a gaishe min da su in


sun dawo.

amarya husnah ne zan wuce sai mun zo biki, Amma zamuye kewar ki ba kadan ba.nima
zanye kewar ku sosai auntie. baba na wuce sai mun zo biki. to Aisha ki gaida gida
mungode sosai. nice da godiya ai baba daga haka ta shiga motar ta tayi gaba abun
ta. Saida suka ga tafiyar ta kana suka koma cikin gida.

*****

Aisha koda taje gidan bata tarar da kowa ba,sai masu aikin ummi.palour ta zauna
tare da dauki wayarta tana latsawa tana jiran dawowar ummi.

Bata Jima da zama ba sai ga ummi ta shigo da sallama fuskar ta cike da annuri.uwar
amarya uwar amarya yau kece a gidan namu.

Kinje ki fa ummi sai kace wace tayi shakara bata leko ba,ko last week ma ai muna
nan. hakane to kin zo lafiya inna husnah yau ba ta beki ba?

Eh nakai ta gida, baba Mariya ta kira shakaran jiya wai tazo gida tunda biki ya
gabato, shiyasa na tattara ta nakai ta. tunda mu bamu da daraj...

"Haba Aisha bansan ki da irin wanan hali ba. Allah ummi bazaki gane ba. yarenyar
nan ni nake rokan ta tun bata kai haka ba,kamar yata nake ganinta fah. na dauka
yanda suka barmin ita tun tana karama haka zazu barta har in aurar da ita amma wai
kwasam suka Kira wai zasu mata aure.

Ni bama wanan ba koda zasu aurar da ita ai yakamata a sanar damu tun farkon
abun,amma wai saida suka gama kome da kome har ansa rana aure ma saura sati daya
shine wai za a wani kira a fada ma mutum.

Nima gaskiya banji dadin hakan ba to amma ya zakiyi masu ya sunce abasu yarsu,kuma
ma Mariya tace ita bata san kome ba sai kiyi hakuri ko. kuma hakan Kar yasa ki
canza musu kome kinji ko. Aa ni ban nuna musu kome kome ba Kawai de banji dadin
abun ba.

To yanzu wace irin gudunmuwa kike son basu?

Ni kaina bansan me zan basu ba,tunda de kinga abun nasu babu notice balle mutum
yace ashirye yake.amma ke a ganin ki me yakamata na basu kudi kome? Eh to kudi ma
zaiyi musu afani amma kisaye abu zaifi koba komai zata na tinawa dake. gaskiya ne
ummi to mai zai hana in dauki nawin kayan kitchen ko ya kika gani? Mashallah hakan
ma yayi Allah ya baki ikon yi.

Amin.wai ummi inna kika ji ne dazu?

na shiga wajan maman walid kin san takara haihuwa to nashiga mata barka ne.
Mashallah Allah Allah ya raya.kowa nata haihuwa amma banda mu shakara da shakaru ta
fada hakan da wata irin murya mai ban tausaye.kul na haneki,kar ki kira cewa haka
haihuwa ai ta Allah ce in lokaci yayi kema zaki haife naki insha'Allah.

Ummi wallahi bakisan yanda nake son ganin nima ace yau ga dana ko yata a duniyar
nan ba.kice gaba da ad'ua nima inna nan ina tayaki da ad'ua insha'Allah zaki
samu.amin kawai tace dan gabadaya mood dinta ya baci.

Yauwa kar na manta baba Mariya na gaishe ki tace wai gobe zata shigo.to Allah ya
kaimu. amin

******

Washegari misalin karfe uku na rana tana cikin bed room dinta tana folding kayanta
da ta wake dazu da safe tana sawa a wardrobe dinta.a hankali ta furta
subhanallah.wai me yake Shirin faruwa da ni ne,mai yasa nake jin faduwar gaba ne
tunda na tashe yau.allah yasa lafiya.daga haka tacigaba da abunda takeyi.can sai ga
kira ya shigo wayar ta.bestie taga kan screen din wayar dan haka bata, bata lokaci
wurin dagawa ba.

Amma me kokafin ma tayi magana anriga ta magana ta hanyar cewa.

Amma kin bani mamaki Aisha,ashe aliyu zai kara aure amma ki kasa gaya min.dama
kawancin kenan ?

Aure kuma a inna?

Banson renin sense fah tom.

Ban gani mai kike cewa ba aure...wazai yi aure?

Karki rena min hankali mana,kina son gayamin baki san mijin ki zai karo miki
kishiya ba.

No ban..bansani ba bai fada min ba ta fada hakan ne da wata iriyar muryar.

Chab lallai kuwa aliyu ba karamin rena miki hankali yayi ba, yanzu ace duk bidiren
nan da ake baki san kome ba lallai ba shaka namiji kenan.kuma duk cikin yan uwansa
arasa wanda zai fada miki? Ba wanda ya fada min,kema kinsan ba fada min zasu ye ba.

to amma...

da wata iriyar shaking voice ta katseta ta hanyar cewa zan...zankira ki batool kitt
ta kashe wayar tare da daura hannayen ta Saman goshin ta.

So take tayi digesting din maganar da aka fada mata, dama dan zai yi aure shiyasa
ya canja mata gabadaya takasa gane kansa,kullum fada da masifa Wanda a da ba haka
yake ba.

Ashe bani da wanan darajar a idanun ka, ashe bani da wanan kimar a wurin ka aliyu
zaka Kara aure Amma ka kasa fadan min.sai dai inji a bakin mutane.kukan ma ta kasa
ye sabon abun ya shige ta.
Hayaniyar da taji a parlourn kasa ne yasa ta sauka daga kan godan ta nufe
palour.tun kafin ta sauka kasa tagane ko suwaye.
"Duumm taji zuciyarta ta buga saka mokon ganin hajjiya da tayi,
Salaamu alaikum!
Shuru suka yi ba wanda ya amsa ta saima idanuwa da suka zuba mata.
A hankali ta taka har zuwa wajan Hajjiya ta zauna kasa kusa da kafufun ta,kana ta
suma gaishe ta.
Inna wuni Hajjiya sannu da zuwa ya hanya.
Banza ta mata saima zaman ta da ta jara kan kujerar.
Hajjiya sannu da zuwa ya hanya,taka ra tambaya.
Yauwa juya mun same ku lafiya?
Ba yau bane karan farko da hajjiya ke kiran ta da wanan sunan ba, amma a duk
lokacin da ta kira ta dashi ba karamin zafi zuciyarta ke ye ba.

Haihuwar nan bafa ita zata bawa kanta ba,wai mai yasa suke ganin lefin ta dan kawai
Allah bai bata haihuwa, idan da wanda yake son haihuwar nan tofa bayan ita ne fah.
Ko naye karya ne?
Ba juya bace ke,aure shekara da shakaru amma ko batan wata baki ye bah.sai dai ki
zauna akawo kici kisha kiyi Kashi.
aure shakara goma ,amma shuru kake ji.yaron nan ba yanda banye da shi ba kan ya
kara aure Amma firr yaki.yaron da bai taba bijera wa umarni na.
Haba hajjiya,kema ai kinsan da wata a kasa haka kurum yaya ba zai bijera wa umarnin
ki ba,inji hamida.
Zahra ce tace, ai kana gani kasan an juya Mishi tunani yaron da ko kara kika aje
bazai tsallake ba shine wai har yaki jin maganar ki.

Balkisu, da tun dazu bata sa musu baki ba tace ai kome yazo karshe,asire dai yasaki
shi tunda shi da kansa ya nemi Kara aure.

Gabadaya suka hadu sai gaya mata bakar magana suke tun tana iya jurewa har ta kasa
tafara hawaye abu goma da ashirin.ganin in tazauna taza iya fashewa da kuka ne yasa
ta mike ta bar parlourn tare da nufan kitchen.share hawayen dake zarya a fuskar ta
tayi tare da lalashin kanta,sai da taga hawayen sun kafe kana ta wanke fuskar
ta.tsaye tayi a kitchen din ba tare da sanin abunye ba. can de ta bude fridge ta
dauke ruwa da drinks ta jera Kan tire kana ta fita,koda ta isa bakin kofar shiga
palour ta tsaya taja dogon numfashi tare da cewa you gat this you can do it,
murmushi dole ta kakolo ta yafa a fuskar ta kana ta shiga palour.
Koda ta shiga ba wanda ya kula ta saima hirar su da suke yi aje tiren a center
table. Hajjiya ga ruwan sha.
To kawai tace mata daga haka tace,dama nazo wajan Aliyu ne inna son magana da
shi,na kira shi a waya yaki daga wa dagabaya kuma naji wayar akashe,shine nazo naga
Dalilin kashe min wayar da yayi. ina ga baya kusa da wayar ne ko kuma yana driving
shiyasa bai daga ba.bai shigo ba Kenan?

Eh bai shigo ba yace sai next week in Allah ya kai mu.to in kunyi waya kice Mishi
inna neman sa,yabar duk abinda yaki yazo ya same ne. Inshallah

Dadare bayan ta gama kome tayi Shirin bace ne taji kamar anna konqasa kofar kasa a
hankali ta tashe ta saka hijab din ta kana ta fita tsoro fal ranta duk da tasan
gidan da matakan tsaro kuma akwai mai gadi,to abun tambayar shine wa zai shigo musu
a wanan daren bayan ansan mai gidan baya gari.a hankali ta motso kusa da kofar Amma
bata Bude ba.jin ankara buga kofar ne yasa tayi jarimtar yin magana.
"WAYE?
"Nine ki bude!
Duk da ta gani mai muryar, hakan baisa ta bude ba,saima kara tambaya da tayi. "kai
waye?
"ki bude Aliyu ne!
Aliyu to mai yakawo shi cikin wanan daren,bayan yace mata sai next week zai dawo.ki
bude mana.A hankali ta bude kofar tare da bashi hanya ya shigo.
Mashallah wani kyakkyawan magidanci na gani wanda a kalla bazai wuce 37 years ba,
ya shiga palourn straight Kan kujera ya zauna tare da sauki ajiyar zuciya.

Bayan ta kulle kofar ne ta nufi kitchen ruwa ta dau Mishi kana ta fita.gaban shi ta
tsuquna kana ta zuba Mishi ruwa a glass cup ta mika Mishi. Karba yayi ya sha.saida
taga ya dan samu nutsuwa kana ta fara gaishe shi.sannu da zuwa ya hanya. Lafiya
alhamdulilah kema na same ku lfy.lafiya,daga haka ta tashe ta wuce bathroom ta hada
Mishi ruwan waka sanan ta cire masa kayan bacci ta aje masa kan bed,kana tazo ta
sanar da shi. Ok thank you yace daga haka yayi bedroom dan sosai yake bukatar
wankan nan.
Kitchen ta Shiga ta hada masa abinci ta kawo masa bedroom din,ta tarar ma yayi
wakan har ma yasa kaya.
Bayan ya gama cin abinci ta jara wajan.ta zauna suna dan hira,na dauka kace sai
next week zaka zo.
Eh na dauka zan kai haka ne, Amma alhamdulilah kome ya tafi daidai daga yanzu
zanfara aiki anan,bani ba zuwa Abuja sai dai in za ayi babban meeting tukuna, daga
Monday zan fara zuwa aiki. Kai alhamdulilah wallahi naji dadin transfer din nan da
ka samu.
Finally I can have my husband by my side all the time.
And I will have my wife all the time ba.
Washegari tun da wuri ta tashi tayi aiyukan ta tajara ko ina tasa turaren wuta,tayi
breakfast tajera a dining kana ta wuce bedroom dinta dan yin wanka.
Dai dai 8:35 kamar hadin baki suka fito a tare ko wanninsu yayi kyau har ya
gaji,sai zuba kamshi suke.
Good morning my king
Morning wifey kintashi lafiya,ya fadi hakan ne tare da manna mata kiss a goshin ta.
Hmm lafiya,let go breakfast is ready daga haka suka nufi dining.bayan tayi serving
dinsu ne yace, wifey after breakfast akwai maganar da nake son muye.duuum taji
zuciyarta ta buga,kai Kawai ta iya Kada Mishi dan taji bakin yayi mata nawi.
Bayan sun Kamala sun zo palour kowa yayi shuru, shi yana taradadin maganar da yake
son fada mata,ita ma hakan ce a wurin ta.jin shuru baiye magana ba yasa ta katse
shurun da ciwa,Jiya hajjiya tazo Neman ka wai ta kira numbern ka baya shiga,tace
tana neman ka.shikainan Habib ya sanar da Hajjiya. Tun jiya da yaga kiran da take
Mishi yasan ba lafiya ba, shiyasa ma ya Kashe wayarsa ma gaba daya, amma wanan
Habib ko kofa yaja a zuciyar shi.zasu hadu ne ai,duk rokon da yayi Mishi dan Kar ya
fada mata.ok ehh takira lokacin wayar bata da caji ne shiyasa amma zanje wurin ta
anjuma.

"Ok kace akwai maganar da zaka fada min?" " Hmm..amm dama dama...
Dama me kafada min karka ji kome.Dama..dama zan kara aure ne ya fada tare da kura
mata idanuwa dan ganin rection dinta.
Duk da tasan da maganar tun jiya ta kuma san shi zai kara maimaita mata,amma sai
taji kamar a mafarki take, sosai zuciyarta ta karye ba abunda zuciyarta ke gaya
mata sai ya gaji dake.
P.2
Sosai tayi kokarin boye damuwar ta ta hanyar sakin murmushi"kai mashallah
congratulations my king na taya ka murna.sosai ya zuba mata idanuwa har na tsawon
lokaci, kana yace,"so you are not angry?" Why should I be angry?kaifa na miji ne
kana da damar auren mata hudu, Allah ya baka wanan damar so who am I to be angry
with you. yaushe ne auren?"
"Three days from now za a daura aure kuma amarya zata tare.kallon shi kawai take yi
nan da three days za a daura Mishi aure da wata, and his just telling her."to Allah
ya kaimu,"amma mai yasa sai yanzu kake fada min? Shuru yayi dan bai san me zaice
mata ba.can dai yace"Sorry wifey wallahi bansan ya zaki dauke maganar ba ne,
shiyasa ban fada miki ba. so yanzu da ka fadamin kasan ya zan dauke maganar kenan?"
No baby ba haka nake nufi ba please try to understand me. "It okay kawai tace,
akwai abubuwa dayawa da take son fada amma bata son ja maganar,bata son abunda zai
kara mata bacin rai.

"Wifey sorry ina son in dan fita ne,akwai inda nake son lekawa bazan dade ba.please
duk wanda yazo nema na kice bana gari kawai kinji.kai kawai ta kada Mishi dan
maganar ma bazata iya Mishi ba.

Sai da ta tabatar da fitan shi tukuna ta jawo wayar ta dake kan stool. Numbern ummi
ta danna wa kira ringing biyu aka daga,ko sallama ma bata Bari sunyi ba kawai ta
fashe mata da kuka."subhanallah Aisha mai yafaru lafiya? bata bata amsa ba sai ma
kukan ta da ta kara."kimin bayani mana mai yafaru? Wani ya mutu ne?nan ma shuru
tayi sai kuka. A dan zafefe tace ni zan kashe wayata tunda baza ki yi magana ba.
mai ya faru? dan sosai taji haushin manna mata da tayi. A hankali ta goge hawayen
ta kan ta fara magana kamar haka,"ummi Aliyu ya gaji da zama dani,ummi Aliyu zai
kara aure shi Kenan wata zata aura min miji waiyyo Allah nashiga uku.

"Ke da Allah kimin bayane ta yanda zan gane cewar ummi da gabadaya ta rude.
Ahankali ta fara bata labari tiryan tiryan daga Kiran da batool tama ta zuwan su
Hajjiya gidan har izuwa yanzu. Shuru Ummi tayi bayan jin labarin da ta gama bata,
gaskiya bata ji dadin abinda Aliyu yayi ba, bai kamata ya boyewa matarshi magana
irin wanan ba.to aikin gama ya gama kuskure dai anriga da anyi shi,baza ta so auren
yar ta ya samu tangarda ba a Dalilin haka, yanzu ba lokacin tada hankali bane.dan
haka tace,"ba abinda zan baki sai hakuri Aisha,dan Allah yana tare da masu
hakuri,"nan ta mata nasiha da da bata misale Kala Kala. Sosai ta nutsu tana
sauraran ta,sai taji gabadaya bacin ran ta ma ya kau. Sun dade a waya,kana daga
baya suka ye wa juna sallama. Sosai taji dadin kiran ummi da tayi,ta kuma ji dadin
nasiyoyen da tama ta,kuma insha'Allah zata yi anfani dasu,jin ta sakayo kamar wace
aka zare mata damuwar ta.
******
Biki ya gabato sai shirye shirye ake ta ko inna,yau saura kwana daya dauren aure.
kuma har yau aliyu bai je amsa kiran Hajjiya ba,dan yasan Dalilin Neman shi da
take,shima kuma baya tunanin zai iyah hakura da muradan shi da ya dau shakaru yana
dakon shi,sai yana gab da cika shi kawai ace za a raba shi da shi,inna bazai yu ba
ace duk wahalan da ya sha kafin azo wanan matakin,shiyasa ma yasa ta a black list
dan kar ta kara Kira dan bai san mai zai ce mata.ya kulle kowaci hanya da zata hada
shi da ita har ma da kanen shi.
Ya kuma hane Aisha sanar da kowa yana gari,sai ranar dauren aure bayan ya tabatar
an daura to shine zai iyah zuwa wajan Hajjiya by then kome ya wuce,yasan yanda zai
tsara ta yanda baza ta ga lefin shi ba.
******
bangarin amarya Husna ma sai dai muce mashallah dan sosai Baba Mariya ta kashe kudi
wurin jaran jiki,mai jaran jiki ta kira tun daga maiduguri tazo tana jara amarya
sosai amarya ta yi kyau har ta wani kara kiba fatar ta har wani shining take. Sosai
yan uwa da abokan arziki zun taru, kusan family gaba daya sun zo wanan biki dan
wanan shine karan farko da baba Mariya zata aurar da ya. Ummi ma tun shakaran jiya
take wurin su,da ita ake hidimdumu. Aisha dai bata samu zuwa ba,dan abun yazo mata
a hade,biki dai yazo rana daya Dan haka bata samu damar zuwa ba,tana can tana jara
ita ma. Dan haka ta Bari bayan aure sai taji taga gidan amarya,duk da bata zo ba
amma ta yi aike kuma ma suna waya da Husna. Mutane sai tambayar ta suke ganin tunda
aka fara tarun basu gan ta ba,nan ne fa kowa yasan za a aurau mata kishiya,nan fa
aka samu maganar yada wa,daga masu tausaya mata kuma da yi mata ad'ua kan Allah ya
yaba ta ciki Dalilin auren nan da mijin ta zai kara,da kuma zaman lafiya mai
dorewa,sai kuma wanda abun yayi musu dadi har da ye mata fatan saki. To haka
rayuwar take wani yaso ka wani kuma ya kika,wani yaso ka badan kome naka ba wani
kuma yaki ka dan wani batare da kamishi kome ba, wani kuma hassada ce qarara.

Ummi ce zaune a dakin Baba Mariya ,wanda gaba daya ya hartsike Dalilin kayan da
jakukunan mutane da suke dakin. Folding din kayan da ta cire dazu tare da sashi a
jakar ta,dan in tabar shi a waje haka zai,shiga cikin tarkacin kayan,Tana cikin
folding din ne inna Hasiya ta shigo dakin bakin ta dauke da sallama. Inna Hasiya
yayar ummi ce uwa daya uba daya. Baban su malami ne malamin Al Qur'ani.
Malam Hamza shine sunan sa,amma ana kiran shi da mai sittin .
Yana da mata biyu yara shida, Rabe ce babba yaran ta hudu, Bashir Hasiya Amina wato
ummi,sai kuma autar su Fatsime.
Sai kuma amarya Karime yaran ta biyu usman da Mariya. Sosai Malam Hamza yayi kokari
wurin samun hadin kai cikin gidan sa,kuma alhamdulilah sosai akwai fahimta tsakanin
su. Sam basa banbanci tsakanin yayan wace ko wace ba.zaman lafiya ake,sai dai kuma
kowa da irin halin sa cikin yayan.musaman ma Mariya da Allah yayi ta son abun
duniya tun ta sowar ta.
" Au ashe kina nan,ana ta neman ki tun dazu ashe ma kina daki.ehh Yaya, nan
nashigo,amma ince de lafiya? "Aa dama Jidda ce ke neman ki. "ai kam inna nan
daki."nikam Amina auren nan gaba daya bangane Mishi ba."kamar ya Yaya? "Eh
mana,tunda fa aka fara bikin nan,ba wanda ya ga angon ko Yan uwan ango,ko kayan
lefe da aka kawo ma,maza ne babu mace ko daya. Ba wanda yasan mijin ko yan uwan
shi,na tambaye Mariya Amma tace wai baya gari,to inshi baya gari yan uwanshi ma
basa garin ne? "To Yaya sai mu zuba ido mugani tunda gobe ne dauren aure ko.
******
Zaune suke a parlour suna hira, Aisha kuma suna can gefi ana rangada mata
lalle,Wanda ba karamin kyau yayi mata ba,ga kuma kitson da aka mata, mashallah
kamar ita ce amarya,dan duk da abun yazo mata a kuraren lokaci,ba ta zauna haka ba,
sosai tayi kokarin jara.dan ma ita tun fil asal mai jara ce, dan ko wani wata sai
taji wurin Mai jaran jiki.
"Uwar gida a gidan Aliyu,kin ganki kuwa hmm kamar kece amarya,ba uwar gida ba ko
amaryar ma sai haka. cewar Batool dake zaune kan kujera.

"Fada mata Dan Allah cewar hafsa,inna gaya mata ta dauka da wasa ne."ai ba batun
wasa anan maganar gaskiya ce ki kara kyau sosai,sai dai kin rame. Ki dena sawa
kanki damuwa ki kashi kanka a banza wallahi,hakan bazai hana shi zama da matar shi
ba."ai gashi ya fara nuna miki halinsu na maza ba.wani abun ma sai bayan aure.

"Ba kowani namiji ne,haka nima ai ina da kishiya and muna zaman lafiya,so maganar
cewa dan an miki kishiya,kiyi tunanin shi kainan ba a sonki ko ba a bukatar ki,kima
cere a ranki. In fa ba a sonka to baza a zauna dakai ba. Abunda nake so dake kawai
kici gaba da hakuri and ki koya kawaice,duk abunda zaki gani ko kiji to kiye kamar
baki gani ko kinji ba. And lastly ki rike girmanki daga haka suka cigaba da hirar
su.

******

Washegari ya kama ranan biki. Alhamdulillah Aisha tayi namijin k'ok'ari wajen ganin
ta cire dukkanin wani abu dake ranta. Mutane kowa sai sha'awa take bashi kaman ba
wacce za'ayi wa kishiya ba. Da yawa munsan matan nu na arewa idan miji zai k'ara
aure shikenan babu kwanciyar hankali. Y'ar kuwa ki kwantar da hankalin ki ki cigaba
da hak'uri da yi masa biya. Wata rana kece da riba. Kyau da Aisha tayi abun sai
MashaAllah. Lasheni a jikinta mai kya gaske da akayi simple d'inki daya sha stones.
D'an kwall shi kuwa an nada mata mashi kaman gwaggwaro. Sosai tayi kyau sai nan da
nan take da mutane fuskar ta cike da fara'a.

P.3

Bangaren su Husna kuwa biki yayi armashi, duk da cewa ta so ayi dinner Amma ango
yace baya so,ko sunyi ba zuwa zai ye ba. Sosai bata ji dadin hakan da yaye mata ba,
dan sosai taci buri kan auren,duk da haka ta bar wanan burin nata har in tasamu
ciki ta haihu, to kuwa sai an dinner ko ya ya ne. Haka dai badan taso ba, suka kira
DJ aka yi wasa,anci an ansha, yayinda aka shirya stab Dan kai amarya gidan mijin
ta. Bayan sallah maghriba aka zo da motocin daukar amarya, nan de aka shirya amarya
aka sa ta cikin mota haka ma sauran yan uwa,nan aka kama hanyar zuwa gidan amarya.
Maimakon aga anyi hanyar gidan amarya sai suka ga anyi hanyar gidan Aisha. basu
kawo komai ba,sai ma tunanin wata kila sai ankai amarya wajan uwar rukan ta kafin a
tafi da ita gidan ta, Wanda a nasu tunanin wanan wata karamawa ce da aka bata duba
da a wajan ta tagirma.

******

Aisha.
Aisha sosai tayi kokarin boye damuwar ta. Amma ita kadai tasan mai take ji a kasan
zuciyarta, barin baqin tayi a parlour tare da Shiga dakin. zama tayi kan gado tare
da yin tagumi, ganin tagumin bazai amfane ta da komai ba ne yasa ta tashiwa toilet
ta Shiga ta dauro alwala tare da gabatar da sallah sanan ta nemi istigifari tare da
karin addu'oi daga mutum ko aljan. Mike wa tsaye tayi ta nufi wurin madubin ta jara
fuskar ta da powder da lipstick kana ta nufi hanyar waje. koda ta fita samun su
tayi suna hira abunsu, Zama tayi kan daya daga cikin kujerun parlourn, nan aka
cigaba da hirar da ita.

Can suka fara jin hayaniyar motoci alamun dai amarya ta iso. Nan suka jara nutsuwar
su tare da jiran yan kawo amarya su shigo da amarya dan gaishe da uwar gida,wanda
al'ada ce wanan.

Sai da suka kwashi fiya da awanni biyu mutune suke jiran ganin kodai amarya zata zo
gaida uwar gida, kamar dai yanda al'adun mu na hausa yake. Shuru shuru suka ga
amaryar bata zo ba,hakan yasa mutune da kadan kadan suka fara watsewa har dai suka
watse gabadaya yayin da aka bar Aisha ita kadai a palour zaune tayi tagumin zaman
jiran Aliyu. Haka tacigaba da zaman yayin da shaidan yake saqa mata abubuwa Kala
Kala a ranta, nan dai ta fara karanto addu'oi domin Neman tsare daga shaidan. Nan
ta cigaba da zaman jira,a karshe dai tayi kwanan palour dan dai Aliyu bai zo ba.

******

Bangaren yan kawo amarya kuwa,suna zuwa aka wangale musu gate suka Shigo gidan.
Bayan motocin suyi parking kowa ya fara fitowa har dai suka fito gabadayan su,nan
aka kama amarya tare da nufan part din aisha da ita,amma sai Kulu kawar Baba Mariya
tace," sai ankai ta part din ta tukuna za a kawo ta wurin uwar gidan ta. Tofah nan
aka fara kallon kallon, mutane suka fara maganganu kasa kasa. Fatsime dake rike da
amarya ne ta juya tare da tambayar Kulu,"mai kike nufi da uwar gidan ta?

"Eh yanda kika ji sai mun fara kai ta part din ta tukuna. "Lallai biri yayi kama da
mutum, duk alkairin da Aisha ta muku,amma da abunda za 'a saka mata da shi!

"To sai mai, ai miji ba dan ita kadai a ka yi shi ba, mijin mata hudu ne dan haka
ko da Husna bata aure shi ba wata zata aure shi. Au haka ma zaki ce munafuka, nan
fa aka fara cacan baki tsakanin Fatsime da Kulu, wanda saura kadan su dambatu, da
kyar aka raba tsakanin su,"wallahi zaku gani ai badai auren cin amana ba,ba baki
nayi musu ba amma wanan auren ba inda zaije,"kana ta juwo Kan Husna da ke tsaye can
gefin mota,tun da aka fara wanan hartsumar ta ja gefi ta tsaya.ta bude baki zata yi
magana Amma sabon takaici ta kasa magana, kai ta kada kawai tare da cewa ba dake
zanyi ba, da babbar munafukar jatumar ki zanyi. daga haka ta kama hanyar fita dan
baza ta iya koda minti daya ne a wanan wurin dan a yan da ta ke jin zuciyarta ke
mata komai zai iya faruwa. Haka dai kowa ya dinga watsewa aka bar amarya da kawayen
baba Mariya. su suka sada amarya cikin part din ta bayan sun dan mata na siyoyi
kana suma suka kama hanyar zuwa gidan bikin.

Husna tana ganin baqin sun koma, ta cire mayafin da take lulube da shi kana ta fara
kale kale yayin da zuciyarta zar babu wani tashin hankali tatare da ita domin burin
ta ya cika, tana mai jin wani irin farinci, mike wa tayi tare da fita parlour tana
mai kale kale yayin da take daukan alwashi kala Kala a ran ta. Koma wa daki tayi
tare da zama kan gadon. Shuru shuru bata ga ango ba bata ga Dalilin sa, tun tana
duba lokaci har ta tashe ta fita parlour,can dai wani abu ya fadan ma ta a rai. to
kodai ya na can wurin Aisha ne, ta hana shi zuwa wurin ta,nan taji wani irin
zazafin kishi ya tasau mata, nan ta shiga daki tare da daukan mayafin ta,ta nufi
hanyar waje, dan wallahi baza ta sabuba za taje taji Dalilin rike mata miji da tayi
bayan kwanan tane. Gabadaya kishi ya rufe mata ido bata san mai take kokarin aikata
wa.

~~~~~~~

Shi kuwa Aliyu yana can wurin Hajjiya yana baran bata ha'kuri, dan dai ta kafe sai
ya saki Husna baza ta kwana da auren shi akan ta ba. Sai ha'kuri yake ta bata amma
inna Hajjiya fa ta kafe ta tsare sai ya saki yar mutane, ita ba ruwan ta ko mata
nawa zai aura baza ta hana shi ba amma banda dagin juya. Ganin baza ta saurare
shine yasa ya fita tare da nufan gidan kawu Bala tare da zaiyane mishi komai, sosai
abune ya ba shi mamaki,"Aliyu ashe baka da hankali bansani ba,dama yarenyar da kasa
muka je karbar maka auren ta kanwar matar ka ce. Shuru yayi dan baisan mai zai ce
ba. Sosai yayi mishi fada karshe dai ya ce su wuce gidan Hajjiyar.

Koda suka isa gidan shi yafara shiga cikin parlourn,tana ganin shi tace "inna ta
kardar sakin bani ita in gani ta fada hakane tare da Mika mishi haunun ta. Zama
yayi a kusa da ita tare da sunne. Ba dakai nake magana ba?"

"Haba hajara da kanki?

"Shuru tayi ba tare da ta furta komai ba, wato Aliyu ya kai karar ta wajan shi, ita
zai yiwa haka akan kawai tace ya saki yar matsiyata.

Kawu Bala ne ya fara mata fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, kana daga
bisani ya yayi musu nasiha gabadayan su. Kayi ha'kuri hakan bazai sake faruwa ba
inji Hajjiya, ta fada ne amma ita kadai ta san matakin da taza dauka akan Aliyu da
matan nasa gabadaya.

Nan dai kawu yace wa Aliyu ya tashe ya koma gidan shi dare yayi. Tashewa yayi tare
da yiwa musu sallama kana ya kama hanyar fita,farin ciki fal ransa. Sabon farin
cikin da yake ciki har ya manta da kazar amarci bai siyo ba haka nan ya zo gida ba
tare da ko mai ba.

Koda ya isa gida kusan karfe 12:10 dan haka bai shigo wurin Aisha ba dan yasan tayi
bacci. Hakan ne yasa straight part din amarya ya wuce.

Koda ya isa bude kofar falo yayi tare yin sallama,babu kowa a falo dan haka ya nufe
bedroom. Ko kafin ya bude kofar yagan ta ta fito,da mayafin a hannu. Ita ba ta ma
lura da shi ba dan gabadaya hankalin ta yana part din aisha.

"Husy baby!

A dan razane ta juya tare da mai fuskan tar sa. "Baby yaushe kazo tun dazu nake ta
jiran ka amma shuru baka zo ba, ta fadan haka tare da yin fuskar tausaye."eyah
sorry baby I keep you waiting. Daga haka ya jawo ta zuwa jikin shi tare da mana
mata k!ss a goshin ta. Kama haunun ta yayi tare da shiga bedroom din da yaga ta
fito daga.

Suna shiga ya ce mata ki shiga ki dauro alwala. Toh kawi ta ce kana ta nufi bayen,
bayan ta fita ne shima ya shigo ya dauro nasa. Darduma ya shimfida musu kana suka
kabbara sallah. bayan sun idar ne ya kama kanta tare da yin addu'oi kana daga bisa
ne ya fara mata tambayoye ga me da addini, kuma mashallah dan tana bashi amsa dai
dai.

Bayan sun kammala sunyi shirin bacci ne ya tuna da ashe fa bai siyo kazar amarci
ba. Gabadaya ya sha'afa. fita yayi palour tare da nufan kitchen fridge ya bude tare
dau musu yogurt da cake, dan tun ana saura kwana biyu biki yasa aka cika fridge din
Aisha da wanan. Trey ya nema ya daura ake kana ya nufi daki.

"Sorry baby! Sabon inna saurin zuwa wurin ki, na manta ban siyo kazar amarci ba. Ya
fadi hakane tare da neman wuri ya zauna. Bakin ciki kamar ya kashe ta, ya zauna a
waje bai shigo da wuri ba, and know yana wani ce mata ya manta da kazar amarci.
Ganin bata motsa daga inda take ne yasa shi cewa,"ki sauko mana.

A hankali ta sauka ta fara ci. Haka dai suka ci abin su kana suka yi shirin bacci.

To amaryar da ango aci amarci lafiya

Asuba ta gari

_______

Washegari da asuba Aliyu ya tashe tare da nufan toilet wanka yaye kana ya dauro
alwala ya fita, sai da ya tashe Husna kana ya nufi masalaci.

Ita ma tashe tayi ta nufi toilet.

AISHA.

A hankali take bude idanuwa ta har ta bude su gabadaya, tunanin ta fada mai take yi
anan? A hankali abunda ya faru jiya ya dinga zuwan mata a brain. Kenan Aliyu bai
shigo mata ba, ranta ne taji ya baci,wato har yayi amarya ya mata da ita. Ganin
tunani ba zai fishe ta ba,yasa ta tashewa ta haura Sama dan yin sallah.

_____

Aliyu koda ya dawo dakin shi ke part din Husna ya shiga tare da sauya kaya daga
jallabiya zuwa kana nan kaya,tare da fesa turaruka kana ya nufi dakin Husna.

Koda ya yaji samun ta yayi kwance kan gado. Bayan tayi wanka tayi sallah ne ta sa
kaya tare da koma wa kan gado. Zama yayi kusa da ita,tare da tambayar ya karfin
jikin ta. A kunyace ta amsa Mishi da lafiya kana ta suma gaishe shi. Amsa wa yayi
kana daga bisani yace,"tashe muji wurin auntyn ki ku gaisa. Duumm taji kirjin ta ya
buga jin ya ambaci auntyn ki da yayi." Aa ni bazan ji ba, gaskiya inna tsoran bata
fa san ni ka aura ba no, I can't."Murmushi Aliyu yayi,yace karki ce haka nothing
will happen,tashe mutafi. Haka dai ba dan taso ba ta tashe tare da saka babban
hijabi wanda yakai mata har kasa. Fita suka yi daga part dinsu kana suka kama
hanyar part din Aisha.

Koda suka isa falon basu ga kowa ba, Amma ko inna kal kal sai kamshin turaren wuta
dake tashe a falon.

"Tsaya a nan bari naji na kira ta."ok kawi tace tare da zama kan kujera, sosai
zuciyarta ke buguwa kamar taza fita daga gurin ta,ga jikin ta da ya fara karkar
wa,kamar kace kass ta arce da gudu.

Aliyu kuwa sama ya hau dan kiran Aisha amma bai ganta ba dan haka ya sauka kasa
tare nufan kitchen,a kitchen ya same ta.

Bayan ta yi sallah tayi wanka ne ta fito ta jara ko inna tare da saka turaren
wuta,kana ta wuce kitchen dan hado breakfast. Sosai ta mai da hankalin ta kan
abunda ta keyi har ma bata san sanda ya shigo cikin kitchen din ba. Ji tayi anyi
hugging dinta ta baya, sosai ta tsorata dan ba ta kawo zai shigo mata nan kusa ba."
Good morning king.

Morning matsoraciya." Ni ba matsoraciya bace, kawai dai you scared me."hmm haka dai
kika ce. is breakfast not ready yet? Am so so hungry wallahi." Eh is not ready amma
ya kusa zaka iya tafiya wurin amarya in nagama zan kawo maka. "Aa ni dai a nan zan
zauna kina aiki inna kallon ki,inna jin dadi. Shuru tayi,bata kara ce masa komai
ba.

"Zo kugaisa da amarya na kami ita ku gaisa. Ok tace daga haka ta kashe gas suka
fita parlour.

Koda suka fita straight wurin kujerar ta nufa,bata ko kalli inda amaryar take ba.
Yayin da su biyun,ko wanin su gaban shi na ta buguwa. Baki na rawa Aliyu yace Aisha
wanan itace amarya ki, kuma dan Allah bana son tashin hankali ku zauna lafiya, nan
dai ya fara musu nasiha. Nasihar da yake musu ne yasa Aisha kallon wajan amaryar
tare da cewa "to amarya ya kike boye fuskar ki ne,ki bude naga fuskar,ni sai nake
ganin kina min kama da wata. "Aliyu ne ya ce Husna ki bude fuskar ki ta ganki. A
hankali Husna ta kunce facemask din hijabin ta tare da daga kan ta sama.

Rass gaban Aisha ya buga yayinda ta mike zunbur tare da nuna Husna da yatsa, baki
na rawa ta furta hu..hus.. Husna...

"Aliyu mai nake gani?"

P.4

Numfashi take ja Ahankali tare fidda shi, a nutse take yin hakan tana son iskar ta
isa har inda ya kamata. Kafin ta iya kallon Aliyu muryarta na dukan dodon kunenta
ta furta, "Husnah?"

"Husna ka aura?"
Kasa magana yayi tunda ji yayi zufa na tsastsafo
masa ta ko wace kafa da yake ji, ga wani kwarjini da ya ga ta ma shi, sosai
zuciyarsana bugawa, bai taba tsammanin zai taɓa Shiga irin wanan yanayin ba a
rayuwar sa.Amma yau ga shi a ciki dumu-dumu. Kusan sau uku yake k'o'karin buɗe
bakinshi dan yin magana amma ya kasa.

Sautin muryarta da yaji ya sa shi dawowa haiyacinsa. tana mai ce wa "Kai ma sha
Allah na tayaku murna Allah ya bada zaman lafiya." Daga haka ta wuce ɗakin,ta bar
so tsaye a nan wajan, ko waneninsu da abunda yake sak'awa a ranshi.

Ita ko tana shiga d'aki ta banko kofar tare da sa mata key, jingina bayan ta tayi
da kofar. Sosai take jan numfashin, tana jin kamar yana barazanar d'auke wa, kamar
mai ciwon asthma.

Ba abunda idonta yake nuna mata sai sai hoton Aliyu da Husna a tare. Ashe kuka ma
rahama ne,So Kawai tayi kukan ko zata ji saukin abunda take ji a ranta, amma kukan
yaki zuwa sai ma wani kololon abun da ya tsaya mata kan maƙoshi da ta kasa had'ewa.
nan da nan wani zazzaɓi ya rufe ta a nan kasan ties ta kwanta tare da kankame jiki
ta.

Ba abunda take anbatawa sai adu'a da tazo bakinta.

Gani take kamar a mafarki, gani take kamar zai zo yace mata wasa yake ba gaskiya ba
ne. ashe dama alkaire ya kan zama sharri, mai ta musu da zasu saka mata da irin
wanan cin amana.
Ya kusa minti 10 a tsaye ba tare da yayi k'ok'okarin matsawa ba, so yake yabi ta,
amma ya kasa hakan, to yabi ta yace mata me. Bai san mai yasa ba sai yaji bai yadda
da farin cikin da ta nuna musu ba. Ya kamata ace ta nuna bacin ran ta ko da yaya
ne, Amma ba ta nuna komai ba,ko alamar kishi bai gani a k'wayar ido ta ba. Tunanin
bata kishinsa ne yasa ransa baci. Wato bata kishinsa shi ya sa ta nuna ko in kulla
tun sanda ya ce mata zai kara aure. Sosai yaji tukukin bakin ciki na taso masa.
Hakan ne yasa ya fita daga parlourn ma gaba ki da, bai ko kali yinda Husna take ba
ya fita abunshi.

Ganin kowa ya tafi ya bar ta ita kaɗai ne yasa ita ma barin parlourn tare da wuce
wa part din ta, ran ta babu daɗi. Sai kuma sake-saken da take a ranta, sosai ita ma
tayi mamakin abunda Aisha tayi,ta dauka da zarar ta gane gaskiyan lamari,taza tada
harzuma da tashin hankali,wanda silar hakan zai sa, zasu dinga samun matsala da
Aliyu. Amma sai taga sabanin haka. Da wanan sake-saken a ran ta ne har ta isa part
din da a yanzu ya;zama na ta.

Zama tayi a parlourn tare da cire hijabin ta, ganin har karfe 9 ta gota bata ga
Aliyun ba ga wata masifafiyar yunwar da take ji ne, yasa ta tashewa tare da shiga
kitchen. Bude_bude ta fara yi,dan ta rasa mai ma zata ci. can dai ta dauki cup tare
da hada tea mai kauri ta suma sha, a nan kitchen din. tana cikin sha ne taji
shigowar sa,dan haka ta aji cup din tare fita parlour. Tsaye ta same shi da ledodin
a hanun shi. Mike mata biyu daga cikin su yayi tare da cewa

"Ga wanan, abinci naje siya na san kina jin yunwa, ki zuba mana a plate muci,inna
zuwa bari inkai wa Aisha nata daga haka ya fita.

Koda ya shiga part din Aisha straight hanyar dakin ta ya nufa dan yasan tana can,
tunda baiji motsin ta a kitchen ba. Yana isa ya fara knocking din kofar bed room
ɗin, Amma shuru baiga ta bude ba, hakane yasa yayi tunanin ko tana bayi ne dan haka
ya koma parlourn tare da zaman jiranta, duk da zafin ta da yake ji.

Tana nan kwance a kasan ties din, ta ma kasa tashi wa daga wurin dan sosai take jin
zazzaɓin ya Karo.

Ringing din wayarta da taji ne yasa ta tashewa a hankali tare duba wa ke kiran ta.
Best Mom ta ga kan screen din wayar dan haka bata bata lokaci wurin daga wayar ba
tare da dauro a kunen ta. Shuru tayi alamun ana magna ta dayan bangaren, sosai ta
nutsu tana sauraran abinda ake fada mata ta dayan bangaren. Haka suka kusan minti
30 akan wayar, kana daga bisani ta sauke wayar. Shuru tayi na dan wani lokacin,
tuninan abunda aka fada mata ni na yawo a brain din ta.

Ganin zama bazai anfane ta ba ne yasa ta tashe wa daga nan k'asa kana ta nufi
toilet, wanka tayi da zinman ko zata dan ji saukin jikin ta. Tana cikin sa kaya ne
taji ana knocking.

Sanin ko wayi ne,ya sa ta kin buɗe kofar. Dan bata son ko jin muryar shi balle har
ma tayi ido hudu da shi. Ganin shi kamar kara fama mata ciwon da take kokarin binne
wa ni.

zama tayi kan gado tare da,kura wa bangon dakin ido. Ita kan da zaka tambaye ta mai
takai tunanin a wanan lokacin, ba sani tayi ba.

Jin Kukan da cikin ta ke yi ne,yasa ta tuna wa ashe fa ko breakfast bataye ba.


Hakan ne yasa ta tashewa tare da fita parlour. Ko kadan bata kawo zata ganshi a nan
parlourn ba.

Ta dauka in yayi ya gaji zai koma ne.


Amma sai ta ganshi a zaune kan kan kujera tare da kallon lABARE cikin talavition.
Kamar ta koma cikin daki, saidai kashh ya riga da ya ganta hakan ne yasa ta sakin
fuskar ta tare da nufan wurin shi,kamar ba abunda ya faru. Tashewa yayi tare da
nufan wurin ta, "tun dazu nake ta zaman jiran ki baki fito ba. "Sorry na shiga
wanka ne." Hmm shi Kenan dama abinci nasaiya shine na kami ki naki."ai kuwa kamar
kasani yunwa nake ji. Daga haka ta dauke ledan.

Hugging din ta yayi tare da cewa" I love you much wifey, Allah ya bani ikon yin
adalci a tsakin ku.

Ji tayi kamar wuta aka watsa mata a jiki sakamokon hada jikin su da yayi wuri daya.
A hankali ta janye jikin ta daga gareshi, kana ta ce "amin.

Shima jinye wa yayi tare da cewa "ya naji jikin ki da dan zafi baki san lafiya ne?"
Eh inna dan jin zazzabi ne amma yanzu lafiya ta klau.

"Shine ba zaki fada min ba, kin sha magani ne ko muji asibiti?"

"Aa no ba sai munji ba na samu sauki fah. "kin tabbata kin ji sauki?

"Ehh na tabbata naji sauki.

To shi kenan tunda haka kika kace, bari in wuce na bar kanwar ki ita kadai kar tace
na dade." daga haka ya kama haryar fita.

Zama tayi tare da bude ledodin kana ta fara cusa abincin, ba dan yana mata dadi ba.

P.5

Koda ya koma samu yayi ta gama jera abinci kan dinning tana mai jiran shi.

Tana ganin shi ta tashi tare da tambayar shi. "Ya ka daɗe ne?"

"Sorry amarya, tana wanka ne da na shiga, so na tsaya ta fita tukuna."

KKallon shi tayi na dan wani lokaci kana daga bisani ta ce. "Ok muje kaci abinci
ko, dan nasan baka ci komai ba."

"kamar kins ani wallahi yunwa nake ji kamar inci babu. Kama haunun shi tayi kana
suka nufi dinning. shi ta fara yi wa sarving tukuna tayi wa kan ta. A hankali suka
suma cin abinci suna hira, cikin hirar ce Husna ta tambaye shi, "Baby ya maganar
karatu na?"

"Karki damu zaki cigaba ai ni na miki alkawari so rest assure zaki fara nan ba da
dadewa ba."

"Wow Baby shi ya sa nake kara son ka, daga haka ta tashe tayi hugging din shi, "ko
kasan bani da buri da ya wuce in gan ni a jami'a , ga shi kuma buri na zai cika nan
kusa."
"Zaki yi karatun amma ba lallai bane in barki kiyi aiki ba, dan ne mata ta bata
aiki. "Haba baby taya mutum zai sha wahalar yin karatu, amma babzai yi aiki
ba,wanan ai aikin banza ne. "Tun da kike kin taba ganin Aisha ta taɓa zuwa wani
wuri da sunan aiki taje? Bata taɓa zuwa ba?" ba wai bata yi karatun ba, ni ne nan
na hana ta. Dan haka ke ma ba zaki yi aikin ba."
"To ta ce mishi, badan ta yar da ba, dan kar ya hana karatun ma gabab ɗaya, Amma
in lokaci yayi dole ne ma ya bari

=========
"Amma Mariya kin bani mamaki,yanzu da ke za ayi haka. Ciwar INNA Hasiya.

"Yanzu ke baki ji kunyar abun da kika yi, yau da ace koda Aisha ba yar yayar ki ba,
abare Kan cewa kawar yar ki ce, in dai kin san ya kamata ai baza a ayi wanan cin
amanar dake ba. "Amma ace yar yayar ki kuma ita ke taimakon ki da yaran ki amma da
abunda zaku saka mata.

"Wai yaya ni mai lefina a nan ne, yaron nan shi yazo da kansa, akan cewa yana son
Husna, yana kuma son auran ta,ba nina ce yazo ba yara dai sun amin ta da juna kuma
sona son auren nan, shi yasa aka d'aura musu. Kuma kina wani cewa ita take taimakon
mu, ni na ce ta temaka mana ko ni nace ta dauki Husna din? Kuma ma ai matar mutum
kabarin shi. Haka kawai kuke son nayi wa Allah shishige, na san mai ya boye ne
cikin auran. Kuma ma mai banbancin da yanzu, tunda da ma gida daya suke yanzu ma
hakan ce, sai su hakura su raba mijin, mai aciki. Tunda koba Husna, indai yayi
niyyar aure zai yi."

"Au haka ma zaki ce butulu.

Inji Fatsime wace take ji kamar ta cakumi wuyar Baaba Mariya.

"Ke Fatsime, ki kiyaye ni Wallahi, dan ni ba sa'arki yin ki bace,sai dai naye da na
gaba dake. Dan haka ki kiyaye ni

"Eh dole kice haka ai munafuka, mai fuska biyu,to bara ki ji, wanan auren ba inda
zai yi, Muna nan zaki gani."

"Ba kin ki ya sare gun tun Kashi. Kar ya kike wallahi,karya kice auran 'yata zai
mutu, sai dai in auren yar ku ne zai mutu. Nan gani nana bari ehe."

Duk wanan abun nan da suke ummi na can gefi tana kallon su.

"Shi kenan bana son tashin hankali, haba sai ka ce yara,kun wani zaqe kuna cacan
baki, a gaban yaran ku." Ciwar INNA rabe mahaifiyar su ummi, wace ita ma tazo
bikin, wanda yanzu ba da dadewa ne,aka fada mata abunda ya faru. Saida aka bar kowa
ya watse tukuna. to shine makasudin zaman nan da aka yi. "Wanan ai rashin hankali
ne ehh, mai kuke son koyawa yaran ku?"

Aure dai an riga da an daura, kuma Allah ya kaddra miji daya zasu aura,to mai na
tada harzuma? Maza-maza ko wacen ku ta tattara inna ta inna ta, ta kama hanyar
gidan ta." Amma inne kina fa...

"Bana son surutu ku wuce gida."

dyaga haka ta juya wurin ummi da tun dazu da suka fara rigimar, tana can zaune
bakin kofar kitchen, ta ma kasa magana dan gabadaya hankalin ta na can wurin tilon
yar ta. Bata san halin da take ciki ba, gashi ta kasa kiran ta. A hankali take
tafiya tare da sake-sake ranta, har ta isa daki ta fara hada kayan ta dan wuce wa
gidanta. Tana jin yanda su Fatsime da inna Hasiya Sai magaganu suke ta yaba wa
Mariya, wanda ita ma ba a bar ta a baya ba,wurin maida musu da martani.

Haka dai suka haɗa kayansu ba dan sun so ba,dan dai kawai innie ce ta umarce ta su,
da ba dan haka ba, to kuwa yau Baba Mariya, sai dai uwar ta haife wata. Dan kuwa
sai sun mata shigen dukan da sai an sada ta da asibiti, in yaso a kama su. Tun da
sun huce takicin da bakin cikin da da ta qunsa musu.

Haka dai suka bar gidan tare da cijen ya tsaya.

Ita ko ummi koda ta zo fita, sai da ta tsaya gaban baba Mariya tare da cewa,
"Mariya mu zamu wuce Allah ya ba da sa'a ya kuma ba yaran mu zaman lafiya a gidan
mijin su, tare da hada kawunan su. Daga haka tayi wuce war ta. Ta bar baba Mariya
da kallon bayan ta. Tare da furta munafur cin banza da wofi, ni zaki ye wa bariki
to tar nake ganin ki wallahi.

"Kuma da bani da niyyar taba Aisha, amma yanzu tunda abun haka yake,to kuwa sai
nayi yan da zanyi naga ta fita daga gidan. Ma ga ta tsayan ai, ai da wani cewa ita
ke taimakon mu, inta fita ma ga wazai taimike wani a cikin mu ai.

******

zaune suke a kan dinning tare da mai jiran fitar war Aisha, dan cin abin cin dare.
Amma tun dazu suka shigo part din ta basu gan ta ba, Amma ga kulolin abinci a kan
dinning din, alamun anyi girki. Rabuwar su da ita tun dazu da rana da ya tara su a
babban falon shi. Kan maganar raba kwana da zai musu sai kuma, kan batun girki.
Yanzu da Aisha ce zata nayin girkin har izuwa sati dayan da zai yi a wurin amarya.
Sai kuma daga nan ko wace zata na girkin ta indai ranan kwanan ta ne. Wanda kuma
tare zasu ci abincin, gabbaki ɗayan su zasu haɗu a babban falon kasa suci.

Ganin sun kusa minti 30 a wurin bata fito bane yasa shi, hada rai tare da tashewa
daga kan kujerar da nufin ya je yaji Dalilin ta na k'in sauka. Sai ga ta ita ma
tana sauka daga stairs din. Sanyi take da wani swez less baki mai ratsin gold wanda
yasha dinkin bubu. Sosai yayi mata kyau ba kadan ba. Sai dan kwalliyan da ta dan yi
a fuskar ta duk da ba mai dan yawa bane. A hankali take ta ko wa kamar wace take
tausayen kasa, tun kafin ma ta isa wurin su kamshin turaren ta ya riga ta isa
wurin. Tsaya wa yayi wurin kallon kyawun da ta masa, shi kanshi yasan Aishar shi
mai kyau ce. A hankali ta taka har ta isa wurin, tare da zama kan daya daga cikin
kujeun dinning din. "Sorry! na ba ta muku lokaci daga haka ta fara zuba wa kan ta
abinci, ba tare da kara kallon inda suke ba.

Ganin ba ta zuba musu bane, yasa shi cewa"madam ya haka?" Ya naga baki zuba mana
namu ba.

"Kallon shi tayi na dan wani lokaci kana tace, sorry bazan iya bane jiki na ciwo.
"Sai ta juya kan Husna tare cewa" amarya sai a zuba wa ango ko. Daga haka ta
sunkiya ta fara cin abincin ta hankali kwance. Ganin haka ne yasa Husna fara zuba
musu, kana su ma suka suma ci. Ba mai magana sai karar cokula da kake ji. Aisha ce
ta fara gama wa dan haka ta wuce falo tare zama abun ta. Bayan sun kammala ne, su
ma suka zo falon tare da kafa hira, wanda duk hirar su Aisha ba ta saka musu baki.
Ganin ta fara jin bacci ne yasa ta tashewa tare da yi musu sai da safe, kana ta
wuce dakin ta.

Su ma sai kusan 10:49 suka wuce part din su.

_____

Washegari ya Kama Monday, Wanda a yau Aliyu zai fara zuwa aiki. Tun wuri ya shirya,
yayi breakfast kana ya wuce aiki.

Husna ce zaune a bakin gado tare da waya a kunen ta. "Aa bata ce min komai ba.
Shuru tayi, alamun tana sauraran mai ake cewa ta dayan bangaren. "Amma baki ganin
yayi wuri yanzu. Da dai mun Dan bari, yanzu dai inna son in fara zuwa makaran ta
tukuna, in yaso komai ya biyo daga baya. "Aa ba abunda na samu ni gaskiya, kuma
baba baki ganin zai gane daga aure sai in fara Mishi sata, "ke dan Allah waya ce
miki sata ne. Ba sata bane kayan mijin ki ne, dan haka zuwa jibi su Kausar zasu zo
wurin ki, sai ki hada duk abunda kika samu ki basu su kawo. Ke ce matsoraciya inna
ma zai gane, ba zai gane ba dan haka duk wani abu da kika ga zai kawo kudi ta ki
dauka ki tura mana nan, zan kai wurin Delu dallaliya. "To baba zan kokarta, duk da
bansan a inna yake aje kudadensa, Amma zan bincike dakin sa, da baza a rasa to.
Yauwa yar albarka yanzu naji Batu.
*****

Kitchen ta shiga dan kawo wa bakin ta ruwan sha da lemon. Kan Babar trey ta hada
musu kana ta kawo mu su falo. Batool ce da yaran ta huɗu suka kama ta ziyara. "Kai
ke kam baki gajiya da hidima yanzu mu baqi ne da zaki wani hada mana wanan lodin
kayan. "Batool kai nan kuba baqi bane amma yana da kyau karama baqon ka ko. Ehh
uwar magana naji bani ruwa in sha karki ishe ne da surutu. Mika mata ruwan
tayi,tare da zama kan kujera. Daura Arafat tayi kan cinyar tare da yi mata wasa.
Sai dariya yaren ke yi. Batool ce tace "Alisha! Mai nake ji ni haka?"

Jiya muke waya da mama, shine take fada min abunda ke faru wa. Ni Wallahi ban sani
ba, kuma ma Habib bai gaya min ba. Shine nace zan zo ingane wa ido na, dan kinsan
ance gane ya kore ji. In ta kama ma nama shegiya duka. Kinga abunda na sha fada
miki ko, Amma kika maida ni mahuakaciya. Ni fa tunda naga yarenyar Ku nan nasan ba
ta arziki bace. Da wanan idanun ta kamar na mujiya. "Kai batool kiyi magana a
hankali kar taji ki. "To taji ne mana, tsoran ta nake ji,inna ma take ne inna son
ganin yar marasa kunya. Daga an temaike ki,an cire ki daga wahalar rayuwa an baki
rayuwa mai kyau mai inganci, ansa ki a makaran ta, idon ki ya bude dan ke yar iska
ce sai kizo ki aure mijin wace ta miki duk wanan abun. Ke ma maganin ki, ba yanda
ban yi dake ba akan zaman ta a tare da ku ba amma wai ke yar uwar ki ce to gashi
sun miki mai gaba daya. Shima da yake munafiki ne, bai gaya miki ita zaiyi aure ba
zai ana jibi biki kuma ya kasa sanar dake ita zai aura."

Ni Wallahi sai gaba ɗaya naji na sare da namarin mazan nan. Haka jiya na fada wa
Habib ai, ga abokin shi ya tsula tsiya, saura kuma nashi tun da komai bakin su
datya. "Ke kam baki gajiya da magana?"
"Bana gajiya da magana baki na halaliya na. "To ya zaman naku yake?"

"Yanzu de muna zaman lafiya tunda kowa yana harkan gaban shi. "Kai Allah ka bani
hakuri irin na wanan baiwar taka. Allah Aisha kina da hakuri cab da nine aka ma
wanan abun ba, hmmmm za'a kuwa ga bala'i dan koni ko ita. "Batool kenan bazaki gane
ba. Daga haka suka shiga wata sabuwar hira. Karshe dai anan batool da yaran ta suka
wuni. Sai can yanma tukana suka wuce da yaran ta. Duk da ta so ta shiga part din
Husna, Amma Aisha firr taki mata dan tasan halin batool. Ba a taba ta ma mai, balle
an taba ta. Sai da taga wucewar su tukuna ta koma cikin gida.

Mafari... Asalin labari...

P.6

_TUSHEN LABARI..._

Aliyu abubakar matawale ɗa namiji ɗaya tilo a wurin Abubakar matawalle wanda
haifaffen garin borno ne a nan anguwar Gongee dake nan birinin shehu. Alhaji
Abubakar kafin rasuwar sa ya kasan ce mutum mai karamci da tattaku tare da taimakon
na ƙasa da shi Wanda sosai mutane ke alfahari dashi.

Matar sa ɗaya hajara wacce ta kasance haifaffiyar garin Zanfara ce dake babbar
birnin Jahar Gusau. Wanda suka haɗu da ita a wajen bikin wani abokin sa da shima
ɗan garin Zanfarane. Shi Kenan soyayyar su ta ƙullu har ta kai su ga aure.
Abubakar matawalle ɗan kasuwa ne ya kasan ce baya da cikekken sana'a, dan duk abun
da yasan zai kawo Mishi Naira to yinshi yake. Kuma alhamdulilah Allah ya dafa mai
dan duk abunda ya taɓa sai kaga Allah ya sa Mishi albarka a Kai. wanda hakan ne
yasa abokan sana'ar tashi suka fara Mishi hassada haka nan suka sa shi a gaba,
wanda har haka yasa shi kasa zaman Maiduguri Can Kano ya koma da iyalin sa da zama.
Abubakar da hajara sun kasan ce suna zaman lafiya da ƙaunar junansu haka har
Allah ya ba hajara ciki. Ta haifi ƴar ta ƴa mace wanda sosai Abubakar ya kasa ɓoye
farin cikin sa, ranar suna yarinya ta ci sunan mahaifiyar sa wato Fatima Zarah.
Wanda sosai mutume suka taru a bikin sunahbkowa sai son barka. Haka dai suka cigaba
da rayuwa arziki sai bunƙasa yake.
Hajara bata ƙara haihuwa ba saida ta kai shakara 5 tukunna Allah ya ƙara bata wani
cikin. Wanda tun kafin sunah yarinyar ta rasu ta ƙara haihuwa wanan karan kuma, ɗa
namiji ta haifa wanda aka sama sa Aliyu wandan yana kama da mahaifin shi sak. Sai
dai ya ɗau duhun fatar mahaifiyar shi wato chocolate color, daga Aliyu kuma sai
balkisu sai kuma autar su hamida. Abubakar da hajara sun tsaya tsayin daka wurin
tarbiyar yaran su da ganin sun inganta rayuwar su. Duka ya sanya ƴaƴan sa a
makarantar kuɗi suje makarantar boko da safe su zo ƙarfe biyu, kana su kuma tafi
Islamiyya da yanma. Shi yake kaisu da motar sa in yana nan, in kuma baya nan motar
haya suke hawa domin yana barin isheshshen kuɗi wurin hajara.

Bayan shakara 27 shakaru sun ja abubuwa da dama sun shuɗe ciki har da rasuwar
alhaji abubakar matawalle. Sanadiyyar hatsarin mota da suka yi kan hanyar shi ta
zuwa maiduguri. Wanda cikin su mutum biyu ne kaɗai suka rayu, amma sauran duka sun
rasu ciki kuwa har da alhaji Abubakar. Loƙacin Aliyu yana da shakaru 25 a duniya ya
gama secondary ɗin sa har ya samu gurbin Shiga B.U.K.

Zarah kuwa tuni tayi aure a Katsina har ta haihu. Balkisu ma tayi auren amma sun
rabu da mijin, sai kuma hamida da sai yanzu zata yi candy.

Mutuwar sa ta girgiza iyalen sa gabaki ɗaya jigon gidan ya koma hannun hajara,
wacce suke kira da hajjiya. Allah yayi Alhaji Abubakar ya bar kadarori da dama ciki
har da gidan da suke ciki. Da motoci da filaye, aka saida wasu domin inganta
rayuwar iyalen sa da shi. Aka cigaba da biya musu kuɗin makaranta har suka kammala.
Zuwa lokacin da Aliyu ya cika shakara 28 duniya ya zama saurayi son kowa ƙin Wanda
ya rasa.

Aliyu kyakkyawa ne wanda ƴan mata sai crushing suke akan sa. Sai dai shuru shuru ne
baya son hayaniya wanda wasu kan ce miskile ne, Amma Sam ba haka bane yana surutu
sosai sai dai ba da kowa bane yake hakan.

Aliyu bayan ya gama makarantar sa ya samu aiki a can Abuja, wani company ya ɗauke
shi aikinbcompany'n electronic ne suna saida ko wanne irin nau'in kayan wuta.
fridge blender iron da dai sauran su.

Ita dai Aisha haifefiyar garin Kano ce anguwar dutsen dala. Aisha ƴa ɗaya tilo a
wurin iyayen ta.yarinya ce mai sanyin hali da hankali. Tashin ta ita kaɗai wurin
iyayen ta cikin gata bai sa ta zama sangartacciya ba. Sai sanyin halin ta uwa uba
kuma tana da haƙuri da kawaici.

Aisha tana da kyau sosai sai kuma dirin jiki da Allah ya mata wanda zamu iya cewa
gadan sa tayi a wurin maman ta. Aisha sam bata da ɗabi'ar yawo gidajen ƙawaye Sai
dai daga gida sai makaran ta. Ƙawar ta ɗaya batool. Wacce suka yi karatu tare tun
suna secondary har suka shiga university a tare. Da farko ba ƙawaye bane sai daga
baya suka zama good friends. Shima saboda akwai wani Rana da Aisha ta taimaki
batool cikin exam hall. Wanda hakan yaja ma ta duka wurin malamin su. To tun daga
ranar batool ta fara shige mata tun bata kula ta har suka zo suka zama best
friends.

Haka har bikin batool ya tashi wanda batool ta kafe ta tsare wai Aisha sai ta zo
gidan su da zama tun ana saura kwana biyar biki. Wanda kuma Aisha taƙi mata sai da
ta haɗa ta da ummi tukunna Ummi ma ganin batool kan zuwa gidan su ta kwana biyu ta
tafi ne wanda kuma Aisha bata taɓa zuwa gidan su da nufin kwana ba. Shi yasa ummi
amince mata da tafiyar Hakan Nan ta tattara kayan ta ta tafi.

Tare suka raba chingom da sweet ɗin bikin.


Ana saura kwana ɗaya biki ango da babban abokin sa suka kawo wa amarya ziyara tare
da tambayar ta me da me suke buƙata ita da ƙawayen ta.

Koda suka zo a can falon baqi aka sauke su tare da kai musu ruwa da drinks. Aliyu
sai mita yake wai anshan yasu Habib sai haƙuri yake ta bashi, dan shi kadai yasan
yanda yayi tukunna Aliyu ya bi shi. dan yace baza shi ba da ƙyar ya yarda yazo.

Suna cikin wannan halin ne sai ga amarya da ƙawar ta suka shigo da sallama a bakin
su.

Amsa musu sallama aka yi amma banda Aliyu dan gaba daya an ɓata Mishi rai.

Hakan ne yasa bai ko ɗago da kanshi ba balle ma yasan da wanzuwar su a wurin, sai
ma hankalinsa daya maida kan wayar sa.

Bayan sun gaisa da Habib batool ta faɗa mishi tsare-tsaren su suka tashi dan
haraman tafiya, Wanda sai a sanan ya ɗago kanshi bai ko sauke idanuwan sa a ko ina
ba, sai a cikin ƙwayar idanun Aisha wanda ita ma sai a yanzu ne ta ɗaga kan ta dan
ganin fuskar shi da kyau, dan ɗazu bata ga fuskar da kyau ba Saka mokon sunkuyar
da kai da yayi ɗazun.

Duumm! gaban ko wannensu su ya buga da sauri ta sunkuyar da Kanta tare da Karanto


duk adda'oin da suka zo zuciyar ta.

Ko bayan komawar sa gida ba abun da yake sai tunanin yarinyar da ya gani.

Ita ma hakan ce a wurin ta.

haka ranar dinner ma suka haɗu wanda a nan ne Aliyu yayi jarumtar faɗa mata abunda
ke ransa. Wanda alhamdulilah ta karɓi tayin sa dan ita ma ta kamu da matsananciyar
soyayyar sa a zuciyar ta.

Ba ɓata loƙaci manya suka shiga maganar aka sa ranar aurensu.

Rayuwar su bayan aure sai dai muce mash Allah, dan suna zaman lafiya abun su. Kuma
dangin shi ma na nuna mata soyayya Musamman ma mahaifiyar shi wato hajjiya.

Haka rayuwar ta cigaba tun ana watan ne har aka zo shakara, Amma Shuru kake ji
Aisha bata samu ciki ba tun abun baya damun ta har ya fara damun ta, sun je asibiti
kuma ance musu duk lafiyar su ƙalau Allah ne bai kawo ba. Aliyu shi yake bata
haƙuri da mata misali Kala Kala, duk da shima abun na damun sa.
Amma ya fawwala wa Allah komai. A nan ne fa dangin Aliyu suka fara nuna wa Aisha
wasu hali da bata san su da shi ba. Ganin sun kusa shakara 4, Amma babu ɗa ko ɗaya.
Bayan ga mutanin da aka yi auren su a baya ma daga mai ɗa ɗaya sai biyu. Nan fa aka
fara zuga Hajjiya tun bata ɗauka har ta fara ɗaukan maganar mutune.
Ba yanda bata yi da Aliyu dan ya ƙara aure ba amma yace shifa baya da ra'ayin
ƙara aure,wanda kuma shi ya karay wa dangin sa tsanar Aisha, dan su a na su ganin
ita ta hana shi ta mallake shi har baya jin maganar mahaifiyarsa.

Aliyu yayi ƙoƙarin kawo wa Aisha mai aiki dan taya ta aiyukan gida dan ana shi
ganin sun mata yawa dan baya son tana shan wahala. Amma taƙi dan gani take masu
aiki ba abun yadda bane.
Haka nan ka ɗauke ƴar aiki kana biyan ta albashin ta duk wata, amma daga baya
sai ka ga ta aure maka miji.
Ita kuma tana bala'in son mijin ta tare da kishin sa, dan haka baza ta iya ɗaukar
mai aiki ba gwara tayi aiyukan ta da kanta ya fiye mata kwanciyar hankali.

Haka nan ya bar ta tunda tace bata buƙatar Mai aikin.


Yau bayan sun tashi tayi aiyukan ta tayi musu breakfast, suna kan ci ne aka ƙira
wayar.
"Hello Assalamu alaikum"
Shiru tayi alamun ana magana ta ɗayan ɓangaren. " Innalillahi wa'inna ilaihir
raji'un!, to ummi insha'Allah sai mun shigo"
daga haka ta sauke wayar daga kunen ta.
"Lafiya baby? Me yake faruwa?"
Aliyu ya tambaye ta. A jiyar zuciya ta sauƙe kana ta fara magana kamar haka.

"Ba kasan auntie Mariya ba Ƙanwar ummi wace kwanakin baya mijin ta yayi hatsari
har muka je dubiya asibiti. To ita ce mijin Allah yayi masa rasuwa jiya da daddare.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Allah yayi masa rahama ya kuma gafarta
masa" Aliyu ya faɗa cike da tausaya wa.

"Amin"
Ta amsa cikin sanyin jiki daga haka tace. "Zan shirya in wuce gidan rasuwar!"
Daga haka suka shirya tare da tafiya wurin rasuwar.

Bayan sadakar uku ne ummi Fatsime da Aisha na cikin daƙi suna hira Nan take basu
labarin Aliyu yana son ɗaukar mata ƴar aiki ita kuma ta hana dan bata so.

"Ah kinyi gaskiya ƴar nan gwara kiyi aikin ki da kan ki yafi miki, kuma ma ni banga
wani aiki ba Mutum kai ba ɗa ba ba jika ba wanne irin aiki za a taya ki da" Cewar
Fatsime.

" Shine nima nace bana bukatar ta" Aysha ta tari Fatsime ta hanyar faɗar hakan.
Ummi dake kwance kan tabarma can gefinsu tace, "nikam inna ga shawara, in zaki
ɗauka"
"Wacce irin shawara kenan ummi?"

"Dama ina tunanin mai zai hana ki ɗauki ɗaya daga cikin ƴan uwanki ki riƙe. Kin ga
dai yanda suke rayuwa abunda zasu ci ma wahala yake musu gashi kuma baban ma baya
nan yanzu, da kin taimeka kema kya samu lada ƙila kema Allah ya dubi zuciyar ki ya
baki haihuwa, Amma shawara ce fa ba dole bane"

"Gaskiya kam yaya da sun samu lada ita da mijin ta. Kinga dai irin rayuwar da suke
ciki babu na yau balle na gobe gashi babbar ƴar ta Husna ma wai ta gama primary
amma babu kuɗin cigaba da karatun sai ma talla da aka fara ɗaura mat. Da kin
taimeka kin ɗauke ta dan wahala idan aka bar ta nan haka to wallahi ba cewa zata
yi"
"Kedai bari Fatsime Wallahi tausayi suke bani yaran nan, kamar wasu almajirai, ko
kayan arziƙi basu da shi kullum ka gansu to babu takalmi ko ka gan su da yagaggun
Kaya. Cewar ummi

" Kai yaya wanan kam lefin Mariya ne haka nake tattara musu kayan basmah na kawo
musu Amma haka nan basa sawa. Wai siyar wa take kinji irin wani son kuɗi irin nata.
Ni bansan kasuwarba na ɗauka na kaimasu. "Ai Mariya kam ki bar ta kawai da halin
ta. Haka suka cigaba da hirar su tsakanin su.

Aisha kuwa sosai wanan shawarar ummi ta shiga ran ta wanda har Allah Allah take ta
koma gida ta faɗawa Aliyu.

Bayan kwana biyu da zancen su tazo wa da baba Mariya da maganar. Sosai baba Mariya
taji daɗin batun amma sai da ta tabatar Aliyu ya yar da tukunna.

Bayan maganar su da ummi Aisha ta samu Aliyu da maganar, Afarko bai yarda ba amma
data nace masa har da yin fushi da shi sai ya yarda amma ba dan ran shi yaso bah
dan kawai ya faran ta mata ne.
Sosai Aisha taji daɗin bata Husna da akayi bayan tazo da ita ne ta fara gyara ta,
dan ba abunda ta iya sai ƙazan ta da tarin kauyanci.

Ganin bata da wasu kayan arziƙi ne


yasa ta karɓi kuɗi wurin Aliyu tare da zuwa kasuwa nan tayi mata siyayyan Kaya.
Wanda har da su kayan bacci da pants. Bata siya mata bra ba saboda a lokacin bata
kai sawa ba. Dan duka duka baza ta wuce 11 to 12 years ba.

Sosai Aisha tayi ƙoƙarin gyara Husna wanda kuma masha Allah ta fara ɗaukan hanya.
Ana haka ne ta nema mata makaranta ta sakata.

Haka rayuwa ta cigaba har yanzu Husna ta kai shekara uku a wurin Aisha. Wanda kuma
ta gama jss zata shiga SS. Wanda kuma a yanzu girma ya kama Husna ta kasan ce
tana da girman jiki, wanda a shekarun ta bazaka ɗauka karama ba ce Sosai girma ya
nuna a jikin ta.

Husna bata da kaya sai ƙana nan kaya dan su Aisha ta fiye siya mata ko kuma da
amata ɗinki wanda ya ɗan kama jikin ta. Haka nan zata sa ƙana nan kaya ta fito da
shi falo, ba tare da tunanin wani abu bane. Aisha ma bata mata magana akan haka
tunda ita ce ke siyan kayan ma Haka ko Aliyu na nan zata fita da mini sket Abun
ta. Wanda Aliyu tun baya sa mata ido har ya fara sa mata. Nan ya fara sha'awarta
kaɗan-kaɗan ya fara jin wani abu game da ita. Tun yana basar wa har yazo ya gane,
ya fara son Husna tun daga ranar ya fara dakon soyayyar ta da sha'awarta a ransa,
har zuwa loƙacin da ta gama secondary Nan ne ya fara bibiyar ta da maganar auren,
tun abun yana damun ta har ta fada wa mamar ta. Loƙacin da ta je gida hutu dan dama
in babu makaranta ta kan je gida, nan take mamar to yanda zaman su yake. Dan ita
take tambayar ta abun da yake wakana a can din.

To haka wanan tafiyar ma bayan taje gida, take sanar da ita abunda yake faruwa Nan
fa Baba Mariya taji daɗi sosai tare da bata goyan baya.

Nan ta amince masa suka fara soyayyar su a cikin gidan ba tare da sanin Aisha ba
Har aka kai kuɗin aure da ma sa ranar biki.

A ɓangaren Aisha kuwa tana can tana fafutukar ganin Husna ta ciga ba da karatu. Dan
tana son sai tayi karatu zata aurar da ita. Kawai kwatsam baba Mariya ta ƙira wai
auren Husna ya tashi dan haka aka kawo ta gida. Sosai abun ya bata mamaki wanda har
ta tambayi Husna dama akwai wanda yake zuwa wurin ta ne bata sani ba. Amm tace Aa
babu wanda yake zuwa wurin ta. To haka dai ta mai da ta gida badan taso ba. Dan
taso ace ita ta aurar da ita Amma ya ta iya masu ƴa sun ce abasu ƴar su kuma har
yanzu Allah bai bata haihuwar ba.

Wannan shine hasalin auren Husna da Aliyu, da irin cin amanar da sukama Aysha.

Cigaban labari......

Page 7

AYSHAH

Bayan ta dawo daga rakiyar su Batool, kitchen daret ta shiga tare da ɗaura musu
abincin dare.

Dambun shinkafa tayi mai kyau ta yanka hanta carot cabbage, da sauran tarkacan
kayan veggies a ciki.
Sai da ta kammala sannan ta zo ta yi source wanda yaji nama da kifi, sai kuma
coconut juice da yaji Madara.

Lokacin da ta kammala an kusa kiran sallah magrib dan haka ba tare da ɓata lokaci
ba ta bar miyar a kan wuta dan ta kara sa nuna.

Bayan ta tabbata komai yayi, sannan ta tafi daki dan yin sallah da wanka.

Fitar ta da kamar minti 10 aka tura kofar falon ta aka shiga, Husna ce ta shigo
tare da kallon cikin falon, ganin bata ga Aisha ba ne yasa ta dan sauke ajiyar
zuciya, dama abinci ne ya kawo ta, gaba ɗaya yunwa na son kashe ta. Ta ɗauka Aisha
za ta aika mata da abincin rana amma Shuru bata ga komai ba. Ita ma ƙwuya ya hana
ta dafawa kan ta. Ganin bata aika mata da na ta ba kuma bata kira ta ba ne yasa ta
zuwa da kan ta dan karbar abincin.

Koda ta iso part din A'ishah, tana kokarin bude kofar part din ne taji hirar su.
Duk taji abin da Batool ke fada akan su. Ba ta dai ji muryar Aisha sosai ba, Amma
taji suna dariya da sauran su. Hakan ne yasa ta kasa shiga ciki ta koma part din ta
tare sake-sake. Ko lokacin da Aisha ke raka su Batool, tana kallon su ta window,
tana ganin yanda Aisha ke ba wa Batool din ha'kurin shiga mata da take son yi.

Tasan a wanan lokacin Aisha na dakin ta, hakan ne yasa ta shigo dan gaskiya yunwa
na neman aikata ta lahira.

Da sand'a ta shiga kitchen ɗin tare da bude-buden tukane, har Allah ya bata sa'a
tazo kan dambun da coconut juice din. Hamdala ta yi cikin ranta sannan ta fara
aikawa cikinta ɗa'amin, sai da ta shak'a iya shaƙa ta kai geji sannan, ta fara
magana kamar haka. "Wannan matar kamar wata aljana sai shegen iya girki'' daga haka
ta cire kwanon ta da tazo da shi daga hijab din ta. Dama ta boye ta ne dan ba ta
san ko zata ga Aisha a kitchen din ba, duk da ta san war haka tana dakin ta. Zuba
abincin tayi tare da source din a kwanon ta. Bude jug din tayi tare da kai wa bakin
ta sai da ta kusan kai rabi kana ta sauke, "wai ma sha Allah kai wanan abun yayi
dadi'' Ganin tana ɓata lokaci ne yasa ta nufi kan fanfo da jug din a hanun ta. Bude
shi tayi tare da sawa a kan fanfon, sai da taga ya kusa cika ta cire tare da mai da
shi wurin sa. Allah yasa baza ki gane ba. Har tazo fita daga kitchen din, sai
maganganun Batool na da zu suka dawo ma ta.

Hakan ne yasa ta koma tare da tuninan mai zata aikatawa Aisha, dan huce haushin su
da take ji. Tana cikin wanan tunanin ne, wani Idea ta fado ranta dan haka ta yi
saurin buɗe kan ta. Murmushin mugunta ta yi tare da buɗe Gishirin hannunta da
barkano.

Bude jug din tayi tare da cika hanun ta da Gishiri ta zuba a ciki. Ita ma miyar da
ke kan wuta bude wa tayi tare da zuba mata barkanon kana ta rufi, gyara koina tayi
kamar ba wanda ya shiga ciki. "Yanzu sai naga yanda zaki yiwa mijin ki bayanin saka
Mishi irin wanan yajin a cikin abinci, bayan kuma kin san yana da ulcer''.

Daga haka ta ɗauki kwanon ta sannan ta bar part d'in.

Sai da ta tabatar ba wanda ya gan ta sannan ta shiga nata bangaren.

******

Ita ko Aisha koda ta shiga daki bayi ta shiga tare da dauro alwala, tana fitowa ta
ɗauki darduma tare da hajibi ta kabbara sallah.

Bayan ta idar ta zauna tare da yin addu'oi, ta sha fa sannan ta ɗan kwantar da kan
ta a kan gado.
Tana tunani, da a yanzu bata rabuwa da shi.
Ganin tana ɓata lokaci ne yasa ta tashi tare da shiga bayin again. Wanka tayi a
wannan Karon tukunna ta fita. Shirya wa tayi tare da shafa jikin ta da turaruka
masu kamshin gaske sai da ta shirya tsaf sannan ta jawo ɗakin tare da sauka ƙasa.

kitchen ta shiga ta samu miyar ta shanye ruwan ta gaba ɗaya tayi kyau sosai hakan
ne yasa bata sake ɗandanawa ba, saboda ta da'ndana shi da farko.

Sauke miyar tayi, sannan ta zuba a kular mai kyau, daga haka ta suma kai wa
dining.

Bayan ta kammala kome zama tayi falo tare da kuna TV ta fara kallo duk da kallon
take Amma ba ta wani gane me ake yi, sabon damuwar da ke damun ran ta na sake
baibayeta.

******

HUSNAH.

Bayan shigo part d'in ta kitchen ta shiga tare da bude abincin ta suma ci, hannu
baka hannu kwarya. Bayan ta gama ci ta sha ruwa ta ji ta ta yi nak, wanke hannun
tayi tare da kwanon gabadaya dan ba ta son wani ya fahimce ta shiga part din Aisha,
dan haka ta wanke komai sannan ta fita falon tare da kwanciya a kan kujera, nan ta
fara jin bacci na daukan ta.

Tana cikin bacci ne taji ana knocking din kofar ta. Tashi tayi tare da bude
kofar,"sannu da zuwa baby sai yanzu'' ta faɗa tare karɓar jakar hannun sa, shima
cikin girmamawa ya ce mata "Yauwa ya gida na same ku lafiya, na biya gidan Hajjiya
ta ce agaishe ku'' ''muna amsawa, ka same su lafiya, ya su Aunty hamida?"

"Lafiyan su ƙalau suna ma gaishe dake. Yayi karya dan shima yasan ko kasan nan zata
hade Hajjiya baza ta taba cewa a gashe da Aisha ba, balle kuma ita da suka fi tsana
ma.

Baya son jan hirar dan haka yace mata ''zan yi wanka please ki hada min ruwa" Ok''
tace daga haka ta kama hanyar ɗakin ta da haɗa mishi, Amma sai ya daka tar da
ita."No toilet din da'kina zan yi amfani dashi''.

Kallon shi tayi, da kamar za ta yi magana Amma da ta tuna hirar da suka yi da Baba
Mariya sai ta ɗan sau-sauta fuskar tare da cewa. "To ranka shi dade, to sai ka
tashe mu tafi ko.

Daga haka suka shiga d'akin na shi.

Suna shiga ta wuce toilet din shi tare da haɗa mishi ruwan waka.

cire kayan sa ya yi tare dauro towel a qugun shi, tare da shiga toilet din shima.

Bayan ta gama hada Mishi ruwan fita tayi ta bar shi dan yin wakan. Falo ta sauka
tare da kara kwanciya kan chair.

Kusan awa daya yayi kafin ya gama ya sauka kasa. "Sweet amarya kin yi bacci?"
"No ban yi ba kawai inna jiran ka mu tafi mu ce abincin dare, Aunty kar taji haushi
tace ni na riƙe ka, Kuma yunwa nake ji kamar zan mutu yau banci abinci rana ba, tun
na breakfast da muka yi''

"What happened baki ci ba?" Baki da lafiya ne ko mai?"

"Aa lafiya na kalau kawai dai ba ayi bane. "Kamar ya ba ayi ba?"

"Eh inna tunanin haka ne, dan ba a kira ne dan mu ci abincin ba kuma ba wanda ya
aiku min da nawa. Shi yasa na nayi tunanin ko ba a yi girkin ba. Ta fadi hakan tare
da yi mishi kollon kasa-kasa, tana jira jin mai zai ce. Dauka tayi ransa zai baci.
Amma sai taga ya na mata wani irin kallon baki da hankali din nan."au dama ita zata
kira ki bansani ba?" Ba ke bace zaki tafi ki taya ta aiki kuyi girkin kuce ba. Ko
da can ba tare kuke yi? Kuma kika ce ba a azo a ka miki wa zai ka miki da ma akwai
yara ne ni ban sani ba, wait tsaya ma tukunna ba dai Aisha kike nufi ta kawo miki
abincin?"

Shuru tayi dan bata san mai zata ce, bata yi tsammanin haka ba daga gareshi ba, Ta
dauka da zarar ta fada masa zai je yayi wa Aisha rashin mutunci ta yanda nan gaba
ba za ta na mata irin haka ba. Dan a yanda Baba Mariya ta fada mata zai yi fiya ma
da hakan. "Haba baby baka fa gane mai nake nufi ba, ai ni bance ita zata kawo min
ba taya ma zan ce haka bayan kamar mahaifiya ta na dauke ta, yanzu sai ince baba
Mariya ta mun a aike dan bani da hankali'' kawai sai ta fashe masa da kukan
makirci. "Kuma ma dan bani da lafiya ne yau tun safe inna kwance ba abun da na iya
yi amma in ba haka ba mai ne girki da bazan yishi ba. Sosai ya rud'e yana mai bata
ha'kuri da lallashi amma inaa kamar kara zuga ta ya ke yi. "Na ce kiyi hakuri Amma
sai kara kuka kike yi mai kike son nayi ne eh sweet Amarya?"

''Fad'a min me kike son a yi yanzu'' Jin yace me take so ne yasa ta ɗan sau-sauta
kukan ta tare da goge fuskar ta sannan ta soma magana."ni ba abunda nake so tunda
ko na fada ma ba lallai ka min ba'' "Please ki fada ko ma mai ne zan yi, in dai za
ki daina wanan Kukan. "Shuru tayi kamar baza ta yi magana ba, can tace da... ''dama
ɗazu munyi magana da baba kuma ta... Tace...tace akwai kudin da karba aro wurin
wani dan hidimar biki da nufin bayan baki da wata daya ko biyu zata biya, to Amma
matar yanzu tace ta ke bukatar kudin in kuma ba haka ba za ta sa a kama ta. What!
Wani kudi ba na bada kudin komai ba kuma nace basai anyi kayan d'aki ba to wani
kud'i ta karb'a. "Mai kake nufi ne baby? Zan maka karya ne, sai ka kira ta kaji ai
kuma ma ni ai bance ka biya ba, aiki zan nema in Sha Allah wanda zan fara zuwa ko
da shara da wanke wanke ne zan yi dan naga mun biya kudin. Da ga haka ta tashi tare
da ko'kar'in barin falon. ''No sweet amarya ba haka nake nufi ba in sha Allah ba
sai kin yi aiki ba ni zan biya tunda nima a matsayen ɗan ta nake''
"Da gaskiye baby zaka biya?

"Na taɓa yi miki karya ne zan biya shi kenan kin dena fushin?"

''Eh na dai na, dama ni ba fushi nake da kai ba kawai dai ka min mummunar fahimta.
"Okay to shi Kenan yanzu muje muce abinci. "Ok daga haka suka fita daga part din.

******

Tun tana duba lokaci har ta suma Gyangyadi ganin har 10 saura ba wanda ya shigo
cikin su ne, yasa ta tashi da nufin Shiga d'aki gabad'aya ma taji abincin ya fita
daga ran ta.

Tana cikin wanan tunanin ne suka shigo hannun su a sak'ale da na juna kamar wanda
aka ce a za a raba su.
Kallon su ta tsaya yi tare da kai idanun ta kan ta hannayen su dake sak'ale.
Nan take wani kullulun abu ya tsaya mata a mok'ushi da wani irin d'acin abu da ta
ji bakin ta. Nan da nan idanun ta suka cika da ruwan hawaye, wanda tayi saurin
maida su.

Amsa sallama su tayi sannan ta jara zaman ta kan kujera dan ba ta tuna nin zata iya
zama wuri ɗaya da su a wanan lokacin, dan tana buk'atar space da za ta dai data
nutsuwar ta.

Bayan sun zauna kan dinning ne yake tambayar ta. "Ke ba zaki ci abincin bane?"

"Eh Kawai tace masa dan gabad'aya ji take kamar zuciyar ta za ta buga.

Mai kika ce da baza ki ce ba?"

"Ohh!da bangan ku ba ne,na zuba naci nawa dan na ɗauka ba za ku zo ba'' Ta fadi
haka tare da kura masa ido.

Shuru ya yi bai k'ara mata magana sai ma Husna da ya umarta da ta yi sarving d'in
su.

Haka kuwa babu ɓata lokaci ta fara yin sarving d'in su.
Tun tana zuba wa yake had'iyan yawu dan sosai abun ya qawatu ga wani irin k'amshi
da yake ba da wa.

Allah Allah yake ta gama ya fara ci. Tana gama wa ya d'au cokali da bismillah ya
kai lumar farko ta abincin bakin shi, sam Bai lura da irin bala'in da ke ciki ba
sai da ya hadiye ya d'aura na biyu a bakin shi, a firgice ya dawo dashi yana sakin
tari, da saure Husna ta ɗauke coconut juice ta mik'a masa ya amsa mata sha mai
makon ya ji sauk'in yajin da yake ji, sai yaji wata iriyar bala'in Gishiri a juice
din yanda kasan cika hannu an zuba masa cikin bakin sa.

P.8

Ai bai san sanda ya fuzar da shi waje ya fara tari kamar zai shid'e. Duk abunda ya
ke tana jin sa Amma b'acin ran da ke zuciyarta ta ya hana ta zuwa wurin da ya ke.
Tun tana daukan abun na wasa ne har ta fara tsorata."Aisha! Aisha!! Aisha!!!. Ki
temaike ni zan mutu, sosai ya ke tare wanda har numfashin shi ya suma yin sama.
"Bud'e fridge tayi tare da daukan ruwa mai sanyi ta bud'e murfin kana ta suma ba
shi a baki dayan hannun ta kuma tana mai shafa bayan shi da ita. Da kyar ya samu
tarin ya lafa, idanun sa sun rine sun yi ja wur. A hankali ya ke maida numfashi
gaba d'aya ya wani lafe mata a jiki kamar wani dan karamin yaro. Sai da suka kusa
minti 10 a haka kana ta ture shi daga jikin ta. ta tashe tare da k'okar'an barin
wurin gaba d'aya ma."tsaya! Waya dafa abincin nan?"

"Ni na dafa mai ya faru?"

"Ke kika dafa bayan kinsan bana cin barkano shi ne kika zuba mai yawa a abincin har
ya kusa kashe ni." "No ni ban zuba barkano a ciki ba sai dai in attargu ne yayi
yawa, Amma ko shima bana tunanin yayi yawa haka tunda sai da na da'ndana. "To wanan
da kika cika shi da Gishire fah?" Gishire kuma?"

Bai sake magana ba sai ma tashewa da ya yi tare da barin falon ma gaba d'aya dan
har yanzu bai dawo daidai ba. Baki bud'e ta ke kallon shi, tana mai kara tambayar
kan ta Gishire? To mai ya kawo Gishire cikin juice din bayan tasan bata yi mistake
din sugar akan Gishire ba tunda sai da ta sha daga shi kafin barin ta kitchen din.
Ba ta ida tuninan ta ba taga Husna na k'ok'ran fita ita ma, gaba d'aya ta tsorata
dazu nan dan ba ta san haka abun zai kasan ce ba. Ta san baya cin yaji Amma ba ta
dauka har haka abun yake ba. Ganin ya tafi ya bar ta a wurin ne yasa ta saurin
barin falon dan ba ta san mai Aisha za ta mata ba idan har ta fahimce tana da sa
hannu a cikin wanan aika-aika.

Bud'e kayan abincin tayi tare da d'and'ana su gaba d'aya,"Ya salam ya aka yi haka?"
da saure ta bar falon ta wuce kitchen din bud'e tukunyar ta yi tare da kara
d'and'ana miyar still dai abu daya"tunawa da akwai dan coconut juice din a fridge
da dazu ya rage sai ta juya a cup din tasa a fridge, ta bud'e tare da dauko wa da
bismilah ta sa abakin ta, Amma mai, sai taji shi normal ba abunda ya same shi. Wato
dai bata mata girki aka yi ba wanda ya zo ran ta sai Husna, no wonder dazu ta ga
sai rakube-rakube take ashe ta san tsiyar da ta shuka. Ai ko za ta yi maganin ta ba
sai ta k'ara samun daman shiga mata part ba tare da sanin ta ba tukunna za ta mata
wanan tsiyar ba.

*****

Koda ya isa part din Husna kasa shiga d'aki yayi sai a nan falon ya kwanta tare da
rik'e gefin cikan sa dan sosai yake jin ciwon na tashe Mishi, wanda ko magana ma
baya iya ye sosai sabon ciwon.

Cikin wanan halin ta sa me shi, tsaya wa tayi akan shi na dan wani lokaci kana ta
dan tabe baki ita kam ta rasa wani irin na miji ne wanan daga dan taba abinci sai
kuma ya koma kamar mai laulayin ciki.

Ganin tunda ta shigo bai tanka mata bane yasa ta yin fuskar tausaye tare da matsowa
kusa da shi. "Baby sannu sannu cikin ne har yanzu?" Kai kawai ya iya kad'a mata dan
shi kadai yasan mai yake ji. "To ko mu tafi asibiti ne dan ni gabadaya na kasa gane
wanan abu, kamar Wanda aka shirya. "Da kyar ya iya furta"shirya kamar ya?" Dan
shuru tayi kamar wance take tsoran abunda za ta fada can dai tace," eh mana baby
dan dai kawai nasan aunty baza ta yi wanan abu ba Amma dai gaskiya da alamar
tambaya cikin wanan lamari, ka ga fa tunda aka yi wanan auren ba ta nuna mana komai
ba. Amma ai bata sake mana kamar da ba ba ta dariya kwata-kwata, kuma dazu da muka
shiga ma kamar tana fushi dan dai kawai kai baka lura ba Amma ne inna kallon ta har
da yi maka harara fah. Ganin kallon da yake mata ne yasa ta cewa in sha Allah ma ba
haka bane taya aunty zata bata abincin ta da kan ta.

Shuru yayi ya na nazarin maganganun ta da alamar tambaya gaskiya indai bata san
akwai abu cikin abincin ba ai baza ta k'ici haka kawai ba. Nan fa ya fara sake-sake
da gani ya fara hawa kan maganganun Husna.

Suna cikin wanan halin ne suka ji an kwankasa k'ofar falo tare da tura ta ciki.
Shigo wa tayi tare da zama a kusa da Aliyu sannu ya jikin, shuru bai tanka mata ba
dan har yanzu yana cikin wanan tunanin ita ke son hallaka shi. Ba ta damu da
yanayen sa ba ta mik'a masa cup din dake hannun ta tare da ciwa ," kasha wanan in
sha Allah zaka samu sauki. Kamar bazai ansa ba Amma jin yanda ciwon ke hau hawa
yasa shi k'arba tare da shan maganin. Bai sauke cup din ba sai da ya gama da
maganin kana ya mik'a mata cup din. Karba tayi tare da daukan remote din falon ta
dan rage gudun AC tare da taya shi cire rigar shi kana ta ce masa "ka dan kwanta
zaka ji sauki." daga haka ta kama hanyar fita ba tare da ko kallon inda Husna take
ba.

ilai kuwa ba babu bata lokaci ya fara samun sassauce dan ciwon ya fara raguwa wanda
sanadin haka har ya dan samu bacci a nan falon.

Husna kuwa ta cika ta yi fam. Wai mai yasa duk abun da ta shirya ma Aisha ba ya yi
ne.

Dazu ma ta dauka zai yi wani abu Amma sai ya gwasile ta, gashi yanzu ma da ta dauka
zai yi wani abu Amma ba abunda ya tsinana sai ma kar bar abinda ta ka Mishi. Kwafa
ta ja tare da wuce war ta d'aki, dan dole ne ma ta fada ma Baba abunda ke faru su
san abun yi tun wuri.

Shi kuwa a nan falon ya kwana dan sai asuba ya tashe tare da jin sa kalau kamar bai
yi ciwo jiya ba. Tuna abun da ya faru jiya da maganganun da Husna ta dinga fada
mishi game da Aisha, sai yaji gabadaya ma yana jin haushin kanshi taya ma zai yar
da abunda aka fada masa akan ita. Sanin kansa ne baza ta aika ta hakan ba sai dai
in a rashin sani ne.

Tuninan haka ne yasa shi mik'e wa tare da nufan part din ta, bai same ta a falo ba
sai ya wuce da'kin ta daret samun ta yayi ta gama aiyukan ta har tayi wanka kawai
breakfast ne take k'ok'ran sauka dan daura musu.

"Good morning wifey. "Morning ka tashi lafiya?"ya jikin hope da dan sauk'i?"

"Yeah alhamdulilah thanks to you nasmu lafiya." "yayi kyau daga haka ta dau hijab
din ta tana k'ok'ran barin da'kin dan gaba d'aya jin ta a takure take. "Inna zaki
ne?"

"Kitchen zan shiga dan dauro mana breakfast lokaci na k'uri kuma zaka tafi aiki.
"No yau ranar hutun ki ce baza ki shiga kitchen. "Kamar ya ranar hutu bangane ba?"

"Eh abunda nake nufi kenan yau amarya zata mana girki dan haka yau ranar hutun ki
ce in yaso daga baya kya yi mana d'add'anan girkin ki nan. Yanzu inna son nayi
bacci dan haka zo ki taya ni baccin.

Shuru tayi tana tuninan" wato dan abun da ya faru jiya shine baya son taya yi
girki, mai yasa tun da can can bai ce amarya tayi girkin ba, sai yanzu. Nan shaidan
ya suma kinsima mata abubuwa a zuciyarta.

Shi ko har ga Allah ba wanan Dalilin bane yasa shi fadan haka kawai dai wanan
mummunar zato da yayi mata ne ya sa shi yanke wanan shawarar.

"zo muyi bacci mana."

"Aa bana jin bacci ne, kai ka yi in kana ji. "Ban yarda ba, tare zamu yi baccin
daga haka ya jawo ta zuwa kan bed din tare da rungumar ta baya.

haka nan ta kwanta ba dan ran ta na so ba ita fa yanzu bata ma son kallon sa balle
har hada jiki da shi. Duk nuk'u nuk'u da take Mishi ya ci ace ya gane Amma baya
gane wa sai wani shishige mata yake.

Dauka wayar sa yayi tare da tura wa Husna tex massage kamar haka:

"Good morning amarya kin tashe lafiya, please kiyi mana breakfast yau dan auntyn ki
ba ta jin karfin jikin ta so ki hada mana. In kin gama zaki iya cin naki muma in
mun tashi za muci namu daga haka ya kashe wayar gabadaya ma dan kar ma a dame sa da
kira.

P.9

Kwance take akan bed tana yin chat da wasu yan class din su wanda magana suke a kan
karatu. Labari su ke bata a kan wasun su har sun fara shiga class sun suma amsan
lecture. Wanda hakan ba k'arimin tayar mata da hankali yayi ba. Kowa ya fara karatu
Amma banda ita. Ganin Tunani ba zai fice ta ba ne yasa ta fita falon dan samun shi
da maganar, duk da ya ce mata yana kan cika-cikan takardun na ta. Amma duk da haka
ita gane take k'arya ya ke mata haba ba tun yau ba yake gaya mata magana daya.

Cikin wanan sak'e-sak'en ne har ta isa falon tare da kiran sunan shi. Amma wayam
bata gan shi ba a kuma wanan lokacin ne wayar ta ta yi haske ma'ana an tura sak'o.
Tana Karanta sak'on tayi wulli da wayar kana ta wuce dak'in shi da gudu dan ganin
ko da gaskiye yana part din aisha.

Ai koda ta shiga wayam ta ga babu kowa, baya dak'in da saure ta fita ta kama haryar
fita daga falon.

sai da ta isa bakin kofar shiga part din Aisha sai kuma ta tsaya dan bata san mai
zata ce musu ba in ta shiga. Koma wa part din ta ta yi tare da safa da marwa cikin
falon.

ita za a maida shasha-sha ba ta san me ta ke yi ba, ranar kwanan ta miji ya je


wurin kishiya, har da wani ce wa ta musu girki wato ga yar aikin gida. inna baza ta
sab'u ba wai an sace zanin mahuakaciya.

Ta kusa minti 40 a haka, ga kuma wata tsinenniyar yunwa da take ji kamar tace babu.
ganin in har bata shiga kitchen ta samar wa kan ta wani abu taci ba, ita ce da
wahala dan ba mai girka mata tunda mai girkin tana turakar mai gida.

Haka ba dan taso ba ta shiga kitchen tare da daura ruwan zafe a kettle kana ta
daura tukunya a kan Gas.

Tana girkin tana mita, "wallahi ni ba Dan kowa zan dafa ba dan kai na ne, kuma daga
yau bazan sa ke ba kowa yayi girkin sa da kansa. Tunda haka abun ya ke." haka dai
ta cigaba da mita har ta gama da jolof din taliya Wanda ya sha kayan hadi kuma ba
lefi yayi kyau a idanu. Zuba musu na su a kula tayi tare da aje wa gefe. Ka na ta
zuba na ta tare da hada tea mai kauri, falo ta fita tare da zaman a kasan carpet
kana ta suma cin abincin ta.

******

ba su suka farka ba sai 9:30. ta riga shi Farka wa, dan haka a hankali ta ke
k'ok'ran tashi Amma ta kasa. tashiwa ta ke son yi Amma ta kasa Dalilin k'am-k'am ta
da ya yi, sai mutsu-mutsu take Wanda kuma shi ya yi silar tashiwar sa. A hankali ya
bud'e indun sa har ya bud'e su tar akan fuskar ta. wanda sai ya mutsa fuskar take
ita ala dole sai ta k'wace Kan ta. Kara k'am-k'ame ta yayi dan ganin gudun ruwan
ta.

"Dan Allah ne ka cika ne." "Uhm ni dai Aa dan ban k'oshi da dumin jikin ki ba."
"Zan shiga toilet ne fa." "Na k'i wayon kina son guduwa ne kawai nasani. I don't
know why you don't like me coming close to you. ko dan hirar nan da mu ke before
you've stop it, tell me what is the problem mai ya canja ki ne?"

Magana ta suma a zuciyarta,"Ka ji dan rainin hankali, you even have the audacity to
question me?" Amma a zahire ta k'ak'olo murmushin dole, "No you are over thinking
it mai zai sa na canza kawai dai bana jin dad'en jiki na ne."

"Are you sure, ba abunda yake damun ki dan bana jin dadin zaman da mu ke mu koma
kamar da."

"No kar ka damu ba ko mai everything will be alright kawai dai jikin ne, yanzu ka
cika ne I want to take my bath." "Ok fine zan barki Amma on one condition."

"What's that?"

"Sai dai mu yi wankan tare in kuma baki yarda ma to sai dai mu ci gaba da zama a
haka dan ne ban gaji da kwanciyar ba."

" Kai! Ita kam ta banuu wanan wani irin na ci ne haka.


"Ok tare zamu yi in kana so ma kai zaka min ma." "Yauwa ko ke fa." daga haka ya sa
ke ta, suka sauka gaba d'ayan su. nan ta fara jara dak'in da gadon, ya zame ma ta
kamar jela duk inda ta juya da zuwa yana nan a bayan ta. Ganin ba zai bar ta ne
yasa ta cewa, "to ka cire kayan ka sai muje mu yi wakan." Kai kawai ya kada mata
kana ya juya tare da k'ok'ran cire kayan sa.

Ta na ganin ya ba ta baya hankalin sa ba ya wurin ta, ta kama hanyar toilet da gudu


ta shiga tare da bank'o k'ofar ta sa mata key.

Da saure ya juyo tare da zuwa bakin toilet din. "Aisha ki bud'e ba haka mu ka yi da
ke ba, ki bud'e k'ofar dan Allah." Yana magana ne tare da buga k'ofar.

"Gwara ma ka ko ma daga inda ka fito dan bazan bud'e k'ofar ba, tunda kayi aure
tare muke wankan da zaka wani ce min tare zamu yi to bazan bud'e ba." " Aisha ni
kike ga ya wa haka?" "Eh din na fada kayi duk abunda zaka yi bazan bud'e ba."

Shuru yayi bai kuma ce wa komai ba sai ma kama handle din k'ofar da yayi tare da
bude k'ofar kana ya kara maida wa kamar wanda ya fita da d'akin.

Jin shuru ba ta kara jin muryar shi sai ma karar k'ofar da taji ne yasa ta sauke
ajiyar zuciya tare da cewa "da karka tafi mana za ka ga Wanda zai bud'e maka k'ofar
ai mutum sai na in tsiya n bana yi ana dole ne."

Tunanin ya bar d'akin ne yasa ta bud'e k'ofar at once ba tare da tunanin kome ba,
ta zo cire kafar ta kenan suka hada ido da shi, tsaye ya ke a bakin k'ofar hannayen
sa a nan nad'e. Wani shegen Murmushi ya sakar mata kana ya daga mata gira
daya."auntie how market?"

Ai bata tsaya jin k'arshen maganar sa ba ta ja k'ofar zata rufe, rik'e k'ofar ya yi
da hannun sa kana ya suma tura ta ciki ita ma hakan ce a wurin ta. Nan suka fara
ture-ture da shi, sai hak'uri ta ke bashi Amma inna yace shi baisan zance ba. Ganin
ya fi karfin ta ne zai iya bud'e k'ofar ne yasa ta saken ta tare da sauren matsa wa
gefi, aiko da k'arfi ya ture ta wanan Karon wanda saura kadan ya fadi saka mokan ta
bar wuri.

Ganin haka ne yasa ta saurin barin bayin, ai bai yi wata-wata ba ya damk'o ta. Sai
zillo take ita alla dole sai ya a je ta. Rok'o yayi mata ba na wasa. Nan fa suka
fara ko kawa wanda biye ma ta kawai ya ke dan ba ta fi karfin ta sukume ta da hannu
daya ba, ganin tana bata mishi lokaci ne yasa shi daga ta sama tare da sab'a ta kan
kafadar ya shiga da ta bayin. Bai diri ta a ko inna ba sai Cikin kwomin wanka wanda
ci ke yake da ruwa. Ihuu! ta sake jin sanyin ruwan ya ratsa ta. Yana dire ta ya
koma ya kulle kofar tare da saka ma ta key. Kana ya juyo kan ta tare da cewa "zaki
fita ni ban hana ki ba malama. Sai kunbura baki ta ke ita ga wanda ake wa lefi ta
mak'i mishi magana. "Haba Indo ta mai nayi kuma daga cewa zaki min wanka shine kike
kunbura fuskar haka." "Bana so ka dena kira na Indo ni bar yar kauye bacci." "To
shi kenan ba zan kara kiran ki da Indon kauye ba, duk da Indon kauye ce.... Ko gama
abunda zai ce bai yi ba ta suma watsa ma sa ruwa a jiki. "Tsaya please ban gama
magana ba." Ba ta tanka mishi ba sai ma shower da ta bud'e ya jika masa ka gaba
d'aya. Shower mai gefi da gefi ne sai kuma ta sama, sosai ya ke son ma ta magana
Amma ruwan ya hana shi sai shigar masa ido da baki ya ke, hakan ba k'arimin Nishadi
ya ba ta sai dariya ta ke masa har ta gama Mishi gwalo.

Cikin wanan halin ne har ya samu daman rik'e hannunta bai yi wata-wata ba ya jawo
ta cikin ruwan ita ma. Nan ita ma kayan ta ya gama jik'e wa tare da man ne ma ta a
jiki da ma ba wasu kayan arziki bane a jikin na ta.

Ganin mood din shi ya fara can za wa har idanun sa sun can za sun kade sun yi ja ga
kuma tudun abin shi ta ji ta bayan ta ne, yasa ta neman hanyar guduwa.
"Where do you think you going madam."

ta suma inda inda da.. dam dama zan fita ne."daga haka ta juya da nufin gudu. Amma
inna ya damk'o ta tare da jawo kugun ta ya hada da na sa.

"King Please." tace tare ture shi.

"You sure have a lot of energy to be stubborn this morning. Let's put it to better
use, shall we?" Ya furta hakan tare da yi ma ta wani killer smile.

"What do you mean?" Ta tambaya ko gama magana ba tayi ba ya hada bakin su wuri
daya, tun tana ture shi ba ta so har ta fa da tarkon shi, ta suma bashi hadin kai.

******

HUSNA.

Bayan gama cin abinci ta maida kwane kan kitchen, d'aki ta koma tare da kwanciya.
bacci take son yi Amma bak'in ciki ya hana ta bacci. So kawai ta san mai su ke yi
da basu tashi ba har yanzu. Kuma yaushe ne ma Aliyu ya tafi can din a nan ya kwana
ko a can ya kwana. Ganin ba mai bata amsar tambayoyen ta ne yasa ta mik'e tsaye
kana ta Suma cewa,"inna gwara na je na duba da idanu na ga ko sun tashi."daga haka
ta fita falon, har za ta wuce sai ta tuna abincin su hakan ne yasa ta koma kitchen
tare dauka abincin kana ta kama hanyar fita. "Yauwa yanzu na samu hujjar kare kai
na ko da sun gan ni."da haka har ta isa part din, tura k'ofar tayi a hankali tare
da lek'a cikin falon. Ganin babu kowa ne yasa ta shiga ciki tare da kalle-kalle ko
inna tsab-tsab ga wani irin sihirtacen kamshi.

A dinning ta daura abincin kana ta koma falo da zama minti kadan ta duba agogo. Tun
tana san ran zasu sauka har ta ga ji. Tsakiii taja tare da mik'e wa sama dan ta
gaji da zaman jira. Gwara ta koma part din ta ta kwanta tun da basu da niyyar fita
yau su.

Har ta isa k'ofar za ta bud'e kenan taji ihun Aisha!. Cakk ta tsaya tare da kasa
kunne dan jin mai yake faruwa, jin magana kasa-kasa da kuma dan hayaniya kamar ana
dambe ne yasa ta saurin koma wa ciki dan jin mai ke faru.

Ganin ba ta jin mai suke cewa a nan kasa ne ya sa ta dan hauro wa sama kadan, nan
ta suma dan jin mai suke cewa. Jin inda Aisha ke bashi hak'uri kan baza ta koma
toilet din bane yasa ta tunanin fada su ke hakan ne yasa ta ke bashi hak'urin nan.

A ba ta san sanda tayi tsale tare da tafa hannayen ta,"yes yes."

Sabon gulma irin na ta hakan bai wa da tar da ita ba sai da ta haura sama gaba
d'aya dan jin mai suke cewa sosai. A hankali ta taka har ta isa bak'n k'ofar tare
da kasa kunne da kyau dan jin mai su ke cewa.

Ai ko ba ta ji kome ba ila maganar Aliyu, inda ya ke ma Aisha sambatu Kala-kala har


da alkawaruru ka ya ke daukar ma ta.

Ai bata san sanda ta daura hannayen ta a saman kan ta tare da zare idanun ta waje
ba tasan lokacin da ta bar wurin da gudu har ta na mai tuntube ta buge k'afar ta da
k'arfen wurin, saura kadan ta sa ke fisare a jiki sabon rad'adin zafin bugun, da
kyar ta iya
kawo kan ta part din ta.

Sai kuka da take wiwi har da tsarabar majina. Abu goma da ashiren suka hadu ma ta
Ga abun da taje ta ji wo, ka kuma ciwon k'afa.

P.10

Bangaren su Aliyu kuwa, bayan sun gama sun yi wanka da sallah, dan a lokacin har
karfe 2 tayi. falo suka sauka dan nema wa kansu abun da zasu ci. gaba d'aya sun ma
manta da wani abincin Husna, direct kitchen suka nufa Nan suka suma girkin su
hankali kwance. Shi ke taya ta yanka albasa da b'are Maggie. Suna hira suna girki
abun ban sha'awa kamar wanda ba abunda ya shiga tsakani. Amma duk da wanan Aisha
still wanan bak'in ciki da damuwar yana nan a zuciyarta dan dai kawai ba yanda za
ta yi ne kawai, tasan duk wanan abunda ya faru kaddarar su ce kuma ba za iya canza
ta b. abun da ciwo Amma ta fauwala wa Allah komai.

Da haka suka gama girkin su, suka haura da shi sama abun su suna hira suna ci duk
da shi ke hirar ita da ga eh sai a'a. Cikin hirar ne ta ce masa "Amma ban ji dad'in
abunda ka yi ba." " Me na yi da baki ji dadi ba?"

Ka san ban karb'i girki ba Amma ka zo nan hakan bai da ce ba, a hakan ka ke son yin
adalci?" gaskiya kar ka kuma." "Ok sorry ba zan kuma ba gimbiya Amma kinsan yau
zaki k'arbi girki ko?" So shi yasa na dauka is normal."

"Duk da haka ai sai dare zan k'arbi girki so har yanzu girkin ta ne, kuma ma ne da
zaka dan kara mata kwanaki, dan gaskiya bana jin d'ad'in jiki na Dan haka ba zan
iya ba." Mai ki ke nufi da baza ki iya ba?" Ya fada tare da hada fuska. "No ba fa
ka gane ba ina nufin a dan kara ma amarya kwanaki ta yan da zaku saba sosai din nan
kaga inda rabo ma sai ta k'unsa ta haifa mana baby's tun da ni shuru har yanzu."
Hmmm na gane Amma maganar kin k'ara ma ta kwanaki ki bar ta can gefi dan ban yarda
da ita ba." Daga haka ya canza hirar zuwa wani abu da ban. Albishiren ki next week
in sha Allah Husna za ta fara zuwa makaranta burin da kike mata Allah ya yi za ta
cigaba." "Kai ma sha llah Amma na ta ya ta murna." daga haka ta rufe bakin ta. Ta
ci gaba da cin abincin ta, da da ne taji wanan labari da za ta fi kowa murna Amma
yanzu kam su suka sani da ta yi da kar ta yi duk daya ya ke a wurin ta. Da haka
suka gama cin abincin ta tattara kayan ta mai da kitchen tare da wanke su sai da ta
gyara kitchen d'in kana ta fita. A lokacin da ta fito ta tarar dw baya nan hakan
yasa ta tunanin ya tafi wurin d'ayar matar shi dan haka ta kulle k'ofar falon ta
tare da koma da'ki. "Naga ta inda za a shigar mini har a shuka min tsaya." Koda ta
shiga d'akin wayarta ta d'auko tare da dan wa ummi Kira.

******

Aliyu.

Koda ya tafi part din Husna bai tarar da ita a falo ba, dan haka a kama hanyar
d'akin ta.

Koda ya shiga, ya tarar ta na bacci. Dan haka a hankali ya bar d'akin tare da jawo
ma ta k'ofar.

D'akin sa ya shiga tare d'auko car key din sa kana ya fito harabar gidan, shiga
cikin motor ya yi kana yayi horn mai gade ya bud'e masa gete ya fita.

Gidan Hajjiya ya ke son tafiya yau satin sa d'aya da zuwa gidan tun ranar da ta sa
shi a gaba sai ya saki Husna bai k'ara zuwa ba, ba wai ba ya son zuwa ba kawai
fadan ta ya ke gudu.
Da wanan tunanin ne har ya isa gidan, a waje ya yi parking din motarsa kana ya
shiga cikin gidan banda bugu ba abunda gaban sa ya ya ke, Dan baisan mai zai Tara
ba.

Da haka har ya isa falon da sallama ya shiga cikin. Samun su yayi suna zaune sai
hira su ke. Jin sallamar sa ne yasa su tsaya wa da hirar su tare da zuba mishi
idanu. Gashe su auntie zara yayi suka amasa mai fuska a sake, kamar ba babu komai
bayan su ke zuga Hajjiyar.

"Hajjiya fa?" "Tana d'aki." "Ok! Da ga haka ya nufi dak'in na ta. A hankali ya turo
k'ofar ciki tare da yin sallama. Samun ta ya yi tana kan darduma tare da jan carbi.
Zama yayi gefin ta tare da jiran ta gama, Sai da ta ga ma ta dau fatiha kana suka
gaisa."ya gidan ka da matayen ka?"

"Lafiya klau alhamdulilah su ma su na gaishe da ke." "To inna amsa wa, daga haka
suka cigaba da hira wanda sosai ya ji dadin haka dan gaba d'aya Hajjiya ba ta nuna
ma sa komai ba, kamar ba abunda ke faru wanan tsoran da fargaban sun bar jikin shi
ya sake sai hira suke wanda daga baya suka fito falo suka hadu gaba d'ayan su as a
big family suna hira da Nishadi. A nan ne ma ya ke jin wai balkisu ta sa mu miji za
ta yi aure. Wanda ba k'aramin dadi su ka ji ba finally after so many years za ta yi
aure

******

BABA MARIYA HOUSE*

KAUSAR ce zaune a bakin murhu tana mai tuk'a tuwo. Wanda sai k'unk'une ta ke wai su
sun gaji da cin tuwo kullun-kullun abu daya. Gaba d'aya haushin su ta ke ji tun da
a ka yi auren Husna shi ke nan sun rabu da cin kayan d'ad'i tun da dama Aishar ce
ke kawo musu, to kuma ga abunda ya faru. Tun da bak'in biki suka watse kayan
abincin ya k'are Baba Mariya tace sai dai kowa ya ce abun da akwai dan ita dai kam
ba za ta siya shinkafa da kudin ta. Sai dai su zauna da yunwa in baza su ci tuwon
ba.

"Wallahi Kausar in kika bar tuwon nan ya yi gudaji sai naci uban ki, shegiya yar
matsiyata za ki fada min in shi uban naki ya bar wani abu kafin rasuwar sa. dan ma
kun ga na cire kudi har aka siya garin tuwon, da na bar ku da yunwa In ga ta tsiya
ai."

"Cikin murya mai kama da na kuka ta suma magana kamar haka, "ba wani nan kina da
kudin Amma Baki son cire su, kuma ke kika ja, da har Madara da Milo muke sha a
gidan nan Amma yanzu yaushe rabon mu da musha kullum abu d'aya tuwon Dawa da miyar
kuka, kuma babu wani kayan miya. Miya duk lami ko dan Nama ko kifi babu jiya kam ko
Maggie babu haka muka ci ki kawo Naira talatin a siya Maggie ma kin k'i wai ba ki
da kudi bayan kuma kina da shi.

"Banzan cire ba, nace bazan cire ba sai ki zo ki kwata da k'arfe in gani kina wani
cewa inna da kudi to wanan kudin akwai abunda nake son yi da su, Delu tace akwai
wani malami da ta ke son hada ni da shi yayi mana aiki. Kin ga dazu Husna ta kira
ne tana min kuka kin ga dole mu tashe tsaye in ba haka ba mu zamu ji kunya. Tun ba
yau ba Delu ta ce za ta kai ni wurin malam din amma inna k'i to yanzu kam a shirye
na ke."

"Amma Baba ni kam inna tsoran kayan Boka kar muje kuma aikinsa baya aiki ko kuma
tsautsayi ya koma kan mashik'iya, Ni dai da ta hakura ta zauna kar ta ja mana yanzu
gobe zamu ji gidan na ta, ta harhada mana abun da ya sauwak'a gaskiya kar ku caja
mana wallahi."

"Dalla shasha wa yace dan ita kadai na ke son zuwa wurin mallam din, kuma shi ba
Boka bani mallami ne wanda ya ke taimakon mutane wa inda suke da matsaloli musam
man irin naki."

"Irin nawa?" "Kamar ya irin nawa dama inna da wa ta lalura da bansan da ita ba."

"Au baki sani ba kenan! Fada min tunda ki ke a gidan nan an taba zuwa bakin k'ofar
gidan nan da zancin anzo wurin ki?" "Nikam na rasa gane wanan wace ire yar masifa
ce wanan. ace gaba d'ayan ku baku da wani farin jini sai bak'in jini irin na
mahaifin ku, Husna ma da k'yar ta samu tayi auren nan ke ma gashi babu mashinshini
ai dole in tashe tsaye kar mak'iya so min dariya abu kamar da saka hannu."

"Kai Baba wallahi k'arya babu kyau dan ko a Islamiya an hana mu k'arya, KAKA fa ta
ba mu labarin ki tsab. In ma bak'in jinin ne da mu to ke muka gado dan mun samu
labarin baki da ma shin shi ne duk kawayen ki sun yi aure sun bar ki Amma ke shuru,
ganin zaki tsofe ne yasa mallam mai sittin ya baki wa Baban mu ganin shi
almajirinsa ne. Haka nan ba yanda ya iya ya amshe ki duk da ba ke ya ke so ba INNA
fastime ya ke so. Ranar wai har da yin party dan ance za a yi auren ki, zaki fita
daga gorin kawaye da su ke miki a kullum in ku ka hadu.
P.11

"Dan ubanki ni ki ke gayawa na yi ƙwante?" daga haka ta soma baza idanunta dan
samun abunda za ta ƙwala mata.

Ludayin miyan da ta gani ne ta ɗauka, tare da saita ta da shi.

Tun kafin ma ta wulla mata shi tuni Kausar ta bar wurin da gudu tare da ce wa ."
Sorry ba zan kuma ba, kawai ina gaya miki abunda Kaka ta faɗa mana ne fah."

" Wato ke yanzu kin balaga ina magana kina magana? na lura da ke kwanan nan rai ni
ya fara shiga tsakaninmu da ke; in kina son aure ki fito fili ki gaya min, ba wai
ki zo kina sa'in sa da ni ba."

Shuru ta yi mata dan ba ta wani damu da maganarta ba, dan sun saba da irin wanan
maganganun na ta, dan haka bai wani dame ta ba.

"Ba za ki zo ki duba wanan tuwon ba sai ya ƙone tukunna ko, dan ba ke ki ke siyan
kayan abincin ba."

Guna-guni ta soma." Ni kam na gaji wallahi wanan wani irin wahala ne, gaskiya ni
kam gobe in na je gidan Aunty HUSNA bazan dawo ba, a can zan zauna da ita sai na
hutu wa raina."

Da haka har ta gama tuwo da miyar ta sauke ƙasa.

Ganin ana ƙiraye ƙirayen sallah mangarib ne, ya sa ta ɗau buta tare da shiga bayi,
wanda saboda son kudi irin na Baba Mariya sau biyu ake bata kudin gyaran bayin,
amma ta ƙi gyarawa haka su ke amfani da ita, gaba daya bayin ya rushe sai tsohun
ƙwano da suke lallaɓawa da shi, wanda in kana wanka ba za ka iya miƙewa ba dan gaba
daya rabin jikin ka yana waje, haka su ke amfani da ita ba tare da ko ƙorafi ba.

Bayan ta fita ne ta soma alwala kana ta ta kabbara sallah.

Bayan ta idar ta tattara komai ta gyara wurin kana ta zauna akan taburma.
Wayarta ta ciro ta fara charting. wayar dama na HUSNA ce, da ta ɓaci sai aka siya
mata wani, wanan kuma sai taba Kausar bayan an gyara mata shi.

Sai a lokacin ƙannenta suka dawo daga yawo. ƙannenta maza uku ne suka shiga gidan,
tun fitar safe da suka yi sai yanzu tukunna suke dawowa gida.

Babu karatu sai bin abokan banza da suke da suna zuwa wata government school a nan
basu da nisa, amma yanzu sun dena wai ana duka su, shi ya sa suka dena zuwa.

Haidar shi ne babba sai kuma Dauda da kuma Autan su ABBA. Gaba daya sun yi wani
nuƙu-nuƙu saboda datti, ga dauɗa da suka yi kamar wanda suka yi shekara ba su yi
wanka ba, kuma in an tambaye su wai ɗazu da safe nan suka yi wanka tare da sa kayan
nan da ke jikin su.

Kan taburmar da ke shinfiɗe a tsakiyar gida su ka zauna, kana suka soma gaishe da
su.

"Baba ni yunwa na ke ji.?" In ji Abba da ke wasa da takalmin Kausar.

Baba da ke cikin ɗaki ne ta ce." Haidar kun yi sallah?."

" A'a ba mu yi ba." Ya amsa mata.

"Mai na ce muku game da sallah ehh? Yau zanga wanda zai ci abinci a gidan nan ba
tare da yayi sallah ba, Shegun yara kullan ina magana da kuyi sallah ba za ku kuyi
ba, nasan kuma tun sallar safiya da ku ka yi ba ku sa ke yi ba ko?"

Shuru su ka yi dan maganar ta gaskiya ce tun safe da su ka yi sallah ba su kuma yi


ba.

"Maza-maza ku tashi ku yi sallah, kuma duk sai kun biya wanda ba ku yi ba, in ba
haka ba yau ba ku da abinci."

Su na jin haka suka tashi da sauri, da yin alwala kana suka kabbara sallah.

Sai da suka biya duk bashin sallan da ake bin su kana suka yi sallah magrib.

********

HUSNA.

Sai kusan mangarib ta tashi, shi ma fitsari ne ya tashe ta. Tun lokacin da ta shiga
part dinta tana kuka bayan ta ya ne, shi ne ta faɗa barcin wahala.

Da kyar ta iya shiga toilet ta yi uzirin ta kana ta fita a lokacin har an an kira
sallan mangarib. Darduma ta shinfiɗa kana ta kabbara sallah.

Bayan idarwa ta shiga kitchen ta sama wa kan ta abu mai sauki ta ci kana ta koma ta
kwanta dan sosai ta ke jin zazzaɓi yana rufe ta.

Ko da Aliyu ya sake zuwa duba ta, ya tarar tana barci dan haka bai tashe ta ba, dan
bai son katsai mata barcinta.

Washegari ma da kyar ta tashi ta yi abunda ya kamata, kana ta koma ta kwanta,,,


yanzun kam sosai ta dan ji jikinta na mata ciwo.
Cikin wanan halin ta ji wayarta tana ringing, a hankali ta daga wayar tare da duba
mai kiran, Kausar ta gani a rubuce dan haka ba ta ɓata lokaci wurin ɗagawa ba.
amma tana d'agawa wayar ta tsinke ma'ana flashing ne.

Ganin haka ne ya sa ta bin kiran, bayan sun gaisa ne ta ke gaya ma ta yau za su zo.

Duk da bata jin daɗin jikinta sosai ta nuna farin cikin ta, da haka suka yi sallama
da nufin sai sun zo anjima.

P.12

Cikin wanan yanayin ya shigo ya same ta. Bayan sun gaisa har ya ke tambayar ta me
ya ke damun ta. "Me ya ke damun ki ne haka jikin ki da zafi?" "Hmm babu kawai
zazzab'i ne kuma ma na samu sauk'i yanzu alhamdulilah." Sannu why baki fada min ba
kin sha magani?"

"Eh na sha magani yanzu da sauk'i kawai ciwon kai ne da nake ji shi ma zan dena ji
zuwa anjuma." "ok tunda haka ki ka ce Allah ya k'ara sauk'i.

Da ga haka ya mik'e tsaye. "to ni zan fita sai na dawo, kina buk'atar wani abu ne?"
"a'a bana buk'atar komai a yanzu, sai su Kausar da muka yi waya da ita d'azu wai za
su zo yau." ok da ga haka ya sa hannu a aljuhunsa tare da cire kud'i, dubu goma ya
irga ya ba ta. "ga wanan ki ba su in sun zo." "to angode ta sa hannu ta amsa kud'in
tare da irga wa ko ya cika. "Na tafi sai na dawo zan fada wa Aisha za ta ka mu ku
abinci tunda ba kya jin dad'i ba za ki iya musu girki ba, ko za ki iya ne?"

a'a bazan iya ba gaba d'aya jiki na ciwo ya ke." Ok kar ki damu za a kawo muku
abinci. sai na dawo daga haka ya bar part din na ta.

******

AISHA.

Yau ma kamar kullun tun safe ta tashi ta yi aiyukan ta tare da yi musu breakfast.
Bayan sun gama karya, ya shirya zai fita ta raka shi har bakin k'ofa tare da yi
Mishi adu'a kana ta koma ciki.

Ko bayan ta koma kitchen ta shiga tare da bud'e freezer ragowar nama da ya rage ta
d'auka, kwano ta dauka tare da saka Naman a ciki kana da aji cikin sink tare bud'e
masa tape.

dan ta na son ya dan sake. Daga nan kuma ta soma had'a kayan miyar ta dan ta na son
ta yi miyar har da na dare ba sai ta k'ara wani girkin ba kawai shinkafa kawai za
ta dafa musu,nan ta soma aikin ta ba wasa.

Tana cikin girkin ne ta ji ringing din wayarta, Amma ko kafin ta wanke hannunta ta
dau wayar ta tsinke.

Kawai sai ta cigaba da abunda ta ke har ta hada miyar ta ta gama ta gyara kitchen
din ta yi mopping floor din kana ta dau wayar tare da kulle kitchen din ta kana ta
haura sama abunta.

Koda ta shiga d'aki toilet ta Shiga ta k'ara wanka dan gaba d'aya jikin ta sai
k'aurin girki.

Lotion ta shafa tare da Saka turaruka masu kamshin kana ta sa ka kaya mara nawi, ta
dan jara fuskar ta da dan power da lips gloss.
Kwanciya ta yi abun ta kan gado kana ta dau wayarta da nufin bin bayan k'iran da
aka ma ta dazu.

Ko da ta bud'e gani tayi ashe ma Aliyu ne ya k'ira. tana k'ok'ran kiran shi kenan
sai ta ga ashe ya ma tura ma ta text massage dan haka ba b'ata lokaci ta bud'e
sak'on nasa.

"Hi wifey na k'ira ki baki d'aga ba, dama ina son fad'a miki kiyi abincin dayawa
dan yau za ku yi bak'i kuma k'anwar ki ba ta da lafiya so kiyi girkin har da su."

dogon tsaki taja tare da furta. "Aikin banza, bazan dafa ba in baza ta iya girka
musu to su zauna da yunwa Kar Allah yasa su ci abinci.

Ko su wa ma za su zo ma ta oho daga haka ta ta tashe tare da sauka k'asa ta ta rufe


k'ofar part din ta kana ta haura sama abun ta in ga ta inda za ku samu damar shiga
part din har ma ku samu hanyar shige min kitchen din ai, ma yunwa ta kawai daga
haka ta koma d'aki tare da kwanciya.

Bacci ta ke son yi dan gaba d'aya a gajiye ta ke, har ta fara bacci sai ta farka
kamar wace ta tuna da wani abu ta dau wayar tare kashe ta ma gaba d'aya, kar in sun
zo ba ta bud'e musu k'ofar ya k'ira ta dan haka wayar ma ta kashe ta gaba d'aya.
Kana ta koma bacci abun ta hankali kwance.

*******

BALKISU.

Sai murna da zumud'i ta ke ba wanda ba ta fad'a ma ba za ta k'ara aure after so


many years, jibi za a zo tambaya kuma suna son a gama ko mai nan da sati daya.

Alhaji Hakim badamasi za ta aura. Wanda shima a nan Kano ya ke tare da matayin sa
biyu zainabu da zhura. yana da y'aya bakwai hudu mata uku maza. Alhaji Hakim dan
kasuwa ne yana da manya manyan shaguna a ka kasuwa ba abunda baya siyar wa.

Alhaji Hakim ba Yaro bane babban mutum ne wanda a k'alla zai kai shakara hamsin da
biyu, amma sam shakarun sa basu nuna ba dan yana da k'arfin sa kamar dan shakara
arbain.

baya wasa da lafiyar jikin shi kusan kullum ya ke zuwa wurin motsa jiki, da kuma
cin mai kyau ba shi da damuwar ko mai sai ta matayin sa da su ka k'i zaman lafiya a
gidan.

kishi ake a gidan ba na wasa ba, gasa su ke a tsakanin su fitina da tashin hankali
a nan ya k'are.

Wanda kuma Dalilin da yasa zai k'ara aure dan samun kwanciyar hankali.

Alhaji Hakim badamasi su biyu ne kacal a wurin iyayen su. Wanda tun suna yara
iyayensu suka rasu sana diyyar gobara da ta kama gidan su.

Shine babba sai kuma k'anin sa mujahid wanda a yanzu haka baya ma k'asar, yana
Japan a can ya ke karatu wanda ya riga da ya gama ma Amma ya k'i zuwa k'asar shi ta
gado.

Kusan kullun-kullun su ke magana d'aya da yayan nashi akan ya zo Nigeria Amma


Kalmar d'aya ce, zan dawo in lokaci yayi.

sun had'u da Balkisu a wani restaurant ne da suka tafi da kawayen ta, Wanda a
lokacin shima ya kasan ce yana wurin.
ganin farko da ya yi mata ya ji ta tafi da imanin sa, dan balkisu ta na da kyau ba
lefi Allah ya yi mata baiwar kyau da kuma dire ma sha Allah za mu ce dan komai ya
ji.

Tunda suka shiga wurin hankalin shi na kan ta har aka kawo musu ordern su suka fara
ci, koda suka gama sun zo biyan kud'in an ce musu an riga an biya musu wanda haka
ya yi ma tuk'ar ba su mamaki.

Koda suka fita kowa ya kama hanyar gidan su wanda su ke da abunda zasu yi sun tafi
ita ma gida ta nufa.

a hankali ya ke bin bayan ta har sai da ya ga gidan da ta shiga ya kuma tabbatar


wanan ne gidan su tukunna ya juya kan motarsa ya koma da nufin zai zo wani lokacin
dan yanzu a na jiran shi akwai abunda ke gaban sa.

Haka kuwa aka yi bayan kwana biyu yazo gidan su, ya ce ayi mishi sallama da
yarinyar gidan nan. "to alhaji wace a cikin su?" Shuru yayi na dan wani lokaci dan
gaba d'aya bai san mai zai ce shi da ko sunan ta bai sani ba.

Can dai ya gyara muryarsa kana ya fara Mishi bayani ta yanda me gadin gidan zai
gane.

"Na gane ta alhaji Balkisu kake nufi lallai ta na gida bara na k'ira ta daga haka
ya shiga cikin gidan nasu.

Kusan minti goma sai ga Iro da Balkisu tafe a bayan sa. "Yauwa alhaji ga ta nan."
Ok ya ce daga haka ya sa hannun sa a aljuhu bai san ko nawa bane kawai ya mik'e mai
ga wanan Baba a siya yara biscuit."

K'arba ya yi tare da yi mai godiya kana ya ba su wuri dan su zan ta.

Bayan sun gaisa ya gabatar mata da abunda ke zuciyarsa babu kwana-kwana dan shi ba
Yaro ba ne, da zai tsaya ya b'ata lokacin sa ba.

Dan haka ya fada mata k'udinrin shi na auren ta wanda kuma in ta amince baya son a
dau lokaci.

Ita ma sosai ya ma ta, musamman ma ta yanda ya fada mata abunda ya kawo shi ba wani
b'ata lokaci dan haka taji ta amin ce da shi Amma ba ta nuna mishi ba, kawai tace
za ta yi Tunani nan suka yi exchange din number daga haka suka rabu da nufin duk
shawarar da ta yanke za ta k'ira shi.

Kamar yanda ya ce, bayan kwana biyu ya k'ira ta bayan sun gaisa ya ke tambayar wa
ce shawara ta yanke?" "na amince Allah ya nuna mana ranar." " kai alhamdulilah na
ji d'ad'in amince war ki Allah ya sanya wa lamarin albarka." "Amma gaskiya ni ba
budurwa bace kamar yanda ka ke tunani, na tab'a aure." "ai kar ki damu na riga da
na san da haka tunda saida na yi bincike kafin nazo wurin ki, kuma alhamdulilah ke
ma baki boye min ba hakan na nufin ba yaudara ta ki ke ba."

tun daga wanan suka fara sabawa sama-sama har suka shak'u sosai wanda a yanzu ko wa
na yaushe zai mallaki dan uwan sa.

Wanan shine asalin Hakim da kuma silar haduwar sa da Balkisu har suka k'ulla
soyayyar su.

Cigaban labari.
P. 13

HUSNA.

Sai kusan k'arfe 12 da wani abu bak'in na ta su ka iso. A lokacin ta d'an samu
sauk'i har ta samu ta fita falo. duk minti sai ta duba agogo ganin har yanzu babu
su babu d'uriyar su ne yasa ta d'au wayarta tare da dailing din numbern Kausar din
Amma sai ta ji shi a rufe.

nan ta fara tunanin ko sun fasa zuwan ne tunda har yanzu ba su zo kuma ga wayar
Kausar ma ba ta shiga.

Ko gama tunanin ba ta yi ba ta soma jin hayaniyar su tun kafin ma su iso part din
na ta dan haka da sauri ta sauka da ga kan kujerar tare da zuwa bakin k'ofar.

Bud'e musu tayi kana ta tsaya a bakin k'ofar tana mai jiran isowar su.

tana ganin su ta ruga da gudu ta rungumi Kausar da ita ma ta rungume ta sai murna
su ke kamar wanda su ka yi shakara ba su had'u ba, bayan sun janye jikin su ne suka
soma gaisa wa kana ta juyo kan k'annenta maza ma su ka gaisa.

"Ku shigo ciki mana ya kuka tsaya a nan?"

Nan suka shiga tare da barbajewa a falon, sai kalle-kalle da su ke cikin falon, yau
ce ranar su ta farko a gidan na ta tunda aka yi auren ba su zo ba.

Sai Kausar da aka kawo amarya da ita, duk da ita ma ba ta wani k'are ma gidan kallo
lokacin da suka kawo ta Dalilin abunda ya faru ranar so basu samu wanan damar ba
sai yau da Allah ya kawo su.

Kitchen ta shiga tare da kawo musu ruwa da drinks sai kuma dan snacks da ba za'a
raba amarya da shi ba.

Ai ko ba b'ata lokaci suka fara loda wa cikin su dan dama da yunwar su suka zo dama
ba wani karin kirki suka yi ba dan koko ne da suka sha da safe wanda ko sugar ma
bai ji sosai ba sai dan ragowar d'umamin tuwon jiya da ya rage.

Nan da nan suka gama da snacks din kana suka sauk'e da drink din nan suka soma hira
abunsu ga TV da AC duk an bud'e musu.

Can dai su Haidar wai su za su je wurin Aisha. "a'a ku zauna an jima sai mu tafi
gaba d'aya mu."in ji Kausar.

"a'a mu yanzu mu ke son zuwa." "no Haidar ku bari anjuma za mu je k'arban abinci
sai mu tafi tare kun ji?"

"to kawai suka ce ba dan son so ba da ga haka suka cigaba da kallon su.

"Yaya ina da tambaya?" in ji Kausar.

"yi tambayar ki mai ya faru?"

"a'a naji kin ce zamu je karb'an abinci ne to shine nake tunanin dama ba kya girki
sai in ita ta ka miki?

d'an tab'e baki ta yi kana ta ce. "no kowa na girkin shi da kanshi kinsan farko-
farko ya ce duk mai girki ita za ta yi yanda kowo zai ci. to dai ita ta ke yi sai
shakaran jiya da ya ce wai ni in dafa saboda bata jin dad'i."
"Chab lallai, ko da yake ke ki ka ja wa kan ki, tunda ki ka ce sai mijin Yayar ki.
Amma kuma an yi bala'in rena miki hankali fa."

"Hmmm baki san wani abu ma ba sai na fad'a miki wanan abincin da na dafa na kai
musu ba su ko tab'a shi ba ma,

Ka min shi har nan falo aka yi duk da bansan ko waye a cikin su ba Amma ba su ko
tab'a ba."

"to ba zan dai yi magana ba tunda ko me ki ka gani ke ki ka ja wa kan ki, kin biye
wa hud'ubar Baba kun ci Amana gashi yanzu tun ba a je ko ina ba ki ke ganin
matsaloli. Nikam dan Allah kar mu yi biyu babu kar ki yi abunda zai sa ya sake ki
dan wallahi bazan yafe miki ba, baza ku hana mana jin dad'i ba duk abunda a ka miki
kiyi hak'uri dan an ce rayuwar aure sai hak'uri balle ke da ki ke auren mijin
wata."

"Kausar ni ki ke gayawa magana haka to ba zan yi hak'uri ba, in dai an min ba dai-
dai ba sai nayi magana haka kawai na zauna ciwon hak'uri ya kashe ni wato ga
mar'atul saliha. Kuma da ki ke cewa mijin wata na aure din dan ita kad'ai a ka
haife shi da bazan aure shi ba, yanda ya ke mijinta to same goes for me miji na ne
nan gani nan bari."

"to Hajjiya me ya faru da ki ke wani tada jijiyar wuya haka, daga fad'an gaskiya
sai ki zo kina wani ta da jijiyar wuya, ke karan kan ki kinsan abunda ku ka yi bai
da ce ba duk da ba wai lefi ne a wurin Allah Amma ai ana barin halak dan kunya ni
fa kawai kallon ku na ke, dan dai kawai ban yi magana ba ne.

dan ma kun had'u da auntie Aisha mai tsoran Allah ce da kuma hak'uri da ba dan haka
ba da yanzu sunanki sorry wallahi sai tayi yanda tayi ta cire ki a gidan.

Dan haka dama nazo ne dan na fad'a miki gaskiya kar ki biye wa Baba dan za ta kai
ki ne ta baro ki, gashi yanzu kin biye mata kun b'ata mana zuminci tunda dai
k'addara ta gifta an yi auren dan Allah na rok'e ki kar ki biye wa maganar Baba ku
zauna lafiya.

dan na ga ita kam ta yi nisa ba ta jin k'ira yanzu sani ya rage na ki da ki ji da


kar ki ji nikam na fad'i na wa."

Daga haka ta dau hijab d'in ta tare barin falon, "Abba zo mu tafi wurin auntie mu
gaishe ta."

Haka suka tafi suka bar ta baki bud'e dan ta ma rasa me za ta ce.

Yes ta sani abunda Kausar ta fad'a ma ta gaskiya ne dan ko ita aka ma wanan cin
amanar sai ta yi yanda za ta yi duk inda za ta shiga sai tashiga dan ta ga wanan
auren bai ji ko ina ba, Amma kuma abun tambayar a nan shine za ta iya abunda Kausar
ta fad'a ma ta dan ita fa har yanzu ta na zargin Aisha akwai abunda ta ke shirya ma
ta dan shurun nan da ta ma ta da akwai wata a k'asa.

Ita ma ba za ta zuba ido haka kawai ba a tsammace ta gwara ta zauna da Shirin ta.

******

Su kuwa suna isa part din Aisha su ka tarar k'ofar a kulle, k'onk'sa k'ofar su ke
Amma ba alamun za a bud'e dan haka sun yi tunanin ko ba ta nan dan haka sun kama
hanyar koma part din Kausar sai kawai suka ji ana k'ok'rin bud'e k'ofar dan haka su
ka tsaya.
Bangaren Aisha kuwa bayan ta tashi daga bacci ta shiga toilet ta yi uzirin ta ta
fita k'asa ta sauk'a tare da shiga kitchen tea ta had'a mai kauri tare da had'awa
da cake kana ta fita falon. Zama tayi kan d'aya daga cikin kujerun falon kana ta
soma ci abin ta.

Ko minti goma da zama ba tayi ba taji ana knocking din k'ofar falon na ta tana jin
su lokacin da su ke magana ko b'ata nan ne. dan bata yi niyyar bud'e musu k'ofar ba
Amma da da ta yi tunanin ba a biye wa mutum kar abunda ke tsakanin ta da Husna ya
shafi kowa na ta ne yasa ta tashiwa tare da nufan k'ofa. tana jin lokacin da su ke
k'ok'rin bar wurin.

dan haka ba ta b'ata lokaci wurin bud'e k'ofar ba, tana bud'ewa ta ga ashe su
Kausar ne. "Ohh! Ku ne yaushe ku ka zo?" "ina wuni auntie eh mune fa dazu maka zo
ba mu d'ade da zuwa." "Ok to ku shigo mana ya ku ka tsaya a nan." daga haka ta
matsa musu.

bayan sun shiga ta kulle k'ofar kana ta koma falon wurin su suka gaisa kana ta ka
mu su ruwa daga haka kowa ya yi shuru sai dan kallo da su ka yi.

Ganin ba yanzu za su koma ba ne yasa ta shiga kitchen tare da dafa musu taliya kan
jar miyar da ta dafa d'azu. Bayan ta gama ta zuba musu kan tire kana ta ka musu.

Yaran kam sun ci Amma Kausar ta k'i ci wai a k'oshe ta ke bayan ba haka bane, kawai
tsora da fargaba ne ke turmurmursar ta, gane ta ke kamar Aisha za ta rufe ta da
duka gaba d'aya jin ta ta ke a kure ta ke.

Bayan Yaran sun gama sun kai tiren kitchen sun wanke hannayen su sun sha ruwa suka
zo falon da zama.

Kausar ce ta tashi tare da cewa. "auntie mu za mu tafi dama mun ce b'ara mu shigo
mu gaisa ne.

"to na gode ku gaida Baba in kun koma gida."

"to za ta ji! daga haka su ka bar part din ta.

P.14

Koda suka koma samun ta suka yi a nan falon dan tun tafiyar su ba in da ta motsa ta
nan zaune.

nan suka barbaje a falon su na hira, da lokacin sallahn azzahar ya yi tashiwa suka
ji suka yi.

Daga haka kuma suka soma jiran abincin da za a ka musu shuru-shuru har kusan k'arfe
2 da rabi ba su ga abinci ba hakan ne ya sa Husna fita zuwa part din Aisha dan
karb'an abincin na su.

Koda ta isa tarar ta yi part din a kulle dan haka ta hau knocking d'in k'ofar Amma
Shuru ko motsin mutum ba ta ji ba balle a ce za a bud'e k'ofar.

Hakan ne ya sa ta k'ara k'arfin bugun dan a na ta tunanin ko Aisha ba ta ji ba ne


shi yasa.

A bangaren Aisha kuwa tun ma kafin ta iso part d'in na ta ta gan ta, ta saman
window.

Ta dan tsaya a bakin window dan viewing d'in compound d'in gidan, ta na jin ta Amma
ta yi burus da ita dan ta ga abun na su ya fara wuce gona da iri wanan ai har da
renin hankali.

Ganin ba ta bud'e ba ne ya sa ta koma wa part d'in ta a tunanin ta wai ko ba ta nan


ne dan kwata-kwata ba ta kawo tana nan kawai ba ta ga damar bud'e ma ta k'ofar ba
ne.

ko da ta shiga part d'in ta wayarta ta d'auka tare da tura mishi text massage kan
cewa sun je karb'an abinci amma Aisha ba ta nan dan sun ta k'wank'asa ma ta k'ofar
ba ta bud'e ba alamun ba ta nan.

Tana aika sak'on ta aje wayar tare da shiga kitchen din domin dafa musu abinci dan
baza su zauna da yunwa ba.

Tana cikin yi ne Kausar ma ta biyo ta kitchen din nan suka cigaba da girkin a tare
su na hira su na girki haka har su ka gama girkin su.

Bayan sun gama sun zuba wa yaran na su a tire." Dauda zo ku dau abincin ku." Daga
haka su ma suka zuba nasu kana su ka koma falo, nan su ka soma cin na su su ma.

Bayan sun gama sun gyara wurin tare da kai kwanikan tare da wanke su,kana su ka
koma falon tare da sa ka ma yaran abunda su ke so a TV din su kuma su ka wuce
bedroom d'inta.

Ko da su ka shiga d'akin direct kan gadon su ka fada. "Kai Yaya kin ji yanda gadon
nan ya ke da laushi kamar auduga?" Wallahi kin ji d'ad'in ki irin wanan jin dad'i
haka, waiyyo! Allah mu ma kaba mu miji na gari kuma mai kud'i mu yi auren nan mu
huta."

Dariya kawai Husna ta yi dan ita kam ba wani sabon abu bane a wurin ta.

"Ke kin fiya k'auyanci wallahi, mutum ba zai iya fita da ke anguwa ba sai ki ba shi
kunya Allah."

"Kai ai dole na yi k'auyanci abun da babu a house, shi yasa ai na ke adu'ar Allah
ya kawo min miji Mai kud'i nima in more rayuwa wallahi na gaji da talaucin nan
kullun mu babu cigaba sai ci baya."

"Bar ni da kayan takaici, ni ba wanan ba bara na baki wa an nan kayan ki kai wa


Baba."

Daga haka ta bud'e a kwatin ta tare da cire a tanfofi uku ta mi k'a ma ta ki kai ma
ta zamu yi magana da ita." Karb'a tayi ba tare da ta ce ko uffan ba dan ta San sa
rai mai za a yi da su wato duk maganar da ta fad'a ma ta d'azu bai shiga kunen ta
ba, ai sai suyi ba za ta sake mu su magana ba.

Husna kam ba ta ma san me ta ke sak'a wa ba dan abunda ke gaban ta kawai ta ke,


bud'e wondrope ta yi tare da fito da wa ta wrist watch mai tsada ta mik'a ma ta.
"Ga wanan ki b'oye kar wanda ya gani, shima ki kai ma ta shima duk zan ma ta baya
ni a waya kinji?"

"Eh!to amma Yaya ina ki ka samu wannan agogon dan da gani ma zai tsada kin ga yanda
sai shining ya ke, Ni kam gaskiya zan dauka dan ya min kyau."

Dan uban ki ni ce banga kyawun sa ba a ka gaya miki, ba na wa ba ne na Aliyu ne


wallahi in ki ka kuskura ki ka barshi ya gani to ki san abunda za ki fad'a me."

"To na shi ne za ki bani in kai wa Baba yanzu har da wanan tsadadiyar wrist watch
din nan ku ke son sa ka a kasuwar kin san ko na wa za ta kai?"
"To uwar shishigi wa ya sa da ke ina ruwan ki ko shi da kan sa zan sa a kasuwa,
sak'o na ba ki ki kai ma ta."

"To na yi shuru amma Yaya ta ya a ka yi ki ka saci wanan kuma bai gane...

Shuru tayi ganin harar da ta ke zabga ma ta.

Kiyi hak'uri ba sata na ke nufi ba ai abun mijin ki ne ko kin d'auka ba sata ba


ne."

"Tsakiii ta ja kana ta soma magana kamar haka. "Ranan ya shigo da ita nan d'aki na
so da zai alwala zai tafi masallaci ne sai ya cire ya a je a nan kafin ya shiga
toilet din, to sai na yi anfani da wanan damar na d'aura hijabi na a kai to Allah
ya rufa asire ko da ya fita bai tuna da ita ba ya tafi masallaci. Bayan fitar sa
kuma na d'auke ta tare da b'oye abina sai bayan kwana biyu ne ya ke tambaya ta wai
ya bar agogan shi a nan ni kuma na ce ban gan ta ba to in takaice miki magana tare
muka baza ma nema ta. A k'arshe dai na sa shi tunanin ko ya bar ta a bangaren
Auntie Aisha ko kuma ta fad'i ba tare da sanin sa ba."

Kausar ai ba ta san lokacin da ta fashe da dariya ba."shegiya wato har da ke a aka


baza ma neman ta Amma ke muguwa ce, wanan abar da gani sabuwa ce ba za ki bar bawon
Allah nan ya dan more abar sa ba ki ka sa shi hasara haka yanzu shi d'auka yayi
fad'uwa ta yi?"

"Eh fa ko shakaran jiya nan ma ya mun maganar ta wai sau biyu kacal ya tab'a sa ta,
kuma wai kusan dubu d'are da wani abu ya siye ta. Haka nan na dinga bashi hak'uri.

"Kuma bai gane k'arya ki ka mishi ba, ko da ya ke ta ya zai gane ko da can da ki ke


musu yan tsince-tsince ai ba sa gane wa balle yanzu da ke ma ki ka zama yar gidan."

Ni fa har mamaki ki ke bane wallahi ta yanda duk satar da ki ke yi ba a tab'a ka ma


ki ba, ni kin san ranar mu ka tafi gidan Alhaji Musa d'iban ruwa in baki labari,
tun sawun farko na ga wayar nan amma ban tab'a ba sai a sawun uku da banga ko wa ba
sai kawai na yi sama da ita na sa a cikin riga ta zan wuce to ashe Idris wanan
babban d'an su nan ya ga lokacin da na d'auke wayar, Amma bai mun magana ba sai da
na zo fita ya tsayar da ni wai ki ka wo wayar da kika d'auka na ce ni ban d'auka ba
ai in baki labari wanan mugun sa wa yi Yara su hau bishiya su tsonko mai reshe to
da na ga haka ba sai in bashi in gudu ba, Amma sai na tsaya sabon taurin kai. Ke
kin ga dukan da ya yi min kuwa wallahi har da fisari sai da na yi a jiki kuma ya sa
Yara yi min wak'ar baruuniya tun da ga ranar wallahi na din ga tsoran sa ta wallahi
duk da ba wai na dena ta bane amm ina tsoran a kama ni. Ko dazu da muka shiga wurin
Auntie Aisha ko wallahi na ga irin wanan abun nan da ake sa a kunne kamar earpiece
Amma shi bashi da wire nan kawai sa wa za ka yi sai ka yi connecting da wayar ka
ban san sunan shi."

"Eh na gane shi nima ban san sunan shi ba."

"Yauwa shi na gani wallahi har na d'auke ta fa amma tsoro ya sa na mai da ta."

"Waiyyo Allah ciki na, Kausar ke ce ki ke cewa kina tsoro?" yaushe ki ka ko yi


tsoro ban sani ba."

"Lallai ni yanzu fa satan nan ba ko ina nake yin ta ba fa tun da na sha dukan nan
ba ko ina na ke yi ba, kinsan abunda ya bi jinin ka dena wan sa zai yi wuya. Balle
ma Auntie Aisha ni gaba d'aya ma tsoran ta na ke ji tun lokacin da mu ke k'ana na
na tab'a yi ma ta rashin kunya ta fasa min baki to tun lokacin na ke tsoran ta bana
ma son abunda zai k'ara had'a mu har ta k'ara min wani illa.

P.15
Haka dai suka cigaba da hirar har k'arfe 4 ya yi suka tashi dan azamar sallah. To
bayan sun yi sallah sun gama ne, Husna ta ja Kausar kitchen. Ko da suka shiga
kitchen bud'e canta tayi tare da d'auko babban foli bag kana ta maida ta rufe daga
haka kuma su ka shiga store din kayan abinci.

Shinkafa ta fara auna wa kana ta zuba a cikin wanan ledan daga haka kuma sai ta ja
jarkan mai da manja ta zuba musu a robobin Eva da suka sha.

Daga nan kuma suka koma kan kayan miya ma, Maggie onga albasa da dai sauran spices
na abinci.

Komai ta hada musu har da taliya da indomie wanda ledan ma ya cika ba inda wasu
kayan zasu shiga, sai da suka aika a aka ka musu Bako.

Daga haka suka koma falon dan a lokacin har k'arfe 5 da wani abu ma ta yi, hakan ne
yasa su haramar tafiya gida. Koda suka shirya suka fita harabar gidan, Hamza
drivern gidan ya zo wurin su tare da gaishe su dan. "Yauwa Hamza dan Allah ka d'an
temaka musu da kayan nan su fita waje kafin su samu napep." "Ai Hajjiya k'arama mai
gida ya ce a mai da su in za su koma."

"Yauwa an zo gidan sauk'i ma, ga wannan ka d'an taya mu rik'e wa." "To Hajjiya."
Daga haka ya ta ya su d'aukan kayan har mota boot ya bud'e tare da saka kayan gaba
d'aya a ciki kawai abunda bai sa ba sai ledan da ke hannun Kausar wanda ba komai ne
a ciki ila wa a na nan kayan da Husna ta ba ta dazu a d'aki agogon kuma ta sa
handbag d'in ta.

Bayan ya kammala sa ka kayan ne ya bud'e wa mazan murfin baya suka shiga tare da yi
wa Husna bye bye, kana ya bud'e ma Kausar murfin gaba.

Sai da suka k'ara gaisa wa tukunna ta shiga motar ita ma tare da d'aga wa Husna
hannu da nufin za su yi waya.

Haka Hamza ya tayar da motor su ka bar harabar gidan, Ta na d'aga musu hannu har
sai da ta ga fitowar su.

Koda su ka koma ba ta shiga ciki ba sai ma zagaye gidan da ta soma yi dan tunda aka
kawo ta gidan a matsayin matar gidan, to ba ta fita bai sai yau koda ta ke fita
zuwa part din Aisha ne ta ke zuwa amma ba zagaye compound.

Tana cikin wannan zagaye-zagayen ne har ta hange Aisha da ke zauna a kan kujera
k'afa d'aya na kan d'aya sai kuma d'an madaidai cin table da ke gabanta wanda robar
5alive ne da dambun nama a kai.

Bak'ar Abaya ce a jikin ta zuben yan dubai mai ratsin gold ta Saman rigar sai kuma
mayafin da ta yi rolling d'in shi, sai d'an makeup da ta d'an yi sama-sama a fuskar
ta. Ma sha Allah kawai za a ce dan ba wanda zai ga Aisha ya yi tunanin ta kai
shakara 30 ba, d'auka za a yi irin ba ta wuce shakara 20 ko 22 ba.

Sabon ta bud'e baki tana kallon ta har ba ta san sanda Aisha ta d'ago da kanta suka
had'a idanu, wanda sai a lokacin ta farga da abunda ta yi ji ta yi kamar k'asa ta
tsak'e ta shiga ciki, da irin wannan abun kunyar. Ganin ta zura mata idanuwan nan
ta masu kaifi ne ya sa ta nad'e taburmar kunya da cewa. "Ina wuni Auntie dama na
raka su Kausar ne shine na ce bari na d'an zaga na d'an sha iska." Ta fad'i haka ne
tare da d'an sosa gefin wiyar ta alamun mara gaskiya.

"Hmmm hakan ya yi kyau daga haka ta ce gaba da latsa wayarta tare da saka hannunta
a plate d'in dambun nama ta na kai wa baki tare da tauna wa a hankali.
Ganin ba ta nuna ma ta wa ta alama na rashin mutunci ne yasa ta d'auke d'ayar
kujerar tare zama a kai.

Kusan minti goma su ke zaune a haka ba umm balle uuhhm-uuhhm, Aisha kam ko a jikin
ta dan sai ma latsa wayar ta da ta ke yi tare da cin dambun ta tare da sauk'e wa da
juice din ta mai sanyi hankali kwance.

A kasin haka, Kausar gaba d'aya a ta kure ta ke dan tunda ta zauna Aisha ko d'aga
kai ta kalle ta ma ba ta yi ba balle kuma ta ce gashi ke ma ki tab'a.

Ganin babu fuskar a gun Aisha ne yasa ta tashiwa tare da cewa. "Auntie ni zan shiga
daga ciki akwai abunda zanyi."

"To Allah ya cauta daga haka ta maida hankalin ta kan wayarta, ita Husna ta wuce
part d'in ta da haushin Kan.

To haka daddare ma bayan sun gama cin abincin sun koma falo suna hira wanda duk
Husna da Aliyu ne ke hirar Aisha ko kanzil ba ta ce musu ba sai ma kallon TV da ta
ke yi gaba d'aya ma ba ta sauraran hirar su hankalin ta na kan kallon da ta ke yi.

Labarin zuwan su Kausar ta ke bashi daga nan kuma su ka koma kan yan gidan su har
dai suka gangara zuwa na makaranta.

Har k'arfe sha d'aya da wani abu ta nan a part d'in Aisha ba ta koma ba sai hira su
ke ko a jikin ta, hankalin ta da tunanin ta bai ba ta cewa ya kama ta ta koma
sashen ta ba sai ma k'ara zak'iwa da ta ke yi.

Ganin lokaci ya k'ure ne ya sa Aisha tashiwa tare da yi musu sallama kana ta haura
sama abun ta.

Koda ta shiga d'aki toilet ta fara shiga tayi uzurin ta ta fita ta kana ta canja
kaya zuwa na bacci ta shafa ko ina na jikin ta da humra mai k'amshi kana ta haura
gado abun ta.

Sai da ya k'ara kusan minti talatin kana ta shiga d'akin shi ma. Direct toilet
shima ya shiga ya yi wanka da brush ya fita tare da saka pyjamas d'in sa da ya ga a
kan cushin, daga nan ta fesa turarukan kansa masu tsada kana ya haura saman gadon,
sai da ya musu addu'ar bacci kana ya Kashi musu wutar d'aki.

Daga nan kuma sai mu ce asuba ta gari Alhaji Aliyu na Aisha angon Husna.....

Haka bangaren Husna ma bayan koma war ta part d'in ta yi shirin bacci ta hau gadon
ta kana ta dau wayar ta tare da hawa online nan fa ta soma chatting, ba ita ta yi
bacci ba sai kusan k'arfe 4 na dare ta yi bacci wanda kuma ya ta yi lattin tashiwa
sallahn asuba duk da Aliyu ya zo har cikin d'akin ta ya tayar da ita. Amma yana
fita ta koma bacci ba ta re da ta tashi tayi sallah ba.

Sai kusan k'arfe 9:30 ta tashi a dan firgice, ganin rana tar kamar rana ne yasa ta
tashiwa sama da wuri."inna lilahi." Daga haka tayi azamar shiga toilet sai da tayi
wanka tayi alwala kana ta fito d'akin.

Nan ta shinfid'a darduma kana ta kabbara sallah. Bayan ta idar ta tashi tare da
saka kaya kana ta dau wayar ta ta fita da d'akin shi koma falon nan ta soma gyara
shi duk da ba wani datti ya yi sosai na. Tana cikin gyran ne ta ji wayar ta rurin
wayarta dan haka ta a je pillow case da ta ke gyara ta d'aga wayar tare da d'aura a
kunnin ta.
"To ina zuwa." daga haka ta sauke wayar tare da shiga d'aki ta dau hijab d'in ta
kana ta bar part din na ta.

Ko da ta isa tarar da su a dinning area dan haka can wuce tare da gaida su wanda
Aliyu kad'a ya amsa ma ta, Aisha yi tayi kamar ba ta ji ta ba sai ma fara sarving
din Aliyu kana ta yi wa kan tq daga haka ta a je sarving spoon din ta fara cin
abincin ta.

"Inna na Husna?" Ya baki zuba ma ta ba?"

"Tana da hannu ai za ta iya zubawa da kan ta."

"Kamar ya ta na da hannu ni nace miki ba ta da hannu ne?"

"Ah a kamar ya baka hannun ta ba, na man ta ne ban zuba ma ta ba ba shi kenan ba ai
ita ma da hannun ta sai ta zuba ai tun da ba yarinya ba ce ta san ciwon kan ta ta
tunda har kwana ta ke amsa." "Aisha wai maiya...

"Oh! na fad'a maka bana jin dad'i amma I don't know why ka ke son k'ara min ciwon
kai, ba abincin ba ne zan zuba ma ta me a ciki da ga haka ta yi k'ok'rin tashiwa
dan zuba ma ta.

"A'a ki bar shi za ta zuba da kan ta, na man ta ni sorry.

P.16

"No ki barshi za ta zuba da kanta. Ya yi maganar ne tare da fuskantar Husna. Kai ta


kad'a mai dan ita ba wani abu ba ne dan ba'a ayi serving da ita ba.

Daga haka kowa ya soma cin abincin sa ba ka jin komai sai k'arar cokula. Bayan sun
kammala Aisha tattara kwanikan ta kai su kitchen tare da wanke su. Koda ta fita
tarar tayi har sun bar dinning din sun koma falo kuma da gani akwai abunda suke
tattauna wa, hakan ne yasa ta ba ta tsaya a nan ba ta haura sama abun ta.

Su kuwa ko da suka koma falon da zama hira suka soma jefi-jefi wanda a cikin hirar
ne ta ke tambayar shi ta na buk'atar kud'i za ta je saloon.

Shuru ya yi na d'an wani lokacin kana ya ce." Yaushe ki ke son tafiya?" "Da wai yau
na ke son zuwa amma ban sani ba ko ka na da kud'in."

"Ok kawai ya ce daga haka bai sa ke yin magana ba sai ma tashiwa da ya yi ya haura
sama. Koda ya shiga d'akinsa bud'e bedside drawer ya yi wanda a nan ya ke aje wasu
kud'aden saboda hididdumun gida da sauran su. Dubu 20 ya k'irga tare da sakawa a
aljihu kana ya maida sauran tare da kulle drawer.

Koda ya sauka bai same ta a nan ba hakan ne yasa shi nufan part d'in ta.

******

Husna kuwa ganin bai ce mata komai ba sai ma haura wa sama da ya yi ne ya sa ta


tunanin ko bai amince ba ne.

Ganin haka ne ya ta barin part din na su.

Koda ta koma part d'in ta a falo ta zauna abun ta tare da had'a hannayen ta biyu ta
yi tagumi. Ita kam gaskiya ta fara gajiya da zaman gidan nan wallahi ace tun safe
har dare kai kad'ai ba mai ta ya ka hira sai wayar ka ko TV in kuma miji ba ya tare
da kai kuma haka za ka zauna, sai taji ma da ma ba ta yi auren ba ma da yanzu tana
da freedom. Amma kuma da ta yi tuna cewa yanzu fa ba kamar da ba ne, anything tana
buk'tar yan kud'ade ta na magana za ta samu. Amma da fa ba ta isa ta rik'e dubu
d'aya ma Aisha sai ta sa ta a gaba da tambayoye ina ta samu wa ya ba ta. Ba abunda
za ta ce sai hamdallah.

Ganin tunani-tunani ba zai kai ta ko ina ba ne yasa ta dau wayarta tare da shiga
WhatsApp, Ganin ba ta da wani sak'oni ne ya sa ta fita daga nan ta shiga Facebook.

Tana haka ne taji an ture k'ofar tare da shiga ciki. Sanin ko waye ne ya sa ta rufe
Data tare da aje wayar kana ta fuskance sa.

Shi ko koda ya shiga bai wani zauna ba sai ma tambayar ta nawa ne kud'in saloon
d'in. "Nawa za a miki kitson?"

"Nima ban sani ba sai na tafi kuma ya danganci style d'in da za'a min."

"Uhmm ta ga wannan." ya mik'a ma ta dubu biyu.

Karb'a tayi tare da d'an yamutse fuska kana ta ce dubu biyu?" Ba za ta yi ba kuma
har da k'unshi za a min." Bai ce komai ba sai ma k'ara zare dubu uku da ya ba ta. "
ga shi ki had'a ya zama dubu biyar ki san yanda zai ishe ki bani da kud'i gari babu
kudi."

Haka nan ta karb'a ba dan ta so ba dan a gaskiya ta rena dubu biyar d'in nan kawai
ba yanda ta iya ne amma ba ga kud'i ta na gani ba kawai ba ya son cire su ne, Amma
ai ba haka ya ke ba Aisha ba. Ko nawa ta ce ya ba ta ba ta ya ke yi.

Maganar sa ce ta katse mata tuninan da ta shiga. "Hamza zai kai ki kuma ya dawo da
ke a na gama miki ku dawo ba na son yawo." Daga haka ya kama hanyar barin falon.

Ita ma d'aki ta shiga tare da shirya wa kana ta fita harabar gida tare da fad'a ma
Hamza inda zai kai ta wanda dama ya san da fitar ta dan Aliyu ya fad'a Mishi.

******

Shi ko Aliyu koda ya bar part d'in ta part d'in Aisha ya nufa. Koda ya shiga d'aki
tarar ya yi ta na kwance kan coush da ke d'akin tare da waya kan kunnen ta wanda da
gani waya ta ke. Ganin haka ne yasa shi zama a kusa da ita tare da jiran ta gama
wayar.

Ganin ya zauna kusa da ita ne yasa ta katse wayar da nufin za ta kira anjuma.

"Ya kika katse da kin yi wayar ki ai am not in a rush." ya fad'i haka tare da jan
yatsun k'afar ta. "No kar ka damu is not that important."

"Ok tunda haka ki ka ce." daga haka ya sa hannun shi aljihun shi tare da zare dubu
biyar ya mik'a mata. "Ga wannan kud'in kitso da k'unshi na ba Husna ma dubu biyar
ke ma ga na ki." "To na gode Allah ya sa ka da alkhaire ya kuma k'ara Bud'e."

"Amin ya ce dan sosai ya ji dad'in addu'ar da kuma yanda ta nuna ba ta raina na su


ba, duk da da ba haka ya ke ba ta ba amma still ba ta nuna komai kamar yanda Husna
ta nuna.

Kissing d'in forehead d'in ta ya yi tare da mik'e wa tsaye to ni na fita sai na


dawo." "To Allah ya tsare." Daga haka ya fita harabar gidan, har ya isa wurin
motarsa ya bud'e ya shiga zai ta da motar sai ga Hamza da mai gadi sun zo gaida
shi. Bayan sun gaisa ne ya fad'a ma Hamza zai kai Husna anguwa kuma zai dawo da
ita, To! alhaji." Daga haka ya tada motarshi ya bar gidan.

******
Koda suka hau hanya ita ta ke kwatan ta mishi hanyar har suka isa saloon d'in wanda
a nan Aisha ma ta ke zuwa, sanadin ta ne ma ta san wurin tunda nan ta ke zuwa dan
yin kitso da k'unshi da kuma gyaran jiki duk nan ta ke zuwa.

Bayan ta sauka daga motar ne ta ce masa. "zaka iya zuwa uzurin ka in anjuma sai ka
zo ka dauke ni." Daga haka ta yi wuce war ta ciki.

Koda ta shiga bayan sun gaisa da mai shagon har ta ke tambayar ta ina Aisha yau ba
su zo tare ba dan dama tare su ke zuwa. "A'a ba mu zo tare ba." "Ok! Matar tace
daga haka aka nuna ma ta kujera tare da ka ma ta ruwa mai sanyi.

Bayan ta zauna an ka ma ta ruwan ta sha tare da jiran a gama wa wand'an nan matan
da ta zo ta samu a ke musu. Amma abu d'aya da ta lura da shi shine cikin matan nan
akwai wanda kamar ta san ta ko kuma kama ce kawai amman gaskiya wannan kamar ta yi
ya wa, to kodai lubnah ce ta zama haka. Kai no ba ita ba ce lubnah ai ba ta kai
wannan wayewa ba kuma wannan fa da gani yar masu kud'i ce ina lubnah da zuwa irin
wannan waje sai dai in a mafarki. ita take yar talakawa kuma mai auren talaka
futik. Tuna hakan ne yasa ta basar da zancen tare da cigaba da latsa wayarta.

To hakan ce ta ka san ce wurin matar nan ita ma tunda Husna ta shiga ta ke hankal
ce da ita. Minti biyu sai ta kalle Husna ta mudubi Amma b'ata dai yi magana ba. Can
dai da ta kasa hak'uri ta yi magana. " Husna?" Da saure ta d'aga kanta sama tare da
fuskantar tar ta. Ta mudubin su ka k'ara had'a idanu wanda hakan ne ya k'ara
tabbatar wa da ko wanenin su cewa yes lailai abunda suke zargin ne.

"Lubnah dama ke ce?"

"Lallai Husna ni ce kinyi mamakin gani na Kenan?" "Eh gaskiya nayi mamaki na d'auka
ma maybe mai kama da ke ni." "Lallai to ni ce ba mai kama da ni ba ce, to ya kike
gaskiya mun d'ade ba mu had'u ba fa ina ga tun tafiyar ki wurin yayar ki da ki ka
yi shi Kenan ba mu k'ara had'uwa ba." "Gaskiya mun d'ade Amma ai ko bikin ki ma na
zo ko kin man ta ne?" "Oh! Yeah kin zo biki kam to ya kike na ji ke ma wai kinyi
aure?"

Lafiya lau eh na yi aure Amma ai baki zo ba." "Wallahi na so zuwa amma bansa mu
lokaci ba kin san a lokacin bana nan ina Lagos."

Lagos?" Mai ya kai ki can ko dama can kuka koma da mijin ki?"

"Miji?" tun yaushe muka rabo.

P.17

"Miji?" Ai mun rabo tun yaushe."

"Kun rabo yaushe?" "Ke dai bari is a long story ba maganar nan bace yanzu ki ban
numbern ki." "Ok! Daga haka ta amshi wayar lubna k'irar iPhone 15, dan zare
idanuwan ta tayi tare da kad'a kai nan ta sa ma ta numbern ta tare mik'a ma ta
wayarta. Sai da tayi dailing d'in numbern ta ga ya shiga tukunna ta yi saving d'in
sa.

Haka ma Husna ta yi saving d'in na ta, Amma zuciyarta fal Tunani wai lubnah ce ta
zama haka, ba ta tashi shan mamaki ba sai da aka gama mata ta ga dank'areriyar
motar da ta shiga.

Tunani ire-ire ya dinga zuwan mata ya aka yi lubnar da ta sani ne ta zama haka.
Da wannan tunanin da sake-saken har layi ya zo kan ta aka soma mata ita ma. Kitso
da lalle aka mata wanda kuma dubu uku ta biya sauran canjin ta sa a jakarta.

Koda suka isa gida har k'arfe 4 hudu ma tayi dan haka ba ta b'ata lokaci ba ta
shiga toilet tare da dauro alwala dan gabatar da sallahn al-asar.

Koda ta idar kwanciyar ta ta yi a wurin Dan mik'e bayan ta. gaba d'aya ma ta manta
yau za ta karb'i girki, a nan bacci ya sure ta.

Cikin bacci ne ta ji kamar wayarta na ringing dan haka a hankali ta bud'e idanun ta
tare da dau wayar ta daura a kunnen ta. "Kun dawo ne?" "Eh tun dazu ma muka dawo."
"Good dama na kira naji ko kun dawo." "Tun k'arfe hudu ma muka dawo yanzu haka ma
bacci na ke kafin ka k'ira." " Ok! To yanzu me zaki dafa ma na na dare?"

"Na'am me ka ce?" "Na ce me za ki dafa mana yau?" "Wai ita fa shab ta man ta da
wani girki da za ta yi wallahi. "Wai da nace zan dafa taliya, Amma ban san me ka ke
son ci ba." "No! Ni tuwo da miyar kuka na ke so." "To ranka shi dad'e zanyi tuwon."
"Yauwa! Daga haka suka yi sallama ta kashe wayar tare da duba lokaci, Ganin har
k'arfe biyar saura ne yasa ta tashi wa da saure tare da cire hijab d'in ta ta shiga
kitchen dan d'aura sanwar dare.

Kusan k'arfe 6:48 ta gama girki tare da gyara ko ina kana ta koma d'aki dan gabatar
da sallar magrib.

Koda ta gama ta shiga toilet tayi wanka ta sanya kaya masu kyau kana ta zauna tayi
kwalliya tare da jiran mai gida ya shigo.

********

Bangaren Aisha kuwa bayan fitar shi wayarta ta k'ara dauka tare da danna wa Eeman
k'ira wanda dama suna cikin wayar ne Aliyu ya shiga.

Bugu biyu ta d'aga tare da cewa. "Har ya fita kenan." "Yeah ya fita." Yauwa dazu
muna magana yaushe kike tunanin za mu tafi?" Gwara mu sa date cikin wanan satin mu
tafi dan kin san upper week zan koma school." "Ni fa am free kin ga ko gobe kika ce
mu tafi zamu iya zuwa tunda yau na gama girki da ga gobe har jibi am free." "To shi
Kenan zan fadawa Inna kin ga ko jibi ne sai mu tafi ma ta yine in yaso sai na biki
gidan ki ke ma sai na miki ko kwana d'aya ne, Amma ki fada mata zai fi kar muje
kuma baza mu same ta ba."

"To Allah ya kai mu amma Batool kam she's always at home kamar ni nan ina za ta
ji?" Tana nan amma duk da haka i will let her know, ta san da zuwan mu yafi dan ba
mu san halin da suke ciki ba haka kawai muje musu."

"Yeah gaskiyan ki ne wallahi yanzu kowa managen kansa ya ke, manager da kika ce
your are always at home, yanzu shanty bakya komai no zuwa aiki no any business da
ki ke yi?" I thought We've talked about this?"

"Nasani kema kin san Aliyu ba zai tab'a barina nayi aiki ba da dai sana'a ce
to,itama dai kinsan yanda anguwar nan take fa me za ka yi da za a siya babu, kuma
koda ka yi ma to Saida bashi da wannan za su kashe ka. Kuma ma ni alhamdulilah ba
abunda na bukata na rasa komai ina so yana min so why zan ta damun kai na da wani
sai nayi aiki ko sana'a."

"Ah lallai kice har yanzu ba'a koya Miki hankali ba ashe, dan ba abunda ki ka nima
ki ka rasa shi yasa ba za ki nemi sana'a ba. To ai shi kenan bazan yi magana ba ina
nan zaki nemi ni kan wannan maganar wallahi balle ke da yanzu kun zama biyu in da
dubu goma ya ke baki to yanzu fa dubu biyar zai baki dan raba wa biyu zai yi ya
baki rabi haka ita ma ya bata.
Ko mu da ba muyi auren ba ma gashi mun tashi neman na kan mu sana'a dai ba wace ba
ma yi duk abunda zai kawo mana kud'i yi muke yi amma banda wanda ya sab'a wa
addinin."

"To Hajjiya naji kuma zan yi tunani a kai, wai ina Inna Hasiya ne yau banji
muryarta ta background ba" ta fad'i tare da yar dariya." "Ah lallai kice ke ma kin
lura ashe, to yau yan jikokin ta basa nan kin san sun koma makaranta dan haka kowa
ya koma gaban iyayensa."

"Kai tana k'ok'ri fa haka ranar ma na zo na same ta da su sai b'arna da suke ma ta,
ga kuma neman tsokana kuma wai kar a dakar mata da su."

"Ke dai bari lokacin su ne suyi su matsa ma yaranmu masu zuwa." "Amin ya rabbi."

Daga haka suka canja wata hirar daban.

Wacece Eeman?

Eeman ya ce ga Inna Hasiya yayar ummi mahaifiyar Aisha.

Ita ce Autar cikin su hudu. Wanda yayyen ta mata biyu Fatima da Jawahir, kuma duk
sunyi aure har ma da yaran su, sai kuma yayan su Ashraf Wanda shine Babba cikin su,
matarsa daya Amina sai kuma d'an su d'aya Fajar wanda a yanzu shakarar sa biyar.

Eeman da Aisha sun tashi kusan sa'ani wanda Aisha ta girme mata da shakara biyu,
tare suka tashi kusan komai nasu iri daya ake musu sanda suke k'anana.

Haka in an basu hutun makaranta haka Eeman za ta had'a kayan ta tazo gidan su Aisha
da zama har sai hutun makaranta ya k'are.

Shak'uwa ce mai k'arfe a tsakanin su, ana haka kawai kwatsam aka yi transfer din
baban su Eeman Katsina dan dama shi soja ne.

Wanda Dalilin rabuwar su kenan wanda kuma bayan tafiyar ta ne kuma Aisha ta k'ara
had'uwa da wata sabuwar k'awa wato Batool.

Duk da rabuwar su ba abunda ya canja dan kusan kullum suna kan waya.

Wannan Kenan

Sai da suka kusan awa daya suna waya kana daga bisa ni suka yi sallama ta kashe
wayar.

Koda ta duba loakci sai taga har 2 ta gota. "Wai haka lokaci ya k'ure hmm lallai."
Daga haka ta jara kwanciyar ta kan coush din tare da rufe idanun ta dan bacci, yau
tana off ne shi yasa ba ta yi sallah ba tun jiya da dadare ya zo ma ta.

Ba ita ta tashi ba sai kusan k'arfe hudu da wani abu tukunna wanda sosai ta yi
mamakin baccin da ta yi haka, babu b'ata lokaci ta shiga toilet tare da tsabtace
jikin ta da canja pad, kana ta fita falon tare da zama kan kujera.

Jin kukan da cikin ta ke yi ne yasa ta shiga kitchen tare da hada indomie tare da
soya kwai biyu a kai kana ta koma falo ta fara ci abun ta.

Koda ta gama ta maida plate d'in ta koma falo tare da bud'e TV ta sa zee world kana
ta fara kallon favorite series d'in ta wanda dama k'arfe biyer a ke sa wa.

P.18
Aliyu koda ya tashi daga aiki ba gida ya koma ba Direct gidan Hajjiya ya tafi, Dan
d'azu tasa hamida ta k'ira ma ta shi kan tana da buk'atar ganin sa. Dan haka ne ma
yana tashi wa daga aiki can ya fara zuwa dan shi zaifi Mishi sauk'i Kan ya koma
gida kafin ya k'ara fita d'in, to shi yasa ma ya fara zuwa wurin mahaifiyar shi
tukunna duk da ita b'ata ce masa lallai-lallai sai yau ba kawai ce masa tayi "duk
sanda kasamu lokaci ka zo." To a can ma yayi sallah magrib har da Isha ba shi ya
dawo gida ba sai kusan k'arfe 9 da wani abu.

Koda ya dawo darect part d'in Husna ya nufa tunda ita ce mai girki, amma koda ya
shiga bai ga ko mai almar ta ba ma balle mai kama da ita. To amma sai yayi tunanin
ko tana can wurin Aisha ne dan haka bai wani damu ba sai shiga d'akinsa da yayi
domin yin wanka.

Kusan minti 40 sai gashi ya fito sanyi da wando three quarter da bluen riga mai ga
jerin hannu, ma sha Allah ba k'arimin kyau kayan suka masa sai kamshin turaruka da
ya ke yi. Yana fita sai part d'in Aisha dan yasan Husna ma na can d'in.

*******

Bangaren Aisha kuwa haka ta cigaba da kallon ta har series d'in ta ya k'are sai
gobe kuma in Allah ya kai mu za'a sa wani episode d'in.

Ganin k'arfe shida tayi ne yasa ta canja wa zuwa tashar tafsir, daga nan ta tashi
tare da d'an kakk'abe gidan tare da sa ka turaren wuta, Kana ta haura sama domin
wankan. Koda ta gama ta sauka, zama tayi akan d'aya daga kujerun falon kana ta dau
wayarta ta soma chatting. A nan ne ma taga Batool na online dan haka ta tura mata
sak'on gaisuwa kana daga nan suka soma hira tare da tambayar juna ya bayan rabuwa
dan gaskiya sun kwana biyu ba suyi magana ba. A nan ne takai sanar da ita ko tana
nan jibi ita da Eeman za su zo mata. "Ah dan Allah da gaskiye za ku zo ina nan
wallahi ina ko zan tafi." "To shi kenan zai kin ganmu jibi ki aji mana abu mai
dad'i." Ta tura mata tare da saka emoji a karshen maganar ta.

Tana cikin wannan chatting ne taji ana knocking din k'ofar falon ta dan haka ta
aje wayarta tare da tashin wa kana ta isa wurin k'ofar. "Waye?" "Aunty ni ce." Sa
rai ta gani muryar amma sai ta k'ara cewa."ke wace?" "Husna ce." "Ok! Daga haka ta
bud'e mata k'ofar tare da d'an matsa wa gefe amma bata bar bakin k'ofar ba.

"Oh Husna mai ya faru lafiya?" "Eh hmm dam.. dama Yaya bai zo bane shi yasa na
kawo mana abincin nan muci." "Sai da ta mata kallon tun daga sama har k'asa kana ta
dan tab'e baki kana ta matsa mata alamar ta shiga ba tare da ce mata ko kanzil ba.
Ita fa karfin halin yarinyar nan mamaki ya ke ba ta, amma bata yi magana ba sai
maida k'ofar da tayi kana ita ma ta koma falo tare da zama abun ta.

Husna kuwa koda taga har 8 ta gota Aliyu bai zo bane ya sa ta tashi wa tare da
hada abincin mutum biyu kana ta nufi part d'in Aisha da shi. Duk da tasan ba lallai
bane ta bud'e mata k'ofar amma haka nan ta tafi dan gaskiya ta gaji da zaman shuru
d'in nan gwara ta je can ta rage kadai ce. Ita da ma a son ranta ne da zata fi
kowa jin dad'i idan za su koma kamar da, dan tun ranar da Kausar ta zo kuma ta mata
fad'a nan, sai taji duk wani rashin mutunci da tugu da ta zo da shi ta wasar. Yanzu
kawai so take su zauna lafiya.

Koda ta zo part d'in Aisha ma zuciyarta sai lugudar bugu ta ke dan ba san wace irin
tarba za ta mata ba. To koda ta bud'e mata k'ofa ta shiga sai taji duk wannan
tsoran da fargaban da ta ke ji ya kau.

Da can dining ta kai kulolin abincin, Amma da ta ga Aisha falo ta koma bayan rufe
k'ofar ne yasa ta dawo da su falon tare da ajewa a kasan carpet kana ita ma ta
zauna tare fara bud'e kulolin ta zuba musu a tire su ci tare.
Duk abunda take Aisha na kallon ta gefen idanun ta, amma bata ce mata komai ba sai
ma cigaba da latsa wayarta da tayi. "Aunty sauka muci abinci." Ok! Kawai tace kana
ta sauka suka soma ci.

Koda suka gama ta tattara kwanikan kana ta koma da su part d'in ta.

Aisha kam da mamaki ya kusa kashe ta da wannan sabon salon da Husna ta zo mata da
shi ne yasa ta yi gum da bakin ta dan bata san da wace tazo mata ba wannan karon
kuma ba, tunda wancan Karon da aure mata miji ta zo wannan ma da walak'in goro a
miyar. Dan bata yarda da wannan sunne kai da ta ke.

Bata gama wannan tunanin ba taga an turo k'ofa an shigo Husna ce ta k'ara zuwa,
koda ta shiga samun wuri tayi tare da zama ita ma kana ta cigaba da kallon.

Aisha ma ba tace mata komai ba sai ma k'ara concentrating kan wayarta.

Haka dai su ke zaune ba hmm balle uhm uhm.

Suna cikin haka ne suka ji an d'an k'onk'sa k'ofar kana a aka ture ta ciki tare da
shiga, Aliyu ne ya shigo tare da sallama a bakin shi tare da zama kan kujera.

Amsa mishi suka yi tare da gaishe shi. Wanda shima ya amsa musu fuska a sake tare
da tambayar su ya gida ya same su lafiya?" Lafiya suka amsa masa kana suka yi shuru
na d'an wani lokaci.

Can dai Husna ta ce, "A ka maka abincin ka nan ko a can zaka ci?" "Sai da ya d'an
tab'a cikin sa kana ya ce ki kawo nan muci tare."

"A'a fa mun riga da munci mu, kawai ki ka mish wanda zai ishe shi kawai in kuma
zaki taya shi ci ne kuma to." Ciwar Aisha. "A'a nima gaskiya a k'oshe nake." "Ok!
To ki zuba min kad'an dan sai da ma na ce abinci wurin su Hajjiya can kafin nazo."
"To tace daga haka ta fita dan ka mishi."

"To ya ka baro su Hajjiya?" "Lafiya lau suna ma gaida ku." "To muna amsa wa."
Daga haka suka soma wata hirar da ta shafi wurin aikinsu.

A haka har Husna ta ka mishi abincin, ya sauka k'asa ya fara ci. Ko bayan ya gama
ta tattara komai ta maida kana ta koma aka soma hirar da ita. sai kusan k'arfe 11
da wani abu tukunna suka koma part d'in su Aisha ma ta kulle k'ofar ta tare da
kashe TV da wutan falon kana ta shiga d'aki ita ma domin bacci.

To haka washegari ma bayan sun tashe kowa yayi aiyukan shi aka yi breakfast an
karya mai gida ya fita aikin saura su kad'ai kowace ta koma part d'in ta.

Ba su k'ara had'uwa ba sai dare da suka had'u kan dinning room. A wurin ne ma Aisha
ta ke sanar da shi fitan da ta ke son yi gobe, kuma ya yarda. Amma kuma sai yace
wai ta tafi da Husna mana za'a bar ta ita kad'ai a gida haka babu dad'i kad'a ci
zai ma ta yawa.

P.19

"Gaskiya bazan iya zuwa da ita ba da can tare muke fita?" And beside bani kadai zan
tafi ba so ko mun tafi tare ba za ta ji dad'in fitar ba."

"Wai ke Aisha me ya ke damun ki ne?" Na lura da take-taken ki these days bakya son
zaman lafiya."
Sai ya juya kan Husna da tun fara maganar su bata ce uffan ba. "Ki shirya ku tafi
tare ko kuma ki shirya ni zan kai ki da kaina."

Cikin bacin rai da k'unar rai Aisha ta ce. "Ai baka burge ni ba Aliyu sai ka goye
ta ka kai ta da kafafun ka ba wai da mota ba kuma fitar ma na fasa sai taje ita
kadai, ai da ban ce zan fita ba ba ka ce zaka kaita ba."

"Ni ki ke wa tsawa a kai?" Ni kike wa tsawa dan na ce ku fita tare, naga da tare
kuke fita, ko kuma wani sabon salon rashin son zaman lafiya ne."

Dariyar takaici tayi kana tace."da kenan lokacin da idona bai bud'e ba, kuma da ka
ke wani cewa bana son zaman lafiya ai kai ne baka son zaman lafiya Aliyu da kana
son zaman lafiya da baka je ka Auro min k'anwa ta ba, ka kamin a matsayin kishiya.
Ita ma da ya ke bak'ar munafuka ce duk alkairin da na musu ita da yan uwanta amma
ta rasa da me zata saka min sai aure min miji." Ta fad'a hakan ne tare da wulla ma
Husna wani banzan kallo.

"Aunty kiyi hak'uri wallahi ban...

"Dal Allah rufe min baki bak'ar munafuka an gaya muku zan k'ara yarda da ku ne, ki
min shuru ko in mammake ki a na nan. In ina magana da mijina kar ki kuskura ki sa
min baki." Ta k'are maganar ne tare da nuna ta da yatsa.

" Don't! Duk abunda zaki yi ya kasan ce tsakani na dake kar ki k'ara saka min mata
a ciki."

"To me mata ka ja mata kunne kar ta kuskura ta sa min baki cikin magana dan wallahi
ka ji na rantse me raba ni da ita sai Allah."

"Rashin kunya zaki min kenan ina magana kina magana."

"Ni ban maka rashin kunya ba gaskiya na fad'a maka kuma kasan d'aci gare ta."

Kadai kai kawai yayi yau wai shi Aisha ke mishi rashin kunya wai shi Aliyu a ke ma
rashin kunya kuma a gaban Husna dan kawai ta rai na shi aikuwa sai ya koya mata
hankali Da shi ta ke zanje.

"Husna ki wuce ciki ina zuwa." To! Ta ce amma bata bar wurin ba can nesa da su ta
tsaya tare da kallon draman da ke faruwa zuciyarta tass ko ba komai yau Aliyu ya
nuna ma Aisha matsayin ta, yanda take alfahari matarsa ce to haka ita ma matarsa ce
sai wani d'aga kafada da wani hura hanci wai ita ga mai miji to yau dai an nuna
mata iya kar ta.

Bangaren Aisha kuwa yau Aliyu ya kai ta wuya wanda duk yanda ta so ta sarrafa
zuciyarta da tunanin ta ta kasa, hakan be duk abunda ya zo bakin ta take fad'a.

Nuna ta da d'an yatsa ya yi kana ya ce. "Wallahi ki kiyaye ne, duk abunda ki ke ji
dashi a kan ki zan sauk'e miki shi dan kin ga ina lallab'a ki shine kike son kamin
rikici a gida?" To ki sani bazan lamin ta ba, gwara ki sauya hali tun wuri dan baza
ki ji dad'in abunda zai biyo baya."

"Bazan shiga hankali na ba na ce bazan shiga hankali na ba Aliyu, me zaka yi?" na


ce me zaka yi?" duka na zaka yi kai ma kasani wallahi duk ranarda kuskura ka sa
hannu ka tab'a lafiyar jiki na to auren nan ya zo karshe har abada kuwa. tunda ba
kai ne autan maza ba mijin daya dai kam bazan rasa ba, ko yanzu na bar gidan ka zan
samo mijin da yafi ka da komai Aliyu in kud'i ka ke tun k'aho to akwai wanda yafi
ka in ma kyau ne akwai wanda yafi kuma zan same shi na aur....Shuru tayi da bakin
ta ganin nan da nan yanayen sa ya canja wanda har sai da zuciyarta ta buga sabon ta
tsorata da yanayen na sa.

Aliyu kuwa tunda ta ambaci auren wani, duk kofofi da jijiyoyin kishin sa sun tashi
idunun nan nasa sun wani rik'id'e sun koma kamar gauta sai huce ya ke kamar wani
zaki.

"Wato da auren shi akan ta amma ta ke tunanin wani can daban har ma wai zasu zauna
lafiya lallai Aisha ta na son yayi kisan kai kenan. Gaba d'aya idanunshi sun rufe
ba abunda ya ke gani sai Aishar sa da wani can gardi suna buga soyayya, sabon kishi
ya rufe idon shi har gizau suke Mishi. Nan ya k'ara hawa kamar balloon.

A hankali ya soma takawa zuwa inda take da wata iriyar murya ya ce "waye shi?" Ina
yake? Me sunan sa kuma a ina Yakee?" Ya kare maganar da wata irin tsawa da ta sa
Aisha sakin fisari a jiki nan jikin ta ya soma b'ari.

Ganin ya soma tukarar ta ne yasa ta soma ja da baya sau uku take kokarin magana
amma ta kasa dan da zarar sun had'a ido sai bakin ta ya mutu. Ita kam wani tsotsayi
ni yasa ta anbatar wani, yau mai k'wace ta a hanun sa sai Allah.

Tswar da ya dakaa mata ne yasa ta dawo haiyacin ta. "Na ce me sunan sa ina ya ke?"

"Wallahi wallahi ka yarda da ni subutar baki ne kawai nayi kuma ni me had'i na da


wani bayan ina da aure. dan Allah kayi hak'uri bazan sake ba." Ta fad'a tare da
had'a hannayen ta biyu tana mai bashi hak'uri.

"Oh baza ki fada min ba." Daga haka ya soma cire rigarsa ko me zai yi da ita oho.

Ai Aisha na ganin hankalin shi ba a nan ya ke ba yasa ta tattara kayan ta ta kasa


kana ta fal-fala da gudu tare da barin part d'in Husna da ya ke dama a falon ta
suke. Ba abunda ta ke cewa sai. "waiyyo na shiga uku."

Aliyu kam ganin ta tsere mai ne yasa shi shima mara mata baya tare da ce wa 'ki
tsaya karki bari na kamaki da kaina."

Amma ina Aisha bata ma jinsa sai fal-fala gudu take har ta isa part din d'inta bata
tsaya nan ba ta haura sama tare da shiga d'aki ganin in ta tsaya nan ma zai iya cin
mata ne yasa ta shiga toilet tare da bank'o k'ofar tare da kulle ta wanda kuma
alokacin Aliyu ma ya shiga d'akin.

Jin k'arar kulle k'ofar ne ya tabbatar mishi da cewa tana ciki, nan ya tsoma
knocking d'in k'ofar kamar zai b'alla ta Allah ya rufa asire k'ofar mai kyau ce da
badan haka ba da tuni ta b'alle.

"Ki fad'a min inda ya ke in je in kashe shi har ni zai kalle min mata hmmmm." Daga
haka kuma ya soma buga k'afar. "Ko a mafarki kika yi tunanin wani bani ba to ki
sani sai na kashe ki na kashe kaina, ki bud'e ki fad'a min inda ya ke." Matata har
ya ke tunanin kusan tar ta?"

Sai da ya gaji dan kansa kana ya fita ya bar part d'in na ta gaba d'aya.

Aisha kuwa tunda ta kulle kanta cikin toilet ba abunda ta ke sai adu'a gaba d'aya
jikin ta ya jik'e da gumi kafufun ta sai rawa suke ba abunda zuciyarta ke yi sai
bugu fat-fat.

Jin shuru bata k'ara jin muryar sa bane yasa ta fahimce ya bar wurin, a hankali ta
bud'e k'ofar tare da lek'a wa dan tabbatar da ya tafi.

Ganin baya nan ne yasa ta sauren fita tare da kulle k'ofar dak'in tare da sauka
wata iriyar ajiyar zuciya.

Sai a lokacin ma ta lura da jik'ankan kayan ta. "Wai kar dai har fasari nayi a
jiki?" Kai ba dole ba amma na taki sa'a da na shiga hannun shi yau da sai dai uwata
ta haifi wata ba dai ni ba. Mutum sai bak'in kishin tsiya."

Daga haka ta shiga toilet dan tsabtace jikin ta.

Aliyu kuwa koda ya bar part d'in Aisha na Husna ya nufa direct, koda ya shiga tarar
yayi Husna na falon ta na mai jiran sa.

"Ban ce ki ki shiga ciki ina zuwa ba?" Oh wato kema zaki nuna min ban isa ba
kenan?"

P.20

"A'a kawai na fito in sha ruwa ne kuma bangan ka ba shi yasa na tsaya a nan falon."

Daga haka ta wuce d'aki abun ta dan in tace zata tsaya to kuwa komai zai iya
faruwa.

Kwafa ya ja kana shi ma ya shiga d'akinsa tare da kulle k'ofar dan kar ma Husna ta
ce za ta biyo shi har ta dame shi, abunda ya ke ji ma ya ishe shi kar ta k'ara
tunzura shi ya huce a kan ta yanzu dai he want to be alone.

Husna kuwa koda ta shiga d'akin wata iriyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta samu
wuri kan gado ta zauna. "Gwara na zauna a nan abuna in ba son ya juya haushin shi a
kai na ba a nan ma zan kwana abina.
Ringing d'in wayarta da taji ne ya katse mata tuninan da ta ke. "Waye kuma da k'ira
cikin daren nan?." Ta furta tare da duba agogon da ke bangon d'akin, k'arfe 10:37
amma shine za'a wani dame ta. Kamar baza ta daga ba sai ta daga tare da daura wayar
kan kunnen ta ba tare da ta furta komai ba. Jin an d'aga wayar ba tare da yin
magana ne me kiran yace. " Husy Luby ce na miki magana ta WhatsApp baki bud'e ba."
"Oh! Lubna ke ce ok bara na bud'e data kin san tun jiya ban samu na hau WhatsApp ba
shi yasa amma ki kashe yanzu zan hau." "Ok! Kawai Lubna ta ce tare da katse kiran.
Tana sauke wayar ta bud'e data kana ta shiga WhatsApp, sai da ta d'an jira
message's suka gama shiga gaba d'aya tukunna ta shiga duba numbern da aka aika mata
da sak'on. Koda ta shiga numbern da ta ga aka tura mata da, "Hi Husyy lubnah ce."
"Nan ita ma ta shiga tura mata sak'on ta gane ta, daga haka suka soma gaisa wa da
tambayar juna ya bayan rabuwa da dai sauran su nan ne Husna ta ke jin wai sun rabo
da mijin kuma har da rabo a tsakani amma yaron na wajen ta. Sosai suka yi hira har
kusan k'arfe 2 da wani abu tukunna ta sauka daga online d'in.

Lubna da Husna k'awaye ne tun kafin Husna tazo hannun Aisha, Sun had'u a yawon
talla. Lubna irin Yaran nan ne da basa jin magana ta gagari iyayen ta kuma tun tana
k'aramar ta tasan maza idon ta a bud'e ya ke. A wurin talla suka had'u da Husna
wanda a lokacin Baba Mariya ta fara d'aura mata d'an wanke ta fita da shi, ita kuma
luban tuwo da shinkafa da wake ta ke siyar wa. Sosai suka k'ulla k'awance da har
lubna kan zo gidan su haka ita ma Husna kan zo gidan su lubna. To komai ya tsaya ne
lokacin da Aisha ta d'auke Husna ta tafi da ita. Bayan tafiya Husna ne Lubna ta
k'ara had'uwa da wasu k'awayen da suka fita bud'e war ido. To fa nan Lubna ta k'ara
lalacewa idon ta ya k'ara bud'ewa wanda hakan ne yasa Baban ta ya aurar da ita ga
d'an abokin shi, wanda anyi auran ne amma duk basa son junan su. Haka dai aka yi
auren amma babu zaman lafiya kullun-kullun sai mak'ota sun ji su, to karshe dai
auren ya mutu ta koma gidan su. To bayan rabuwar da wata hudu sai ciki ya b'illo
wanda kuma shi mijin ya ce fafir ba na shi bane sai dai a nemi uban wanda yayi mata
ciki amma ba dai shi ba. Wannan furuci na shi sosai ya tsosa ma iyayen ta rai wanda
kuma suka ce baza su yarda ba sai sun kai shi Kotu. Koda aka je kotu mijin ya k'ara
maimaita maganar sa na cewa bashi ne uban cikin ba ita kuma ta dage wai shine
ubansa. Ganin haka ne Kotun ta bar shariyar sai bayan ta haihu za'a yi DNA test
wanda shi zai tabbatar da gaskiyar magana.

Bayan ta haihu d'an yayi wayo aka je aka yi DNA test wanda results ya fita negative
d'a ba na shi bane.

Anyi anyi ta fad'i wa ya mata ciki ta k'i fad'a ita lallai wai shi ne uban d'an
bayan ga abunda results ya ce. Bak'inci da zuciya suka d'ibe mahaifin ta ya kore ta
daga gidanshi ya sallama wa duniya ita. duk cikin yaransa ba wanda ta tab'a bashi
ciwon kai kamar ita ba. Koda ta bar gidan iyayen ta ta had'u da wasu yan barikin
k'awaye wanda suka k'ara bud'e mata ido tare da had'a ta da su sugar daddies, wanda
itama ta zama Hajjiyar kanta yanzu ba inda bata zuwa.

Cigaban labari*

Tun ranar da wannan abun ya faru Aisha bata bari sun k'ara had'uwa da Aliyu ba,duk
hanyar da ta san zata had'a su sai tabi ta tushe ta. Ko abincin da suke ci a babban
falon ma ta dena zuwa girkin ta take a bangaren ta. Ba su had'u ba sai da ta karb'i
girki wanda sai d'ari-d'ari ta ke da shi. Da ta ga bai yi mata maganar ba kuma bai
nuna kamar awkai abunda ya faru ne yasa ta ita ma sakin jiki har ta gama Ranakun
girkin ta Husna ka karb'a.

To haka rayuwa ta cigaba da tafiya tun ana k'irga kwanaki aka zo sati har yanzu
wata hudu suka wuce kamar kibtawar ido. Cikin wata hud'un nan abubuwa da dama sun
faru ciki har da auren balkisu da aka yi wanda ba'a yi wani shagali sosai ba dan
ango Hakim ya ce shi albarkar aure ya ke nema ba. bashi da matsala in za suyi abun
su suyi shi bai hana ba amma kar ma su sa ran zai zo wurin. Ganin haka ne Aliyu ma
yace kawai a daura aure ba wani shagalin da za'a yi. ana gobe za a d'aura aure suka
k'ira DJ a ka yi shagali washegari aka daura aure. Da daddare kuma aka kai amarya
gidan ta.

Gidan Aliyu kuwa sai dai mu ce alhamdulilah tunda ana zaman lafiya ba lefi duk da
baza a rasa matsala ba irin ta yau da kullum.

Bangaren Husna da Lubna ma sai mu ce ma sha Allah d'an sun d'inke sun zama best
friend yanzu kam husna bata ma jin maganar Baba Mariya sai ta Lubna ko mai sai tayi
shawara da ita.

Baba Mariya ma ba a bar ta a baya ba wurin bin malamai kan duk yanda za'a yi Aisha
sai ta bar gidan tunda duk abunda suke tunanin ba shi ke faruwa ba. Sun d'auka in
anyi auren zai dinga rawar kai a kan Husna ta yanda duk abunda suke ce suna so zai
bada ba tare da tambayar ba a si.

Ita ma Aisha yanzu ta kwantar da hankalin ta suna zaune da mijinta lafiya sai
abunda ba za'a rasa ba.

Tsakanin ta da Husna kam sai a hankali duk da ba fad'a ba kawai dai kowa na zaman
shi babu ruwan kowa da waniyanzu girki ma kowa yi ya ke a part d'in shi, Aisha ce
ta fad'a mishi gwara kowa yayi abun shi a part d'in shi, duk wace miji ya na wurin
ta sai tayi har da shi. Da ya k'i amince wa amma da ta zaunar da shi ta yi mishi
bayani sai ya amince.

Husna ce kwance kan kujera mai daukan mutum hudu, ba bacci ta ke ba amma idanun ta
a rufe suke. Aliyu ne ya fito daga kitchen hannun sa rik'e da tire, wanda shayi da
breadi ne akai sai kuma butter. A hankali ya matsa kusa da ita tare da tab'a kan ta
da yayi zafi kamar wuta. "Ki tashi ki sha ko tea d'in ne mu tafi asibiti." "A'a ba
sai mun tafi asibiti zan samu sauke." "No I don't want to hear anything tun
shakaran jiya kike cewa zaki samu sauki, ko magani ma kin k'i ki sha dan Allah ki
tashi kar ki b'ata min lokaci yau Monday zan fita office." A hankali ta tashi tare
da zama kan kujerar da kyau kana ta ce to bani tea d'in." "Ok! Daga haka ya mik'a
mata cup d'in tare da shiga d'aki dan d'auko mata da hijab d'in ta. Ita kam da kyar
ta iya shan tea d'in tare da aje cup zuciyarta sai tashi take kamar ta amayar da
shi. A haka ya fito ya same ta. " Sannu ga shi kisa mu tafi na ji me ya ke damun ki
haka in ma allura ce su baki." Amsa tayi ba tare da cewa komai ba dan bata da
k'arfin yin maganar ma. Da kyar ta iya saka hijab d'in kana ya kama hannun ta suka
fita harabar gidan shi ya bud'e mata murfin mota ta shiga tukunna shima ya zaga ya
shiga kana ya tayar da motar mai gadi ya bud'e musu gate suka fita.

Koda suka shiga asibiti shi ya k'ara zaga ya bud'e mata murfin mota kana ya rik'e
hannunta suka shiga cikin asibitin.

Koda da suka shiga ciki derect office d'in Dr suka shiga kasan cewar Dr abokin shi
ne so tun a hanya ya sanar da shi isowar su.

Koda suka shiga gaban Dr bayan sun gaisa Aliyu ya fara mishi bayanin abunda ya kawo
su. "bata cin abinci komai ita bata so ko tasamu ta ci to sai ta amayar kuma ga
zazzab'in dare da take yi."

Tunda ya fara magana likita sai kad'a kai kawai yake har sai da ya ga ya kai aya
tukunna ya ce.

"Kar ka damu ba wani abu bane in sha Allah abun arziki ne." Daga haka ya mik'a mata
wata roba tare da nuna mata toilet. " Muna bukatar fisarin ki dan test."

Kai kawai ta kad'ai mai kana ta tashi ta shiga toilet dan kawo fisarin. Bayan kamar
awa daya da jira results ya fita. Wanda Dr tun kafin ma ya sanar da su ya ke ta
Murmushi. "Congratulations Aliyu Abubabar matawale finally abunda ka d'ade kana so
ne matar ka na d'auke da juna biyu.

P.21

"Congratulations Aliyu Abubabar matawale finally abunda ka d'ade kake nema ne Allah
ya kawo matar ka na d'auke da juna biyu."

Sabon murna Aliyu baisan sanda ya rungumi likitan ba ita kan ta Husna abun sai ya
zo mata a baza ta dan bata tab'a kawo ciki ne gare ta. Sosai farin cikin ta ya fito
nan ta fara k'insima abubuwa a ran ta tare da kallon Aliyu da kamar wanda ya fita
cikin haiyacin shi sabon murna.

Nan ya saka hannun shi a aljihu tare da fito da wallet d'in shi gaba d'aya kud'in
da ke ciki ya cire tare da mik'a ma likitan tare da ce wa. "Wanna tukwicin ka ne na
fad'a min wannan labarin mai d'adi. Daga haka ya juya kan Husna tare da rungumi ta
kana ya tsuguna k'asa tare da shafa cikin ta, wai shi ne yau matar shi ke d'auki da
ciki shi Aliyu bayan ya cire ran zai ga jinin shi shakara da shakaru gaba d'aya
baisan ina zai sa ransa ba sabon farin ciki, nan ya soma kararo addu'a tare da
shafa cikin da shi kana ya manna ma cikin k!ss kana ya d'aura kanshi a wurin tare
da yin magana k'asa-k'asa alamar da cikin ya ke magana. Kamar wanda aka mintsina ya
tashi tare da rik'e hannunta suka bar office din likitan ba tare da sun ma mishi
sallama ba ma.

A hanya ma haka ya ke ta washe baki kamar wanda a ka mishi albishir da gidan


Aljanna. Da hannu da ya ke driving d'ayan hannun kuma ya d'aura kan cikin ta a haka
har suka isa gidan, koda suka iso bayan sun sauka har ta fara tafiya fa amma sai ya
tsayar da ita ta hanyar ce wa. " No kar ki wahalar min da baby." Daga haka ya sure
ta kan kafadar shi kana suka shiga part d'in su.

Suna shiga ya zaunar da ita kan kujera tare da tambayar ta me take buk'atar ci ya
kama ta in ma shi take son ya dafa zai dafa ya kama ta."

Husna fa an samu abunda a ke so sai wani lank'wab'ewa ta ke. "A'a bana buk'atar
komai yanzu." "Kin tabbata bakya buk'atar komai?" "Uhmm bana buk'ata." "Ok! Daga
haka ya cire wayarsa daga aljihu tare da danna wa Aisha k'ira. Ringing biyu aka
d'aga bai ma jira ta yi magana ba ya riga ta ce wa. " Ki zo part d'in Husna yanzu."
Daga haka ya sauke wayar tare da Kiran yan uwa da abokan arziki ya na fad'a musu
wannan d'add'anan labarin.

Husna da jin ya k'ira Aisha ta tashi tare da zama kan cinyar sa kana ta d'aura kan
ta a kan kafadar sa tare da yi mishi kukn shagwab'a." "Cikin saure ya tallafi
hab'ar ta kana ya soma tambayar ta me take buk'ata." Cikin shagwab'e murya tace."
baby yana son cin tuwo kuma yanzu-yanzu." "Ok bara na fita na duba ko zan samu in
ma ban samu ba zanje gidan Hajjiya nasan ba za'a rasa ba." Had'a rai tayi kana tace
"bana son na waje na nan gidan na ke so ni." Har ya bud'e bakin shi dan yin magana
sai suka ji an k'wank'asa k'ofa tare da ture ta ciki. Aisha ce ta shigo tare da
neman wuri kan d'aya daga cikin kujerun falon ta zauna kana ta ce. "Ga ni." "Aliyu
kam gaba d'aya kunya ta dabaibaye shi, sai tura Husna ya ke daga jikin sa amma sai
k'ara shige masa ta ke.

A hankali ya sunkuya tare da yi mata rad'a da sauka. Ba dan ta so ba ta sauka dan


ta so ta k'unsa ma Aisha bak'in ciki amma duk da haka bata b'a ce ba tunda ko haka
ma tasan taji haushi kawai dai baza ta fito fili ta nuna ba,hankali ta sauka tare
da hararn ta gefin ido har da murgud'a baki.

Aisha kam tun da ta shiga taga yanayen da suke zuciyarta ta harba ga wani bak'in
kishi da ya zo mata wuya har za ta juya ta koma part d'in ta amma is too late
tunda sun riga da sun gan ta, haka nan ta danna kishin da ta ke ji ta shiga tare da
zama kan kujera kana ta d'au wayarta tare da latsawa yi tayi kamar ba abunda ya
dame ta amma Allah kad'ai ya san me take ji a zuciyarta kamar ta shak'e su ta ke
ji. Sarai ta ga lokacin da Husna ke hararn ta amma bata yi magana ba dan bata son
jawo Raine tsakanin su Husna har yanzu Yarenya ce so bata kai level d'in da zata
zauna tana cacan baki da ita ba is wasting of time. Amma sosai halayen Husna na
bata mamaki gaba d'aya ta canja daga Husnar da ta san ta ta koma wata can da bata
sani ba.

Gaba d'aya bata san ma ana mata magana ba sabon ta lula duniyar tunani ba, sai da
ta ji karshen maganar da ya furta ne ya sa ta dawo wa haiyacin ta. Ba komai bane
ila maganar Husna na d'auke da juna biyu, Amma sai bata d'auka abunda ya ce bane
k'illa wani abu daban ya ce ba wannan ba, Amma jin ya k'ara mai-maita mata ne yasa
dib numfashin ta ya d'auke na wucin gadi.

"M...me..me ka ce?" Ta k'ara tambayar sa dan k'ara tabbatar wa da kunnen ta abunda


taji ya fad'a haka ne she didn't misheard him.

"Na ce Husna na d'auke da juna biyu yanzu haka ma daga asibiti mu ke Dr just
confirmed it. Ashe rashin lafiyar nan da ta ke yi these days abun alkairi ne." Ya
fad'a tare da jawo Husna jikin shi, gaba d'aya Bai lura da canjawar ta ba sabon
farin cikin da ya ke ji. Ji ya ke kamar ya goye Husna a bayan shi ya yi yawo da ita
kasuwa-kasuwa yana sanar da su irin farin cikin da ya ke ciki.

Husna ma hakan ce ta ke a wurin ta Allah Allah ta ke ta keb'en ce ita kad'ai ta


samu ta k'ira Baba Mariya ta sanar da ita wannan abun al kaire finally abunda suke
nema Allah ya basu dama boka ya fad'a musu duk abunda zasu akan Aisha ko Aliyu ba
zai ci saboda soyayyar dake tsakanin su amma kuma in zata iya samun ciki to kuwa
aiki su zai ci dan gaba d'aya zai d'aura soyayyar sa kan d'an ne wanda a lokacin su
kuma su yi affani da wannan damar dan ganin sun shiga tsakanin su wanda in lokacin
aikin ya taso baza su sha wahala wajan raba su ba.

Baki na rawa Aisha ta furta." Ciki Husna na da ciki?" sai kuma ta yi yar dariya
kana ta ce. "Wow ma sha Allah amma na ta ya ku murna Allah ya kawo baby duniya
lafiya." Daga haka ta tashi tare da nufan k'ofa dan fita bata son sakin kukan da ta
ke kokarin rik'e wa ba, har ta isa k'ofar ta ji amon murya sa ya me ce wa. "Please
ki dafa mata tuwo wai tuwo ta ke da buk'atar ci yanzu kuma ban san ina zan samu
yanzu ba please ki dafa mata ki kawo nan." Ok! kawai tace kana ta wuce part d'in ta
da sarsarfa. Ba abunda kunnen ta ke ji yo mata sai Husna na d'auke da juna biyu.
bata san ta na hawaye ba sai da ta isa part d'in ta tare da zama kan gado kana
tab'a fuskar ta kuka w..wh..why am I crying nan ta soma goge fuskar ta Amma da ta
tuna kale sa sai kawai ta knife Kan ta kan gida tare da fashewa da wani sabon kuma
Wanda ita kan ta bata san na me ba.

Ta san dai ba bak'in ciki ta ke musu ba amma abun da ciwo, ace Husna da aka auro ta
jiya-jiya nan har ta samu ciki amma ita shuru, shakara goma auren ta da Aliyu amma
ko b'atan wata ne bata tab'a yi ba balle b'are. Ita kam shi kenan tata tak'are dan
mudin Hajjiya ta ji wannan labari tofa zaman gidan nan ma sai ya gagare ta. Da ma a
ka k'are balle yanzu Sosai tayi bak'in cikin Husna riga ta samun ciki dan ta so ta
zama ita ce macen farko da za ta haifa masa d'a ko y'a to amma Allah bai yi ba. Duk
da haka tana mai taya su murya na da samuwar cikin. Ko ba komai Aliyu zai samu
abunda ya ya d'ade ya ke nema wanda ita ta gagara bashi kuma ma yaran Aliyu ai
yaran ta ne in da kara balle kuma Husna da ke yar uwar ta.

Haka ta yi ta sake-sake a zuciyarta, ganin lokaci na wuce wa yasa ta tashi wa tare


da shiga toilet ta wanke fuskar ta kana ta sauka kasa tare da shiga kitchen domin
d'aura tuwon.

Kusan awa d'aya da rabi ta d'auka cikin kitchen kana ta gama tuwon semo da miyar
kuka da ta ji nama har ma da man shanu kana ta d'auka tare da nufan part d'in
Husna.
Koda ta isa part d'in samun su ta yi a yanda ta bar su d'azu da alamun ma ba su
motsa ba, da sallama ta shiga falon kana ta wuce dinning da abincin. "No ki ka mata
nan zata ci." "Ok! Kawai ta ce kana ta kawo tsakar falon tare da tsayawa ko suna
buk'tar wani abun ne. Ganin ba wanda ya tanka mata balle ace suna buk'tar wani abun
ne yasa ta juyawa da nufin barin wurin, amma ya tsayar da ita ta hanyar cewa. "Za
mu yi baqin kuma Hajjiya ma na kan hanya so ban san me zaki dafa musu ba." Ya fad'a
tare da kafe ta da idanun sa. Lallai ma Aliyu me ya ke nufi da ita ne ita ya ke
fad'a ma za suyi baqi and su na buk'tar girki bayan ba girkin ta ba ne dafa wa
matar shi abinci bai yi ba sai tayi ma baqin ta ma, yes baqin ta mana tunda ba
wurin ta za su zo ba tasan labarin cikin ne ya iso su shi yasa za su zo, kuma har
da ma su zuwa dan yad'a mata magana kawai za suyi ba zuwan Allah da annabi bane
gulma ce kawai zata kawo su. Ganin in tayi magana yanzu gani za'a yi kamar bak'in
ciki ta ke ne hakan ne yasa ta cewa.' ok ba damuwa sai sun zo." Daga haka ta juya
da nufin za ta fita amma me zai ta ji muryar Husna na ce wa. "Me wannan gaskiya
bazan iya ce ba ware fa ya ke." Da saure ta juya tare da fuskantar su gaba d'aya su
tare da jiran me zai ce. "Wari kuma abincin ne ya ke wari ko me?" "Eh baby wari ya
ke gaskiya ni bazan iya ce ba kuma ma ai tun d'azu na buk'ata amma ba a kawo ba sai
yanzu yanzu gashi ban san me aka zuba a ciki ba kar in ce kuma ya tab'a lafiyar mu
ni da babyn." Yana jin zai tab'a lafiyar babyn sa ya rud'e tare da ture tuwon gefe
kana ya ce. " Me kika zuba cikin abincin ya ke wari haka?" "Wari kuma?" Abincin ne
ya ke wari?" "Baki ji me ta ce bane bata son warin please ki fitar da shi daga nan
bana son ganin sa." "Kamar ya in fitar da shi bayan na sha wahala na dafa yanzu
kuma kace wani in fitar da shi to in fitar in kai ina." I don't know for you ki Kai
duk inda zaki kai ba za ta iya cin shi ba is not healthy for her and the baby. A ka
miki wani abun ne?" Ya tambaye Husna da ke ta yamutsa fuska kamar wace taga Kashi.
Kai kawai ta kad'ai me kana ta ce. "abu me ya ji." "Ok! Ya ce kana ya juya kan
Aisha, zai yi magana kenan ta daga tare da shi ta hanyar ce wa. "ya ka ke kallo na
haka ohhh! wait ba wani ki ke son sani in dafa mata ba, in ma abunda ka ke tunani
ne to gwara ma ka rik'e shi dan wallahi bazan dafa ba wannan ai renin hankali ne."
"Ok yanzu in na sa ki dafa wani baza ki dafa ba kenan?"

Ban Kai in sa ki abun ki ba kenan ko me ki ke nufi.

cikin wannan tension ne suka ji diran motoci ma'ana baqin har sun iso. Bata yi
magana ba illa d'auke abincin ta tare da fita daga part d'in ma gaba d'aya tana jin
shi lokacin da ya ke k'wala mata k'ira amma ta yi banza da shi.

P.22

Aisha ko da ta koma part ɗin ta direct kitchen ta nufa tare da aje coololin abincin
kan benchtop, kana ta haura sama.

Tana shiga ɗaki direct wurin cupboard ta nufa tare da jawo suitcase ta ɗaura kan
gado, kana ta fara zuba Kaya a ciki, sai da ta tabbatar duk abunda ta ke buƙata na
yau da kullum ya na ciki tukunna ta zuge zip ɗin kana ta jawo shi ƙasa tare da aje
shi kusa da cupboard.

Zama ta yi a bakin gado tare da haki dan ba lefi ta cika suitcase ɗin da kaya,
hakan ne ya sa ya yi nauyi wanda da kyar ta iya jawo shi zuwa cupboard side.

Zaman ta da kamar minti uku sai ga ƙiran ummi, wanda ta tabbata labari ne ya iso
ta, shi yasa ta ƙira ta dan kwantar mata da hankali. Kamar baza ta ɗaga ba dan ta
tabbata in har ta ɗaga tofa abunda take ƙoƙarin ai watar wa zai wargaje.

Tana gani ƙiran ya katse, again wani ƙiran ya shigo ganin in bata ɗaga ba ummi
might think there's a problem and bata son ta ta shi hankalin ta because of that
and apart from this ma ummi na da ciwon hawan jini any small tension sai kaga ya
tashi mata, shi ya sa ma bata cika faɗa mata matsalolin gidan aurenta ba yanzu za
ka ga ta shiga damuwa.

Ganin ƙiran zai tsinke ne ya sa ta sauren ɗaga wa tare da ɗaura wayar a kunnen ta.
"Assalamu-alaiki ummi kin wuni lafiya?."

" Lafiya Aisha ya ku ke ya gida?"

"Lafiyan mu ƙalau." Aisha ta ta ce daga haka ba wanda ya sake magana na ɗan wani
lokaci.

Sai chan Ummi ta ɗan gyara murya ta fara magana. "Dama Aliyu ne ya ƙira Babanki
yanzu ya ke sanar mana da cewa wai Husna na da ciki."

Shuru ta yi tana mai tunani a ranta, ' Lailai Aliyu wato har iyayenta ya ƙira ya
faɗawa matarsa na da ciki?' kafin ta ce. "Eh Ummi haka nima naji."

" To Allah ya sauke ta lafiya kuma kema Allah ya baki na ki."

" Amin"

" Amma kuna zaman lafiya ko? babu wata matsala ai ko?"

Sai da ta ɗauki yan mintina kana ta ce. " Eh Ummi lafiyan mu babu wata matsala."

"To madalla haka nake son ji." Ummi ta faɗa duk da ta san ba haka bane, kawai dai
ba za ta faɗa mata bane dan kar ta tashi hankalin ta amma tasan akwai abunda ke
faruwa, tunda taji muryar ta ta tabbata akwai abu a ƙasa Amma tunda bata son faɗa
mata ba za ta tilas ta ta ba sai ma taya ta da addu'a, amma sai ta yi afani da
wannan damar tayi mata nasiha Sosai akan haƙuri da duk abunda zata gani yanzu ta
kau da kai akai, Sosai tayi mata nasiha wanda kuma ya shiga jikin ta.

Haka suka yi sallama da nufin zuwa next week zata shigo ita ma. Aisha bayan ta
sauke wayarta ga kunnen ta kwanciya a kan gado tare da fad'a duniyar Tunani.

Tunani take kan rayuwar aurenta tun farko har izuwa yanzu da ta ke fuskantar
matsaloli wanda kuma tasan yanzu ne da matsalolin za su taso tunda tun yanzu ta
fara ganin canji nan da nan idanun ta suka cika da hawaye, a hankali ta sa hannu ta
goge tare da tashewa saka makon karar motoci da taji.

A hankali ta taka zuwa bakin window tare da matsar da labulen kad'an dan ganin ko
su wa suka k'ara zuwa. Tun kafin ma ta ga sun fito daga motar tagane ko waye ne dan
haka ta yi sauren buya a bayan labulen kana ta fara lekan su ta yanda ba za su
ganta ba.

Bayan anyi parking d'in motar driver ya zo ya bud'e mata k'ofar ta fita a hankali
tare da bin ko ina da kallo kana ta juya kan hamida da take k'ok'rin bud'e boot dan
d'auko abubawan da suka zo dashi wato gift Dan ba uwar unborn. "Ki bar su kayan nan
tukunna ni har yanzu ban san wani daga cikin su mai d'auke da cikin ba ki bari sai
na gan ta tukunna." Ta k'are maganar tare da wulla idanun ta saman windown Aisha
wanda tayi sauren boya kar ta gan ta. "To Hajjiya amma ni sai nake tunanin k'illa
aunty Aisha ce kinga ita ce ta d'ade a gidan kuma ma ni Wallahi bana son wannan me
kama da shanu nan Allah ya sa ma ba ita bace duk da ita ma Aisha ba wai ina son ta
bane." "Ban san surutu wuce mu tafi." Ta fad'a tare da mik'a ma ta handbag d'in ta
kana suka kama hanyar part d'in Aisha dan Hajjiya ta rantse tun kafin auren shi da
Husna kan ko kar ya kuskura ka mata Husna gidan ta kuma ita ma ko taje gidan sa ba
abunda zai sa ta je wurin ta.

Aisha ganin sunyi nan wurin ta ne yasa ta saka hijab d'in ta tare da sauka k'asa
saida ta tabbatar ko ina is tsab kana ta zauna kan kujera amma banda bugu ba abunda
zuciyarta ke yi dan tasan Hajjiya kullum in ta zo gidan nan tofah ranta sai ya
b'ace duk da ta lura lokacin bikin balkisu nan gaba d'aya Hajjiya ta can ja mata ba
kamar da ba. Da ko taje gidan su sai sun yab'a mata magana da sauran su amma
lokacin bikin nan Hajjiya ta canja duk da bata wani ja ta a jiki ko ta gaya mata
magana mai dad'i ba amma yanda ta karb'e ta ya bata mamaki wanda har ta zo gida
take tunanin ko Hajjiya ta fara son ta ne ko me.

Jin knocking da ake yi ne ya katse mata tuninan da ta ke. Tashi wa tayi tare da
bud'e k'ofar. "Ahh! Hajjiya ashe ku ne bismillahi ku shigo." Ta fad'a tare da matsa
wa daga bakin k'ofa. Hamida ne ta amsa sallamar ta amma Hajjiya yi tayi kamar bata
ji ta ba amma fa idon ta a kan ta ya ke kurr so take ta gani ko ita ce mai cikin ko
wacan yar matsiyatan ce da shi. Haka suka shiga falon tare da bajewa kan kujera
kana ta ce yauwa sannun ki ya gida ya kuma nawin jiki." Ta fad'i tare da kallon
cikin ta. "Lafiyan mu k'alau alhamdulilah." Daga haka ta tashi tare da shiga
kitchen tare da had'a musu ruwa da drinks ta ka musu kana ita ma ta zauna can gefe
tare da tambayar zarah da yaran ta wanda ita ma ta ga canji daga gare ta sosai
lokacin bikin nan. "Lafiyan su kalau tana gaishe ki ita ma." Ce war Hajjiya. "Ina
amsa wa, ya balkisu ita ma tana lafiya ni rabo na da ita ma tun ranar biki wallahi
ina ta cewa in na samu lokaci zanje in k'ara duba ta amma ban samu na je ba."
"Lafiyan ta k'alau kawai matsalar kishiyoyin ta ne sun sa ta a gaba, sai da na
fad'a mata kar ta aure mai Mata amma ta ce taji ta gani yanzu gashi tun ba'a yi
nesa ba tafara fuskantar matsaloli shakaran jiya nan ma aka sallame ta daga
asibit." "Asibiti?" Tayi rashin lafiya ne?" Gaskiya ni gaba d'aya banji ba wallahi
ai da na je na mata ya jiki." "Hmmm ba wani rashin lafiya, kullum in ta gyara part
d'in ta sai su tura Yaransu su b'ata mata shi wanda kuma wai bata isa tayi magana
ba kuma ba iya nan ba har kitchen suke shiga mata su b'ata mata girki ko kuma su
fasa mata abubuwa Wanda ita kuma bata yarda tana musu doka wanda shi yasa iyayen su
suka had'u suka mata doka wanda shi yayi silar kwanciyar ta a asibiti ashe ma har
k'arimin ciki ne da ita wanda sana diyyar wannan fad'an ya zube." Inna lillahi!
Subana kai banji ba shi ma bai fad'a min ba wallahi ai da na je duba ta kai amma ba
su kyauta ba." "Hmmm ai na so d'aukan mataki na ce sai na k'ira musu police any
arresting d'in su amma yaran sun hana ni da ban haka ba da kuwa sai sunyi kwanan
jail." "Hmm to Allah ya kyauta." Daga haka suka shiga wata hirar daban ba lefi
Hajjiya ta d'an sake ana hira kuma gaba d'aya ta canja towards Aisha wanda da ne
baza a yi five minute bata jefa ma Aisha bak'ar magana ba amma dubi yanzu wai har
hira suke.

******

Bangaren su Aliyu da uwar babyn sa kuwa tunda Aisha ta fita ya ke ta k'wala mata
k'ira ta k'i dawo wa ya kudire sai ya koya mata hankali dan ya lura ta fara rena
shi dan kawai ya na sake mata shi yasa ta ke tunanin zata iya yin komai. Kwafa yaja
kana ya tashi tare da shiga kitchen domin had'a ma Husna ko indomie ne tun da Aisha
tace baza ta dafa wani abincin ga shi kuma ita Husna ta sa shi a gaba da kuka wai
shi ya dafa mana ko sai d'an ya mutu daga yunwa. Yana cikin kitchen d'in ko gas bai
ida kunna ba suka ji ana musu knocking dan haka ya bar abunda ya ke ya fita falon
tare da bud'e k'ofar tare da shigo da bak'in ciki kana suka fara gaisa wa. Abokan
shi ne wanda suka d'ade ba su had'u ba and ba su samu damar zuwa auren sa na biyu
shi yasa suka sa rana dan zuwa har gida dan goge lefin su. Wanda kuma ya zo dai-dai
kan wannan murnar da ya ke ciki. Nan suka cika falon da hayaniya wanda ya sa Husna
shiga d'aki ta bar su bayan ta gaishe su.

Koda ta shiga ciki first numbern Lubna tayi dailing dan ita take son fara fad'a ma
wannan albishir amma sai dai mai numbern baya shiga wanda ta rasa Dalili. "Wait kar
dai lubna da gaskiye ta ke da tace min zata tafi Dubai dama da gaskiye take." Tana
cikin wannan tunanin taji an turo da k'ofa tare da shiga. Aliyu ne ya shiga tare da
rufe k'ofar kana ya ta taka zuwa inda take kana ya fara magana." "Ya jikin?" "Da
sauk'i yanzu tunda har ciwon kai ma ya bar ni." "Good tun da kin samu lafiya yanzu
dan Allah ina son ki fito ki had'a ma ba bak'i na abun sha da da abinci kinji."
"Chab girki fa kake nufi gaskiya bazan iya ba ko ka man ta bani da lafiya ne." "Ba
yanzu kika ce kin samu lafiya ba?" "Eh na samu lafiya amma ba na girki ba haka
kawai kake son na k'ara ta yar da ciwo gaskiya bazan iya ba aunty Aisha ta dafa
mana naga ita lafiyan ta k'alau kuma ba wani nawi ni da ita." Shuru yayi na da d'an
wani lokaci kafin ya kad'a kai kana ya fita daga d'akin ba tare da ya ce mata uffan
ba. Kitchen ya shiga tare da d'auko tire ya aje kan benchtop kana ya bud'e fridge
tare da d'auko ruwa da drinks sai cake da su biscuits duk ya had'a a tire d'aya
kana ya fita falo da shi. Suna ganin sa da tire suka sa mishi ihuu! Wai ga mijin
tace shi ya ke entertaining Bak'i ba matar gidan ba. Da zaka bud'e zuciyar Aliyu a
lokacin da sai sauro ya kama ka sabon bak'in ciki da takaici ga haushi abu goma da
ashiren and again wai shi ake cewa mijin tace bawon mata. Sosai yayi kokarin
maintaining b'acin ransa tare da cewa no ba haka bane madam ni b'ata da lafiya ba
mu d'ade ma zuwa daga asibiti ba. "Hmmm me ya ke damun ta hakane." Hamza d'aya daga
cikin guy d'in ya fad'a tare da yi ma Aliyu wani kallo wanda su kad'ai suka san
meaning d'in sa. "Kar ka cinye ni yes abunda kuke tunani ne."

"Yehhh suka sa mishi ihuu tare da saluting d'in shi wai yayi aiki me kyau nan suka
cigaba da hira abunsu. Basu d'ade ba suka ce su zasu koma wanda Aliyu su tsaya su
abinci tukunna amma sun k'i wai akwai inda za su amma za su shiga in sun samu
lokaci daga haka ya raka su har wajan mota su ka tafi. Har sai koma ciki amma mai
sai ya lura da motar Hajjiya wanda sosai ya yi mamaki yaushe suka iso ne.

P.23

Daga haka ya kama hanyar part ɗin Aisha dan yasan can Hajjiya ta ke. Koda ya iso
part ɗin gani yayi a buɗe yake wanda babu ɓata lokaci ya shiga ciki tare da sallama
a bakin shi. Tarar yayi suna zauna a ƙasan carpet ga abinci na gaban su wato tuwon
da husna ta ce baza ta ci ba shine Aisha ta ɗumama musu ta kama musu suke ci wanda
tare ma suke ci.

A hankali ya taka har ya shiga falon tare da zama ƙasan carpet kana ya soma gaida
Hajjiya yayin da Hamida ta gaida shi ma. Bayan sun gaisa ne Aisha t tashi tare da
nufan kitchen dan zuba mishi abinci shima amma sai ya da gatar da ita ta hanyar ce
wa. "A'a kar ki zuba min a ƙoshe na ke yanzu na ci snake's so ba wurin saka
abinci." "Ok!kawai tace mishi daga haka ta zauna suka cigaba da cin abincin su
while shi kuma yana ma Hajjiya hira har suka gama Aisha da Hamida suka gyara gurin.

"Ina kuma ƴar sarkin wato ta fi ƙarfin zuwa gaishe ne, ko ni take jira naje wurin
ta." "A'a Hajjiya ba haka bane bata jin daɗi ne shi yasa kuma ma bata san kin zo ba
da tazo gaida ki." "Hmm ka ce haka ai wato ga ƴar gwal bata da lafiya shi yasa ba
za ta zo gaida ni ba to bara ni naje na gaida ta tunda ni lafiya ta ƙalau." Hajjiya
ta faɗa tare da tashi wa dan zuwa gaida husna. Da saure Aliyu ya miƙe tare da kama
hanun ta jana ya fara magana. "No hajjiya ki yi haƙuri ba abunda nake nufi ba ta ya
ke zaki je ki gaida ta bayan ita ce ƙarama." Daga haka ya fita tare da cewa "ina
zuwa bara na ƙira ta dan na tabbata bata san kina nan ba da tazo tun ɗazu." Hajjiya
kam taɓe baki tayi tare da ko ma wa kan kujera tare da cewa wato dai wannan ƴar
matsiyatar ke da ciki uhmm." "Wallahi hajjiya sai naji duk murnar da nake yi na
Yaya zai samu baby ya ɓace wallahi ni kaina ban san me wannan Yarinyar tamin da
bana son ta gaba ɗaya tun fa kafin ma Yaya ya aure ta ni bana son ta allah sai nake
ganin kamar ba abunda ta ke nuna ita bace she's fake. Kinga fa yanda take da aunty
Aisha amma babu kunya ko tsoron allah ta aure Yaya." "Yayan na ki ne yana da kunyar
ko da ya aure ta." "No ba abunda nake nufi bane kawai dai bata kyauta ba kuma ma
Yaya ai namiji ne duk abunda yayi ado ne,amma ita fa ƙanwar ta ne fa kuma tana
zaune da ita gaskiya aunty Aisha jarumace chab in ni ne ko allah bazan yarda ba ni
tausaye ma ta ke bane." "Ummm that served her right me bata yi ba lokacin da na
hana zaman ta da su ba nifa tun farkon gani na da Yarinyar naji bana son ta hakan
ne yasa na hana zaman ta tare da su amma ba sun ƙi ji ba musaman ita Aisha ai ina
sani har yaji tayi kan na hana Aliyu reƙe Yarinyar yanzu da ta aure mata miji ai ta
shiga taitayin ta." "Gaskiya kam dan gaba ɗaya na lura ta zama ƴar shuru–shuru."
"Uhmm wannan kuma tsakanin su ne bazan sake sa baki na a lamarin su ba tunda ance
dan ina bani da kirki wai nasa su a gaba na hana su zaman lafiya wai na tsani Aisha
da sauran su Allah na tuba ko na tsane ta ai ita ta jawo wa kan ta tunda ta ke ta
taɓ....shuru tayi da maganar da ke bakin ta saka mokan turo ƙofar da aka yi. Shine
a gaba sai kuma Husna da a bayan shi tana sanyi da hijab mai hannu wanda ya kai
mata har ƙasa wanda ba ƙaramin kyau yayi mata a hankali take takawa har suka shiga
falon. Can ƙasan carpet ta zauna tare da gaida Hajjiya wanda ba abunda take sai
mata kallon ƙwarilla so take ta tabbatar cikin nan da aka ce tana da shi da gaskiye
ne dan ita fa har yanzu abunda banbara ƙwai ta ke jin sa, ba wai bata yi farin ciki
ba da cikin kawai wace take ɗauke da shi ne bata son ta har zuciya. "Hajjiya tana
miki magana." Ce war Aliyu da ya lura da kallon da hajjiya ke ma Husna ba tare da
amsa gaisuwar ta. "Sai da ta ɗan gyara muryar ta tukunna tace. "Yauwa sannun ki ya
nawin jiki daga haka ta juya ga Hamida da ke latsawa kamar bata ga shigowar su
Husna ba dan ko gaishe bata yi tace. "Wai ina Aisha ce ina ta shiga ban gan ta ba."
"Ina ga kamar ta haura sama tun ɗazu da muka gama cin abinci amma bara na je na
duba ta." Daga haka ta tashi tare da hawa sama dan ƙiran Aisha.

Husna kuwa gaba ɗaya sai taji ta a takure dan ba abunda ta tsammani ba ta ɗauka
yanda Aliyu ya ke ta rawar kai a kan ta da babyn ta to haka Hajjiya ma tunda ta san
yanda ta ke son taga ɗan Aliyu amma sai taga kamar ma bata yi farin ciki ba hakan
ne yasa ta ta kurewa wuri ɗaga tare da kallon ikon Allah dan in bata man ta ba
Hajjiya fa bata son Aisha ko kaɗan amma ji yanzu wai har tambayar ta take ke.

Ba ɗadewa sai ga Aisha da Hamida sun sauko tare. "Sannu Hajjiya Hamida ta ce kina
ƙira na." Ta faɗa tare da zama a ƙasa ita. "Ehh ƴar nan zamu wuce gida." "Har zaku
koma da kun ɗan zauna ai in yaso ko da daddare ne sai ya kai ku." Tana nufin Aliyu.

A'a gwara mu koma dan ina da baƙi da za su zo min anjima kin ga ai gwara su zo su
same ne a gida ai." "Eh hakane kam to a gaida gida daga haka ta tashi tare da haura
wa sama.

Hajjiya kuwa juya kan Aliyu tayi tare da yi mishi nasiha kan ta yayi adalci tsaknin
matayin sa kar ya ce dan wannan allah ya bata ciki sai ya ƙiyi yin adalci Allah na
ganin sa duk abunda yayi kuma in bai yi adalci ba gobe ranar ƙiyama zai tashi da
rabin jiki, sosai ta shi nasiha wanda kuma babu lefi jikin shi yayi sanyi ya kuma
mata al ƙawari zai kaman ta adalci. Suna haka sai ga Aisha ta sauko da leda a hanun
ta tare da miƙa ma Hamida ya ga wannan in kun tafi gida ki buɗe daga haka ta ɗauki
jakar Hajjiya kana suka fita harabar gidan gaba ɗayan su.

Har mota suka raka su kana Aisha ta juya da nufin zata koma tunda ga Aliyu da Husna
duk suna wurin wanda ita kuma bata ma son ganin fuskokin su, amma Hajjiya sai ta
tsayar da ita ta hanyar cewa. "Tsaya! Ke Ali zo ka buɗe mana boot ɗin nan." " ok ya
ce daga haka ya buɗe tare da matsa wa baya dan ba Hajjiya dama. A hankali ta fara
fita da kayan da ke cikin boot ɗin har ta cire gaba ɗaya tare da raba shi biyu
kana tace kowace ta ɗauka kaso ɗaya. Haka kuwa aka yi ko wace ta ɗauki ɗaya tare da
yi mata gode daga haka suka hau mota dan tafiya. Aliyu ya so kaisu da kan shi amma
sai Hajjiya ta hana shi tace yamma tayi ya zauna a gidan sa da iyalan sa driver zai
kai su.

Da haka suka yi sallama da su suka bar compound ɗin gidan.

Aisha ɗauke kayan ta tayi tare tare da wuce wa bangaren ta ba tare da ko kallon
inda suke ba dan ba ƙaramin haushin su take ji kuma jira takwai take su mata magana
da juya msu kwandon balai'i sai aka yi sa'a ba wanda yayi mata magana cikin su sai
ido da suka zuba mata har saida suka ga shigar ta tukunna suka kauda kai daga
kallon ta.

Aisha koda ta shiga part ɗin ta darect ɗaki ta wuce tare da aje kayan dake hannunta
kana ta sauka ƙasa tare da fara gyara ko ina tare da saka turaren wuta kana ta wuce
kitchen ma ta fara wanke–wanke bayan ta gama tayi mopping ta fita tare da kulle
ƙofar falon ta kana ta haura sama. Koda ta shiga ɗaki toilet ta shiga. Bayan kamar
minti 20 ta fita tare da nufan cupboard tare da cire kaya marasa nawi ta saka kana
ta zauna kan kujerar mudubi ta fara shafe–shafe, bayan haka kuma darduma ta dauka
ta shinfiɗa tare da saka hijabin sallahn ta kana ta kabbara sallah asir. Koda ta
idar ta shafa fatiha ta cire hijab ɗin tare da nannaɗe shi ta maida wurin sa haka
dardumar ma kana ta zauna kan gado tare da buɗe kayan da hajjiya ta ba su. Kaya ne
masu kyau da tsada atamfofi ne da sarƙa sai kuma kuɗi a cikin envelope sosai ta ji
daɗin wannan cautar nan ta hajjiya yaishe rabon da hajjiya ta bata koda ta kadda ne
da nufin cautar tana ganin tun tana amarya.

Haka dai tayi ta zumuɗin ɗin dinta har ummi sai da ta ƙira ta faɗa mata abunda ya
faru da canjawar Hajjiya gare ta wanda ita ma sosai tayi mamaki da kuma taya ta
add'a kan Allah ya dai–daita tsakanin su.

Washagari talata Aisha ta karɓi girki wanda tun wuri ta yi aiyukan ta ta gama
dinner ta jera kan dinning kana ta koma falo tare da jeran zuwan sa daga masallaci.
Amma koda ya zo sai ta ga ba shi ƙadai ya bane da Husna suka zo. Da kamar zata yi
magana amma sai tayi shuru dan ganin iya gudun ruwan su me suke nufi da ita ne.

"Sannu da zuwa." "Yauwa sannun ki ke ma." Ya faɗa tare da taɓa cikin sa. "Ya abinci
ya nuna ne cause am really hungry." "Yes ya nuna gashi can kan dinning mu tafi nayi
serving ɗin ka ko." Ta faɗa tare da wullah ma Husna wani kallo alamun she's not
needed here." Wanda ita kam bata gani ba ko kuma ta gane amma tayi kamar bata gane
ba. "Ok! Wifey ya ce daga haka ya tashi tare da nufan dinning area. Bayan ya zauna
ta fara serving ɗin sa ne Husna ma ta taka zuwa wurin su tare da ƙoƙarin zama kan
ɗaya daga cikin kujerun amma sai taji muryar Aisha ta tsayar da ita ta hanyar ce
wa. "Ke kuma fa daga ina?" Cak ta tsaya ba tare da sanin mai zata ce ba. Aliyu ne
yayi ƙoƙarin cewa dan Allah ki yi haƙuri let her site." "Amma kasan this is not the
rule ba why can't she cook her own food sai nawa naga nima zama naye dafa." Sorry
bata hin ɗadi ne and bata iya shiga kitchen zuciyar ta na tashi kuma kinsan she's
not alone." "Uhmm! Kawai tace daga haka ta fara cin abincin ta ba tare da ko kallon
inda Husna take ba ita bata ce ta zauna taci ba ita bata ce koma ba. Haka ta cigaba
da tsayawa ba tare da sanin me zata yi kar ta zauna kuma Aisha ta tashi a kan ta
dan ta lura kamar tsoran ta yake je tunda tana magana bai sake magana ba sai ma
abincin shi da ya cigaba da ci bai ko kalli inda take ba balle ya ce ta zauna, dan
haka ta juya tare da barin part ɗin ma gaba ɗaya haushi kamar ya kashe ta. Haka ta
isa part ɗin ta tare da ɗumama abincin ranan ta ta soma ci dama tana da abincin
kawai tana son cin na Aisha ne kuma ta hana mata.

Da daddare bayan sun kwanta har sunyi bacci amma sai wayar Aliyu ta fara ringing
wanda sau biyu ake ƙira yana kashe wa saboda bacci yayi musu daɗi amma wayar sai
ringing take wanda ya sa shi tashi tare da kunna bedside lam kana ya duba ke ƙiran
sa cikin wannan lokaci amma sai ya ga Husna ce ke ƙiran sa wanda ba ɓata lokaci ya
daga tare da cewa. " Husna lafiya me faru kike ƙira na cikin daren nan kinga lokaci
kuwa?" Firit Aisha ta tashi ita ma jin ya an ba ci Husna. "Na zo?" me ya faru da
kike son na zo?" Ok ina zuwa kar ki damu kinji." Daga haka ya sauke wayar tare da
fuskantar Aisha da ke jefan shi da wani irin kallon tunda taji ya ce wai yana zuwa
ina zai tafi cikin daren nan. "Husna ce wai in zo tana jin tsoro kuma ma wai jikin
ya tashi mata.

P.24

"Husna ce wai in zo tana jin tsoro kuma wai jikin ya tashi mata." " ok to yanzu ya
za'a yi kenan?"

"Kamar ya ya za'a yi baki ji tace bata jin daɗi ba."shuru Aisha ta yi ba dan ta
rasa abun faɗa ba ne kawai bata son su yi rigima da shi a daren nan. Tana gani ya
tashi ya saka kaya ya fita ba tare da ya ce mata uffan ba. Bayan fitar shi falo ta
fito ta zauna tare da zaman jiran shi dan bacci ma ya ƙaurace mata gaba ɗaya. Haka
ta cigaba da zaman jiran sa har bacci ɓarawo ya ɗauke ta a wurin ba tare da Aliyu
ya da wo ba.

Aliyu kuwa koda ya isa part ɗin Husna samun ta ya yi kan kujera hannayen ta bisa
cikin ta. Da saure ya ya zo kusa da ita yana me tambayar ta me ya ke damun ta. Ban
da shisheƙa ba abunda ta ke sai washh ciki ta ke, ganin bata bashi amsa bane yasa
shi shiga ɗakinsa da saure tare da ɗauka key na mota kana ya fita. "Ki tashi mu
tafi asibiti." Jin yana anbatar asibiti ne yasa ta ɗan sau–sauta kukun da take ta
ce. "A'a ba sai mun tafi ba zan samu sauƙi dama an ce min hakan na faru in mace na
da ƙaramin ciki to zata na ciwon ciki." "No!ban yarda ba gwara mu tafi asibitin in
yaso ko magani ne a baki zai fi." Nan fa ta ruɗe ta soma inda–inda da ƙyar ta shawo
kan sa kan ba sai sun tafi asibiti ba. Ganin ta ɗan samu sauƙi ne yasa shi ce wa.
"Tunda kin samu sauƙe ni zan koma sai gobe in jikin bai barki ba sai mu tafi
asibitin." Tana jin ya ce zai koma ta fara kuka wai ita kar ya bar ta ita kaɗai
tana tsoro ga rashin lafiya in jikin ta yayi tsanani wa zai taimeke ta da sauran su
hakan nan ya zauna ba dan yaso ba dan yasan Aisha bata yi bacci ba tana nan tana
jiran shi.

tunanin haka ne yasa shi ɗaukan wayar sa tare da tura mata saƙo kan tayi bacci ba
zai samu zuwa yanzu ba kawai tayi bacci shima yana nan zuwa daga haka ya aje wayar
tare da fuskantar Husna da sai wani yamutsa fuska ta ke dan kawai ta ga yana turawa
Aisha saƙo.

To haka wannan daren Husna ta hana mishi bacci dan da ta ga ya ɗan soma gangaɗi sai
ta nemi abunda sai ya tashi Aliyu bashi ya samu bacci ba sai kusan asuba. Ko bayan
ya dawo daga masallaci darect part ɗin Aisha ya nufa bai ko kalli part ɗin Husna ba
dan ya san yanzu tana ganin shi baza ta bar shi yayi bacci sai ta dame shi da
rikici wanda ya sami mishi suna rikicin masu ciki.

Tana nan falo kwance bata tashi sallahn asuba ba ta makara dan daɗewar da ta yi a
farke last night. Ƙarar buɗe ƙofar da taji a cikin bacci ne ya farkar da ita. A
hankali take buɗe idanun ta har ta buɗe su tarr a kan sa, wanda ya rufe ƙofar kenan
ya juya zai shiga ɗaki suka haɗa ido da shi sai yanzu ma ya lura da ita dan bai
kawo a nan zai same ta ba. Sai da tayi mishi kallo tun daga sama har ƙasa tukunna
ta kau da kai gefi wato sai yanzu ma ya ke dawo wa, da bata gan shi ba da sai dai
ya shiga ciki ya kwanta kamar wanda a nan ya kwana hmm kwafa taja a ran ta tukunna
ta tashi tare da wuce war ta ɗaki ko kallon inda ya ke bata yi ba balle har ya samu
darajar gaisuwa.

Aliyu kam sabon mamaki ya ma kasa magana shi Aisha ta gani amma tayi banza da shi
kamar wanda baya wurin, to me ya faru da da har zata ganshi amma ta tsallake shi ba
tare da ta nuna ta ma ganshi balle ta mishi magana. Ganin ba mai ba shi amsa ne
yasa shi mara mata baya.

Aisha kam koda ta shiga ɗaki toilet ta fada tare da yin uzirin ta ta fita tare da
saka hijab da shinfiɗa darduma ta kabbara sallah.

Tana cikin sallah ya shigo ɗakin tare da zama a bakin gado, yana zaune ta idar da
sallah tare da shafa fatiha ta tashi tare da ƙara shiga toilet wannan karan wanka
tayi har ta fita yana wurin gaba ɗaya ma ya kasa yin magana da zarar ya buɗe baki
zai yi magana in ya ga yanda ta haɗe fuska sai ya kasa.

Har ta gama shiryawa ta saka ƙaramin hijabi kana ta juya kan shi. "Ina kwana." Daga
haka tayi waje abun ta bata ma tsaya taji ya amsa mata ba ta bar mishi ɗakin.

Aliyu fa ya shiga ruɗu gaba ɗaya jikin sa ya yi sanyi baccin da ya ke ji ma ya


watse ya ma rasa me zai yi haka nan ya tashi ya bi bayan ta.
A tsakiyar staircase ya tsaya tare da zuba mata idanun nan nasa masu kaife. Tana sa
ne da stayuwar shi amma sai bata nuna ta ma san wata halitta na wurin ba har ta
gama gyara ko ina na falon ta yi shara da mopping duk yana tsaye a wuri ɗaya shi
bai shiga falon ba shi bai hau sama ba, har ta gama ta shiga kitchen.

Aliyu fa yau ya zama jela dan har kitchen sai da ya bi ta har ta gama haɗa musu
breakfast yana wurin. Haka duk inda ta shiga sai ya bita ba tare da ɗaya daga cikin
su ya yi magana ba.

Koda ta gama jera abun kare kan dinning suka zauna cin abincin bata kulla shi ba
sai ma serving ɗin sa da ta yi za ta zuba wa kan ta kenan ya riga ta ɗaukan serving
spoon ɗin ya soma serving ɗin ta.

Koda ya gama zuba mata bata nuna rection ba kawai karɓa tayi ta fara ci ba tare da
ce wa komai ba wanda shi ya ke ƙara daga mishi hankali.

Ganin lallai tabbas in bai yi magana ba to Aisha baza ta yi ba and is killing him
baya son tana fushi da shi ko kaɗan ne.

Dan gyara murya yayi kana ya soma mata magana. "Am sorry na san ban kyauta ba."
"Uhmm! Kawai ta ce daga haka ta cigaba da cin abincin ta. "I said am sorry ke ma
kin san haka kawai bazan yi haka ba ba muna tare ta ƙira ba." "Uhmm! Kawai ta sake
yi. "Wai what is wrong with you ne eh why are you behaving this way dan kawai yar
uwar ki bata da lafiya na tafi wurin ta shine kika wani abu kamar wanda aka kashe
miki mutum." Ya faɗa a ɗan zafafe. A hankali ta aje spoon ɗin dake hannun ta tare
da nannaɗe hannayen wuri ɗaya kana ta soma magana. "How am are behaving?" Tell me
how am behaving?" Oh my God! You know what tunda ka kawo wannan topic da kanka let
me ask you one question, da ka je wurin ta me ka mata? Don't tell me ka kai ta
asibiti dan nasan ba ku tafi ba, so what on earth ka je ka mata ta faɗa da ɗan
ƙarfi tare da tura plate ɗin da ke gaban ta wanda ya faɗi ƙasa ya tarwatse. Bata
kulla da wannan ba ta cigaba da magana. "Dan kawai bana magana you assume za ka ka
yi duk abunda ka ga dama or what Ali.

"What are you doing ne haka ya kike behaving kamar wanda aka mata abu babba rashin
lafiya ne fa wanda ke ma zai iya hawa kan ki kuma ma ba na tura miki da saƙo kan
kiyi bacci zan dawo daga baya." "I know why ka ke min duk wannan abubuwan dan kawai
ni allah bai bani haihuwa ba shi yasa ka ke treating ɗina haka daga haka ta fashe
da kuka. "Kullun–kullun sai ka nemi one thing or the other dan ƙuntatamim dan haka
ne na yanke shawara gwara na bar gidan kowa ya huta." "Me kike nufi da zaki bar
gidan." "Yes yanda ka ji zan bar gidan in huta wa raina cause i can't take it
anymore tunda ka ƙara auren nan kullun sai kun min abinda zai ɓata min rai ko dan
kun ga bana magana ne eh?" Ta faɗa da ƙarfi wanda ya sa aliyu tashi wa tare da
matsawa kusa da ita. "Don't even try coming near me dan ba abunda zaka faɗa min da
zai sa ni canja ra'ayi na ba. A hankali ya ke takawa har ya isa in da take tsaya
tare da riƙe hannayen ta biyu kana ya soma magana a hankali. "Please stop this dan
allah in ma wasa kike to ki dai na bana so, lefi ne nayi kuma na baki haƙuri dan
allah kiyi haƙuri hakan ba zai sake faruwa ba please." Ya faɗa tare da haɗa ta da
jikin shi. Gaba ɗaya ta tattara ƙarfin ta da allah ya bata ta ture shi tare da ce
wa. "Ai haka ka ke ka ma mutum abu sai kazo kana bashi haƙuri kuma hakan ba shi zai
hana ka ƙara mai–maita ba." Tana gama faɗan haka ta haura sama da gudu. Aliyu ganin
fa da gaskiye take ne yasa shi sauren mara mata baya.

"Dan allah kiyi haƙuri wallahi allah hakan ba zai sake faruwa ba kuma maganar
kwanan da nayi jiya zan biya ki amma dan allah kar ki ce zaki bar gidan nan please.

Aliyu ya faɗa bayan biyo ta ɗaki da ya yi ya ga tana jan suitcase ɗin ta kan ita fa
sai ta bar musu gidan in yaso suyi duk abunda suke so, wanda ganin ta ƙi saurarn
shi ne yasa ya kulle ƙofar ɗakin tare da cire mukullen ya saka a aljihunsa kana ya
cigaba da magiya.
Da kyar aliyu ya shawo kan Aisha kan ba zai sake mata abunda ya yi jiya da daddare
ba kuma zai biya ta kwanan ta tukunna ta haƙura.

Sai da ya tabbatar ta huce zuciyar ta tayi sanyi tukunna ya buɗe ƙofar koda ya zo
fita ma sai da ya aje mata kuɗaɗe kan wai ƙilla tayi marmarin abun ta siya tukunna
ya fita aiki bawon allah ko breakfast bai samu ya ci ba ya fita office sabon
tention da Aisha ta kunnu mishi.

Haka yau ma da dare bayan sunyi shirin bacci har sun fara bacci sai ga ƙiran Husna.
Aliyu yana jin ƙarar wayar shi zuciyar shi ta soma bugawa da saure ya ɗau wayar
tare da saka ta silent ya koma ya kwanta duk da ya saka wayar a silent haka bai
hana wayar vibrating ba, ganin hakan ne sai ya kashe wayar ma gaba ki ɗaya duk
abunda ya ke Aisha na kallon shi amma sai tayi kamar bata gani ba. Babu jimawa sai
ƙaramar wayarsa ta soma rure ita ma Aliyu fa ya ruɗe ya rasa me zai yi nan ita ma
ya danna ta a silent kana ya koma ya kwanta.

Aisha ce ta tashi tare da ce mishi "me yasa ka kashi wayoyin ka ba naga ana ƙiran
ka ba." "No! Kar ki damu kawai ki baccin ki gobe zan bi ƙiran." ya ce daga haka ya
kashe ɗayar wayar ma. "Okay! Daga haka ta koma ta kwanta tare da tunanin me za ta
yi wa husna ne don dole sai ta koya mata hankali dan ta ga abun na ta ya fara wuce
gona da iri ko dan ta ga bata kulla ta ne. "Yes! Ta faɗa dan ƙarfi sako mokan tuna
yanda zata gama da ita cikin ruwan sanyi ba tare da wani tashin hankali ko faɗa ba.
hmm Husna just wait for me zaki gane shaye ruwa ne yarinya ke har kin isa ki ce
zaki raba ni da mijina humm allah ya kai mu gobe sai nayi maganin ki."

Washagari safe Husna ta musu san mako tana sallah ta dawo part ɗin Aisha wai ta zo
wurin Aliyu jiya da daddare jikin ta ya tashi mata tai ta ƙiran shi ya ki ɗaukan
wayar har saƙo sai da ta tura mishi amma bai ƙira ta ba da dai sauran su. Aliyu
kuwa sai faman bata haƙuri ya ke.

Aisha da ke gyara falon bata tanka musu ba sai ma cigaba da gyaran ta take amma
duk abunda suke faɗa tana jin su. Bayan ta gama ta haɗa breakfast ta yi wanka ta
sauka duk Husna na nan kuma da gani bata da niyyar tafiya, dariyar mugunta Aisha
tayi da ta tuna abunda ta shirya ma Husna.

Husna kuwa tana can falo da Aliyu sai faman mita take masa wai wannan na mata ciwo
sai wannan na mata ciwo. Aliyu tun yana ce mata sorry har ya gaji ya zuba mata
idanuwa.

Aisha bayan ta kammala jera abincin kan dinning ta dawo falon tare da sanar da
Aliyu breakfast fa ya zama ready ya zo su ci. Husna na jin haka sai ta ƙara marai–
rai cewa wai ita ga mai ciki.

Aliyu zai yi magana kenan sai Aisha ta da katar da shi ta hanyar cewa. "No my king
ka bar ta yau kaɗai nan muye breakfast tare beside na mata na ta special wanda ita
kaɗai za ta ci dan na masu ciki ne." Gaba ɗayan su suka tsaya suna kallon ta dan ba
suyi tsamanin haka ba. "What ya kuke min wannan kallon ne, kawai dai naga tana shan
wahalar cikin bata bacci da daddare kuma bata iya girki da kanta kuma ko an mata
bata ci sai an ƙara wani ne yasa na na fara bincike kan maganin wannan matsalar ta
ta, kuma gust what na samu maganin kuma daga babbar macece ta tace na mata girki da
shi in sha allah zata warke har ta haihu baza ta ƙara jin wani abu me kama da
laulai ba. Ka ga shine ma yanzu na dafa mata dashi za ta ji daɗin sa sosai." Da
gaskiya dama akwai maganin laulayi shine ta ce min babu." Ya faɗa tare da fuskantar
Husna da gaba ɗaya ta shiga ruɗu kan maganar Aisha wanda har ta rasa me zata ce.
"No! Babu maganin laulayi haka ne amma akwai irin nata wanda ta na shan wannan
farfesun nan zata warke garau abunta.

P.25
Tana gama faɗan haka ta tashi tare da zuwa wurin dinning ta fara serving ɗin su.
Koda ta zo zuba wa Husna sai da ta saki murmushin mugunta kana ta zuba mata
farfesun kayan ciki da ta haɗa mata ita kaɗai kana ta ƙira su da su zo ta gama
serving.

Ba tare da tunanin komai ba Husna ta zauna kan kujera tare da jawo plate ɗin
ferfesun gaban ta sabon ƙwadayi bakin ta har tsinke wa ya ke.

Bata yi wata–wata ba ta sa a baki, dummm taji kanta ya ba da saka mokon jin wani
irin bala'i a bakin ta wanda har kwanyar ta sai da taji. Ba abunda ya faɗo kan ta
sai wannan ranar da ta shiga ta ɓata wa Aisha girki dan kuwa yaji ne na fitan
hankali da kuma ɗacin bala'i a cikin ferfesun. Da saure ta haɗe tare da ɗaukan cup
ɗin ruwa da Aisha ta aje mata kusa da ita ta soma sha, amma mai makon ta ji sauƙin
abun sai ta haɗu da wata iriyar bala'in gishire a ciki zata zubar kenan Aisha ta
ce. "No! Ki haɗe magani ne ta ya zaki zubar." Husna sabon abunda ta ke ji ta ma
kasa magana sai ma ƙoƙarin barin wurin da ta ke, Aisha na ganin haka tayi sauren
cewa ina zaki tafi kuma bayan baki gama ci ba ko taɓawa baki fah." "No! No aunty na
ƙoshe bazan iya ci ba." "Kamar ya baza ki iya ci ba bayan na sha wahala na girka
miki shine zaki ce ba zaki iya ci ba." Aisha ta faɗa da muryar tausaye. Aliyu ganin
haka ne ya ce da Husna ta zauna ta ci koda rabi ne tunda Aisha ta sha wahala ta
dafa. "No! Bazan iya ci ba babu daɗi fa kuma ɗaci kamar ansa kanwa a ciki ga yaji i
can't." Aliyu zai yi magana kenan Aisha ta da katar da shi ta hanyar ce wa. "Babu
damuwa dama na saba ai in na dafa mata abu bata ci wanda na rasa gane me yasa, kuma
ma taya kike son magani yayi daɗi dama ance zafi shi ke cire ciwo baki san yanda na
sha wahala wurin neman wannan maganin ba da kin sani da baki ce baza ki ce. Ki
daure ko kaɗan ne ki ce zan ji daɗi amma in baza ki ci ba ma babu damuwa zan
zubar." Ta ƙare maganar da murya me sanyi irin an maka abu baka ji daɗi ba. Ganin
haka ne Aliyu ya ce Husna ta koma ta zauna taya za'a sha wahala wurin nema mata
magani amma ta wani ce baza ta ci ba. Ganin yanda ya haɗe fuska ba alamar wasa ne
yasa Husna koma ta zauna tare da kallon abincin ba tare da sanin me zata yi gaba
dan gaskiya ba za ta iya cin wannan abincin ba, ban da ɗaci da yajin da ke ciki ba
ko gishire babu balle maggie. Ganin bata da niyyar ci ne yasa Aisha ɗauke plate ɗin
tare da matsawa kusa da ita kana ta fara ɗebo tana saka mata a baki duk da Husna
bata son buɗe bakin ta Aisha sai danna bakin take har sai ta buɗe sai ta zuba mata
a baki da zarar taga tana buƙatar ruwa sai ta zuba mata ruwan gishiren da ta haɗa
gefe nan da nan Husna ta fara kuka amma Aisha bata bar ta ba sai faman ɗura mata
take.

da zarar taga Aliyu zai yi magana sai tayi sauren cewa. "Dama matar ta ce ba
lallai ta iya ce ba sai an mata dole amma da zarar.ta cinye tofa lafiya ta samu da
yardan allah." Da jin haka Aliyu yayi shuru da bakin sa dan shima karan kansa ya
fara gajiya da wannan rikicin husna gwara ta sha maganin shima ya ɗan huta wa
ranshi.

Aisha saida ta tabbatar Husna ta sha rabin ferfesun tukunna ta sake ta kana ta
tattara kayan ta kai kitchen tare da wanke plate da cup ɗin kar tsautsaye yasa
Aliyu taɓa su ya gane ba magani ba ne.

Husna tana ganin Aisha ta shiga kitchen tayi anfani da wannan damar ta bar part ɗin
gaba ɗaya in banda kuka da hura wa bakin ta isa ba abunda take, koda ta shiga part
ɗin ta darect toilet ta shiga tare da ɗaukan brush ta fara dirja bakin ta dan har
yanzu take jin yajin da ɗacin a bakin ta gishren kam ba a magana. Ganin har tsawon
minti 30 ta ɗauka tana dirja bakin amma still tana jin wannan zafin wanda bakin ta
har ya fara tsalewa ne yasa ta barin toilet ɗin ta tafi kitchen tare da buɗe
fridge. Yogurt da juice masu zaƙi ta ɗauka wanda ta san zai canja mata test ɗin
bakin ta fara sha, duk da haka wannan test ɗin yana nan a bakin ta ganin ba zai
ɓace ne yasa ta haƙura da shi ta koma falo tare da kwanciya kan kujera kana ta soma
tunanin abunda Aisha ta mata kuma tayi alƙawari sai ta rama. ba dai suna gida ɗaya
ba sai ta ma ta abunda zai ɓata mata rai ita ma.

To tunda daga wannan ranar Husna koda wasa bata sake zuwa part ɗin Aisha ba har
girki ya zo kanta. Haka nan Aisha bayan tayi sallah magrib da isha tayi kwalliya ta
nufi part ɗin Husna a can taci abinci abunta har ƙarfe 11 Aisha na can kuma ba ta
da niyyar dawo wa part ɗin ta dan hira ma suke da Aliyu. Husna tun tana ciwa lokaci
ya wuce fa a wasa dan dai kawai Aisha ta gane ta kuma ba su waje har ta fara zirya
ta shiga ɗaki wai ita zata yi bacci in kuma bata ga ya biyo ta ba sai ta ƙara
komawa falon gaba ɗaya ta rasa ya zata yi da Aisha ne tunda ta mata hannun ka mai
tsanda amma bata gane ba.

Aisha kuwa tana sane da duk abunda Husna ke yi amma sai ta yi banza da ita tayi
kamar bata gane me take ba dan ta ce yau sai ta kai Husna maƙura yanda take mata
haka ita ma zata mata daga yau duk abunda ta mata to ita ma sai ta mata in bata so
ta gyara in kuma ba haka ba to kuwa haka za su ƙare dan ta rantse ta dena raga mata
wallahi tunda ita ba hankali ne da ita ba ba ta san ya kamata ba.

Sai 11:25 ta bar part ɗin su ta koma na ta koda ta tashi dan kawai ta tusa ma Husna
baƙin ciki ta ce wa Aliyu ya raka ta baza ta iya tafiya ita kaɗai ba dan tsoro take
ji. Banda cika da batsewa ba abunda Husna ke yi sabon baƙin ciki ko magana ta kasa,
tana ji tana gani ya raka Aisha har part ɗin ta tukunna ya dawo.

Wannan kwana biyun da suka wuce haka Aisha ta ke tsiro da abubuwa duk abunda ta san
Husna tana mata to shi take yi kuma ba lefi sosai yake ɓata ma Husna rai, wanda da
girki ya ƙara zaga yowa kan Aisha Husna bata taka tazo wurin Aisha ba har ta gama
girki ta karɓa, hakan ne yasa Aisha dena abunda take mata tunda ta dena mata.
Yanzu zama suke kowa na side ɗin shi ba abunda ke kawo wani bangaren wani Duk da
zaman su nan bai hana Husna yin makirci ba, dan duk abunda tasan zai sa suyi faɗa
to sai tayi Aisha ta ɗauka Husna zata shiga hankalin ta amma ina abun sai ma ƙara
gaba ya ke.

Husna kuwa sosai ta ke bin huɗubar Baba dan sun rantse ko yaya ne zai sun cire
Aisha a gidan, wanda kuma sun kusa cima manufar su tunda ba'a rana ɗaya ba su samu
saɓani tsakanin ta da Aliyu.

Zaune suke kan couch ɗin ɗakin Husna, Husna ce ke ba lubna abun farin ciki da ya
same ta wato ciki da take da shi, sabon tayi nesa a zubar da take bata lura da irin
kallon da lubna ke bin ta da shi ba, sai gaya mata abubuwan da take son cin ma da
cikin na wanda dayawa daga su ta samu Sai da ta kai aya tukunna luba ta mata kallon
sama da ƙasa tukunna ta ce da ita. "Ashe ke shasha ce ban sani ba." "Kamar ya
shasha?" Me kike nufi." "Eh mana yo in ba shasha ba wa ya ce miki yanzu ana aure
kawai sai a haifu." "Wait nifa ban gane me kike nufi ba ki yi min baya ni." "Kinga
duk kyaun ki nan ta kina haihuwa zai ɓace kinga wannan breast na ki da kike ji da
shi ko baki saka bra ba ma yana nan da kyaun sa to wallahi kina haihuwa zasu zube
su zama kamar slippers kin ga yanda nonon Baba ya ke to kema haka na ki zai zama.
karki ga yanzu yana ta rawar kafa a kan ki dan kina da ciki kiyi tsammanin haka zai
miki bayan kin haihu dan kuwa duk wannan soyayyar zata koma kan babyn ke kuma ko
oho." "Wait ki min bayani ta yanda zan gane mana." "Ke baki ga Aisha ba yanda take
da kyaun ta har yanzu kamar wace bata taɓa aure ba kullum ƙara kyau take, baki ga
yanda ya ke gujewa ɓacin ran ta ba kinga har yanzu bata haifu ba amma gaba ɗaya bai
damu ba." "Me hakan ke nufi." Husna ta tambaya.

"That only means bai damu da haihu ba kuma kina haihuwar nan kin zama tsohuwar
yayi, ke wahalar baby kaɗai ma ta ishe ke wallahi." Nan fa lubna ta soma ɗaura ta
kan keken ɓera tun bata ɗauka har ta fara ɗaukawa sai yanzu ita ma abun ya zo kan
ta nan fa ta fara sake–sake.

"To amma luby ya kike ganin za'a yi yanzu tunda dai cikin ya riga da ya shiga kuma
Baba tana son anfani da wannan cikin ta fitar da Aisha da kuma cika burin mu na
zama ni kaɗai a gidan Aliyu."

"To ai bata ɓace ba har yanzu zaki iya cire ta da shi kuma ki cika burin ki."
"Kamar ya ban gane ba."

"Uhmm za mu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne yarinya." "Kamar ya ni fa har yanzu
ban fahimta ba."

"Kawo kunnen ki ki ji." Daga haka ta soma raɗa mata magana a kunne wanda nan da nan
fuskar ta ta mamaye da farin ciki. Tass suka tafa kana Husna tace. "Amma ba kya
tunanin za a gane ba." "Ke dalla wa zai gane in ba ke bace zaki faɗa ba wa zai
sani, ke dai kiyi abunda na sa ki kawai zaki ga aiki da cika wa ke yanzu wa ya ke
ta boka. "To shi kenan yanzu kamar yaushe kike tunanin zamu ai wa tar da shirin."
Ko gobe ki ka ce ma ni am ready zan ka miki maganin kawai ki san yanda zaki yi Baba
ta zo ranar kuma Aliyu ma ya kasan ce yana gidan ranar. And don't forget kar ki
faɗa wa kowa daga ni sai ke.

P.26

"Ai karki damu ba wanda zai ji maganar nan daga ni sai ke." "Yauwa yar gari ko ke
fa kin ga ko ita Baba ba zata ta san me ya faru ba sai dai ta ji labari dan kuwa in
kika kuskura ki ka faɗa mata to fa baza ta taɓa barin mu mu cigaba da plan ɗin mu
ba, dan zata ce miki za ta yi maganin matsalar ne har cikin ya girma baza ta kawo
miki ma fita ba kinga kuwa in cikin ya girma ba zaki iya zubar da shi ba, sai dai
ki haife shi in kuma ba haka ba to sai dai ki mutu fa."

"Chab karen hauka ne ya cije ne da zan faɗa mata ke kin san irin burin da ta ke da
kan wannan cikin kuwa, ai da in faɗa mata zan zubar da cikin nan gwara na ce mata
na kashe wani ne dan wallahi baza ta taɓa yar da ba." "To kin ji sai kiyi hattara
da bakin ki." Daga haka suka soma shirya plan ɗinsu ta yanda ba wanda zai zarge su.

Bayan kwana biyu, Aisha na zauna cikin falon ta tana kallon indain series ɗin ta da
ta saba kallo, gaban ta snacks ne da zobo me sanyi a jug. Sosai ta mai da hankalin
ta kan kallon da har bata san sanda aka tura ƙofar aka shigo ba. Sallamar ta da
taji ne yasa ta ɗaga kai ta dube ta tare da amsa sallamar daga haka bata sake
magana ba. Husna kam ko a jikin ta ta nema wuri ta zauna kana ta soma jefa wa Aisha
hira sama–sama. Aisha kam daga uhmm sai uhmm kawai dan bata yarda ta sake da ita ba
dan ta san akwai abunda ya kawo ta dan haka kawai Husna baza ta zo wurin ta ba.
Husna kam ko a kwalar rigar ta dan ba hira da Aisha bane ya kawo ta tana da motive
ɗin ta amma saboda kar Aisha ta zarge ta sai ta cigaba da kallon ita ma da yi mata
hira sama–sama duk da Aisha ba wani tanka mata take ba.

Ganin Aisha na shan zobo ba tare da yi mata tayi bane yasa ta tambaya. " lahh Aunty
wannan zobe ne?" "Hmm! Kawai Aisha ta ce daga haka ta cigaba da shan zobon ta.
Ganin ko wani minti Husna sai ta ɗaga kai ta kalle ta ne yasa ta tunanin ko zobon
ne ya shiga ranta abun ka da me ciki, tunanin hakan ne yasa ta ɗauko ɗayan cup ɗin
tare da zuba mata kana ta miƙa mata. Husna na ganin ta miƙa mata cup ne tayi sauren
karɓa kana ta soma sha kaɗan–kaɗan. Jin kamar ƙaure na tashi ne yasa Aisha sauren
tashi tare da nufan kitchen chap ta manta ta ɗaura abu a kan wuta ta zauna wa kallo
ga shi abu ya ƙone.

Husna na ganin Aisha ta bar falo tayi saure ta cire ƙullin maganin da ta zo da shi
tare da buɗe uku daga shi ta sa a zubon ta kana sauran ta tusa a gefen kujerar da
Aisha ta tashi daga ita kana ta saka hunnun ta cikin cup ɗin ta fara juyawa sai da
ta tabbatar ya juyu da kyau tukunna tayi sama da cup ɗin ta shanye gaba ɗaya ba
tare da ta rage ko kaɗan a ciki ba. Duk wannan abun nan da take idon ta na kan
ƙofar kitchen dan ganin ko Aisha na zuwa sabon tsoro da fargaba jikin ta har rawa
yake ga kuma zufa da ke karyo mata ta ko ina.
Ta gama sha kenan sai ga Aisha ta fito daga kitchen ɗin tare da zama kan kujerar ba
tare da ta ankara da abunda Husna ta sa mata ba ta zauna tare da cigaba da kallon
ta. Husna ganin ta ai watar da abunda ya kawo ta ne yasa ta miƙe wa. "Tom Aunty ni
zan koma part ɗin na ina ɗan jin bacci." "Ok! Kawai Aisha tace.

daga haka Husna ta bar part ɗin da dariyar mugunta ita kadai ta san me ta shirya
mata. tun kafin ta isa part ɗin ta ta soma jin ciwon ciki wanda da kyar ta isa part
ɗin tare da zama a ƙasan carpet. Ganin ciwon sai ƙaruwa yake ne kuma gashi ta fara
ganin jini ne yasa ta ɗauke wayarta tare da danna wa Aliyu ƙira bugu biyu ya ɗaga.
bata barshi ya yi magana ba ta katse shi da kuka kan ya dawo gida yanzu babu lafiya
cikin ta. Da jin haka Aliyu ya katse ƙiran tare da ƙara wa motar gudu dan dama yana
hanyar dawo wa ne Husna ta ƙira.

Babu ɓata lokaci Aliyu ya zo gidan tun kafin ya iso gate ya ke faman danna horn
wanda me gadi na ji ya hanzarta ya buɗe mishi gate. Aliyu bai ko bari an buɗe mishi
gate ɗin gaba ɗaya ba ya danna kan motar ciki.

Yana shiga ya buɗe murfin motar ya fita da saure ya nufi part ɗin Husna, wace a
yanzu ta gama jigata dan da gani ta sha maganin overdose ne dan sosai take bleeding
a yanzu kuma bata ma san ina kan ta yake ba.

Koda ya shiga ya gan ta a wannan halin hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba dan
haka bai jira tambayar ta me ya faru ba, kawai ya ɗauke ta tare da fita da ita tun
kafin ya isa motar ya ke ƙwalla wa me gadin ƙira da ya buɗe gate. A bayan mota ya
saka ta kana shima ya zaga ya buɗe murfin direba ya shiga tare da kunna motar a 80
suka bar gidan sai asibiti.

Aisha na kitchen tana kwashe sanwar dare lokacin da Aliyu yazo har ya fita jin
hayaniyar motarsa ne da muryar sa lokacin da yake ƙwallawa mai gadi ƙira ne yasa
ta bar abunda ta ke ta fita waje dan ganin me yake faruwa ne haka. Amma koda ta
fita ba ta tarar da Aliyun ba sai mai gadi da ke rufe gate bayan fitar su Aliyun.

"Baba mai gadi wai me ke faruwa ne ina ta jin hayaniya haka." "Uhm Hajjiya babba ni
ma ban sani ba kawai dai na ga Alhaji ya fito da Hajjiya ƙarama cikin tashin
hankali kuma da gani bata numfashi dan in banyi ƙarya ba kamar jini na gane a rigar
Alhaji da zai shiga mota." "Husna?" Jini?" Wata hajjiyar ne kake nufi ba dai Husna
ba?" "Ai ita ce Hajjiya amaryar Alhaji ba." "Ok Baba na gode." Daga haka ta koma
falo tare ƙiran Aliyun a waya amma ba ya ɗaga wa daga ƙarshe ma kashe wayar yayi.
Nan fa Aisha ta shiga tashin hankali kan me ya samu Husna bayan yanzu–yanzu babu
ɗadewa ta zo wurin ta kuma har ta koma lafiyan ta ƙalau, to me ya faru ne haka da
har tana zubda jini kuma ma wai bata nunfashi.

Bayan zamab jira na awa ɗaya da rabi Dr ya fito tare da kallon sa kana ya ce da shi
ya biyo shi, ba musu ya bi bayan Dr zuwa office ɗin shi.

Bayan sun shiga office Dr ya zauna kan kujerar sa kana ya nuna mishi wuri da ya
zauna shi ma.

Dr sai da ya ɗauke kusan minti biyar yana rubuce rubuce kan wata farar ta karda
kana ya ɗago ya dubi Aliyu, sai da ya sauke nunfashi tukunna ya soma magana kamar
haka." "Me haɗin ka da patient da ka kawo?" "Mijinta ne ni Dr dan allah faɗa min me
same ta." Sai da Dr ya ƙara mishi wani kallo tukunna ya ce." Kai ne mijinta?" To
amma me yasa za ka bar ta tasha irin wannan maganin bayan kun san me hatsare ne ko
cikin maganin zubar da ciki shi me hatsare ne a ina ma ku ka samu dan irin wannan
ba ko ina ma ake siyar wa ba." "Zubar da ciki?" Me kake nufi Dr kana nufin matata
ta sha maganin zubar da ciki?" " yes matar ka maganin zubar da ciki ta sha kuma
overdose ta sha." Banda innalilahi wa inna ilaihi rajun ba abunda Aliyu ke an bata.
Ganin irin halin da ya shiga ne yasa Dr cewa da alama ba tare da sanin ka ba aka yi
wannan ta asar ba yanzu dai kayi haƙuri tunda aikin gama ya gama sai a kiyaye gaba.
yanzu dai cikin ya zube an kuma yi mita wankin ciki zuwa gobe in sha allah in komai
yayi dai–dai za'a sallame ku." Daga haka ya miƙa masa wata farar ta karda "Ga
wannan magungun da ake buƙata ne nan." Ba tare da ko uffan ba Aliyu ya ƙarbi ta
kardar tare da fice wa daga office ɗin, shi kaɗai ya san me yake ji a zuciyar shi
ace yanda ya sa rai kan cikin nan shi ne Husna ta rasa da me zata saka mishi sai
zubar kashe masa ɗansa eh jininsa.

Husna ce kwanciye kan gadon marasa lafiya hannun ta ɗaya a sakale da drip. A
hankali ta soma buɗe idanun ta har ta buɗe su tar kan fuskar shi da gaba ɗaya babu
alamar murshi a ciki sosai ya haɗe fuska babu alamar rahama a ciki, idon nan sunyi
jajur da su kamar gauta sai nunfashi da ya ke sauke wa a hankali dan baya son
zuciya ta ɗebe shi ya aikata abunda bai kamata ba.

Sosai ta tsorota dashi, sai yanzu komai yake dawo mata daki–daki a kai da saure ta
ɗaura hannunta a kan cikin ta jin babu wannan kaurin da dungulewar ne ya tabbatar
mata da cewa cikin ya zube, duk da da yar dar ta aka yi komai amma sai da taji
zafin zube war cikin tunda ko ba komai jinin ta ne.

Ganin duk abunda take yana kallon ta ne yasa ta kukun munafurici wai ina cikin ta
ya ke ina aka kai mata ɗan ta a fito mata dashi me yasa bata jin motsen sa. Aliyu
tun yana ɗaukan abun na ta iskanci ne har ya faɗa tarkon ta dan kuwa ƙaramin hauka
ta tayar musu da kyar ya shawo kan ta ta nutso. Kana ya soma tambayar ta me ta ci
kuma akwai inda ta fita ne da dai sauran su. Nan ta fara sanar dashi ba abunda ta
ci tun breakfast ɗin ta kuma ba inda ta tafi sai part ɗin Aisha kuma ma bata ci
abinci ba sai zubo da Aisha ta ba ta. Nan fa Aliyu ya shiga tunanin ina Husna ta
samu maganin zub da ciki kuma me hatsare haka, Aisha ce ta faɗo mishi a rai nan
take ya kau da tunanin daga ransa tare da alƙawarin sai yayi bincike.

After some minutes Husna ta samu tayi bacci sakamakon allurar bacci da aka mata
wanda sai a alokacin Aliyu ya samu damar buɗe wayarsa tare da duba lokaci, ganin
har margrib ma ta kusa ne yasa shi fita da nufin zai koma gida ya sanar da Aisha
sai kuma ya ɗauko ma Husna wasu kayan.

Koda ya isa gida bai samu Aisha a falo kuma bata ɗaki amma ya ji ƙarar zubowar ruwa
a toilet wanda hakan ya tabbatar masa da tana wanka dan haka bai tsaya jiran ta ba
ya koma falo tare da zaman jiran ta.

Koda ya koma falon bai zauna ba sai faman zirya da yake da ya gaji da tsayuwar sai
ya zauna kan kujera amma sai yaji abu na sukan shi wanda hakan ne yasa shi tashi wa
tare da duba kujerar. Nan ya saka hannun shi tsakanin kujerar ba ɓata lokaci ya
cire maganin tare da ɗaura shi kan center table da tunanin ko maganin Aisha ne ta
bar shi a nan, amma bai san me yasa ba wani abu ya ce ya duba ya gani wani irin
magani ne. Ya na duba wa kuwa ya ga maganin zubar da ciki ne. amma bai yarda ba nan
ya cire wayarsa tare da shiga Google nan yayi research kan sunan maganin. Nan ya
tabbatar da maganin zubar da ciki ne kuma me hatsare ma kuwa, nan maganar Husna na
ɗazu ya faɗo masa kan Aisha ta bata zobo ta sha ya dawo kan shi nan da nan ɓacin
rai ya mamaye shi. Bai yi wata–wata ba ya nufi ɗakin Aisha.

Fitar ta kenan daga bayi ta na me shafa me a jiki ta ji an banko ƙofar da ƙarfi da


har ta tsorota, ganin shi ne yasa ta ɗan sauke nunfashi tare da zuwa wurin shi nan
ta soma tambayar shi me ke faruwa ne ɗazu taga ya fita da Husna cikin tashin
Hankali. Sai da ya mata kallon tsab tukunna ya soma magana. "Why kike tambaya ne
akwai abunda kike jira ya faru ne?" Aisha da bata gane ina maganar shi ta dosa ba
tace. "Eh!amma ina fatan komai lafiya ko naji wai har bleeding take." Jin ta amsa
mishi da eh ne ya ƙara tabbatar mishi da abunda yake zargin ta dashi. "Dazu Husna
ta shigo miki ne?" "Eh! Amma ma ke faruwa ne." Ta tambaya dan ita bata ga dalilin
wannan tambayoyin nasa ba. "Hmm akwai abunda ta ci ko ta sha?" "Aa bata ci komai ba
amma ta sha zobo gaskiya." "Ok! Ya ce daga haka ya miƙa mata maganin tare da cewa
ga maganin ki nan kin man ta a falo." Aisha da bata san me ke faruwa ba ta ƙarbe
maganin ba tare da ko kallon sa ba ta a aji gefi tare da cewa yauwa na gode ko
kasan tun ɗazu ina ta neman shi ban gani ba." Ita duk a tunanin ta maganin ciwon
kai ne da ta aje ɗazu amma bata gani ba. Jin haka ne Aliyu ya ƙara har zuƙa ya soma
tambayar ta. "Why me yasa kika aika ta?" "Me na aika ta ban gane ba." Cikin ihu da
karaji ya ce. "Na ce me yasa kika aika ta ehh me yasa kika zubar mata da ciki?"
Cikin ruɗe Aisha ta ce. "Ban fa gane maka ba wa aka zubar wa da ciki." "Don't even
try it nasan ke ce kika zubar mata da ciki me yasa?" Ohh! Yanzu na gane baƙin ciki
kike da ita wato baƙin ciki kike mana dan kawai ke allah yayi ki juya bakya haihuwa
shi ne kike min baƙin ciki." Sai yanzu ta fara gane ina ya dosa wato Husna tayi
ɓari shine ya ke ɗaura mata lefin, ba abunda ya karya mata zuciya cikin kalamansa
sai juya da ya ƙira ta da. Cikin murya kuka ta nuna shi da yatsa kana ta soma
magana. "Aliyu ni kake ƙira da juya ni kake ƙira da juya dan kawai matar ka tayi
ɓari." Sai yanzu ya farga da yayi suɓutar baki amma dan ya nuna mata ɓacin ransa
sai yace. "Karya nayi?"

Na ce ƙarya na miki dan kawai kinga yarinya tana zuwa ta samu ciki shi kenan kin bi
kin tashi hankalin ki tun ba yau ba na lura da ke sai neman fitina da tashin
hankali kike da ita dan kin ga bana magana ina lallaɓa ki duk hakan bai ishe ki ba
sai da kika san yanda kika raba ta cikin, wata iriyar zuciya ne da k....ji kake
tass! tass!! tass!!! Sakamakon wasu zafafan maruka da ta ɗauke shi da kana ta
cakumi kolar rigar shi kana ta ce. "dan Allah Aliyu in ka cika dan halak ka sake
ne, na ce ka sake ne dan na gama zama da kai." Cikin ɓacin rai yace "sakar min
wuyar riga." "Bazan saki ba sai ka sake ne Aliyu dan wallah kaji na rantse in har
baka sake ni ba to kuwa komai zai iya faruwa, ka sake juya ka je can ku ƙarata da
ita dake haihuwa." Ganin baza ta sake shi bane ya fincike rigar shi wanda hakan
yasa ta faɗuwa ƙasa har kanta ya bugu da karshen gado nan da nan jini ya fara wanke
mata fuska amma bata bi takan ciwon ta ba ta ƙara cakumu shi. "Wallahi ba inda
zaka je yau sai sake ni, "Aisha kibar ni fa kar naji miki ciwo." "Cikin kuka da
ƙaraje ta ce. "Sau na wa kuma zaka ji min ciwo bayan wanda ka ji min, mugu kawai
azzalumi Allah sai kama ka, ma yaudare kawai."

Jin maganganun da take jifan sa da su ne ya ƙara harzuƙa shi idon sa sun rufe sabon
ɓacin rai idanun sa har ruwa suke fitar " ba saki kike so ba to ki tafi gidan ku ni
Aliyu na sake ki saki ɗaya. daga haka ya ture ta tare da barin ɗakin.....

P.27

"Ba saki kike so ba to ki tafi gida na sake ki saki ɗaya." Daga haka ya bar ɗakin
tare da banko mata ƙofar.

Aisha kuwa ɗib ji da ganin ta ya ɗauke na wucin gadi dan ba abunda ke amsa kuwa a
kunnen ta sai kalmar sa ta. "Ki tafi gida na sake ki saki ɗaya." Ba ita ta dawo
hayyacin ta ba sai da taji ƙarar horn da yake buga ma mai gadi na fitan hankali ne
yasa ta dawo hayyacin ta tare da durƙusa a ƙasa ta fashe da kuka me sauti tana
anbatan sunan Allah.

sai taji Aliyu gaba ɗaya ya bata haushi, ace duk hallaci da ta mishi ya rasa da me
zai sa ka mata sai da wannan, duk haƙurin da take da shi shine ya rasa da me zai
saka mata sai mummunar fahimata ace duk zaman da suka yi na shakaru amma har ya
yarda zata iya akai ta wannan abun. Bai dace ya yanke mata hukunci irin wannan ba
dan kawai ta ce tana buƙatar saki shine sai ya sake ta. Sai taji duk ta tsane shi
da komai na gidan, kamar an tsikara ta ta miƙe ta shiga toilet tare da wanke fuskan
ta kana ta fito ɗaki tare da neman ɗan kwale ta ɗaure goshin ta da shi wurin da ta
faɗi ɗazu dan har yanzu yana fito da jini. Daga haka ta saka hijab tare da ɗauke
wayarta da kuma jakar hannu ta fita daga gidan bata ma tsaya ɗaukan kaya ba ta bar
gidan. lokacin har ƙarfe tara ma ta wuce babu ma abun hawa sai da ta taka da kafa
har zuwa babban layi tukunna ta samu mai napep da ya sauke wasu ƴan mata ne ya
ɗauke ta sai gidan ummi.
******

Aliyu kam koda ya bar gidan cikin ɓacin rai asibiti ya koma, koda ya koma sosai
yayi mamakin ganin Baba mariya a wurin dan a iya sanin sa bai faɗa mata hasali ma
ko Hajjiya ba kai da faɗa mata ba ma, amma sai ya ɓoye mamakin sa tare da suƙuna
ƙasa ya gaida ita, amma ina ko kallon inda yake ma bata yi ba balle har ta amsa
gaisuwar sa, banda girgiza da hura hanci ba abunda take. Hakan nan ya ya miƙe tsaye
tare da ƙoƙarin fita daga ɗakin kenan ya ji muryar Baba na ce wa. "Me na kuka ke
kam, ai jira nake kawai gari ya waye aje har gida a kama ta dan wallahi ba zamu
yarda ba dan ko ba'a faɗa ba an san ita ta zubar miki da ciki dan kawai tana ɓakin
ciki da ke, dan ke kin samu naki ita kuma gata nan shakara da shakaru babu ko ɓatan
wata bare ɓari. yo ke kika ɗaura mata, da za ta zuba haushin ta kan ɗan ko duniya
bai zo ba, to Wallahi sai tayi kwanan jail dan kuwa baza ta ci banza ba." Da saure
ya juyo tare da kallon Husna dake zaune kan gadon marasa lafiya tare da ƙurban
shaye da Baba ta haɗa mata tukunna ya kai duban sa kan ita Baba da ke maganar.

Sai da ya ɗan sauke numfashi na calming kansa tukunna ya ce. "Baba waya ce Aisha
ce ta zubda cikin?" Sai da taja dogon tsakii tukunna ta soma magana. "Yo sai wani
ya faɗa min ai ko ba'a faɗa ba an san waya aika ta, haka kawai yarinya baza ta yi
ɓari ba dama ance min tun samu war cikin nan take nuna baƙin cikin ta ƙarara gashi
yanzu sai da ta san yanda tayi ta zubda cikin kuma kar tayi tunanin taci banza dan
wallahi gobe ba za ta kwana a gida ba sai police station dan ban ga me hana ni
ɗaukan fanza wa ƴata ba."

******

Aisha lokacin da suka isa gidansu dare yayi dan har 10:23 ma tayi dan haka su ummi
har sun kulle ƙofa dan haka bata wani ɓata lokaci wurin ƙonƙasa ba kawai wayarta ta
cire tare da danna wa ummi ƙira wanda a lokacin suna falo suna hira da kallo da
Baban Aisha wato Alhaji Hamza ranar ya kasan ce yana gari da yake shi matafiye ne.
bugu biyu ta ɗaga Aisha bata bare tayi magana ba ta katse ta ta hanyar ce wa azo a
buɗe mata ƙofa tana waje, Da farko ummi ta ɗauka da wasa ne amma yanda taji muryar
Aisha ne ya tabbatar mata da cewa babu lafiya dan haka babu ɓata lokaci ta sanar da
Abbu wato mahaifin Aisha babu ɓata lokaci ya zo ya buɗe mata ƙofar da kansa.

Ko bayan da suka shiga ciki ta zauna Abbu da ummi suka sa ta a gaba ba tare da
sanin abun yi ba dan kuwa tunda ta shiga ba abunda take sai kuka sunyi sunyi ta
faɗa musu abunda ke faru ta kasa sai kukan da take, ganin baza tayi magana bane
ummi ta ce kawai a ƙira Aliyu a tambaye shi tunda ita ta kasa musu bayani ƙila ma
ba da sanin sa ta zo ba cikin daren nan in kuma abu ya same ta fa.

Da jin haka Aisha ta sau–sauta kukanta tare da ce. "Ba sai kun ƙira shi ba dan da
sanin sa na taho nan." "What?" Abbu ya ce sakamakon tozali da kan Aisha da yayi dan
tun ɗazu a ɗurƙushe take wanda hakan ne yasa ba su lura da ciwon da ke goshin ta
ba.

"Dukan ki yayi?" "A'a amma ya sake ne." Da saure ummi ta dafe ƙirji da hannaye
biyu. "Saki?" Saki Aisha, me kika mishi haka ne da zai sa ya sake ki." Ban da kuka
ba abunda Aisha ke yi dan ko magana ma ta kasa yi sabon ciwon abun. Ganin irin
kukan da take ne yasa Abbu umartan ummi da ta bar ta haka nan da tambayoyin nan da
wanne za ta ji, yanzu ta kai ta ɗaki ta huta yan yaso gobe bayan ta samu natsuwa sa
yi magana. Ba musu ummi ta riƙe Aisha tare da kai ta har ɗakin ta wanda tun kafin
tayi aure na ta ne kuma har yanzu yana nan ba abunda ya same shi saboda duk sati
ummi na saka masu aiki su gyara mata shi haka nan duk ko wani shakara in za'a canja
kayan kayan gidan irin su kujeru da beds to har da nata ake canja wa dan haka a ko
wani lokaci ɗakin yana nan tsab–tsab kamar akwai wanda ke zama a ciki.

Koda suka shiga ɗakin Aisha ta zauna a bakin gado ummi kuma darect bayin ta shiga
tare da haɗa mata ruwan wanka, Ko bayan ta haɗa mata ta fita tarar tayi har yanzu
kukan take. Da kyar ta lallashe ta tare da lallaɓata ta shiga toilet domin wanka.
Ummi ko bayan shigar Aisha toilet bata bar ɗakin ba sai ma nema mata kayan bacci
daga na Eeman da take bari a nan gidan su, kan gado ta ɗaura mata shi kana ta fita
daga ɗakin babu daɗewa ta zo da first Aid box da basa rasa shi a gida saboda
emergency. A lokacin ne kuma Aisha ta fita daga toilet tana mai shafa me, ganin
haka ne yasa ummi bata wuri dan ta shirya. Ummi koda ta fita ba falo ta koma ba
kitchen ta shiga tare da haɗa mata abu mai sauƙe da zata iya ci, koda ta koma ta
tarar har ta gama saka kaya ta na mai dressing ɗin ciwon ta. Har ta gama dressing
ɗin ba wanda yayi magana cikin su ko wa yayi shuru sai tunanin da suke. ita ummi
tunanin ta bai wuce me ya faru tsakanin Aisha da Aliyu ne da har zai ji mata ciwo
irin wannan da kuma saki bai tsaya a nan ba ya tise musu yarinya cikin daren nan ta
zo gida ba tare da tunanin komai ba bai yi tunanin wani abu zai same ta ba, ko da
yake ko wani abu ya same ta ai bashi da hasara. sosai take cikin ɓacin rai amma
bata nuna ba dan bata son ƙara ma ƴar ta wani tention, Allah Allah take da gama ta
je wurin mai gidan ta su san me za suyi dan ita ma wannan abun na Aliyu ya ishe
ta..

P.28

Hajjiya ce ke a falon ta na alfarma. Zaune take kan darduma tare da jan jarbi wanda
dama al adan ta ne tasbihi bayan sallah. Can gefi kuwa yan jikokin ta ne zaune suna
wasa ƴayan Zarah kenan wanda suka zo mata ziyara, sai kuma Hamida dake zaune kan
kujera tare da yin chatting ɗin ta da ta sama. Wayar Hajjiya dake kan tv stand ne
ta soma ruri wanda yaran da jin haka suka soma faɗa kan wa zai kai mata, wannan ya
ce shi zai kai wannan ma ya ce zai kai. Duk wannan abun nan da suke Hamida bata ma
jin su sabon ta maida hankali kan waya, Hajjiya sai tafa musu hannu take da su bari
kar su fasa mata wayarta amma ina basa ma jin ta. Har ƙiran ya tsinke wani ƙara ya
shigo ba su kawo ba su na rigimar ni na riga ɗauka. Ganin sun ƙi ka mata wayar ne
kuma ga Hamida dake kusa da su ta na ganin abunda suke kuma bata tsawatar musu ba
ne yasa Hajjiya tsula mata carbin da ke hannun ta tare da nuna mata inda yaran
suke.

Cikin ɓacin rai da jin haushin yaran Hamida ta tashi tare da bawa ko wannen su
dundu a baya tukunna ta karɓi wayar ta ka ma Hajjiya lokacin har ƙiran ya tsinke.

Koda ta miƙa mata wayar Hajjiya bata amsa ba sai da ta ƙara tsula mata carbin
tukunna ta miƙe hannu ta karɓa, ta ƙara miƙa mata hannu da ta kawo ta ta wayar ma.
Haka nan Hamida ta miƙa mata wayarta ba dan ta so ba. "Wuce ki duba abinda kika
ɗaura kan wuta shasha kawai ana girma ayi hankali amma ita kullun ta na girma ni
bata hankali." "Na fa duba na gani kuma ma har na tuƙa tuwon kawai jira nake yayi
sai na kwashe." Hamida ta faɗa cikin muryar kuka dan ta san tunda Hajjiya ta ƙwace
mata waya nan to fa ita da wannan wayar sai Baba ya gani and gashi ita bata iya
kwana ɗaya babu waya."ki wuce ki bani wuri banza kawai ba abunda kika sani sai waya
in kinga wayar nan shi kenan baki da hankali jin ki da ganin ki ɗauke wa yake, haka
zaki je gidan miji kina yi ehh?" haka zaki ji gidan miji kina yi ki ɗaura abu a kan
wuta sai ki zauna kan waya har sai abincin ya ƙon... bata gama maganar da take ba
aka ƙara kiran ta dan haka ta yi shuru tare da ɗaukan wayar.

"Lafiya Ali fatan kuna lafiya ya matan naka?" Subhanallah! Yaushe?" To Allah ya
kiyaye gaba amma abu bai yi kyau ba. To to shi kenan sai goben in allah ya kaimu
amma wani asibiti ne?" Tohm daga haka ta sauke wayar tare da duban Hamida da gaba
ɗaya ta ƙosa taji me ke faru.

"Yayan ku ne, wai matar shi tayi ɓari suna asibiti." "Ɓari yaushe kuma?" "Uhmm wai
ɗazu ne shima baya gidan lokacin da abun ya faru." "To allah ya sauwaƙe amma dai to
bara dai nayi shuru." "Yanzu kin kwashe tuwon ne ko kin bar shi sai ya gama ƙone
wa?" "Ohh! Sorry yanzu zan kwashe." Daga haka ta tashi da gudu ta nufi kitchen ɗin
ƙwafa Hajjiya taja kana ta cigaba da lazimin ta.
*******

washagari...

Zaune suke kan kujera mai ɗaukan mutum biyu tare da fuskantar ta. "Yauwa Mamana
muna sauraran ki, ki faɗa man duk abunda ke faru karki ji komai mu masu goyan bayan
ki ni kinji." Abbu ya faɗa. A hankali ta gyara zaman ta tukunna ta soma basu
labarin tun auren Husna da irin zaman da suke har izuwa samun cikin ta da kuma
abunda ya faru a jiya wanda shi yayi silar rabuwar ta su amma ta ɓoye musu abu ɗaya
wato na ita ta nemi saki a wurin sa.

Tun kafin ma ta gama basu labarin Alhaji Hamza wato Abbu jinin sa ya fara tafasa
dan shi dama mutum ne me zafin rai balle kuma an taɓo masa da yar lelen shi, baya
wasa da duk abunda ya danganci Aisha ko me ƙanƙansa kuwa dan shi yasa ma ummi take
hana Aisha kai mishi ƙorafi ko wani iri ne dan yanzu–yanzu zai ɓata da kai ba
abunda ya shafe shi indai a kan Aisha ne, kai gwara ma ka taɓa shi akan ka taɓa
ƴarsa.

Ko auren Husna da Aliyu yayi ba ƙaramin ɓata masa rai yayi ba amma da lallaɓawar
ummi ne ya sauko. "Duk wannan abun ya faru amma shine baki faɗa mana ba, in ma ni
in kin ce baza ki iya faɗa min ba baza ki faɗa ma Ummin ki ta gaya min ba? Kika
zauna yana wulaƙanta min ke?" Haka muka yi da shi lokacin da yazo neman auren ki.
Shi har ya isa ya ƙira ki da juya" dame yake taƙama da kuɗi ko me?" an gaya mishi
mu matsiya ta ne?" "Haba Alhaji ka yi haƙuri haka tunda aikin gama ya gama." "Kar
ki ce min nayi shuru ni dama na san har dake a cikin wannan aika–aika ai tunda kin
san halin da take ciki amma kika kasa yin komai dubi yarinya gaba ɗaya ta lalace ta
rame haka na bashi ita." Yau fa an taɓo Abbu dan ta inda ya ke shiga ba ta nan yake
fita ba. Da kyar da ɗikon goshi tukunna suka samu ya ɗan sauko, shima sai da ya
ƙira ɗaya daga cikin yaransa da suke masa aiki kan su ɗauko babbar mota da zata
ɗauke kaya su jira shi da ita dan a yau ɗin nan za'a je a kwashe mata kayan ta gaba
ɗaya dan ko rana ɗaya ba zai kwana a gidan shi ba.

Hakan kuwa aka yi dan kuwa mota biyu Abbu ya ɗauka suka tafi gidan Aliyu a lokacin
baya ma nan Da farko mai gadin ya so hana so shiga amma da yaga Aisha sai ya bar su
suka shiga nan da nan suka soma haɗa kayan duk abunda suka san ba na ta bane nashi
ne sun bar mishi, amma duk kayan Aisha sun haɗa tare da loda wa a mota daga haka
suka bar gidan.

******

"Me kike nufi da na yi haƙuri eh?" Baba mariya ta faɗa. "Eh Baba kiyi haƙuri ba sai
kin tura mata police ba ni na yafe mata." Inji Husna da gaba ɗaya ta tsorota da
Baba dan ta san muddin aka sa yan sanda a cikin lamarin nan gaskiya za ta fito dan
kuwa sai anyi bincike, in kuwa aka yi to fa ƙaryar ta tazo ƙarshe dan ƙila ma ita
za'a maida jail tunda ta ƙulla ma Aisha sharri. "Kina da hankali kuwa?" kin san
irin hasarar da ta ja mana kuwa?" "Na sani Baba to amma tunda aikin gama ya gama
sai muyi haƙuri da ƙaddara ko kuma ma na san ba zai zuba mata idanu haka ba dan
dole sai ya ɗau mataki dan haka kar mu yi gaggawa aikin shaiɗan tunda ba mu san
wani irin hukunci zai ɗauka ba, kar mu ɓata wa kan mu mu zuba ido muga me zai faru
waya sani ma ko abunda muka daɗe muke nema ne ma zai faru." "Na me fa." Sai da ta
ɗan murmusa takunna ta fara magana. "Abunda nake nufi a nan shine ba sai mun tashi
hankalin mu kan wai sai mun ɗau fanza ba, kawai muye anfani da wannan damar ta
yanda zamu juya shi yanda muke so kuma kinga daga nan sai mu san yanda zamu juya
mishi tunanin bata sonshi shi yasa ma ta kashe mishi ɗa." "Kuma fa hakane, amma ina
son sanin gaskiya, ita ta zubda cikin nan ko kuma?" Ta kare maganar ne tare da yi
ma Husna wani kallo na ban yarda dake ɗin nan ba. "Ko kuma me Baba?" Wait kar de ki
ce kina zargi na da zubda cikin, taya ma zaki yi tunanin hakan bayan na san yanda
yake da muhimmaci a wurin mu shi ne sai na yi wannan ganganci?." "Na san muku ne
ƴayan zamani yanzu sai ki canja ra'ayi ki ce bakya son haihuwa. Amma in dai haka ne
to lallai Aisha ta ban mamaki yanzu duk shuru–shurun ta nan shine ta iya aikata
wannan abun ga?" "Ke dai ki bari Baba in tayi silar zubewar wannan to ai akwai gobe
dan na tabbata nan ba da jimawa ba zan samu wani." Husna ta faɗa da fatan Baba ta
bar wancan topic ɗin dan ta lura Baba na iya gano ta dan haka ne ta gaya mata
abunda ta san yanzu zai sa ta manta da wan can maganar.

Illai kuwa nan da nan Baba ta washe baki ta fara mata nasiha kan kar ta kuskura ta
yi planing ta yanda tana koma wa zata samu wani cikin. Suna cikin haka sai ga Aliyu
da mahaifiyar shi. shine a gaba sai Hajjiya da Hamida da ke riƙe da basket ɗin
abinci. Ciki suka shiga Aliyu ya jawo wa Hajjiya kujera ta zauna kana ta zuba wa
Husna idanu na ɗan wani lokaci kana ta taɓe baki ba tare da tayi magana ba dan a
ganin ta ai ba ita zata fara gaishe ta ba ita ya kamata tayi. Duk abun nan da take
Baba na kallon ta da kamar ta share ta ita ma amma da ta ga Aliyu na wajan kuma sai
tayi danne zuciyarta ta gaida ita. Hajjiya kam sai yanzu ma ta lura da ita dan haka
ba tare da ko in kula ba ta amsa mata tare da kai duban ta kan Husna da ta sunkiyar
da kai ƙasa kamar ta Allah, Kana ta ce. "ke kuma haka aka koya miki a gidan ku ƙin
gaishe da babba?"

Sai san nan ta ɗaga kan ta tare da gaida Hajjiya da sai da ta taɓe baki tukunna ta
amsa mata." "To sannu mun ji labarin abunda ya faru sai a kiyaye gaba." Baba za
tayi magana kenan Husna ta riƙe mata hannu tare da amsa wa hajjiya da in sha allah.

Daga haka kowa suka yi zaman kura me dan ba mai magana duk cikin su musamman ma
Hajjiya da Baba. Sunyi zaman minti talatin Hajjiya ta ce da Hamida ta a je musu
basket ɗin su wuce, haka kuwa aka yi ta aje musu kana ta dube Aliyu da gaba ɗaya
hankalin shi baya ma kan su sabon ya lula duniyar tunani kana ta ce.

"Yaya zaka maida mu ne ko mu hau napep?" "No mu tafi zan kai ku." Daga haka ya
tashi tare da fita daga ɗakin. Hajjiya ma ta tashi tare da duban Husna kana tace.
"To mu zamu koma Allah ya ƙara sauke." Daga haka suka fita.

Tsaki Baba taja bayan fitar su Hajjiya kana ta juya kan Husna. "Da me take takama
ne?" Da baki hana ni gaya mata baƙar magana ba ai."

******

Aliyu bayan ya sauke su Hajjiya a gida bai koma asibiti ba gida derect ya koma.
Koda ya parker motor shi part ɗin Aisha wuce dan yana son yayi wanka da cin abinci
dan tun jiya rabon sa da cin abinci and ba abincin kowa ya ke son ci sai nata, ba
tare da tunanin komai ba ya shiga part ɗin ta, amma me wayam ya ga babu komai a
falon. Ɗaki ya shiga nan ma ya ga wayam babu gado da sauran kayan.

P.29

Wurin mai gadi ya fita tare da tambayar sa akwai wanda suka zo ne da baya nan. "Eh
Alhaji Hajjiya Babba ce suka zo ɗazu da ba ka nan, kuma nayi ƙoƙarin ƙiran ka a
waya amma numbern ka baya shiga, kaya suka zo kwashewa." Wato har sun zo sun kwashe
kayan ta daga abunda ya ɗan faru jiya wanda ya ɗauka zasu zauna su sa santa abun su
kamar yanda suka saba shi ne ta tafi gida kuma harda zuwa kwashe kaya, to me take
tunani zai je ya dawo da ita ne ko me? hmmm bayan ita ta mishi laifi, taje tayi duk
abunda ta ga dama amma shi kam ba zai je bikon ta yanzu ba sai taji jiki tukunna
sai ta gane tayi Babban kuskure, amma for now ba zai je bikon ba dan a yanzu baya
ko son ganin fuskar ta ne saboda tuna mishi da abunda tayi take. yana buƙatan space
a yanzu dan haka ta cigaba da zama a gidan na su zai fiye mishi.

"Amm Baba ko kasan dawa suka zo?" "Ina ga Baban ta ne dan naji tana ce masa Appu ne
ko abu ne ban sani ba." "Ok Baba na gode daga haka ya shiga motarsa tare danna
mishi horn.
Aliyu koda ya fita asibiti ya nufa darect dan karɓan sallama, ɗazu sun yi magana da
Dr and ya ce zuwa anjuma za'a sallame su tunda ta samu sauƙi, amma abu ɗaya ne da
ya tsaya mishi a rai da kuma tada mishi hankali, maganar da Dr ya faɗa mishi ko shi
kansa ta tayar masa da hankali balle ita. yanzu bai san ta inda zai sanar da ita
ba, abunda ya yanke shi ne ba zai faɗa mata yanzu ba abun sai ya mata yawa da wani
zata ji.

Da wannan tunanin ya isa asibitin. Babu ɓata lokaci ya cika takardun sallama aka
sallame su suka ɗau hanyar gida. ya ɗauka Baba mariya zata tafi da Husna gida ta
yanda za'a kulla da ita sosai kamar yanda yake gani ana yi, Amma sai Baba tace A'a
ba sai anyi haka ba kawai ta koma gidan ta zai fi ita ma zata kulla da kan ta. Babu
musu kuwa ya kama hanyar gidan shi da su.

"Kin ga wannan matar tun jiya kike asibiti bata je ta duba ki ba har aka sallame mu
mun dawo gida yanzu amma ta kasa shiga ta miki sannu." Ce wa Baba. Tun ɗazu da
Aliyu ya kawo su ya koma aiki take ta sa ido taga ta inda Aisha zata ɓullo amma
shuru kake ji. "Hmm Baba ke ce ma kike wani damuwa da ita wallahi, da ta zo da kar
ta zo duk ɗaya a wuri na ne." "Ba dole nayi magana ba ace duk abun nan da faru da
ke jiya ta kasa zuwa duba ki ai dole nayi magana kuma ma ni an gaya miki haka kawai
nake son zuwan na ta ne?" "Ni fa ba abunda ya shafe." Husna ta faɗa amma ban da
bugu ba abunda zuciyarta ke gaba ɗaya ma bata son abunda zai haɗa ta da Aisha ma
saboda ƙullin da ta mata sai take ganin kamar zata iya shigowa yanzu ta tauna mata
asiri.

Bata san cewa Aishan bata ma cikin gidan dan Aliyu bai sanar da ita komai ba hasali
ma ko maganar Aisha bai yi mata ba balle tasan abunda ke faruwa. To haka take ga
Hajjiya ma bai sanar da ita ya saki Aisha ba koda da dare ya koma gidan ta tambaye
shi ita ƙarya yayi mata wai tana lafiya kuma tana gaida ke.

Yau sati biyu kenan da sallamar Husna daga asibiti kuma har lokacin Baba mariya na
tare da su dan ta ƙi koma wa gidan ta wai ta zo kulla da ƴar ta wanda ba haka ba
kawai kwaɗayi ne irin nata, tun Aliyu na tambayar Husna yaushe zata koma har ya
gaji ya zuba mata ido dan a gaskiya yana takura sosai da ita a gidan amma bai taɓa
nunawa ba amma kam abun ya bashi mamaki. Ba zai iya tuna rana ɗaya da Ummi ta taɓa
zuwa musu haka kawai ba tare da wani abu ba balle har ace ta kwana kai shi zai iya
rantse wa ma Ummi bata taɓa kwana a gidan su haka nan shi da Aisha za suyi ta mata
magiya da ta kwana amma sai tace ita mai zai kai ta kwana a gidan sirki haka kawai
babu gaira balle dalili. kuma banda haka ma ko Hajjiyar shi bai taɓa ganin taje
gidan Zarah ko Balkisu ta kwana ba ko Balkisu da tayi ɓari kwana kin baya Hajjiya
bata je ta zauna da ita ba sai zuwa duba ta tayi. Shi yasa yayi mamakin abun nan
nasu amma sai yayi shuru dan baisan ko haka al adar su take ba.

Kuma har yanzu bai faɗa ma Husna rabuwar su da Aisha ba, ita ce dai da sa ido da
kuma bin ƙoƙƙafi har ta san abunda le faruwa, dan kuwa tunda suka dawo bata ganin
Aisha kuma bata jin motsin ta a gidan haka in dare yayi bata ganin wuta a part ɗin
ta wanda hakan ne yasa taje har part ɗin domin gaskata abunda take zarge.

Elle kuwa abunda take zarge ne dan tarar tayi part ɗin a kulle kuma wajan gurin ya
ɗan fara ƙura wanda shi ya ƙara tabbatar mata da cewa Aisha bata gidan. Ba tare da
ɓata lokaci ba taje wurin mai gadi ta tambaye shi kuma ya ƙara tabbatar mata da
cewa Aisha bata gidan tun ranar da tayi rashin lafiya aka kai asibiti kuma a
washagari suka zo da mota aka kwashe kayan ta.

Faɗin irin daɗin da suka shiga a ranar ɓata baki ne dan abunda ba suyi tsamani bane
dan basu taɓa kawo zai iya sakin Aisha ba duba da yanda sunyi shige da fice amma
jiya iyau.

Husna fa duniya ta dawo sabuwa dan kuwa duk abunda take so shi take yi Aliyu baya
magana dan shi yanzu tausayen ta ma ya ke ji shi yasa ma in tayi wani abun ko yaso
yayi magana sai yayi mata uzuri.

Ɓangaren ƙawancen ta da Lubna kuma sai abunda yayi gaba dan kuwa tunda tabi
shawarar ta kuma taga aiki da cika wa, ta ƙara manne mata sai abunda ta ɗaura ta
akai.

Yau lahadi tun da safe Baba take haɗa kayan ta dan a yau zata wuce gida duk da ba
da son ran ta bane, dan tunda tazo gidan ta ji daɗin rayuwa shi kenan taga wuri dan
kuwa taƙi komawa gidan ta, Ba yanda Kausar tayi da ita da yayi haka nan ta dawo
gida wannan ko jego Husna ke yi ai yayi haka tunda yanzu har ta fita daga wata amma
Baba ta ƙi, ganin ta ƙi kullun sai tace wai gobe jibi ne yasa Kausar kai ƙarar ta
wurin Yayan Baban su wanda suke ƙira da Baffa Isah shi ya ƙira ta yayi mata faɗa
sosai to shine take haɗa ka zata koma ba dan ran ta yaso ba.

Bangaren Hajjiya kuwa duk tana sane da abunda ke faru a gidan Aliyu amma tayi shuru
da bata yi magana ba dan kuwa sosai ya ɓata mata rai kan sakin da yayi ma Aisha ba
dan tana son ta ba A'a dan ya yanke mata hukunci ba tare da yin bincike ba kuma ma
wai rasa me zai saki Aisha a kai sai kan Husna, wannan ba ƙaramin baƙin jini ya
ƙara yaja mata wurin Hajjiya ba, duk da ita ma Aishar ba wai tana son ta bane kawai
dai tafi mata Husna tunda Aisha da yardan ta ya auro ta kuma ma ita fa Aisha nan ba
wai haka kawai take ƙin ta ba. Ita taja take ƙin ta tunda farkon auren su wace
iriyar soyayya ce bata nuna mata ba.

******

Haka bangaren Aisha ma sai hamdallah dan kuwa irin soyayya da kulawar da take samu
wurin su Ummi shi ya ƙara taimaka mata wurin manta wa ds duk abunda ya faru, rayuwa
take ta kwanciyar hankali babu wani ɓacin rai da takaicin ɗa namiji. sosai tayi
kyau tayi fresh da kuma ƙiba abun ta. Kuma har yanzu Aliyu bai zo biko ba kai ko
text bai taɓa tura mata ba balle kuma ya ƙira wanda kuma shi ya ƙara basu Abbu
haushi amma ganin Aisha ko a jikin ta rayuwar ta take ya sa su shuru da bakin su.

Bangaren Aisha kam a yanzu bata ma son jin sunan Aliyu dan a yanzu inda akwai wa
ƴanda ta tsana bata son ko ganin su to bai wuce Aliyu da matar shi ba, dan sai a
yanzu ma take jin takaicin kanta da ta tsaya ta juri wannan abun da suka dinga mata
gashi duk yanda tayi haƙuri ta zauna dan kawai a zauna lafiya amma yanzu da me ta
tashi da tutar babu. Hakan ne ma yasa tayi blocking ɗin su gaba ɗayan su duk da
tasan ba wani neman ta da za suyi ba amma kwanciyar hankalin ta ne hakan. Da farko
dai ta shiga damuwa da tunani–tunani amma sana diyyar kulawar su Ummi da kullum
ƙoƙarin su bai wuce su ga sun faranta mata ba ne yasa tayi ƙoƙari sosai wurin faɗa
da zuciyarta wurin manta da komai da ya faru wanda kuma Alhamdulillah komai ya wuce
a wurin ta dan kuwa har mantawa ma take da ta taɓa aure, tukunna bata fita daga
idda ba amma ta kusa.

******

Aliyu ne tsaye kan Husna dake ta sharara bacci kamar babu gobe. agogo ya duba ya ga
har ƙarfe 8:28 amma bata tashi tayi sallah ba balle har tayi masa wani breakfast
yaci kafin ya fita office.

"Husna! Husna!! Husna!!!

"Ki tashi kiyi sallah malama ko kinsan ƙarfe nawa ne yanzu?"

A hankali ta tashi tana mai misisika ido tare da turo baki gaba irin an dame ta
nan. "Ki tashi kiyi sallah fa kar ki koma bacci ni zan wuce sai na dawo." Daga haka
ya nufi ƙofar fita.

Zunbur ta miƙe tare da bin bayan shi. "Dan allah ka tsaya na maka abu me sauƙi
sharp–sharp ka ci tukun ka fita." Sai da ya dubi agogon da ke manne a bangon falo
tukunna ya ce. "Ki duba lokaci ƙarfe nawa ne yanzu da sai yanzu kike tashi wa ko
sallah baki yi ba kike faɗa min na jira ki dafa min, in da rashin ci na yana damun
ki da tun wuri zaki tashi ki ki dafa min ai yau ma zan je na ci a waje kamar yanda
na saba tunda ba yau na fara ba." "Dan allah kayi haƙuri zan gyara." "Hmm yanzu dai
ki je kiyi sallah ni ba dan ni zaki canja ba, in ma baza ki tashi da safe ki min
breakfast ba to ki tashi kiyi sallah." Daga haka ya juya ya fita abun shi bai ko
jira yaji me zata ce ba ya bar gidan.

Husna tunda tayi sallah ta fito falo ta ɗau waya ta shiga group ɗin su na classic
lady da lubna tayi adding ɗin ta a ciki, to shi kenan ta manta da wani aikin gida
nan ta zauna wa chatting.

P.30

Nan ta zauna wa waya ba tare da tayi ko wanka ne balle aikin gida. Sai da ta ga
yamma tayi Aliyu ya kusa dawo wa ta tashi ta shiga toilet tayi wanka ta fita tare
da saka kaya sharp–sharp ta shirye tukunna ta fito falo tare da ɗan tattara shi ba
tare da ta share ba ta shiga kitchen ta haɗa wanke–wanke ta soma yi.

Lokacin da ta gama gyara kitchen ɗin har an soma ƙiraye–ƙirayen sallahn magrib dan
haka abu me sauƙi ta ɗaura musu dan ta san war haka Aliyu ya dawo bai kai da
shigowa bane sai yayi sallah tukunna zai shigo dan haka bata ɗaura abu mai nawi da
babzai nuna a kan lokaci ba.

Nan da nan ta gama ta zuba a coola tare da ajewa kan dinning daga haka ta ɗauki
wayarta da tasa a charge ta soma aikin na ta da ta sama wato danna waya.

Babu ɗadewa sai ga Aliyu ma ya shigo da sallama a bakin shi. Tana jin muryar sa ta
aje wayarta tare da nufan shi da gudu tayi hugging ɗinsa. "Sannu da zuwa baby nayi
missing ɗinka." "Hmm yauwa sannun ki da ƙoƙari kema na same ki lafiya?" "Lafiya
fatan kai ma kana lafiya?" "Yeah lafiya daga haka ya miƙa mata ledar hannun shi
kana ya ce mata. "Bara na watsa ruwa a jiki na tukunna." Karɓan ledan tayi tare da
ce wa. "okay sai ka fito." daga haka ta juya falo ba tare da tunanin haɗa mishi
ruwan wankan ba.

Kai kawai Aliyu ya kaɗa tare da wuce wa ɗakinsa yana me mamakin halayen Husna na
yanzu wai dama haka take bai sani ba ko kuma canjawa ne tayi, dan gaba d'aya ta
canja mai.

Da wannan sake-saken har ya isa ɗakin ba tare da tunanin komai ba ya tura ƙofa ya
shiga. amma me yana shiga ɗakin ya tarar yanda ya fita ya barshi haka ya same shi.
Gaba ɗaya ɗakin a harzik'e yake tun ba gadon ba dan kuwa harda ɗanyen towel da tayi
wanka maimakon ta shanya ya bushe sai ta barshi a kan gado haka, ga kuma bed sheet
da tayi nuƙu–nuƙu da datti wanda tun shakaran jiya yake fama da ita da ta wanke ta
sa wata amma har yanzu bata yi ba.

Kai kawai ya kaɗa tare da nufan bayin dan kuwa ya san ko yace zai yi magana yanzu
ranshi ne zai ɓace a banza dan kuwa baza ta canja ba tunda ba tun yau suke magana
kan abu ɗaya amma ta kasa gyara wa. A daddafe yayi wanka ya fito daga toilet ɗin
dan kuwa hatta ita toilet ɗin tayi datti tana buƙatar wanke barin ma tiles da yayi
ja sabon datti har yauƙi yaki dan in baki yi hankali ba zaka iya zame wa ka faɗi.

KO bayan ya fita daga toilet ya buɗe wodrop ya soma duba kayan bacci da zai sa amma
bai samu ba dan kuwa gaba ɗaya sun yi datti suma ba tare da an wanke su ba dan kuwa
haɗa su aka yi da sauran kayan dattin gidan wanda sabon sun shiga cikin kayan datti
har tsami suke. Aje su yayi tar da neman dogon wando da singlet ya saka kana ya
fita falo zuciyarsa zafi take masa sabon haushi da takaici wai ace shi ne yau yayi
wanka ya rasa kayan sawa? sai ya tuna Aisha da yanda take kula dashi, yanda take
kula da abincin shi da kuma in ya dawo take haɗa mishi ruwan wanka ta zaɓa mishi
kayan sawa haka da safe take tashi wa dan girka mishi breakfast da wuri, duk wannan
wahalar shi bai san ta ba bai san yunwa ba baisan me datti ba amma dube shi yanzu
wai a gidan shi ya rasa kayan sawa ma. Hmm dole ne ma yaje ya dawo da ita dan yasan
yanzu ta gane gaskiya dan haka ta dawo suyi zaman su dan ya tabbata zata yi farin
ciki da hakan ita ma.

Da wannan sake–saken ya isa falon tare da zama kan kujera tare da ɗaukan remote ɗin
tv ya canja zuwa tashar labare kana ya kai duban sa ga Husna da ke danna waya.
"Madam ina abinci na ko yau ma zan kwana da yunwa ne?" "Da sauri ta aje wayar tare
da cewa. "sorry ban san ka fito bane bara na kama ka." Daga haka ta nufi kitchen
shi kuma ya cigaba da kallon sa. Kamar wanda aka ce masa ya juya kansa gefe ya ga
ledan da ya kawo ya bata ne a wurin dan da gani ma ba a ko duba me ke ciki ba aka
barshi a wurin. Aliyu sabon takaici ya ma kasa magana ka kawai kaɗa tare da cigaba
da kallon sa.

Husna kuwa kamar abun arziki ta haɗa mishi abincin cikin coola tare da ɗaura wa kan
tire ta ka mishi tsakar falon.

Ba tare da ya dube inda take ba yace da ita. "Me yasa baki saka wancan ledan a
shara ba kika bar shi a nan."

"Wani leda kenan?" Ta faɗa tare da dube–dube can dai ta hango shi tare da zuwa
wurin ta ɗauka kana tace. "Wannan kake nufi?" "Akwai wani ledan ne banda wannan?"
Ya tambaye ta tare da ƙura mata idanu. "A'a amma ai wannan wanda ka kawo ne?" "Hmm
na ɗauka bashi da anfani ne ai." Sai yanzu ta gane maganar sa wato magana ya sakar
mata. Ba tare da ta sake cewa komai ba ta nufi kitchen da ledan ta buɗe tare da
fito da abunda ke ciki, fruit ne a ciki sai kuma ice cream da har ya fara narke wa
a rabon.

Sunan ta da taji ya ke ƙira ne yasa ta saurin barin abunda take tare da nufan
falon.

"Me wannan da kika dafa min?" Ya faɗa da ɗan ƙarfi. "Taliya da manja." "Tunda kike
a gidan nan kin taɓa ganin an dafa min taliya a matsayin abincin dare ko kin taɓa
ganin na ci garau–garau da yaji?" "A'a ta faɗa murya na rawa. "Shine kika dafa min
wannan a matsayin abincin dare bayan kuma kin san bana cin yaji saboda lafiya ta."
"Kayi haƙuri lokaci ya ƙure ne shi yasa." Lokaci ya ƙure?" Me kike tun safe da na
bar gidan nan?" Gaya min abunda kika yi tunda na fita, ba abunda kika yi yanda na
fita haka na zo na samu hatta ɗakin kwananki baki gyara ba haka na zo na same shi."
Daga haka ya tashi tare da fice wa daga gidan zuciyarsa sai tafasa take.

Husna kuwa tana ganin ya fita taja wani dogon tsaki tare da zama kan kujera. "To
sai me dan baka ci yanzu ba duk inda zaka je ka dawo yana nan jiran ka wallahi in
ma baka ci yanzu ba to gobe zaka ci Haba mutum sai mitan tsiya abu kaɗan sai yayi
magana wannan in ka tsufa na ga wanda zai zauna da kai. Aiki kuma bazan yi ba in ka
gaji ka kawo mai aiki bazan kashe kai na ba." Daga ta ɗauki abincin ta mai da
kitchen kana ta zo ta zauna tare da cigaba da chatting ɗin ta kamar ba abunda ya
faru.

Aliyu kam koda ya fita ya rasa ina zai tafi cikin daren nan ya samu abinci gashi
baya son cin abincin siyar wa kuma baya son zuwa gidan Hajjiya dan ko ya tafi ba
bashi abinci zata yi ba dan kuwa ta hana mishi abincin gidan ta, ga kuma Habib
abokin shi baya gari balle ya ce zai je gidan shi. Ganin bashi da ma fita sai siyan
abinci ne yasa shi juya motar shi zuwa restaurant.

Ba shi ya koma gida ba sai kusan ƙarfe sha ɗaya, koda ya shigo bai tarar da Husna a
falon ba dan haka ya nufi ɗakin ta dan yana son suyi magana ta fahimta ya gaji da
irin abubuwan da take mishi wanda da ba haka take ba.
Koda ya shiga samu yayi tana baccin ta hankali kwanciye kamar ba abunda ke faruwa.
Tsaye yayi bakin ƙofar ya ma kasa shiga cikin ɗakin, wato ita bata ma damu da
yanayen da ya fita a ciki ba bata damu da ta ƙirashi dan jin ya yake ba sai ma
baccin ta da take sharara ko a jikin ta.

Sai ya tuna Aisha da yanda take shiga damuwa da tashin hankali duk ranar da bai
shigo da wuri ba, bata taɓa iya bacci ba tare da tasan yana cikin ƙoshin lafiya ba.
Sai yanzu yake dana sanin biye mata da yayi ya sake ta Da duk bai shiga wannan
halin ba.

Washagari ya kama Asabar dan haka Aliyu bai fita aiki ba, tun safe da ya tashi bai
koma bacci ba dan kuwa aikin gyara ɗakinsa ya kama dan ya lura in ya zauna wa Husna
ta gyara mishi to zai tsufa ne tunda ba tun yau yake faɗa mata ba amma kullun in ya
fita haka zai zo ya same shi.

Haka ya zauna ya gyara ɗakin tare da shiga toilet ɗin ma ya wanke kana ya fita ya
tattara kayan shi mai datti ya kai mota dan kuwa ba zai iya wanke su ba bayan uban
aikin da ya sha, kai sai yanzu yake jinjinawa Aisha da take duk aikin gida ba tare
da ko ƙorafi ba tunda har me aiki ya so ka mata amma tace bata buƙata.

Bayan gama aikin gyara ɗaki da toilet da yayi, kitchen ya shiga tare da kunna Gas
ya ɗaura tukunya kana ya fara girki duk da bai iya sosai ba amma ya na ganin yanda
Aisha take yi dan haka da kyar da ɗuƙon goshi yayi jollof ɗin shinkafa da wanke ya
zuba a coola kana ya juya sauran a plate ɗin shi tare da aje mata tukunyar da
sauran kwanikan da ya ɓata a sink kana ya ɗau coolar shi da plate ɗin shi ya bar
kitchen ya koma falo.

Har ya gama cin abincin shi Husna bata tashi ba kusan ƙarfe 9 da wani abu amma bata
tashi ba, kai baya tunanin ma ta tashi tayi sallahn asuba ba ma.

Ya nan wurin bai tashi ba dan kuwa tunda ya zauna ya ci abincin nan sai yaji gaba
ɗaya jikin shi yayi mishi nawi saboda gajiya, dan haka kwanciyar sa ya gyara kan
kujerar kana ya rufe idanu domin bacci.

Cikin bacci ya soma jin kamar ana ƙiran sunan shi. A hankali ya buɗe idanun sa tare
da duban ta daga sama har ƙasa kana ya ce. "Me haka ba ki ga bacci nake ba." "Kamar
ya me haka?" Ina da idanu mana ai shi yasa ma ban tashi ka da ihu ba." "Me kike
buƙata." Ya tambaya dan ya san tana buƙutar abu ne dan shi ne kaɗai zai sa ta neman
shi. "Hmm ashe ka gane, to ba wannan ba zuwa nayi na san wace shegiyar ce ta shigo
min gida?" "Waye wannan kuma?" Ya faɗa dan shi gaba ɗaya bai gane me take ce wa ma
sana diyyan ciwon kai da ya kama shi lokaci ɗaya. "Kar ka rena min hankali fa sarai
kasan me nake nufi, dan haka ka faɗa min wata yar iska ka kawo min har gida?" Ta
fad'a da k'arfi kamar zata Mishi duka.

"Ni kike wa tsawa Husna?" ni kike k'ira da d'an iska Kenan?" Ya fad'a hakan ne tare
da nuna kansa. "Ni yaushe na k'ira ka da hakan kawai da kana son k'ulla min sharri
ne in ba haka ba taya zaka fad'a abunda ban ce ba sai dai in kuma." Sai tayi shuru
ba tare da ta k'arasa maganar ba. "Sai dai kuma in d'an iska ne ni ko?" "Ni ban ce
ba." To me kike nufi fad'a min, na ce fad'a min me kike nufi da na kawo yar iska
nan?" "To in ba yar iska ka kamin nan gida ba taya za'a yi na gyara kitchen d'ina
tsab Amma na zo na gan shi kamar na mahaukata komai a watse yake ga kuma tukunyar
abincin wanda alamu sun nuna cewa girki aka yi a ciki to fad'a min wa yayi affani
da kitchen d'in?" Haka kawai ake son cuta ta Dan kawai angan ni k'arama bana magana
sai ake son a shiga hakki na." "Ohh! Dama ke akwai abunda ya dame ki ne?" Na d'auka
ai yanda kike nuna ba ruwan ki da komai to ba zaki damu Dan na kawo wata ta yi miki
aikin ki ba." "Me kake nufi?" yanzu da gaskiye wata ka kawo Aliyu?" "Ba wace na
kawo gidan nan kuma kayan da kika gani ni ne nan na b'ata su saboda na shiga nayi
wa Kai na girki, tunda na zama matar ke kuma mijin. Kuma maganar kawo wata Kar ki
damu nan ba da Jimawa ba zata zo amma ba'a matsayin karuwa ba a'a a matsayin matar
gidan." Daga haka ya nufi d'akinshi ba tare da ko kallon inda take ba. "Da saure ta
bi bayan shi tana me ce wa. " Me kake nufi da zaka kawo wata ehh ban gane ba, kar
ka ce min aure zaka k'ara?" Ta fad'a zuciyarta sai lugudan uku-uku take.

"Yes in dai baza ki canja ba ko to kuwa ki tsammace zuwan ta, kuma ni ki fitar min
daga d'aki tunda ba ke kika gyara min ba Kar na sake ganin k'afar ki a nan." D'an
turo Baki gaba tayi kana ta ce. " Yanzu korata ka ke Dan kawai na shigar ma ka
d'aki?" "Eh na kore ki Kar ki sake shigar mini nan ki je can ki k'arata da
k'azantar ki sani ya rage naki in zaki zauna ki gyara gidan ki ko kuma zaki bar shi
haka." Daga haka ya kama hannun ta tare da fitar da ita daga d'akin kana ya ce. "In
kina son na barki ki shiga min d'aki to sai ki je ki koyi tsabta in kuma ba haka ba
babu ke babu da'kina." Daga haka ya bank'o mata k'ofar a fuskar ta.

P.31

Ƙwafa taja tare da barin wurin.

Aliyu kuwa koda ya kulle ƙofar kan gado ya zauna tare da cire wayarsa daga
aljihunsa tare da dailing ɗin numbern Aisha amma baya shiga, ganin hakan sai yayi
tunanin ko wayarta bata da charge ne shi yasa bata shiga. Da wannan tunanin ya
maida wayar aljihunsa kana ya bar ɗakin.

"Ina zaka je kuma?" Ya ji muryar ta.

"Inda kika aike ni." Daga haka ya bar gidan ba tare da ko sauraran maganar da take
mishi ba. Shi fa yanzu ba ya ko son ganin fuskar ta dan ƙara mishi ɓacin rai take,
he wonder how ma he falls for her har ya aure ta ma.

******

"Me kike nufi da kin bashi number na?" Aisha ta faɗa da ɗan ƙarfi tare da miƙe wa
tsaya. "Yes! Abunda kika ji kenan na bashi numbern ki and his coming next
tomorrow." Eeman ta faɗa. "Eeman what have you done dan allah me yasa zaki ba wani
can stranger number na ba tare da izini na ba?" "Saboda naga baki da niyar bashi ne
shi yasa and beside Lukman is a nice guy kuma ga kuɗi and kyau ma duk da bai kai ex
husband ɗinki kyau ba amma yana da na shi kyaun. Yanzu see just look at this ki
duba ki ga duk irin rashin mutunci da kika yi mishi bai duba ba yazo har gida dan
ganin ki duk da kin nuna min ban isa ba kin ƙi fita kin shanya shi a waje duk
wannan bai duba ba ya bada a ka miki wannan kayan dan allah faɗa min wa zai maka
irin wannan alkaire in ba masoyin ka na ƙwarai ba." Ta ƙare maganar ne tare da baza
kayan a kan gadon. Sai da ta sauki ajiyar zuciya tukunna ta koma ta zauna kan gadon
itama kana ta soma magana. "Baza ki gane ba Eeman right now bana son duk abunda ya
danganci namiji ne balle soyayya ni yanzu ba wannan bane a gaba na dan haka, ki
tattara masa kayan sa ki maida mishi bana buƙuta." "Wannan ne kuma baki isa ba dan
kuwa zuwan shi na ɗazu sun haɗu da Abbu and from look of things yayi na'am da shi
dan naji yana faɗa wa Ummi Yaron kirki ne kuma mai tarbiyya ke bara na takaice miki
zance Abbu ya bashi daman zuwa wuri ki dan haka ki ma cire wannan Aliyu a zuciyarki
ki ba Lukman dama, na fa gane ki duk wannan nuƙu–nuƙu da kike yi bana son soyayya
bana son maza duk dan shi kike yi." Tsaki kawai Aisha taja tare da barin ɗakin ma
gaba ɗaya dan ta lura Eeman so kawai ta tilas ta mata amince wa da Lukman shi yasa
take saka Aliyu cikin zancen saboda ta san ta tsani shi bata ma son jin sunan shi
shi yasa take son anfani da hakan dan kawai ta amince wanda ita kuma baza ta yi ba.
dan a yanzu ba aure ne a gaban ta tana son ta samu space ta yanda zata yi healing
ɗin zuciyar ta da kuma man ce komai.

******

"Baby kaga wadan nan kayan sunyi kyau?" Cewar Husna tare da nuna mishi wasu kaya da
aka tura a group wanda kowa ya siya saura ita kaɗai ce bata siya ba.

"Uhm sunyi kyau." "Ba kasan Bintu ba?" "Wacece kuma haka?" "Oh baka san ta ba
ƙawata ce ita ma kuma next month ne auren ta to wannan ne ankon ta ta tura mana
cikin group kuma kowa ya siya saura ni kaɗai kuma ma babu tsada." "Hmm yayi kyau
sai ki siya ai." "Ɗan turo baki gaba tayi kafin ta tace. "To ka kawo kuɗin sai in
bada nima a ka min nawa kaga fa kowa sai tambaya ta yake wai bazan siya ba ne.
"Kina da kuɗi ai sai ki siya dan ni kam bani da kuɗin da zan baki." "kamar ya baka
da kuɗin siya min ehh?" "Yes abinda kika ji kenan bani da kuɗin da zan baki ki siya
anko kuma ko kin siya ba inda zaki tafi dan haka gwara ma ki aje maganar nan da
wanne kike son naji ne ehh?" jiya kika ce min kayan abinci sun ƙare wanda ni ban
san ta ya ma aka yi suka ƙare ba tunda dai ba wani dafa abincin kike ba kullun a
waje nake cin abinci to taya kayan abincin suka ƙare?" Banda wannan ma last week
Baba ta ƙira wai tana buƙatar kudi na tura mata and yanzu kike wani faɗa min wai
wani anko to ni ina ruwa na da anko, ni ta gidana nake ba ta wani anko ba ke ma ai
kina da kuɗin sai ki siya mana." "Me kake nufi da baka san inda kayan abinci suke
tafiya ba dai zargi na kake da ina fitar maka da kayan abincin ba?" kuma da kake
wani ce wa Baba ta ƙira ka ta karɓi kuɗi a wurin ka ka faɗa min ne ko kuma ni na
tilas maka sai ka tura mata da zaka gaya min kuma ma duka–duka nawa ka tura mata da
ka ke wani cewa ka tura mata kuɗi. Kuma ni bani da kudi da ina da shi da bazan zo
nan ina tambayan ka kuɗi ba kuɗin ma da za'a baka azo daga baya ana maka gorin
shi." "Nawa na bata?" Nawa na bata ma kike tambaya?" Yau ne take ƙira ta tambaye ni
kuɗi in tura mata na kuma tura mata na taɓa faɗa miki hakan ko kin san kusan sati–
sati take ƙira in tura mata kuɗi tunda na aure ki kin san nawa na bata ko ni ban
faɗa miki ba ai ita tana faɗa miki amma kin taɓa ko sau ɗaya ne kin taɓa min godiya
ko nuna jin daɗi kan haka, shine yanzu kike gaya min wai duka–duka ma nawa na
bata?" Koda yake banga laifin ki ba tunda ko ita Baban bata min godiya haka kawai
take ƙira tace in tura mata kaza ba tare da ko sanin ina da shi ko bani da shi
wanda ko ita Hajjiya bata hakan amma hakan bai dame ni ba saboda ko ba komai ita
uwa ce kuma ina auren ƴar ta dan haka nima kamar ɗan ta nake but you, har kina da
bakin magana ko kin ɗauka ban san kina min halin ɓera ba ko dan bana magana shine
kike tsammanin ban san komai ba." Ganin kamar ransa ya ɓace kuma ya fara tauna mata
asiri ne yasa ta saurin canja maganar da ce wa. "To yanzu me na kawo duk wannan
magan–ganun dan allah, abar maganar yanzu kawai anko ne fa nace ka siya min kuma
nasan kana da kuɗin ne shi yasa na faɗa maka kuma ma ni da ina da kuɗin ai bazan ma
tambaye ka ba."

"Uhmm ina kuɗin da nake baki monthly?" " babu shi nayi anfani da shi." "To ai shi
kenan daga haka ya miƙe tsaye tare da ce wa to ni na tafi aiki sai na dawo." "Ɗan
tsaya dan allah ina son fita." "Zuwa ina?" "Gidan su lubna." "No baza ki je ba."
Daga haka ya fita ba tare da sauraran magiyan da take mishi ba.

Tsaki taja bayan fitar shi tare da cewa "wannan wani irin mutum ne haba, haka kawai
yake son sani kunya a gaban ƙawaye kowa yana ganin ni matar me kuɗi ne amma ace
common anko na kasa siya haba bazai yu ba duk yanda za'a yi sai na siya nima dan
bazan bari ayi min dariya ba. Mutum sai rowar tsiya duk abunda nayi tunanin samu a
wurin shi kafin na aure shi ban samu ba i wonder how Aisha ke mishi da yake kashe
mata kuɗi kamar me amma ni in na tambaye shi sai ya sani a gaba da tambayoyi kamar
wata ƙaramar yarinya yanzu kuma har ido ya fara sawa. ya aka yi ma ya gani kayan
abinci yana ƙare wa da wuri ni ne kuma wai har yasan ina mishi halin ɓera. hmmm duk
wannan bai dame ni ba ko ka bani kuɗin ko kuma na ɗauka da kai na dan na rantse
baka isa ka hana ni siyan ankon nan ba." Daga haka ta shiga ɗakin ta tare da nemo
spare key ɗin ɗakinsa da ya hana ta shiga tun ranar da ya fara gyara wa da kansa.

Tana buɗe ƙofar ta shiga yi mishi bincike a ɗaki ta ko ina amma bata samu komai ba
dan haka ta juya tare da nufin fita sai ta tsaya cak tare da ƙara buɗe bedside
drower. Tana buɗe wa kuwa ta ga bandir ɗin dubu–dubu a ciki wanda tana gani ta rufe
baki da hannu biyu kana da saure ta soma zare daga ko wani bandir sai da ta zare
daga cikin ko wanne tukunna ta maida shi wurin sa da wuri tare da rufe drower kana
ta fita daga ɗakin tare da kulle shi kamar ba wanda ya shiga ciki kana ta shiga
ɗakin ta da wuri tare da sauke ajiyar zuciya tare da ce wa. "Hmmmm wai bashi da
kuɗi yanzu me wannan da na samu ni dama can nasan yana da su kawai baya son bayar
wa ne kawai amma ba damuwa ai na samu duk da bai bayar ba ni na ba kai na ai." Ta
faɗi hakan ne tare da kissing ɗin kuɗin kafin ta zauna ta fara ƙirga kiɗin. Tana
cikin haka sai taga wayarta ta ɗan yi haske tare yar ƙara ma'ana text aka tura
mata, sai da ta gama ƙirga kuɗin tukunna ta ɗau wayarta tare da duba saƙon. Tana
ɗuba wa taga kuɗi ya tura mata dubu 50 ai da saure tayi tsalle ta dire tare da
cewa. "Yes! Yes!! Dama na sani ai zaka tura kawai faɗa kawai kake amma zaka tura
Hmmm dai–dai kenan yanzu na samu kuɗin kaya da kuma kuɗin mayafi da jaka yes yanzu
bari nayi saure naje na dawo kafin ya dawo. Daga haka ta ɗauki mayafin ta tare
barin gidan sai gidan Lubna.

Tana gidan Lubna ƙiran shi ya shiga wayarta amma bata ɗaga ba saboda haushin shi da
take ji. Husna ba ita ta bar gidan lubna ba sai da ta bata kuɗin kayan har ma da
kuɗin ɗinki tukunna lokacin har yanma ma tayi kuma Aliyu ya kusa dawo wa.

Tana koma wa gida ta shiga ɗaki tare da kwanciya kan gado domin bacci dan gaba ɗaya
a gajiye take dan haka ba tare da ko tunanin sallah da ba ta ta soma bacci.

Cikin bacci ne taji kamar ana ƙiran wayarta dan haka a hankali ta miƙa hannu ta
ɗauki wauar tare da aza wa a kunnen ta kana ta ce. "Hello! Bai tsaya jin me zata ce
ba ya ce da ita. "Nayi ta ƙiran ki a waya ɗazu baki ɗaga ba." "Eh bana kusa da
wayar ne shi yasa." Tayi ƙarya. "Ok to na tura miki saƙo kin gani?" "Ehh na gani."
Tohm za muyi baƙi ne dan haka ayi girki me kyau mun kusa dawo wa kinji." Nan da nan
ta haɗa rai tare da cewa su waye kuma." "Baki san su ba dan haka a gyara gida da
kuma girki me kyau. Na ɗauka ma kin gama by now ma." "Okay! Kawai tace tare da
katse ƙiran. "Kai wannan wani irin damuwa ne haka haba mutum bai isa ya zauna ya
huta ba sai an dame shi, yanzu su waye ne haka da za su zo su dame mutane ance musu
muna buƙatar su ne." Da haka ta fita falo,sharp–sharp ta gyara ko ina tare da saka
turaren wuta. A Lokacin da ta gama yayi dai–dai da iso war su. Dan haka bata samu
damar shiga kitchen dan ɗauro girki ba suka shigo da sallamar su a baki, shine a
gaba sai sai abokin shi da iyalen sa.

Ko bayan sun zauna da gaisa wa sai ta zauna ita ma ba tare da tunanin ka musu koda
ruwa ne, Aliyu ne ya tura mata text da ta kama baƙin ruwa mana tukunna ta tashi ta
ka musu ruwa da drinks. Tana zama kenan ya ƙara tura mata wani text na cewa fatan
abincin is ready?" wai ita fa ta ma manta da wani abinci sai da ya tunatar da ita
dan haka ba tare da yi mishi reply ba ta tashi tare da shiga kitchen.

Koda ta shiga kitchen ɗin ta rasa me zata dafa musu sharp–sharp da ba zai ɗau
lokaci ba dan da gani baza su ɗade ba, da wannan tunanin ta ɗau tukunya ta ɗaura a
kan Gas tare da zuba ruwa a ciki kana ta buɗe kanta tare da ɗaukan indomie ta fara
buɗe wa dan ita kaɗai zata nuna da wuri dan haka babu ɓata lokaci ta fada indomie
da kwai ta zuba a coola kana ta sauke ajiya zuciya na gama wa da wuri.

Koda ta fita falo samu tayi sai hira suke abun su dan haka ita ma ta shiga cikin su
aka soma hirar da ita.

Koda lokacin sallah yayi kowa ya tashi mazan suka fita masalaci matan ma suka yi
nasu a gida.

Bayan dawo war su aka cigaba da hira. Yanzu ma shi ya tura mata text da ta kawo
abincin tukunna ta kawo abin tare da jerawa kan dinning kamar abun arziki.

Kana ta sanar da su da abinci fa yana dinning su zo su ci abinci..

P.32
Ko bayan kowa ya zauna kan kujerun dining ta soma serving ɗinsu, Koda ta ɓude
coolar nan aka fara kallon–kallon dan ba wanda ya kawo abinda ke ciki ba kenan.
Aliyu kuwa sabon kunya kamar ƙasa ta tsake ya shige ciki sabon kunya ya ma rasa
abun cewa sai ma kanshi da ya sunkuyar ƙasa. Ita ko Husna ko a jikin ta bata ma
lura da irin mugun kallon da yake jifan ta da shi ba, Haka ta zuba wa kowa a plate
ɗinsa suka fara ci. Har baƙin suka koma Aliyu bai k'ara sake jiki ba saboda kunyar
da Husna ta saka shi a ciki. koda ya fito raka su abokin shi ya ja shi gefe tare da
yi mishi magana kan ya lura tunda suka fara cin abinci mood ɗinshi ya canja kuma
yasan dalilin haka amma kar ya damu su ai na gida ne kuma wannan bashi ne farkon
zuwan su gidan shi ba ai, sun San ba haka gidan sa yake ba dan haka ya mata uziri
ƙila bata da lafiya ne shi yasa.

Maimakon kalaman abokin shi yasa ya ɗan ji dama–dama amma a'a sai ma ƙara tunzura
shi da suka yi nan ya ƙara tabbatar da Aisha ita ce matar shi ta rufin asire sai ya
tuna da ita da kuma yanda take kula da baƙinshi da ma Y'an uwan shi gaba d'aya,
da bai biye wa zuciya ba da duk wannan bai faru ba. Da haka ya raka su har mota sai
da ya ga fitar su tukunna ya koma ciki.

Yana shiga falon ya shiga kwalla mata ƙira kamar an aiko shi. "Husna! Husna!!
Husna!!!

"Na'am lafiya?" "Au tambaya ta ma kike?" "Kamar ya?" Ban gane ba me ya faru?" Aliyu
sabon takaici ya ma kasa magana dan ji yake kamar ya tattake ta a wurin. Bai yi
magana ba sai ma shiga kitchen da yayi tare da ɗauko ragowar indomie dake cikin
coola tare da cewa me wannan?" Husna da bata gane me yake nufi ba ta ƙara cewa.
"Abinci ne mana me ya same shi?" Wanda hakan ma ƙaramin tunzura shi yayi ba dan
haka ya wurgo mata da coolan gaban ta da ƙarfi da yasa ta buɗu abincin gaba ɗaya ya
watse a wurin kana ya ce. "Me wannan da kika dafa?" Na ce me wannan da kika dafa wa
baƙina ehhh?" Duk cikin gidan nan ki rasa abunda zaki bawa baƙina sai wannan abun?"
Ya faɗa da ƙaraji da har sai da ta firgita ta soma ja da baya dan sosai ya bata
tsoro.

"K..ka..kayi haƙuri." Ta faɗa murya na rawa. "Me haƙurin ki zai canja?" Na ce me


haƙurin ki zai canja?" ai kin riga da kin cuce ni kin bata min suna ace nayi baƙi a
gidan amma a rasa me za'a basu sai taliyar Yara?"

"Na ce kayi haƙuri kuma ma da kake magana baka fa faɗa min da wuri ba and me kake
son a dafa musu dan allah bayan kasan abubuwa sun ƙare." Sai da ya ɗauki kusan
minti biyar yana mai ƙoƙarin calming down dan ya san a yanda yake nan in yace zai
biye wa zuciyar to kuwa zai aikata abunda zai zo yayi da nasani dan haka sai da ya
ɗan sauko tukunna ya soma mata magana a hankali.

"Ban tura miki kuɗi ɗasu ba, ko baki gani bane?" "Na gani." Sai da ya ƙara jan
numfashi tukunna ya cigaba. "Bayan na tura miki kuɗi na ƙira ki ko ban ƙira ki ba?"
"Ka ƙira amma ai nace maka bana kusa da wayar." "Ok! Amma ai na tura miki text
massage da kice da driver ya kai ki kasuwa ki siya abunda babu ayi girki zamuyi
baƙi ko ban tura miki ba?" Dummm! Gaban ta ya bada. "Kuma koda ace baki ga saƙon a
kan lokaci ba Husna kina son faɗa min duk gidan nan babu abunda zaki girki wa baƙi
ba sai indomie?" "Kayi haƙuri wallahi ban san kuɗin cafane bane." "Me kike nufi da
baki san kuɗin cafane bane?" "Uhm..uhmm na ɗauka kuɗin anko ne ka tura min."
"Anko?" Wani anko?" Ba mun yi maganar nan da safe ba to me ya kawo shi yanzu?" Ba
ma wannan ba yanzu ina kudin da na tura miki, ki maido min da su yanzu nan gobe
zanje kasuwan da kai na dama ai ni nake zuwa." "Babu su." Ta faɗa da muryar
tausaye. "Har ya juya zai wuce ɗaki sai ya tsaya cak tare da juyawa. "Me kike nufi
da babu kuɗin?" "Da ka tura min su na ɗauka na anko ne kuma ma ni banga massage
ɗinka ba na wai kuɗin cafane ne ba." "Yanzu ina kuɗin suke?" "Na riga da na tura
su."

"Innalillahi wa inna illahi Raju'un."


Kawai ya ke anbata wa, bai sake yin magana ba ya juya ya shiga ɗakinsa.

Husna kam tana ganin shigar shi taja wani dogon tsaki kana tace. "Haka kawai ya
fasa min coola ya sani hasara. Sai kuma ta tsaya tambayar kan ta. "To amma me
laifin indomie, naga ita ma abinci ne kuma sun ci to me na wani damun kan a da na
mutane. hmmm lallai fa ashe ba kuɗin kaya ka tura ba hmm wannan kuma sani ya rage
naka dan kuwa na samu abunda nake so kuma ma ai kai kaja komai tunda na biki ta
lalama kace baza ka siya ba to dama sai ka jira sakamako dan ma wai bai san ina na
samu sauran kuɗaɗin ba, ai ina ga ma ƙila ya suma mutum sai rowar tsiya kana da shi
amma baka son bayar wa. Hmmm za mu gani ai kai baka son bayar wa ni kuma bana
ɗaukan no for an answer.

Ɓangaren Aliyu kuwa yana shiga ɗaki ya faɗa toilet tare da sakar ma kanshi ruwa dan
sau–sauta mishi abunda yake ji. Sai da ya ɗauki kusan minti 30 a toilet ɗin tukunna
ya fita gugun shi ɗauri da towel, bai ko tsaya shafa mai ko sa kaya ba ya haura kan
gado tare da lulluɓa jikin shi da blanket kana ya faɗa duniyar tunani.

Washagari koda ya tashi bai bi ta kanta ba ya tafi aiki, ko a wurin aiki ma ya kasa
tabuka komai dan kuwa sai gwada numbern Aisha yake amma abu ɗaya ake faɗa mishi
wayar a kashe take wanda yasan ba haka bane dan ba yanda za'a Aisha zata zauna har
kwana biyu ba tare da waya ba sai dai in babu lafiya. Hakan ne yasa koda ya tashi
daga aikin bai wuce gida darect ba ya nufi gidan su Aisha.

******

"Yes! Yanzu komai yayi." Ce war Eeman bayan gama wa Aisha makeup dan karɓan baƙon
ta wato Lukman. "Kai amma kin gan ki kuwa?" Kinga yanda kika yi kyau wallahi da ba
dan ni ce na miki wannan kwalliyar ba da sai ince wannan bake bace kin zama kamar
ƴar sweet 18 ɗin nan fah." "Bana son renan hankali dan allah ni ki yi ki bani
wuri." Aisha ta faɗa a ɗan hasale. "Sorry Hajjiya a yi haƙuri ai mun gama ma ai
saura wannan kaɗai." Ta ce tare da ɗaukan turare ta fara fesa mata shi. "Yanzu kam
komai ya kammala saura fitowar ki amarsu, amma dan allah Aisha na roƙe ki please
karki bani kunya dan allah kinga yanda mutumin nan yake ta jigilan zuwa gidan nan
dan kawai kiyi accepting ɗinshi. Nasan abunda kike ji wa tsoro and i asure you
lukman ba haka yake ba na san shi tun baya yau ba and his my friend brother kuma ma
in har yana da wani abun aibu ke kanki kin san i will never allow that, lukman
mutumin kirki ne kuma kowa ya shaide shi da haka. Dan haka ina roƙon ki da kiyi
accepting ɗinshi na san bakya son shi amma with time zaki so shi." Sai da ta sauke
nannauyan ajiyar zuciya tukunna ta ɗan muskuta kana ta ɗubi ta kana tace. "In sha
allah zan ƙoƙarin naga na bashi wannan damar duk da ina jin tsoron haka amma zan bi
shawarar ki, dan ko ba jima ko ba daɗe dole na yi auren nan and nima gaskiya na
yaba da halayen Lukman tun ba yau ba, kawai matsalar a nan shine ina tsoron auren
mijin mataciya." "No! Karki damu kanki da wannan da kuma maganar mutane abunda yasa
bai ƙara aure ba tun rasuwar matar shi ba bai samu wace yake so bane shi yasa amma
karki wani damu kanki ba abunda zai faru kinji?" Kai kawai ta kaɗa mata. "Good
yanzu sai ki tashi mu tafi ko kar mu barshi shi kaɗai." Daga haka ta kama hannun ta
tare da barin ɗakin.

A falon baƙi suka same shi zaune a ƙasan carpet waya ce a kunnen sa da gani waya
yake. Ma sha allah Lukman kyakkyawa ne babu laifi fari ne bashi da jiki amma yana
ɗan tsaye shi.

Da sallama a baki suka shiga falon tare da neman wuri a ƙasan carpet suka zauna
tare da jiran ya gama wayarsa.

Aisha banda bugu ba abunda zuciyarta ke yi, ganin abun take wani sabo. Sai ta tuna
farkon zuwan Aliyu gidan su zance, irin kwalliyar da ta mishi da kuma..zungurin ta
da Eeman tayi ne yasa ta dawo wa haiyacin ta tare da gyara nutsuwar ta.
"To in-law ni na shiga ciki." "Haba dan Allah da kin zauna ai Nima ba wani dad'ewa
zanyi ba ai." "A'a wallahi gwara da na shiga ciki kuma ma ina da abun yi." Daga
haka ta sunkiya ta ma Aisha rad'a a kunnen kana ta bar falon.

Kowa yayi shuru cikin su bayan fitan Eeman, Aisha bata ma San me zata ce ba dan sai
taji gaba d'aya yayi mata kwarjini da ma ta kasa daga ido ta kalle shi ma. Amma
tana jin idanun sa a kanta Wanda haka ba k'arimin takura mata hakan yayi ba.

Ganin ya k'i yin magana sai idanun da ya zuba mata ne yasa ta Dan gyara zamanta
tukunna ta ce. "Sannu da zuwa fatan ka iso lafiya." Sai a lokacin ya dawo haiyacin
sa daga kallon nata tare da amsa gaisuwar ta. "Lafiya Humaira fatan na same ku
lafiya?" "Lafiya, ya gida da su Mama." "Lafiyansu k'alau suna ma gaishe ki." "To
ina amsa wa." Daga haka suka d'auki shuru na wani lokaci kafin Lukman ya gyara
muryar tare da cewa.

"Maganar gaskiya Humaira, na ganki kuma naji kin min Dan na yaba da halayen ki da
kuma tarbiyyar ki Wanda shi ya ja ra'ayi na a kanki naji ina son k'ulla wata alk'a
dake wace ba komai bace sai alak'ar aure. Kin san ni kin kuma San y'a uwa na Dan
haka babu b'oye-b'oye a cikin wannan lamarin in kin amince ko ko next week ne zan
iya turo iyaye na a zo a nema min auren ki. Dukkan mu ba yara bane da zamu zauna mu
b'ata wa juna lokaci, na zo nan ne dan jin me ra'ayin ki game da ni?" Kar kiji
komai duk abunda ke ranki ki fad'a min I will respect your decision."

"Babu komai Allah yasa hakane mafi alkhairi, Allah ya kuma nuna mana ranar."
"Alhamdulilah alhamdulilah Allah na gode maka." Daga haka suka soma hira sama-sama,
koda ya tashi tafiya ya buk'aci da ta raka shi Moto

zai d'auko abu.

Koda suka fita waje ya bud'e boot tare da fito da ledoji ya mik'e mata Amma sai ta
k'i amsa, sai da yayi ta mata magiya da karb'a tukunna ta karb'a. Kamar wace aka ce
ta d'aga Kai Sama ta ganshi tsaye a d'an neesa da su. Dumm! Taji gaban ta ya ba da.

Da saure ta juya kan Lukman dan ganin ko shima ya gan shi Amma sai ta ga sam Bai ma
San me yake faruwa ba. Nan da nan taji zufa na tsatsafu mata ta ko ina sabon tsoro
da fargaba har rawa k'afafun ta ke yi. K'ara duba inda yake tayi tare da saurin
kawar da kai gefe kamar bata ganshi ba.

Aliyu kuwa in banda tafarfasa ba abunda zuciyarsa ke, gaba d'aya jijiyoyin kanshi
da wuyan shi sun mik'e idanun sa sun rik'id'e sun yi ja jur wanda har ruwa suke
fitar wa. Gaba d'aya idanun shi sun rufe ba abunda yake gani sai fuskar Lukman da
ta Aisha, yanda ta saki jiki sai dariya take.

Lukman Bai sani ba sai zuba hira yake da dariya Bai Ankara ba kawai yaji an kai
Mishi noshi a fuska tare da cakumo wuyar rigar shi tare da kai Mishi wani noshin a
hanci nan da nan hancin ya fara bleeding. Aliyu Bai tsaya a nan ba ya cigaba da kai
Mishi noshi ta ko ina, Lukman ma ganin sai Kai Mishi noshi ake ta ko ina ne ya sa
shi ma fara kai ma Aliyu noshi nan fa dambe ya kacame a tsakanin su.

P.33

"Humaira! Humaira!! Humaira!!!

Firgigit ta dawo haiyacin ta tare da duban Lukman kana ta juya wurin Aliyu da har
yanzu yana tsaye a wurin bai motsa ba sai da ta d'an sauke ajiyar zuciya tukunna ta
dubi Lukman da yake tambayar ta ko lafiya tunanin me take haka. "Lafiya babu komai
kawai Kai na ne ke ciwo." "Ok!sannu Amma kin sha magani?" "Eh na sha." Ta fad'a da
d'an sauri tare da duban wurin Aliyu da har yanzu yake kallon su da ace kallo yana
kashe yana kashe mutum da kuwa ya kashe su. "Ok to shi kenan ni zan wuce sai na
sake dawo wa." Daga haka ya shiga motarsa tare da barin wurin.

Aisha sai da ta ga ya wuce tukunna ta juya kan Aliyu da ya zo wurin ta tare da


tambayar ta "waye wannan?" Sai da ta mishi kallon Sama da k'asa tare da tsuke fuska
kamar bata taɓa dariya ba kana ta tambaya shi. "Me haka Malam na san Ka ne?" Da
mamaki ya dubi ta tare da nuna Kan shi. " Ni d'in ne Baki sanni ba?" "Waye Kai?"
"Aisha dan Allah ki dai na wannan wasan please ba ma wannan ne ya kawo ni ba dan
Allah ki yi hak'uri da abunda ya faru ki koma gida mu zauna lafiya kamar yanda muke
da can." "Halan Ka rasa tunanin Ka ban sani ba?" yo in ba Ka rasa tunanin Ka ba Kai
har kana da idon da zaka dube ni Ka ce na koma gidan ka?" "Na san ban miki adalci
ba Amma Dan Allah kiyi hak'uri na miki alk'awarin hakan ba zai sake faruwa ba."
"Hmm amma baka duba calendar ko?" Dan ba yanda za'a yi ace kana dubawa ba and ka zo
min da wannan maganar ba, Kai bara ma kaji ko da ace ban gama fita daga idda ba
Aliyu na gama zama da kai. Ka ga Wanda Ka gan mu tare, to shine mijina in Allah ya
yarda Dan haka zai yi kyau Ka tattara k'afafun ka bar nan wurin tun kafin Abbu ya
zo ya same ka a nan dan baza Ka ji da dad'i ba."

Daga haka tayi shigewar ta ciki ta barshi Baki bud'e dan ya ma rasa abun fad'a ma
sabon mamakin ta. Yana haka sai ga motar Abbu ta danno Kai, da sauri ya matsa kusa
da motar dan gaishe da Abbun ma sai yaga sai ma d'aga glass d'in motar da yayi tare
da danna wa mai gadin horn. Abbu ko da ya shiga sai da yayi wa Mai gadin gargadin
cewa Kar ya kuskura ya bar Aliyu ya shigo masa gida in kuwa ya Bari to fa ya nemi
wani aikin ba dai wannan ba. Mai gadin yana jin haka ya ce. "Ai Alhaji Kar ka damu
hakan ma bazai faru ba, Abbu Bai ko tsaya Jin maganar sa ba ya wuce cikin gidan rai
a b'ace.

Aliyu kuwa da bai San komai ba ya tura k'ofar gate d'in tare da shiga ciki, Amma
tun kafin ya shiga Mai gadin ya tsayar da shi ta hanyar ce wa. "Alhaji yace Kar a
barka ka shiga." "Kamar ya Kar a barni na shiga, ko Ka San ni waye a gidan nan?"
"Kayi hak'uri Amma Me gidan ne ya hana." Daga haka ya ture Aliyun waje tare da sa
sakata ya kulle k'ofar.

Ya da d'ade a tsaye ba tare da sanin abun yi ba, abunda ya fi bashi mamaki ma wai
shi Aliyu yau ake hana shi shiga gidan sirkan shi. Ganin ba abunda tsayuwar za ta
mishi ne yasa shi shiga mota tare da barin wurin amma da alk'awarin zuwa gobe.

Ɓangaren Abbu kuwa yana shiga ciki ya soma ƙwalla wa Aisha ƙira. Aisha! Aisha!!
Aisha!!!

Ummi ce ta fito daga kitchen tare da tambayar shi lafiya. "Lafiya alhaji?"

Bai bata amsa ba sai ma tambayar ta ina Aisha take. "Tana ɗaki." Ta faɗa.

Zai sake yin magana sai ga Aisha ma sun fito. "Na'am Abbu kana ƙira na." Ta faɗa.
Sai da yayi mata kallon tsab tukunna ya tambaye ta. "Me wannan Yaron ya zo yi?"
Na'am! Ta ce a ɗan ruɗe. "Kar ki min ƙarya dan na gan ku tare." "Wallahi nima ban
sani ba kawai nima na gashi." Ni zaki wa ƙarya eh, ke wato baki da ma zuciya har
kin manta da abunda yayi miki." "Allah Abbu nima ban san me ya kawo shi ba kawai na
na fita karɓan abu ne kawai sai na ganshi kuma ma shi ya tsayar dani." Kwafa ya ja
tare da nuna su gaba ɗayan su har da Ummi kana ya ce. "Koda wasa kar na ji ko ganin
Yaron nan a gida na." Sai kuma ya juya kan Aisha. Kar na sake ganin ki da shi kai
ko a waya ne." Daga haka ya wuce ɗakinsa ba tare da ko duba Ummi dake faman bashi
kaƙuri.

*******

Aliyu koda ya koma gida bai tarar da Husna a gida ba kuma bai tsaya neman ta ba ya
wuce ɗakin shi, har dari yayi bai fito daga ɗakinshi ba ko sallah ma a ɗakin yake
haka Husna ma da ta dawo tayi ta ƙonƙasa masa da ya fito ya ci abinci amma shuru
bai bata amsa ba balle har ya buɗe.

Washagari ma haka da sassafe ya fito ko breakfast bai yi ba ya tafi gidan su Aisha


amma me gadin ya hana shi shiga dan haka can gefi ya samu ya tsaya tare da jiran
fitan Abbu.

Yau ma kamar jiya ne dan kuwa Abbu koda ya fita sai yayi kamar bai ganshi ba ya ja
motarsa ya tafi.

Jiki a sanye ya shiga motar shi shima ya wuce wurin aiki.

To haka wannan satin Aliyu sai fama gwada numbern Aisha yake da kuma ziryan bin
Abbu kasuwa dan kawai ya bashi dama amma Abbu ya ce bai san zan ce ba dan kuwa har
police yace zai ka mishi in har bai dai na zuwa mishi kasuwa da gida ba.

Aliyu fa ya shiga tashin hankali dan kuwa tun yana ɗaukan abun da wasa ne har yazo
ya fi ƙarfin sa dan kuwa har sabon sim ya siya ya ƙira Aisha da shi amma tayi
blocking ɗinsa bayan ta mishi rashin mutnci. Ya rasa ya zai yi har rama ya fara yi
sabon tunani–tunani da ya sa a gaba ko abinci bai iya ci sosai ga kuma wahalar
Husna da kullun sai tayi abunda zai yi magana.

*********

"Hmmmm sai yanzu kasan kayi kuskure?" Na ce sai yanzu kasan kayi kuskure kenan."
"A'a Hajjiya kiyi haƙuri dan allah." "To ni me ka min Aliyu da kake bani haƙuri."
"Dan allah Hajjiya kiyi haƙuri ki yafi min." "To ni laifin me ka min." "Ni me laifi
ne a wurin ki tunda har na ƙi jin maganar ki na biye wa son zuciya." "Uhmm yanzu
dai me kake so ne da kazo kana ta wani bani haƙuri kamar na kirki dan nasan haka
kawai baza ka zo kana bani haƙuri ba sai da dalili." Shuru yayi na ɗan wani lokaci
dan bai san ya zata ɗauki maganar ba amma duk haka zai gwada sa'ar sa. "Ummm dama
Hajjiya ina son ki tafi gidan su Aisha ki basu haƙuri dan Allah hajjiya hakan ba
zai sake faruwa ba." Ya faɗa da muryar tausaye. "Haƙurin me zan basu?" Kayi wani
abu ne da da bansani ba da har kana son in basu haƙuri." "A'a ba abunda nayi kawai
abunda ya faru kwanakin baya. Nan ya zayyane mata komai."

Ɗan taɓe baki tayi tare da ce wa. "To sai me dan ya ce ƴar shi baza ta koma gidan
ka ba." "Hajjiya dan Allah kiyi haƙuri nasan in kin tafi da kanki zasu saurare ki
please hajjiya." "Lokacin da ku kayi abun ku ka sanar da ni?" Sai yanzu zaka wani
kwashe ƙafa kazo wai inje in ba da haƙuri to tsaya kaji ba ruwa na da wata Aisha
dama na faɗa maka ai na cire hannuna a kan lamarin ka kuje can ku ƙarata." Daga
haka ta ɗaga wayar ta dake ringing.

Hakan nan ya bar gidan zuciyar shi babu daɗi. Yana komawa gida kuma ya tarar da
wani ɓacin ran dan kuwa tarar yayi Husna ta fita ba tare da izinin shi ba, ga kuma
gidan ta barshi kaca–kaca. Kai kawai ya kaɗa tare da wuce wa ɗakinsa, ko zama bai
yi ba wayar shi tayi ruri. Koda ya duba me ƙiran sai yaga ma Mubarak ne abokin
aikin shi ne wanda ya bashi ajiyar kuɗi, dalili kuwa anyi hacking ɗin account
ɗinshi ne wanda bai kai ga gyara wa ba kuma kuɗin da ya bashi nan ba nashi bane
kuɗin auren ƙanwar shi ne da aka kawo to shine ya ba Aliyu da ya aje masa zuwa
lokacin da zai gyara komai ya amsa.

"Ok! Daga haka ya kashe wayar tare da buɗe drawer ya ɗauki kuɗin dake ciki ba tare
da ya tsaya ƙirga ba ya fice daga gidan. Yana fita ya ga Mubarak tsaye can gefen
wata bishiya, bai tsaya wata–wata ba ya nufi wurin tare miƙa mishi hannu suka gaisa
kana ya miƙa mishi kuɗin.

"Yawwa ɗan uwa na gode."daga haka ya saka kuɗin a aljihunsa. "A'a baza ka ƙirga
ba?" "A'a ba sai nayi ba ai na yarda da kai." "A'a da dai ka ƙirgan zai dai fi."
"Ok tunda ka nace amma in ta ni ce ba sai na ƙirga ba." "Eh duk da hakan kasan
lamarin kuɗi sai a hankali." "Kuma haka ne fa." Daga haka ya fara ƙiragawa, koda ya
ƙirga sai ya ga kuɗin bai cika ba dubu ɗari biyar ne babu dubu sittin da uku a
ciki.

"Basu cika ba." Mubarak ya faɗa tare da duban Aliyu da gaba ɗaya ma hankalin shi
baya wurinsa hankalin shi na can wurin Husna da ke rigima da me napep kan sai ta
biya shi kuɗin shi." Sai da ya ɗan taɓa shi tukunna ya juyo kan shi tare da
tambaya. " ya sun cika?" "A'a babu dubu 63." Kamar ya, ƙara kirga wa mu gani dai."
Ya faɗa dan baya son abunda ya fara zuwa kanshi ya tabbata. Ba musu Mubarak ya sake
ƙirga kuɗin, wannan karan tare suka kirga kuɗin babu dubu 63.

Ba tare da cewa uffan ba ya cire wayarsa tare da ce wa. "Turo account numbern ka."
"A'a ka barshi babu damuwa." "No ka tura na maka transfer." A'a fa nace ka barshi."
Aliyu bai sake ce wa komai ba ya mai da wayar shi aljihu kana ya juya gida ba tare
da ko yi ma abokin shi sallama ba." Ganin yanayen sa ne Mubarak yasan babu lafiya
dan haka yayi saurin kama hannun shi da nufin tsayar da shi amma ina Aliyu ya fi
ƙarfin shi dan ture shi gefe yayi tare da wucewa fuu kamar isa.

Husna ko bayan sun sha rigima da me napep kan sai ta bashi ɗari biyar ita kuma tace
baza ta bayar ba in zai karɓi dari biyu to in kuma bazai karɓa ba to, haka ɗai suka
sha rigima da shi har a ƙarshe dai yaja mata Allah ya isa kana ya wuce.

Koda ta shiga cikin gida darect ɗakin ta ta shiga tare da fito da kayan da taje
amsa wato ankon, nan ta fara gwadawa.

Babu tsammani taji an banko ƙofar tare da shigowa, da sauri ta juya tare da ɗaura
hannu a kan ƙirji kana tace. "Kai! ka tsorota ni wallahi."

"Me yasa?" Ya tambaye ta tare da kafe ta da idanun sa. Dummm! Taji gaban ta ya bada
amma sai ta dauri ta tambaye shi. "Me yasa me?" Tana ganin yanda yasa hannun shi ya
dafe kansa ya runtse idanu kafin ya ware su a kanta. Sosai yake kokawa da duk
ƙarfin zuciyar shi na tuna mishi da akwai igiyar aure a tsakanin shi da ita, da ba
abunda zai hana shi dukan ta a gidan nan yau ta yanda gobe ko da wasa ne in an ce
ta taɓa abu ba tare da izinin me shi ba baza tayi ba.

P.34

Sosai yake kokawa da duk ƙarfin zuciyar shi na tuna mishi da akwai igiyar aure a
tsakanin shi da ita, da ba abunda zai hana shi dukan ta a gidan nan ba yau. Ta
yanda gobe ko da wasa ne in an ce ta taɓa abu ba tare da izinin mai shi, ba za tayi
ba.

"Ki tauna maganar da zaki yi min Husna dan gab nake da wanka miki mari, kar ki
gwada wasan banzan ki a kai na yau dan ba zai mana daɗi ba. "me yasa kika taɓa min
kuɗi?"

Kallon shi Husna tayi tana jin zuciyarta na cigaba da dukawa dan bata taɓa ganin
shi cikin wannan yanayen ba amma a ƙasan tsoran ta akwai maganganun shi da suka
ɓata mata rai, ta ya zai ce zai mare ta tana matsayin matar shi sai ka ce wata jaka
da ba'a san mahimmancin ta ba.

"Wai wani kuɗi?" Ta faɗa tana ƙara kwance sauran wani hankali da Aliyu yake jin
yana ruƙe da kwakwalwar shi.

Ya ko ɗauke ta da wani irin mari da yasa ta Jin kamar idon ya fad'o, da sauri ta
saka hannu kan idon tana laluɓawa taji kwayar idanun na cikin shi.

Wani irin nunfashi take ja tana son kukan ya kwace mata ko zai rage mata radaɗin da
take ji.

"Na faɗa miki ki tauna maganar da zaki faɗa min baki ji ba, uban me yasa ni da
gidana bazan a je kuɗi inda nake so ba, me yasa zaki ɗauka?" Me yasa zaki ɗaukar
min?"

Rashin hankalin ki bai faɗa miki zai iya kasance wa ba nawa bane, ban faɗa miki
cewa bani da kuɗi ba Husna?" Ba sosai take jin maganganun Aliyu ba, duk da hargowar
da yake kamar wanda yake jiran ƙiris ya rufe ta da duka.

"Abunda na ke miki bai ishe ki ba sai kin ɗaukan min kuɗi?" Kin ɗauka ban san kina
zara min ba duk idan na a je, ban miki magana bane saboda ina guje mana zuwa inda
muke yanzun. Kin san kuɗin wa ki ka ɗauka?" Kin san irin kunyar da kika sani a
ciki, me kike son in ce mishi ni na ɗauki kuɗin ko ke ki ka ɗauka?" Me yasa zaki
min haka eh, duk ƙoƙarin da na ke miki amma shine ki rasa da me zaki saka min sa da
wannan."

Zuwa lokacin raɗaɗin da take ji ya fara yin ƙasa sai hawayen baƙin ciki da ke
sulalo mata suna busar da tsoron shi da take ji, Ta ɗauka ya fi ƙarfin dubu 63 da
har zai zauna yana mata masifa da tijara akan su.

" eh ni na ɗauka saboda na tambaye ka ka hana ni shi yasa na gani na ɗauka, me yasa
kai ba ka faɗa min ka a je kuɗin ba?" me yasa baka faɗa min ba na ka bane?" Ta faɗa
da tsantsan rashin kunya. "A kan dubu 63 ne zaka mari ne, ni ba jaka ba ce da zaka
zauna kana jibga, in da ka saba yi wa matarka ba ta magana to ni baka isa ba tunda
ba jaka ka aura ba. Husna Ta faɗa tare da zazzare mishi ido kamar zata rama marin
da yayi mata.

Kai Kawai Aliyu ya kaɗa tare da juya kan shi gefi dan idan ya cigaba da kallon ta
zuciya ce zata ɗauke shi yayi mata dukan da har sai yaji wani daga ƙasusuwan ta
yayi ƙara alamar karyewa, zai daketa da har baza ta iya tashi balle alamar kuka da
har zata samu damar ta kalle tsabar idon shi har ta yi mishi rashin kunya. dan haka
ne ya nema musu abunda yafi da ce wa da su a yanzu. "Ki tafi gidan ku Husna, ki
tafi gidan ku ki huta nima in ɗan huta."

Sheƙeƙe Husna take kallon shi baki bude tana jin gaba ɗaya ya fara fitar ma ta rai.
gaba ɗaya burukan ta da take son cinma bata tunanin zata samu a wurin shi ba gaba
ɗaya sai yanzu take dana sanin garajen auren shi, gaba ɗaya abunda take gani a
wurin Aisha da kuma soyayyar da ta ke hangowa kanta in tashi ga gidan bata samu a
wurin shi ba , in banda masifa da tijara ba abunda ya sani.

Sai ta tuna maganganun Lubna da ta ke ce mata ita ta ɓata wa kan ta da kanta tunda
har ta yarda da shi kuma har ta aure shi, ba tare da wani shire, kuma ko yanzu ne
ta fita daga gidan shi ba zata rasa mijin aure ba me kudi da kyau wanda suka dama
shi a kyau da kuma arziki, tunda ita ma tana da kyaun ta irin ta ne ma maza ke nema
amma ta ɓata lokacin ta akan shi.

Amma duk da haka baza ta bi shawarar ta ba dan baza ta taɓa ba maƙiyan ta damar yi
mata dariya ba, duk abunda zai faru sai dai ya faru amma zama cikin gidan nan yanzu
ta fara sai ta cinma burukan ta tukunna in ma za ta yi tunanin rabuwa da shi, dan
baza ta taɓa aikin banza ba ace duk wahalar da tasha tun kafin auren har ma da
bayan auren dan samun abunda take buƙata amma ace rana ɗaya ta tashi a tutar babu,
inaa ba zai yu ba baza ta taɓa barin hakan ya faru ba.

"Ina ka ke son na tafi bayan wannan ne gidana gidan aurena, kuma da ka ke son na
koma gida ɗin da wata shaida kake son na tafi eh?" Ba dai saki ka ke nufi ba?" In
ma wannan ne tunanin da ka ke to gwara ma ka cire shi a ranka dan kuwa ba inda
zani, kai bara na faɗa maka wani abu zaman auren nan yanzu muka fara dan haka kama
cire duk wani tunanin rabuwa da ni dan ni da kai mutu ka raba takalmin kaza. Kuma
fa zaman lafiyar nan kai ka ƙi shi, tunda tun farko na ce maka a kawo ƴar aiki da
za ta dinga taya mu girki da aikin gida amma ka ƙi wai baka da kuɗin, wanda kuma
nasan ba haka bane kawai baƙin hali ne da kuma rowar tsiya ce ta hana. In kana son
a zauna lafiya kuma na dai na ɗaukan maka kuɗi to ka fita ka nemo kuɗin nan ko ta
ina ne dan bana juran babu ne. Kuma fa karka ɗauka wai dan ina sonka ne bazan rabu
da kai ba, a'a bana son shiga bakin mutane ne amma in banda haka miji goma ai ba
uba goma bane kar kayi tunanin kai wani ne dan ko yanzu na fita na bar gidan ka zan
samu wanda ya ma fika, Kuma mari na da kayi ban yafe ba tunda ba jaka ka aura ba."
Ta na kai wa nan ta fece da gudu ta shiga toilet tare da saka key kana ta buɗe
murya tace. "Allah ya isa ban yafe ba mugu kawai Allah sai ya saka min marin da
kayi min kuma kuɗi yanzu na fara ɗauka matuƙar baza ka biya min buƙatuna ba."

Aliyu sabon shock ya ma kasa motsa wa sai da ta shiga toilet ƙarar rufe ƙofar ce ta
dawo da shi haiyacin shi tare da gaskata abunda ya faru yanzun nan ba mafarki bane.
Ya daɗe a tsaya cikin ɗakin kamar wanda aka daskarar shi a wurin kana a hankali ya
kama handle ɗin ƙofar ya fita. koda ya fita ya kasa tafiya ko ina sai ma zama kan
ɗaya daga cikin kujerun falon tare da ɗaura hannu a kanshi ya shafa fuskar shi tare
da tunanin abunda ya faruwa tun auren shi da Husna har izuwa yanzu da wannan abun
ya faru. Lallai ɗan adam ba abun yarda bane wai ace Husna?" Husna yarinyar da ya
riƙe a gidan sa tun bata kai wannan munzalin ba, tun bata san ciwon kan ta ba, ya
kula da cin ta da shanta har ma da karatun ta shine yau take gaya mishi baƙar
magana har da ja mishi Allah ya isa?" Hmmm bai ga laifin ta ba, laifin kanshi da ya
ruɗe da surar jikin ta da kuma sharrin shaiɗan. Shi fa sai yanzu ma ya gane cewa ko
da can ba ba son Husna yake ba, kawai Sha'awar ta kawai ya ke yayi tunanin so ne
amma ba son ta yake ba. Yanzu dubi inda ya jefa kanshi a ciki gaba ɗaya ya zama
kamar wani mahaukaci saboda kuskure ɗaya, ya ƙi sauraran abokin shi kuma aminin shi
ya ƙi kuma jin maganar mahaifiyar shi ya kuma rufe ido ya aure ƙanwar matar shi ba
tare da tunanin komai ba bai dubi irin kusancin su bai tsaya tunanin ya zata ji ba
ya aiwatar da muradin shi, Duk wannan abun yayi su ne saboda ita amma yanzu dubi
abunda take mishi. Tunda yake da Aisha bata taɓa ɓata mishi rai da gangan ba koda
wasa a kullun burin ta ta farnta mishi ko ta yaya ne amma ya ɓata komai ya ɓata
komai yanzu Aisha ta tsane shi bata ma son kallon fuskar shi. amma kuma bai ga
laifin ta ba, tunda ko shine aka yi wa irin abunda yayi mata bazai ya fi ba. Sai
yanzu ne ma yake auna irin mijin ƙoƙarin da tayi lokacin auran shi da Husna, yanda
bata nuna mishi komai ba bayan ya faɗa mata ƙarin auren da zai yi kuma a ƙureren
lokaci kamar nashi. Sai yayi tunanin ranar da ya tafi gidan su Aishar ya gan ta da
wanin shi ba shi ba Allah kaɗai yasan me yaji a ranar dan ji yayi kamar ya kashe
wannan mutumen ko zai ji sanyi, duk da yasan babu aure a tsakanin su a yanzu amma
bazai iya juran ganin Aisha ta aure wani ba shi ba. Tunanin zata aure wani ba shi
bane ya sa shi saurin ɗaukan wayarshi tare da ƙiran ta da sabon layin da ya siya
yau dan ita kawai tunda bata ɗagan ƙiran shi.

Sai da wayar tayi ta ringing kamar baza a ɗaga ba har ya cire rai tukunna ya ji an
ɗaga tare da yin sallama. Bai yi magana ba sai da ya ɗauki kusan minti 2 yana
saurarn muryarta mai zaƙi da take tambayar waye ne. Wata sanyayyer ajiyar zuciya ya
sauki tare da ɗan gyara murya kana a hankali ya ce. "Ayush ni ne, dan Allah karki
kashe wayar please, dan allah Aisha kiyi haƙuri ki yafe m... kitt ya ji ta katse
wayar. Da kallo ya bi wayar ba tare da sanin abun yi ba dan a gaskiya ya gaji da
irin wannan abun bai san taya zai shawo kanta da ta bashi koda minti biyar ne suyi
magana.

******

Ɓangaren Aisha kuwa tana kitchen ne tana wanke–wanke taji ringing d'in wayarta dan
haka bata ɓata lokaci ba wurin wanke hannayen ta da kuma goge su kafin ta ɗaga
wayar koda ta ɗaga sai taji shuru ba'a yi magana ba ɗan haka ne ta sa wayar a
speaker tare da tambayar waye ne dan taga sabuwar number ce. Har zata kashe wayar
kenan taji muryar shi yana roƙon ta da kar ta kashe wayar, shi yasa ta tsaya ba
tare da ta kashe ba tana sauraran abunda yake ce wa. Ba zato taji an warce wayar
daga hannun ta tare da wurgi da ita nan tayi kaca–kaca a wurin. Da sauri ta juya,
dumm!ta ji zuciyarta tayi tsalle tare da harba wa nan da nan jikin ta ya hau rawa.
"Wallahi Abbu ba abunda kake tunani bane, nima ban san shine ya ƙira ba sai da na
ɗaga." "Ki same ne a babban falo." Daga haka ya juya ya bar kitchen ɗin cikin ɓacin
rai.

Aisha hannu ta sa a kanta tare da zama dirshan a ƙasa tare da cewa "na shiga uku ni
Aisha wayyo Allah me na jawa kai na." Daga haka ta matsa wurin wayarta da ta riga
da ta ragar gaje.

Abbu ne tsaye a gaban su ya ƙura musu ido na ɗan wani lokaci kana ya juya kan Ummi
da bata san me yake faruwa ba, tana ma sallah lokacin da ya buƙaci ganin ta a
babban falon shi dan haka bata san me ke wakana ba. "Wato ni ban kai matsayin da
zan bada umarni a gidana kuma abi ba ko?" Ya faɗa ne yana kai duban shi ga Aisha da
ta sunkuyar da kai ƙasa kamar me niyyar sujjada. "Me ya faru ne Alhaji?" Ummi ta
tambaya dan son gane ina maganar shi ta dosa dan bata gane maganar shi na bai isa
da gidan shi ba. "Eh abunda kika ji na faɗa dai–dai ne ga ta nan ki tambaye ta me
na tarar take yi a kitchen ɗazu." Ya faɗa tare da nuna ta da yatsa. "Aisha! Me kika
yi ne haka da har ya ɓata wa mahaifin ki rai haka." "Ba wani nan ai harda ke aciki
kar ki wani yi kamar baki san komai ba dama bakin ku ɗaya ai na sani ko in ce ke ki
ke ɗaura ta akan hanayar, tunda na lura tun farko kike nuna rashin jin daɗin ki kan
hukuncin da na yanke a kan ta da wannan banzan Yaron." Ya ƙarashe zancin ne da
kunfar baki kamar zai dake su. "Haba Alhaji taya zaka ce ni na ɗaura ta akan
hanayar bayan ban san ma akan me kake magana ba" " hmm tambaye ta me na tarar take
yi a kitchen." "Abu kayi haƙuri wallahi ba haka bane shine ya ƙira da wata number
ni gaba ɗaya ban ɗauka shi bane da na san shine da banzan ko kalli wayar ba." Sai
yanzu Ummi ta gane akan me yake ta wannan sababin, wato dai tarar yayi suna waya
shine yake wannan tada jijiyar wuya. Ita abun dariya ma ya bata haba taya za'a yi
ya hana yarinya magana da wanda take so, Aisha ba yarinya bace yanzu da zai wani sa
mata ido haka ai ta san ciwon kan ta kuma ma in taga zata iya yafe ma shi Aliyun
kuma ta koma gidan shi to me a ciki tunda dai gaba ɗayan su nan ba wanda yasan
zafin abun da yayi mata, tunda basa wurin lokacin da abun ya faru. And kuma in ita
da kanta ta buƙaci koma gidan shi ba sai ta koma ba, me na takura yarinya haka
fisabililah. Duk wannan maganganun a zuciya take yin su dan bata isa ta faɗe su
yaji ba in ba dai tana son tijarar shi bane.

"Na ja ma Yaron nan kunne akan koda wasa ne Kar ya kuskura na ga k'afar shi a gida
na amma yak'i ji hakan ne yasa ne yanke hukuncin da zai yi dai-dai kowa, dan haka
ina son sanar da ku ranar jumma'a za'a d'aura auren Aisha da Yaron nan Lukman in
yaso daga baya ta tari dan munyi magana da mahaifin shi d'azu, dan haka sai ku fara
shirye-shirye." Daga haka ya juya ya bar falon

P.35

Gaba d'aya suka daskare a wurin ba tare da sanin abun cewa ba har ya fita daga
falon. A hankali Aisha ta juya kan Ummi da ita ma ita take kallo. Za ta yi magana
kenan Ummi ta dagatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu. "Bana son Jin komai wannan
hukuncin mahaifin ki ne, bamu da ikon hanawa." Daga haka ita ma ta bar falon aka
bar Aisha kad'ai da tunanin abunda ya faru.

*******

"Shi ma wannan d'in ya gudu kenan?" Hajjiya ta tambaye Hamida. "A'a Hajjiya Nima
ban sani ba." "Kamar ya Baki sani ba ehh?" Na ce kamar ya Baki sani ba, wannan ma
sai da kika yi yanda kika yi ya gudu to ai shi kenan sai ki zauna muna jerawa dake
a gidan nan tunda kin k'i fitar da mijin aure." "Haba Hajjiya kamar ya na k'i fitar
da mijin aure?" Gaba d'aya bansan mai yasa ba duk wanda yazo wurina zance daga na
ce ya fito shi kenan ba zai sake zuwa ba ko na k'ira shi bazai d'aga ba to ni me
laifi na ne Naga auren nan lokaci ne, in lokaci yayi Nima zan zamu mijin auren nayi
auren nan na huta da gorin k'awaye har da na Y'an uwa kowa ya tashi yaushe zanyi
aure?" Ko kuma har yanzu dai na k'i aure sai kace ni na jawa Kai na. Nima fa bana
jin dad'in zaman gidan nan tunda duk k'awaye na sunyi aure wasu harda ma da yara
Amma ni har yanzu shuru, da wani ake so naji ne eh?" Na gaji gaji." Hamida ta fad'i
hakan ne ta na me rushewa da kuka. "To ni yanzu Me na ce miki da zaki wani zauna
min kina min kuka." Hajjiya da gaba d'aya jikin ta yayi sanyi ta fad'a.

Hamida ba tare da ko kallon inda Hajjiya ke ba ta tashi ta shiga d'akin ta tare da


banko k'ofar.

Hajjiya shuru tayi na d'an wani lokaci tana mai tunanin rayuwar y'arta, a kullum in
ta tashi ba ta da wata damuwa da ta wuce rashin auren Hamida da kuma matsalar
Aliyu.

Tun abun baya damun ta har ya fara fin k'arfin ta ace gaba d'aya duk samarin da
suke zuwa wurin ta da zaran anyi maganar auren sai ta gudu baza a sake ganin su ba,
gashi yarinya sai girma take duk sa'ayoyin ta sunyi aure harda yara ma amma ita har
yanzu shuru tun bata magana bata sa abun a ranta har ta fara saka wa Sana diyyar
maganganun mutane. Shi yasa ma kullun-kullun za Ka gan ta da waya a hannu ko fita
anguwa ma bata yi duk saboda maganganun mutane.

Turo k'ofar da aka yi ne yasa ta dawowa daga guntun tunanin ta Lula.

Ido ta zuba mishi tana ganin yanda ya zama kamar ba shi ba cikin k'ank'anin lokaci
kamar ba Aliyun ta ba, ya rame yayi bak'i ga sumar kanshi da tayi yawa Bai je ya
aske ta ba. Tana kallo har ya shiga falon tare da zama kan carpet kana ya soma
gaishe da ita. Bayan gaisuwar ne ta ke tambayar sa ya ta ganshi haka bashi da
lafiya ne. "Lafiya na k'alau Hajjiya, kawai damuwa ta Aisha Hajjiya, na rasa yanda
zanyi duk yanda zanyi naga na samu nayi mata magana ta taushe ta, yanzu fa har SIM
d'in ta cire dan ina k'ira baya shiga na rasa ya zanyi ta yafe min Wallahi Hajjiya
na gane kuskure na dan Allah ki yi mata magana nasan zata ji maganar ki Dan allah."
Shuru Hajjiya tayi, tana mai tunanin ya zata fad'a mishi abunda ke faruwa.

Taje gidansu Aisha jiya domin ba Aisha hak'uri da ta yafe Aliyun abunda yayi mata
tayi hak'uri ta koma gidan shi amma ta tarar da wani abu daban, Dan kuwa tarar tayi
a na shirye-shiryen biki. Haka dai ta zo gida jiki a sanyaye Dan aikin gama ya gama
yanzu dai Aisha ta mishi nesa sai dai yayi Hak'uri in da rabon zata koma gidan shi
to zata koma komin Daren d'adewa. Maganan shine ya katse mata tunani. "Hajjiya
akwai abincin ne, ina Jin yunwa." "Eh akwai bara azo a zuba maka, to amma mai yasa
kwana biyun baka cin abinci a gidan Ka sai nan d'in?" To ma wai tsaya ma ni wai wa
ce irin mata ce kake aure ne ma Aliyu?" Da saurin ya katse ta ta hanyar cewa. "Bata
nan ne Hajjiya sun tafi Kaduna." "Kamar ya sun tafi Kaduna?" Ita da wa suka tafi?"
K'awayen ta." Yayi mata k'arya. Shuru Hajjiya tayi sabon takaici ta ma kasa
magana, sai zubawa Aliyu ido da tayi tana mai k'ara Jin tausayen d'an nata. Hamida
ta kwallawa wa k'ira da ta zo ta zuba ma Yayan ta abinci. To!tace tare da nufan
kitchen dan Ka mishi abincin. Hajjiya sai da ta tabbatar Aliyu ya ci abincin ya
k'oshi tukunna ta fuskance shi tare da cewa. " Yauwa yanzu tunda Ka gama za mu iya
magana. Aliyu, Ina son Ka fuskance ne da kunnen basira, Ka sani duk abunda zai faru
da bawa walau alkhaire ne ko akasin haka kaddarar shi ne, ba wanda ya isa ya guje
ma kaddarar sa. Na sani, nasan auren Ka da Husna kaddarar Ka ce haka ma rabuwar Ka
da Aisha duk yana cikin kaddarar ka ne Aliyu. Jiya na je gidan su Aisha dan nema
maka sulhu Amma sai da.... Sai kuma tayi shuru. Aliyu da gaba jikin shi ya gama yin
sanyi da maganar Hajjiya ya ce. "Kar ki je komai Hajjiya ki fad'a min Dan Allah mai
ya faru." Ya fad'a.

"Uhmm Aliyu ba abunda zan iya fad'a maka sai kayi hak'uri dan kuwa Aisha baza ta
tab'a komawa gidan Ka ba in ba wani iko na ubangiji bane, dan mahaifin ta ya k'i
kuma ita Aishan da bakin ta ta fad'a min baza ta koma gidan ka ba Allah ya had'a
kowa da rabon sa, Dan haka kayi hak'uri ka d'au dangana kaje Kasa santa da matar ka
ku shawo kan matsalar ku, amma maganar Aisha ta wuce." Ta fad'a mishi abunda Aishar
da mahaifin ta suka fad'a mata amma sai dai ta b'oye mishi maganar auran ta ranar
jumma'a.

Shuru yayi kamar ruwa ya cinye shi, baya ma jin mai Hajjiya take fad'a ma, tunda
Aisha har ta iya fad'a ma Hajjiya baza ta koma gidan shi ba ya tabbatar ya gama
rasa Aisha a rayuwar shi. Nan da nan ya had'a zufa ta ko ina. Da kyar ya iya aro
jarimta ya dai-daita kansa tare da cewa Hajjiya. "In sha Allah Hajjiya na miki
alk'awari bazan sake zuwa gidansu ina damun ta da ta koma ba. Na bar komai wa Allah
shi yafi Sanin abunda ya dace da mu."

******

B'angaren su Aisha kuwa Sosai ake shirye-shiryen biki duk da Abbu ya ce ba yanzu
Aisha zata tare ba amma hakan bai hana Ummi k'iran mai gyaran jiki Dan gyara Aisha.
Haka ma Aisha tun tana baya-baya da abun har ta sake ana komai da ita, tsakanin ta
da Lukman ma za mu ce ma sha Allah, dan alhamdulilah gaba d'aya ta tattara lamarin
Aliyu ta zuba a kwandon Shara, dan soyayya suke bugawa da Lukam kamar ba gobe,
Lukman ya mantar da ita duk abunda ya faru da ita a baya, yanzu jin ta take kamar
buduwar da zata yi auren fari. Duk wani lokacin tuninan Aliyu da irin soyayyar da
ya nuna mata da kuma irin kulawar sa gare ta da kuma irin zaman da suka yi tun
auren su har izuwa yanzu, a kullum in tayi irin wannan wannan tunanin sai ta ga
kamar tana shirin tabka babban kuskure ne na auren Lukaman, Dan duk da tana son
Lukman yanzu Amma fa har yanzu da akwai son Aliyu a k'asan ranta, ko zata b'oye wa
kowa wannan ba zata yi wa kan ta k'arya ba. Duk da yayi mata ba dai-dai ba ya aure
k'anwar ta a bayan idonta, ya sake ta akan laifin da bata San komai a kai ba, Amma
kuma fa a wani wurin bashi da laifi. Tunda dai auren shi da Husna yana cikin
Kaddarar su ne kuma ba yanda suka iya, kuma koda ace Bai aure Husna ba tunda har
akwai rabo a tsakanin su tofa ko da a waje sai ta samu cikin nan tunda Haka Allah
ya kaddara. Sakin ma da yayi ita ta nema da Kanta in ba ita ta nema ba zai yi ba,
kuma koda ace ita ce wannan ya faru da ita to tabbas zata yi zargin da gangan aka
yi mata hakan, yanda take son haihuwar nan ace Allah ya bata amma kuma ya karb'i
abunsa tabbas baza taji dad'i ba balle ace zubar mata dashi aka yi ta tabbata sai
ta d'au mataki akan Wanda yayi hakan balle shi da yake namiji. Kuma duk abun nan da
yake faruwa duk ita taja musu, Dan da bata ɗauki Husna ta kawo ta gidan ta ba da
duk wannan bai faru ba, da duk wannan rashin fahimta Bai wanzu ba. Ta nace sai ta
dawo wurin ta amma yanzu dube sakamokon, tunda take da shi Bai tab'a bata mata rai
haka sai dai a rashin sani, a kullun burin shi Bai wuce su zauna lafiya cikin
farinciki da son juna. ko rashin haihuwa su bai tab'a ko da sau d'aya ne ya nuna
damuwar shi a gaban ta wanda tasan shi ya ma fi ta shiga damuwar, baya nuna wa ne
kawai amma ita tasani. Duk irin maganganun mutane da na Y'an uwan shi harda ma
mahaifiyar shi Kan ya k'ara aure matar shi bata haihuwa duk bai yarda ba, akwai
lokacin dama ya tab'a fad'a wa Hajjiya cewa shine baya haihuwa matsalar daga gare
shi ne Dan haka su dena ta Kura mishi da maganar aure, duk irin wannan kyautatawar
da yayi mata ba ta tuna ba dan kawai yanzu yayi mata kuskure kuskuren da ita tayi
silar sa ta d'au tsanar duniya ta d'aura mishi.

Ta d'au tsanar duniya ta d'aura mish sai kace shi kad'a ne da laifi, tabbas yana da
laifi amma kuma haka Allah ya kaddara mishi auren su su biyu, yau koda ace ita bata
kawo Husna gidan ta ba tunda da akwai rabo a tsakanin su to fa sai ya aure ta, in
ma Bai auren ta ta kuwa za su nema junan su ne a waje har a haife yaran nan,
sab'anin da suke samu kuma bai wuce irin makircin da Husna ke k'ulla mu su dan
kawai su rabu kuma gashi tayi nasaran raba su. Duk wannan tunanin bai zo mata ba
sai da Inna Hasiya da tazo biki ita ma ta sa ta a gaba tayi mata fad'a sosai da
kuma nasiha tukunna ta gane iron babban kuskuren da ta tabka Wanda kuma yanzu
lokaci ya k'ure tunda gobe ne d'auren auren ta da Lukman Wanda a yanzu bata san a
wani mataki zata aje shi ba, a da ta d'auka son shi take amma yanzu sai take ganin
son da take mishi bai kai son da take ma Aliyu ba, tsoran ta d'aya kar auren shi ya
kasance a kan kuma zuciyarta ta kasance da wanin sa.

Yau tunda ta tashi take son jin muryar shi koda sau d'aya ne, tana son bashi
hak'uri a bisa abunda ya faru a tsakanin su da kuma fad'a mishi d'auren auren ta
gobe, Dan haka SIM d'in ta sa a wayar Batool da ta zo bikin ita ma duk da ba son
auren take ba, ta zo ne kawai dan kar Aisha taji babu dad'i da ba dan haka ba ba
abunda zai kawo ta. Ita fa har yanzu haushin Aisha take ji da har ta zauna Yarinya
k'arama kamar Husna har ta iya cire ta daga gidan ta, Yarinyar ma da ita ta raina
da Kanta. Tunda tazo sai kushe Lukman take abu kad'an sai tace da da Aliyu ne da
yayi fiye da haka ma, Eeman ma ta d'ayan b'angaren ba a bar ta baya wurin kushe
Aliyun, da zarar Batool ta kushe Lukman ita ma Eeman zata fara kushe Aliyu.

Aisha tun tana ce musu su dena bata so har ta gaji ta zuba musu ido kawai.

Bayan ta sa SIM d'in sai tayi unblocking d'in sa tare da Kiran layin sa, har missed
call 5 tayi Mishi amma bai d'aga wayar ba. Rai babu dad'i ta sauke wayar, haka dai
ta wuni ranar rai ba dad'i, duk da ba wani abu zata fad'a mishi ba kawai tana son
bashi hak'uri da kuma son Jin muryar shi for the last time Dan ta San daga gobe shi
Kenan tsakanin ta da shi.

******

Mai kake nufi da zaka bar garin?" Habib abokin Aliyu ya tambaye shi.

"Eh Habib zan koma Abuja ne na d'an wani lokaci kafin zan dawo Dan Allah Karka
fad'a ma kowa ko Hajjiya ma Kar taji sai na tafi tukunna." "Amma Aliyu mai yasa
zaka koma can d'in bayan Kai Ka nemi a dawo da Kai nan d'in, ko dan saboda maganar
da na fad'a maka ne." " No ba Dan maganar aurenta da Ka fad'a min bane, dama nayi
niyyar barin garin. Nayi ma Hajjiya alk'awarin ba zan sake bibiyar ta ba, kuma in
har ina son cika wannan alk'awarin dole ne in bar garin nan Habib. Dole ne Bari na
wannan garin bazan iya zama a nan ba bayan dukkan abubuwan da suka faru, I need a
break from all this. Aisha kuma ina Mai taya ta farinci da auren da zata yi ina
kuma rok'on Allah da ya bata farin cikin da ni na kasa bata, dama haka rayuwa take
ba duk abunda kake so kake samu ba, and I have learnt my lesson." "Amma ya zaka yi
da ita Husnar ko tare zaku tafi?" "A'a ni kad'ai zan tafi yanzu, Nima zaman nawa a
can cikin biyu ne, dan sai na k'ara rubuta musu letter sunyi approving tukunna."
"Gaskiya abokina naji d'ad'in canjawar da kayi, na d'auka fa in kaji auren na ta
haukacewa zaki wallahi." Dariya kawai Aliyu yayi ba tare da ce mishi uffan ba dan
bazai gane ba, ko yanzu ma shi kad'ai yasan mai yake ji amma ya sa dangana da kuma
tawakali ya fawwala wa Allah lamarin sa.

Aliyu ko bayan ya bar gidan Habib gidan Hajjiya ya wuce a can yayi sallah magrib
har dare tukunna ya koma gida. Koda ya shiga gidan tarar yayi Husna tana had'a Kaya
a trolley. " Me wannan ina zaki kai su?" Ya tambaye ta. "Uhmm Kaya na ne, gobe zamu
tafi Kaduna bikin ai ko Ka manta ne." "Ohh! Kawai yace Dan gaba d'aya ya manta da
tafiyar ta bikin sabon abubuwa sun Mishi yawa. "Yaushe ne tafiyar taku?" Kuma da wa
zaki tafi ke da Baki San kowa a can ba." " D'an turo Baki gaba tayi kafin tace.
"Kai kafiya mantuwa yanzu haba, wai har Ka manta da Lubna zamu tafi ne, kuma ma ai
ni ba yawon zan tafi Kaduna ba aure zamu tafi kuma nasan mutane mana ita amarya ma
ai k'awar mu ce bansan taba zan siya ankon ta?" "Ok tsaya ina zuwa." Ya ce daga
haka ya shiga d'akin sa minti kad'an ya fito da kud'i a hannun shi tare da mik'a
mata su." Ga wannan ki rik'e a hannun ki, Nima ba gobe zan tafi Abuja so ban san
ranar dawo wa ba dan haka ki rik'e su tare da ke." "Abuja kuma?" Me zaka yi a Abuja
kuma?" " Ana buk'ta na ne." Kawai ya ce mata. "To ba damuwa ai ina godeya." Daga
haka ta cigaba da aikin gaban ta shima ya wuce da'kin sa.

WASHAGARI****

An ce Rana bata k'arya sai dai uwar y'a taji kunya, Yau jumma'a kuma a yau ne
d'auren auren Aisha da Lukam. Yau tunda ta tashi da safe zuciyarta sai bugawa take
kamar wani abu mara kyau zai faru da ita Wanda ta rasa mai yasa, koda ta fad'awa
Ummi ta ce mata tayi addu'a ba abunda zai faru kawai fargaba ne irin na ko wace
mace in za'a yi auren ta.

******

Tunda ya dawo daga masalaci Bai koma bacci ba ya shiga had'a kayan sa a trolley,
Koda ya gama toilet ya shiga yayi wanka nan da nan ya shirya. Bai tsaya b'ata
lokaci ba ya bar gidan dan yana son zuwa office dan had'a wasu takardun.

Bashi ya bar wurin aikin ba sai 12:00 ya gama tare da barin office din.

Bai b'ata lokaci ba ya shiga motarsa sai da yayi addu'ar matafiya kana ya fara
tuk'i. Yana cikin tuk'in ne yaji wayar shi na ringing, ba tare da duba suna ba ya
d'aga wayar ya d'aura a kunnen shi. "Hello! Hello!! Hellooo!!! Jin shuru ne ya sa
shi sauke wayar tare da duban sunan mai k'iran, ai yana ganin sunshine yayi saurin
maida wayar kunnen shi. "Nasan kina ji na then mai yasa ba zaki yi magana
ba?"bansan me ke cikin zuciyarki a ga me da ni ba Aisha, amma zan so ki saurari
abunda ke ta wa zuciyar ga me da ke.

Babu ranar da Rana zata fitar da hasken ta, face sai wannan hasken ya kunna fitar
sonki a zuciyata. Aisha ke acikin zuciyarlta haske ce, babu wani d'an Adam da zai
iya rayuwa a cikin duhu, kuma na gane hakan ne a lokacin da na bar hasken
soyayyar ki na shiga duhun kewar ki. Rashin ki da nayi na tswaon wannan lokacin ya
d'and'anawa zuciyata azabar da ko a mafarki bana fatan had'uwa da irin ita. A
yanzu na gani wata gaskiya guda, bazan iya rayuwa da hasken Aishata a tare da ni
ba, Aisha kiyi hak'uri bisa komai. A baya na barki, amma a yanzu ina son kasnce wa
dake na iya tswaon rayuwata, sai da kuma kashh na makara lokaci ya k'ure min Aisha.
Dan Allah ki yafe min duk wani laifi da na tab'a miki, Nima na yafe duk wani laifi
da kika min Aisha. Ina taya ki murnan samun miji mai sonki, duk da bansan shi ba na
tabbata yafi ni nagarta, ina taya shi murnar samun mace kamar ki Aisha, a b'angare
guda kuma ina bak'in cikin rasa ki na har abada. "Dan Allah ki dena kukan nan in ba
so kike nima nayi kukun ba." Ya fad'a da d'an dariya kamar shi d'in ma ba hawayen
yake ba. "Kayi hak'uri Nima Aliyu, Ka yafe min." Aisha ta fad'a cikin muryar kuka.
"Dan Allah ki dena kukan nan karya min zuciya kike Aisha, ina son ganin ki cikin
farinciki Aisha. A duk inda nake idan na tuna kina cikin farinciki da zaman lafiya
da mijin ki zan ji dad'in hakan, kinga ke zaki yi aure kuma zaki zama uwa nan gaba
zaki zama uwa Aisha, wannan ce kaddarar mu Allah bai yi zamu yi dogon zama tare ba
shi yasa ma babu rabo a tsakanin mu. To ni zan tafi Aisha sai wata rana in Allah ya
had'u mu, ki sani a addu'ar ki a duk lokacin da kika tuna Dani." Daga haka ya kashe
wayar Dan ba zai iya cigaba da sauraran kukan ta ba, tab'a shi yake sosai gaba
d'aya shima fuskar shi ta jik'e da hawaye. A hankali ya saka hannunshi cikin aljihu
ya cire hankey ya fara goge fuskar shi da ita.

Bai ankara ba yaji tiii ta bayan shi ko kafin ya san mai ke faruwa motar shi tayi
wilwilwil ta soma juyawa a kan kwalta nan da nan mutane suka taru ganin abunda ke
faru. Motar bata tsaya ba sai da ta ci karo da wata motar dake zuwa ta gaba ji
kake girimmm! suka had'e wurin d'aya.

Shuru wurin ya d'auka na wani lokaci kafin kuma kamar way'anda aka tsikara suka
fara ihu nan da nan mutane suka tunkari mottocin dan taimakon wayanda ke cikin
mottocin.

P.36

Tana sauke wayar ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita, gani take kamar ƙarshen
haɗuwar su kenan.
Batool ce ta shiga ɗakin domin neman wayarta ta ganta a cikin wannan halin, Da
sauri ta matsa kusa da ita tare da riƙe ta kana ta soma tambayar ta me ya
faru."Aisha dan Allah faɗa min me ya faru?" Anyi mutuwa ne?" Dan Allah faɗa min me
ya faru ne, ko in ƙira Ummi tunda ni baza ki faɗa min ba." Ta faɗa tare da ƙoƙarin
tashi wa dan a gaskiya ta tsorata da kukan nan ta gashi ta ƙi faɗa mata abunda ke
faruwa. Da sauri ta riƙe hannunta tare da kaɗa mata kai da kar ta je. "To ki faɗa
min me ya faru ne haka da yasa kike wannan uban kukan sai kace wacce aka aika mata
saƙon mutuwa?" Da kyar ta sau–sauta kukan ta tare da goge fuskar ta da hannayen ta
kana ta riƙe hannun Batool gam kana ta soma magana. "Ba abunda ya faru kawai ina
kuka ne dan zan bar gidan nan, zanyi missing ɗin su sosai." "Shuru Batool tayi tana
mai ƙara kare mata kallo.

"Hmm Aisha kenan bansan yaushe kika fara ɓoye min damuwar ki ba dan nasan abunda
yasa ki kuka, kina kuka ne dan zaki rabu da Aliyu ko ba haka ba?" Look Aisha ban
san me yasa kike haka ba amma na tabbata miki kina ƙoƙarin tabka babban kuskure na
amincewa da ɗauren auren nan, dan ba son Lukman kike ba kawai tausayen shi kike ji
amma baza ki gane hakan ba sai bayan kin shiga gidan sa tukunna. kina gidansa amma
zaki kina tunanin waninsa, Ban ce karki bi umarnin mahaifin ki ba Aisha, amma ina
son ki zauna ki yi tunani kafin lokaci ya ƙure miki yanzu ne kike da damar yanke
abunda yafi dacewa da ke. nan da awa ɗaya everything will be over, yanzu hukunci ya
rage na ki ko kiyi shuru a ɗaura miki aure da wanda bakya so, ko kuma ki zaɓe
farincin rayuwar ki.

Kuma ma ni bansan me yasa ba Eeman take ziga ki akan ki aure Lukman bayan tana
sonshi ita ma." Ta ƙare maganar a hankali ta yanda Aisha baza ta ji ba. "me kika
ce?" "No ban ce komai ba kawai ina faɗa miki abunda ke rai na ne. duk da bansan
abunda ke zuciyar ki ba Aisha, ina da tabbacin har yanzu da akwai soyayyar Aliyu a
ranka, Amma bazan taɓa zama silar ki bijire wa iyayen ki ba sai dai ina son ki sani
kar ki yi abunda daga baya za ki yi dana sanin sa kuma ki sani duk hukuncin da kika
yanke i will always be by your side." Ta ƙare maganar da bubbuga bayan ta.

"Uhm na gode Batool na san me yasa kike duk wannan abun, kina hakan ne dan farin
ciki na, kuma nayi ƙarya in na ce miki ban son Aliyu." A hankali ya soma ja da
baya–baya har sai da ya bar bakin window, dama an ƙira shi a waya ne kuma yana
cikin mutane dan haka ne ya bar gurin tare da zuwa bayan gida dan ƙarasa wayarsa
wanda kuma ya kasance windown ɗakin Aisha na daga wannan ɓangaren. Yaji duk hirar
ta da Aliyu har ma da ta Batool Ba tare da yaji ƙarshen maganar ta ba ya bar wurin
jiki a sanyaye ba tare da ma yin wayar da yake son yi ba.

"Amma yanzu bana yi, yanzu ba wanda nake so sai Lukman kuma shi zan aura, saboda
shi yafi dacewa dani kuma zaɓin mahaifi na ne. Dan haka ki dena min maganar Aliyu,
saboda nan da wasu awanni zan zama matar wani so please bana so yanzu in wani jiki
me za'a ce?" Please karki sake ka min maganar shi, nan da awa ɗaya zan zama matar
wani dan haka bana so." "Ok kiyi haƙuri in na ɓata miki rai da maganar da nayi
miki, hakan ba zai sake faruwa ba."daga haka ta ɗauki wayarta ta bar ɗakin.

******

Zaune suke kan kujerun gardin ɗinsu da ya ƙawatu da bushuyo da furanni kala–kala,
gaban su kuma drinks ne da snacks. Hamida ce ta dubi Balkisu da gaba ɗaya ta canja
kamar ba ita ba, ta rame tayi baƙi kamar ba Balkisu ƴar ƙwalisa da jijji da kai ɗin
nan.

"Kai gaskiya aunty Balki kin gan ki kuwa, gaba ɗaya kin canja kin rame kin yi baƙi
kamar ba ke ba. Wai me ya ke damun ki ne haka?" Ke kin ga yanda kika koma kuwa?"
Allah wani in ya gan ki sai ya zata ke ƴar aikin gidan nan ce ba ƴar gidan ba." Ta
ƙare maganar da ƴar dariya. Ganin hararar da take zabga mata ne yasa ta dena
dariyar tare da cewa. "Kiyi haƙuri, amma kuma gaskiya fa na faɗa wallahi ba wanda
zai ce wannan aunty billy ba ce gaba ɗaya kin wani ƙanjame. "Hmm Hamida ba zaki
gane irin rayuwar da nake ciki ba, duk yanda zan kwatanta miki ita ba zaki gane ba
ni kaɗai nasan me na ke gani a gidan can." "To wai me ya faru ne eh?" "Hamida kin
san Allah, tunda aka yi auren nan har zuwa yau ban taɓa jin daɗin zaman gidan na
rana ɗaya ba. Sun sani a gaba gaba ɗaya bani da ta cewa Hamida, haka nan yaran nan
zasu min abu in nayi magana su min rashin kunya in nayi magana kuma iyayensu su
tashi akai na kai wani lokacin ma haka nan zasu taru a kaina su min duka, in kuma
ya dawo tun kafin na kai ƙarar su zasu ƙulla masa ƙarya da gaskiya akai na. Haka
nan zasu sa yaransu su zo ɓangarena su min ɓarna in kuma na hana su shiga sai a
haɗa min wani ƙullin shi kuma ya hau ya zauna. Abun fa bai tsaya a nan ba, duk
ranar girki na sai ki ga matsala ta tashi, daga Yaro babu Lafiya sai mai tada
Aljanun ƙarya. Bani da wani ƴanci a gidan nan aiki na ke dare da rana Hamida kullum
ni ana cikin ƙulla min sharri, ba ma kwana biyu ba muyi faɗa da shi ba, to ya za'a
ba zaki ganni haka ba." "Hmmm gaskiya abu bai yi daɗi ba, amma kuma sai dai kiyi
haƙuri wata rana sai labari." Zata yi magana kenan suka ji muryar Hajjiya na kwalla
wa Hamida ƙira, dan haka basu ɓata lokaci ba suka tattara kayan su tare da shiga
main house.

"Na'am Hajjiya ga ni lafiya?" "Eh hajjiya lafiya?" Cewar Balkisu. "Ali ya zo ne


bayan na shiga bacci?" "A'a Hajjiya Yaya bai shigo ba yau, amma lafiya dai?" "Ban
sani ba Hamida nayi wani mummunar mafarki ne da shi wanda shi ya tayar min da
Hankali. Zo..zo..zo ki ƙira min shi naji lafiyansa." "Dan Allah Hajjiya ki kwantar
da hankalin ki in sha Allah ba abunda ya sami Yaya mafarki ne kawai ba abunda zai
faru sharrin shaiɗan ne kawai ai mafarki baya zama gaskiya." Cewar Balkisu. "Eh
Hajjiya dan Allah ki kwantar da Hankalin ki mafarki ne ba gaskiya ba." "Zaki ƙira
min shine ko kuma nayi da kaina?" "Hajjiya da gaba ɗaya hankalin ta ba a kwanciye
ba tayi maganar. "Kiyi haƙuri zan ƙira shi." Daga haka ta ɗauki wayarta tare da
dialing numbernsa sai da kuma har ƙira uku tayi mishi amma zancen ɗaya wayar a
kashe. A hankali ta sauki wayar tare da duban Hajjiya da itama ita take kallo.
"Baya shiga ina ga wayar bata da charge ne ko kuma yana meeting ne shi yasa ya
kashe wayarsa." "Eh zai iya yuwa hakan ne Hajjiya dan Allah ki kwantar da Hankalin
ki komai lafiya ba abunda ya samu ɗan lelen ki." Cewar balkisu.

"Yawwa Aunty faɗa mata dai ɗan lelen ta yana nan lafiya yanzu zaki ga yazo ma ina
ga yau akwai aiki dayawa ne a office shi yasa." Da haka suka kwantar ma Hajjiya
hankali kan mafarki ne ba gaskiya dan haka ta dena tashin hankalinta. Suna haka
wayar Hamida ta fara ringing, koda ta duba sai ta ga Yaya Habib. "Waye?" Ki ɗaga
mana." "Yaya Habib ne." "Habib?" Ki ɗaga mana to ki ji." Hajjiya da har yanzu bata
dawo dai–dai ba ta faɗa. "Ok! Tace daga haka ta ɗaura wayar a kunnenta da sallama a
bakinta, da sauri ta miƙe tsaye tare da anbatan. "Innalilahi wainna illahi raji'un,
wani asibiti?" To gamu nan zuwa." Daga haka ta sauke wayar tare da fuskantar su
Balkisu da gaba ɗaya sun shiga ruɗe, tun ba Hajjiya ba da dama jikin ta na bata
babu lafiya. "Yaya ne wai yayi hatsarin mota yanzu haka antafi da shi asibiti." Da
sauri Balkisu ta tari Hajjiya da tayi taga–taga zata faɗi. "Please Hajjiya ki riƙe
kanki dan Allah." Cewar Balkisu da itama hankalin nata atashe yake.

********

Tunda taji an ɗaura aure ta ɓoye kanta a ɗakin Abbu ta in banda kuka ba abunda
take. ba yanda Eeman da Batool ba suyi da ita da ta ci abinci amma ta ƙi, ganin
zasu dame ta ne yasa ta bar musu ɗakin ta koma ɗakin Abbu. A can ta wuni koda Ango
da abokanan sa sun shiga dan yin hotona da ita ma taƙi fita, Eeman tayi neman
duniya nan bata ganta ba ƙarshe dai dole tayi ƙaryan cewa bata jin daɗi ne kanta na
mata ciwo, haka nan dai aka yi hotunan babu ita.

tayi kuka ta gaji bacci ɓarawo ya ɗauke ta, ba ita ta tashi ba sai can yamma ta
tashi shima yunwa ce ta tashi ta dan ba abunda ta ci tunda safe, dalilin damuwar da
ta sa a ran ta. Ganin har yamma tayi ne yasa ta saurin tashi wa tare da ɗaukan
mayafinta kana ta bar ɗakin.
Zata shiga ɗakin ta kenan taji muryar Ummi da Abbu suna magana kuma da gani magana
me mahimmanci ce suke yi, haka kawai taji urged ɗin jin me suka cewa dan haka
hankali ta ta matsa kusa da ƙofar ɗakin Ummi tare da kasa kunne dan jin me suke
cewa.

"Ya mutu ne Alhaji?" "A'a bai mutu ba amma yaji ciwo sosai dan ya faɗa coma ba'a
san ranar tashi war sa." "Coma fa ka ce?" "Eh abunda likitoci suka ce." "Allah
sarki Aliyu Allah ya baka lafiya, kamar yanzu nake ganin zuwan shi na ƙarshe da
yayi gidan nan kasa a ka kore shi. Waya sani ma ko maganar auren nan ce ta tayar
mishi da hankali har yayi wannan hatsarin, yanzu me zamu faɗa ma ita Aisha?"

Da sauri ta sa hannun ta a bakinta tare da barin wurin, in banda hawaye da sunan


Aliyu ta ke anbatawa ba abunda take. Tana shiga ɗaki ta ɗauke wayarta tare da gwada
numbern Aliyu dan tabbatar wa kanta ƙila bata ji dai–dai ba ne amma ƙiran duniya
numbern a kashe yake.

Ganin layin sa baya shiga ne yasa ta tunanin ko ta ƙira gidansu, tunanin hakan ne
yasa ta dialing ɗin layin Hamida, bugu biyu ta ɗaga. "Hello Hamida Aisha ce, dan
Allah ki faɗa min gaskiyan abunda ke faru da gaskiya ne Aliyu yayi hatsari?" "Eh da
gaskiye ne abunda kika ji haka ne Yaya yayi Hatsarin mota kuma sun ce bazai tashi
ba." Ta ƙare maganar cikin kuka. Kiyi shiru waya ce miki ba zai tashi ba zai tashi
in sha Allah kin ji, ina Hajjiya yanzu?" "Tana bacci yanzu, anyi mata allurar bacci
ne dan ta tashi hankalin sosai wanda hakan ya tayar mata da hawan jininta." "Ok!
Yanzu kin san me zaki min kiyi shiru ki dena kukan nan naki please dan ba abunda
zai canja, ki tura min adress ɗin asibitin da kuke yanzu ina zuwa." "What! Za..zaki
zo fa kika ce?" "Eh tura min yanzu please banda ɓata lokaci." Daga haka ta kashe
wayar tare da buɗe walldrop ta ɗauki hijab da facemasks kana ta bar gidan da sanɗa
babu wanda ya ga fitar ta.

P.37

Tana fita ta samu me napep ta tsayar tare da faɗa mishi sunan asibitin kana ta
shiga ya ja suka tafi.

Suna isa asibitin ta sauka tare da ba me napep kud'insa kana ta shiga asibitin,
tana shiga direct reception ta wuce.

"Excuse me ma, dan Allah ward d'in Ali Matawale nake nema." Ta tambaye yarinya da
ke wurin. "Ok! Ina zuwa." Daga haka ta dad-dana abubuwa a laptop kana ta dubi Aisha
tare da cewa. "Yana ward 24 ki bi wannan hanyar zaki samu ward d'in." "Ok na gode."
Tace tare da barin wurin, bata wani sha wahala ba ta samu ward d'in sakamokon ganin
Habib da da su Hamida a bakin ward d'in, Dan haka ta k'ara saurin tafiyar ta.

Balkisu ce da ta gaji da zaman wuri d'aya ta tashi da nufin zata d'an mik'e k'afa
ne ta hango Aisha daga nesa. "Kai wannan ba Aisha ba ce, me ya kawo ta nan kuma?"
Ta tambaya. Da sauri Habib da Hamida suka juya inda suka ga Balkisu na nunawa da
yatsa, dai-dai lokacin da Aisha ta iso wurin.

Koda ta iso wurin bata tsaya wani gaisuwa ba ta soma tambayar Hamida ya jikin na
shi me kuma likitoci suka fad'a. Gaba d'aya ta manta da akwai wasu mutune a wurin,
kawai burin ta ta San a wani Hali yake.

"Yanzu Alhamdulilah sun ce ya fita daga danger amma kuma ya shiga coma Wanda ba'a
San ranar tashi war sa ba." "Ki dena fad'an haka in sha Allah zai samu lafiya da
yardan allah, yana buk'atar addu'ar mu. Amma zan iya shiga ciki in duba shi?" "A'a
sun hana, sun hana kowa shiga ciki sai dai ki ganshi ta waje amma ba sa Bari a
shiga." Kai kawai Aisha ta kad'a mata kana ta matsa kusa da k'ofar ward d'in.

Yana nan kwanciye baya ko motse, an nannad'a mishi bandage akan shi da kuma k'afar
shi ta dama, ga kuma oxygen da aka manna mishi a hanci domin nunfashi, sai kuma
wasu wayoyi da aka manna mishi a kai. Gaba d'aya ya rame yayi bak'i kamar ba Aliyun
ta da ta sani ba, cikin wannan k'ank'anin lokaci nan ya canja kamar bashi ba. Nan
da nan taji hawaye sun suma zubo Mata, ji take kamar ta shiga ta rungume shi ko
zata ji sas-saucin abunda take ji a ranta amma ta San haka ba me yuwa bane tunda ba
kamar da bane da zata iya tab'a shi a ko wani lokacin ba, yanzu komai ya canja.

Habib ne da yaga kamar bata san da wanzuwar su a wurin ne ya kasa hak'uri yayi
magana. "Aisha me kike yi a nan?" Da sauri ta juya tare da goge hawayen da ke
fuskar ta kana ta ce. "Amm.. sorry bansan kana wurin ba." Ta fad'a tare da guje ma
tambayar da yayi mata. "Eh Baki lura da mu ba, to amma ya na ganki a nan?" Kuma ya
aka yi na ganki ke kad'ai?" Wai tsaya ma anya ma an san da zuwan ki nan d'in kuwa
Aisha?" "Amm...umm... Dama.. dama zamu zo tare da...

"Excuse me patient d'in ward 19 ta Farka dan haka zaku iya ganin ta yanzu." Wata
nurse ta katse su. "Ok mun gode suka fad'a a tare kana suka dug'ufa ward d'in. A
hankali ta sauki ajiyar zuciya da yi ma wannan nurse godiya a zuciya na ceton ta da
tayi kana ita ma ta mara musu ba.

**********

Can gida kuwa, bayan sun tau-tauana da Ummi Abbu ya umarce Ummi da ta k'ira Mishi
Aisha da Eeman akwai maganar da yake son yi da su, dan haka su same shi a falon
shi. Babu mutse Ummi ta tashi tare da nufan d'akin Aisha domin isar da sak'on da
Abbu ya bata. Koda ta shiga bata ga Aisha ba sai Eeman da batool a d'akin. "Eeman
ina Aisha?" Kuje Baban ku yana son yin magana da Ku." "To! Amma fa Ummi bansan inda
Aisha ta shiga ba, Dan tun d'azu mu ke ta neman ta ba mu gan ta ba." "Kamar ya Baku
gan ta ba,?" "Eh Ummi bata nan ko nima d'azu na neme ta ban gan ta ba?" "Tofa! Amma
bara na duba b'angaren Baban Ku na gani ko tana can." Daga haka ta wuce part d'in
Abbu amma wayam babu Aisha, ta duba ko ina amma bata ga Aisha ba. Abu kamar wasa
aka nemi Aisha a gida a Ka rasa tun abun Bai damun su har hankalin su ya fara
tashi. Kowa in an tambayi shi sai ya ce Bai gan ta ba, me gadi ma ya ce bai ga ta
fita ba.

**********

Aisha ce zaune Kan gadon asibiti ta na me ba Hajjiya abinci, dan tunda ta tashi ta
k'i cin komai sai damuwar da tasa wa kanta. Ba yanda su Balkisu Ba su yi da ita ba
Kan koda tea ne tasha amma ta k'i sai da Aisha ta sa baki da kuma kwantar Mata
hankali tukunna ta ke d'an tab'a wa.

A hankali ta ke ba Hajjiya abincin a baki, bayan ta gama bata abincin ne ta bud'e


magun-gunan tare da bata ta sha. Daga nan kuma suka taru suna mai bata baki da ta
dena tayar da hankalin ta kuma duk abunda kwanciyar hankali Bai Bai yi ba to tashin
hankali ba zai tab'a yi ba sai dai ma ya b'ata.

Nan ta zauna da su a asibitin har bata san lokaci ya k'ure ba, sai da Habib ya dawo
daga sallahn Isha tukunna ya ke tambayar ta ba zata koma gida bane lokaci fa ya
wuce tukunna ta ankara da haka. Da sauri ta tashi tare da yi ma su Hajjiya sallama
da zata k'ara zuwa duba jikin ta tukunna ta fita daga ward din, har ta fita daga
asibitin zata tsayar da me napep Kenan sai gashi ya tsaya da motar shi a gaban ta.
"ki shiga zan sauke ki lokacin ya wuce yanzu akwai hatsari shiga napep ke kad'ai."
"A'a ka bar shi babu komai zan iya tafiya ni kad'ai ma ai." "Is my duty to take you
home safe and sound, dan haka Kar mu b'ata lokaci ki shiga mu tafi." Ya fad'a da
muryar umarni. Ganin dare ne kuma a gaskiya tsoran shiga napep d'in nan take kuma
da gani zata yi wahalar samu napep d'in ne yasa ta bud'e gaban motar da nufin
shiga, amma sai ya dakatar da ita ta hanyar cewa. "Ki koma baya." "Har za ta yi
magana sai kuma ta yi shuru tare da komawa bayan.
Tun a hanya ta soma tunanin irin abunda za ta tarar a gida, sai a yanzu ne ma ta
fahimce abunda ta aikata, yanzu in an tambaye ta ina ta tafi me zata ce. Ba ita ta
shiga tashin hankali ba sai da suka karya kwanar gidansu tun daga nesa ta ga Abbu
da Lukaman tsaye a bakin k'ofa kuma da gani suna cikin damuwa. Nan da nan taji
hantar cikin ta ta kad'a nan da nan gumi ya karyo Mata ta ko ina in banda rawa ba
abunda jikin ta ke yi.

"In kin shiga ki ma Batool magana ina jiran ta." Habib ya fad'a mata bayan yayi
parking sun fita.

Tunda motar tayi parking a bakin k'ofar suka zuba Mata ido kowa da abunda ya ke
tunani, Abbu yana ganin ta fito daga motar ya gane daga ina take. Dan haka suna isa
wurin su bai tsaya jin daga ina take ba ya ce da ita.

"Wuce ciki." Jiki a sanyaye ta rab'a daga gefe ta shiga ciki zuciyarta sai faman
lugude take dan ta san tabbas yau ta b'ata ma Abbu Rai kuma da gani ya san daga ina
take.

Tana ganin idon Lukaman akan ta har ta shiga amma yanzu ita ba shine a gaban ta ba.

****CIKIN GIDA****

"Ba magana na ke miki ba?" Daga ina kike?" "Mu bi komai a sannu dan Allah Amina ki
dena mata tsawa haka ba shi zai sa ta fad'a miki gaskiyar ina ta je ba." Inna
Hasiya ta fad'a. "Mu bi komai a sannu fa kika ce Yaya?" Baki ga yanda Baban ta ya
ke ta min fad'a ba akan wai duk laifi na ne bana sa Mata ido, da ina sa Mata da
baza ta fita ba tare da fad'a min ba ai wai ma da baki na fita ai." "Kiyi hak'uri
yanzu ba lokacin fad'a bane tunda ba mu san me ya fitar da ita ba." Daga haka ta
juya ga Aisha. "Ke Aisha ina kika fita?" Kuma a ranar d'auren auren ki, me kike son
mutune suyi tunani a kan mu musaman ma Lukaman da danginsa gaba d'aya kin sa mu
cikin tashin hankali." "A hankali cikin muryar tsoro da kuma fargaban abunda ka iya
faruwa tace. "Kuyi hak'uri na je asibiti ne." "Asibiti?" Dama Baki da lafiya ne ba
mu sani ba?" "A'a Inna, Aliyu ne yayi hatsari mota to, to...to..to shine na je duba
shi." Shuru dukan nin su su Ka yi daga Ummi da Inna Hasiya har su Batool d'in ma
sun kasa magana sai ido da suka zuba Mata. "Aisha! Ummi ta fad'a da d'an k'arfi.
"Ashe dama baki da hankali bansani ba?" Nace ashe dama baki da hankali bansani
ba?"da izinin uban wa kika je duba shi kuma ma waya fad'a miki yayi hatsari, da
auren ki?" Da auren kika je wurin wani?" Kin d'auka yanzu da ne da zaki iya yin
komai ba tare da komai ba?" To bara Ki ji yanzun ba da bane dan kuwa auren wani ne
a kanki."

"A gaskiya Aisha baki kyauta ba, yaya zaki bar gida ba tare da kin sanar da kowa ba
kuma a ranar d'auren auren ki, me kike son mutune suyi tunani akan mu. Musaman ma
Lukaman da danginsa in sunji kin je wurin tsohon mijinki ne. Gaba d'aya kin samu a
cikin damuwar rashin ganin ki, karki sake yin haka in zaki fita wani wuri ki
tabbatar kin sanar da iyayen ki tukunna, kinji?"

"Eh naji kuyi hak'uri hakan bazai sake faruwa ba." "Yayi kyau haka Aiken so in
mutum yayi laifi ya ba da hak'uri kuma Kar ya kuma aikata wannan kuskuren. Daga
haka ta juya ga Eeman tare da yi mata sigina da ido, da ta rik'e ta su wuce d'aki.

Suna shiga d'aki direct wurin cupboard ta nufa tare da d'aukan kayan bacci kana ta
shiga toilet ba tare da ta ma tsaya sauraran k'orafen su da kuma tambayoyen su.

Jim kad'an ta fito daga toilet d'in da towel a hannunta ta na me goge fuskar ta da
shi, a hankali ta taka zuwa gaban mirror tare da kallon Kanta ta mudubin. Tunanin
take, tunanin da ko ita bata san na me ba, Kawai dai tasan she's not happy with all
that is happening, komai ya ishe ta. Yanzu tunanin ta yanda gobe zata je asibitin
ne Dan ta tabbata ba wanda zai barta ta tafi wannan ba ba da sanin su ne da ba za
su amince ba, ba damuwa ki bata tafi gobe ba zata nemi abunda zata fad'a musu su
barta tafita.

Ringing d'in wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar Tunani da ta lula, d'an
k'aramin tsaki ta ja ganin me k'iran. Lukman ne, ganin zai dame ta da k'iran ita
kuma bata shirya d'aga k'iran sa ba dan bata san me zata ce masa bayan dukan
abubuwan da suka faru yau d'in nan tana buk'atan space hakan ne yasa ta kashe wayar
baki d'aya.

"Aisha baki fad'a mana waya fad'a miki Aliyu yayi hatsari ba kuma ya jikin na shi
yanzu, fatan bai ji ciwo sosai ba?" Eeman da ke kwanciye Kan gadon tayi maganar.
"Ba sai kinsan wanda ya fad'a min ba, kuma jikin shi babu sauki tunda har yanzu bai
tashi ba kuma ba'a San ranar tashi war sa sai dai muyi addu'ar Allah ya tashi
kafud'un sa." Inna lilahi abun har ya Kai haka, Kai dole muje asibitin mu duba shi
mu ma. Amma me yasa baki sanar da kowa kafin ki fita, ai koda baki fad'a ma su Ummi
sai ki fad'a mana ko kinsa hankalin kowa tashi."

"Dan Allah ya ishe ne haka haba, ban sanar d'in ba, taya ma abun zai zo Kai na nima
ina ji hankali na ya tashi shi yasa na tafi ba tare da na shirya ba. Taya ma wannan
zai zo Kai na, baki sanar baki sanar dan Allah ku barni na ji da abunda ya dame ni
haba. ni na ce ku tayar da hankalin ku akai na?" ai ni ba yarinya ba ce da za'a
sace ni ko kuma na b'ata da zaku wani shiga tashin hankalin kuma ma yau ne na fara
fita da za'a wani dame ni. Na fita ban fad'a muku ba na dawo na bada hak'uri ba
shi kenan ba, me kuma na wani mai-maita min magana." Daga haka ta tashi tare da
nufan wardrobe, bargo ta d'auka tare da shinfid'a a k'asa kana ta d'auki pillow ta
kwanta. "Allah ya baki hak'uri ban fad'i hakan da nufin b'ata miki rai ba, kawai
dai Naga Bai dace bane." "Wannan kuma ke kika Dani madam Bai dace ba." Ta fad'a
tare murgud'a Mata baki.

Batool da tunda suke maganar su bata sa musu baki ba Sana diyyar chatting da take
da Habib mijin ta ne tace. Ashe Habib ya ce ki k'ira ni in kin shiga." "Eh! "Shine
Baki fad'a min ba yayi jira har ya gaji."

"Na manta ne, kuma ma wa ya hana shi shiga ciki in in dai da gaskiyen ne yake son
ganinki ai zai shiga Bai wai zai yi aike bane. Kuma da ban fad'a miki ba ai gashi
yanzu kin sani." "To almasifatu bai shigo ba kuma ba ki fad'a ba shi kenan?" "Da
saura ba shi kenan ba." "Tofah! Yau kuma a k'asa zaki kwana Kenan?" "Eh! Daga haka
ta juya musu baya. "Sai da safe kar ku dame ni, in kun gama ku kashe mana wutar
d'aki." "To almasifatu."

P.38

Washe gari tunda ta tashi bata koma bacci ba ta shiga kitchen domin had'a mu su
breakfast, tana cikin aiki ne Ummi ta shigo kitchen da nufin d'aura breakfast dan
yau ta makara dan haka ne ma koda ta tashi bata tsaya wanka ko wani abu ba ta nufi
kitchen d'in dan lokacin har k'arfe 7:30 ma tayi kuma Abbu zai fita aiki k'arfe 8
kuma gashi suna da baki' a gidan duk da su Inna Hasiya na gida ne amma still bak'i
ne. Koda ta fita ta ga ko ina tsab-tsab an gyara ko ina sai k'amshin turaren wuta
da ke tashi, nan ta gane aikin Aisha ne. Koda ta shiga kitchen Aisha ta gama da
breakfast wanke-wanke ta ke, nan Ummi ta sauke ajiyar zuciya dan a gaskiya bata san
me zata hada ma Abbu cikin wannan k'ank'anin lokaci dan tasan ba zai jera ba sai
dai ya fita da yunwa gashi shi baya cin soyayyen kwai balle a had'a mishi.

Duk da ta ji dad'in hakan bata nuna a fuska ba. "Ummi ina kwana." Shuru tayi kamar
bata ji ta ba sai ma bubbud'e kwanikan abincin da take, tunanin bata ji ta bane
yasa ta k'ara cewa. "Ummi ina kwana." "Uhmm, lafiya." Shuru Aisha tayi ba tare da
sanin abun fad'a ba dan ta tabbata Ummi fushi take da ita akan abunda tayi. "Ummi
dan Allah kiyi hak'uri nasan na aikata kuskure dan Allah ki yafe min ba zan sake
ba." "Ni me kika min da kike ba ni hak'uri Aisha?" ba abunda kika min ai dan haka
me zai sa na yi fushi da ke?" Rashin hankali ne kin yi to ya za'a yi sai ki kiyaye
gaba." Daga haka ta had'a ma Abbu breakfast d'in shi a tire kana ta bar kitchen
d'in. Shuru Aisha tayi tsaya wuri d'aya ba tare da sanin abun cewa ba, ganin tana
b'ata wa kanta lokacin ne yasa ta cigaba da wanke-wanken.

Koda ta gama direct d'aki ta koma ta yi wanka, sharp-sharp ta sa Kaya tare da nufan
part d'in Abbu domin gaishe da shi. Amma can k'asa in banda bugu ba abunda
zuciyarta ke, ta d'auka ma a jiyan zai mata fad'a amma koda ya dawo bai sa a k'ira
ta ba wanda shi ya k'ara saka ta fargaba.

Amma ga mamakin ta Bai kawo maganar ba balle yayi mata fad'a a kai, bai nuna mata
komai ba kamar ba abunda ya faru, Wanda ba k'aramin mamaki hakan ya bata ba dan ta
san waye Abbu. Ganin bai kawo maganar kuma bai nuna mata komai ba ne yasa ita ma
bata kawo zancen ba, dan haka bayan ta gaida shi sun d'an tab'a hira kad'an kafin
ya tashi zai fita.

Ganin hakane yasa ta tattara kwanikan da ya gama cin abinci a cikin su tare da
barin part d'in domin ba su privacy.

*******HOSPITAL******

Habib ne zaune cikin d'aya daga cikin kujerun asibitin da aka tana da ma majinyata,
can gefin shi kuma Hajjiya ce da ita ma alhamdulilah yanzu jiki da sauk'i sai
abunda ba za'a rasa ba, sai kuma y'an matan ta da kuma Zarah da ita ma tun washe
garin ranar da abun ya faru ta zo daga Katsina. Tsaki Habib ya ja ganin Wanda yake
ta k'ira ya k'i d'aukan wayar wanda ba kowa bane fa ce Husna da tun ranar da abun
nan ya faru a ke ta neman layin ta domin sanar da ita amma baya shiga yanzu kuma
yana shiga amma ba'a d'aga ba.

Tsaki ya kuma tare da mai da wayar shi cikin aljihu, dama tun ranar da wannan abun
ya faru a ke son sanar da ita amma duk cikin su ba wanda ya ke da numbern ta ko na
maman ta balle su san gidan su har a je a fad'a ma su ko dan su su fad'a tunda ba
su gidan su ba.

Tunanin Aisha ba za ta rasa numbern ta ne yasa su neman numbern wurin ta amma ita
ma Aisha bata da shi dan ranar da ta bar gidan ta yi blocking d'in numbern da kuma
goge shi daga wayarta. suna cikin haka ne sai ga wayar Aliyun da kuma agogon shi da
da Y'an sandan da suka kawo shi asibitin dan bayan ceton rayukan su da mutunen
wurin sun yi sai da suka k'ira y'an sanda domin yin bincike akan su domin sanin
daga ina suke da kuma sadasu da y'an uwan su. Bayan Kai su asibitin ne y'an sandan
suka fara aikin su na bincike, Wanda cikin takardun driving license d'in shi suka
samu numbern shi da kuma addressed d'in shi har suka zo gidan.

"Baba ko zaka iya mana sallama da ma su gidan." D'aya daga cikin y'an sanda ya
fad'a." "Ai yallabe babu kowa a gidan dan me gidan yayi tafiya matar gidan ma bata
nan." Baba me gadi ya fad'a. "To babu kowa ne da zamu iya magana da shi?" "A'a
babu, amma akwai gidan maman shi babu nesa daga nan." "Eh hakan ma yayi, sai kaba
mu address d'in gidan." "To! Amma lafiya kuke son magana da wanin shi?" Kayi
hak'uri karka ce na muku kasalanda a aikin ku amma inda matsala kam gwara a baku
numbern Alhaji d'in ina ga zai fi akan a fad'a ma maman shi ka ga matane suna da
rauni ba komai za su iya d'auka ba, amma kuyi hak'uri in nayi laifi." "A'a Baba
kayi gaskiya, gaskiya maganar babba ce domin mai gidan nan ne ya gamu da hatsari a
hanyar fita daga gari wanda a yanzu haka yana asibiti rai na hannun Allah, to bayan
bincike da mu kayi ne mu ka samu addressing gidan to shi yasa muka zo nan domin
sanar da iyalan sa." "Inna lillahi wa inna illahi Raju'un, Alhajin ne yayi
hatsari?" "Eh kuma yana asibiti a yanzu haka dan haka dole ne mu sanar da y'an uwan
sa, in ba damuwa zaki iya Kai mu gidan mahaifiyar ta shi ko kuma Ka ba mu address
d'in gidan?" "Gaskiya ya ne dole su sani amma akwai d'an uwan shi ina ga shi ya
kamata a sanar mishi tukun tunda shi na miji ne." "Eh hakan ma yayi akwai numbern
shi a wurin Ka?" "Eh to babu a wurina amma Hamza driver ba zai Rasa ba." Daga haka
ya shiga cikin gida jim kad'an sai gashi da Hamza driver, bayan sun gaisa ne suka
mishi bayanin komai tare da tambayar shi ko yana da numbern Habib. "Eh yallabai ina
da ita."

Daga nan ya ba su numbern, bayan amsan numbern y'an sandan suka musu sallama.

Bayan koma war su suka k'ira habib tare da fad'a mishi dukan abunda ya faru tare da
fad'a mishi komai har asibitin da a ka kai Aliyun duk sun fad'a mishi dan haka ya
zo asibitin suma suna wajen.

Habib koda ya zo ya ga irin halin da Aliyun ke ciki sosai hankalin shi ya tashi
musamman ma da likitocin suka fad'a mishi ba lallai bane ya rayu ba hakan ne yasa
shi neman transfer zuwa babban asibiti.

To bayan komai ya kammala an maida Aliyu wani asibitin ne tukun Habib ya samu
lokaci ya k'ira Hamida ya sanar da ita tare da tura musu addressed d'in asibitin
duk da ya so zuwa da kanshi domin sanar da Hajjiya, amma ba zai iya barin asibitin
a wannan lokacin ba duba da irin halin da Aliyu ya ke ciki dan har zuwa lokacin
likitoci suna kan shi, dan tunda a ka shiga da shi theater room awa uku kenan amma
har yanzu likitoci ba su fita ba.

A lokacin da su Hajjiya suka iso an fito dashi daga theater room d'in amma an hana
kowa zuwa in da ya ke sai dai daga nesa, a nan ne aka sanar da su condition d'in da
yake.

Anyi aiki kuma is successful amma yanzu an mishi allurar bacci ta kwana biyu, duk
da aikin is successful still fa akwai risk dan in har bai tashi nan da kwana biyu
ba tofa akwai matsala. Da jin wannan maganar ne Hajjiya ta tashi hankalin ta wanda
har yayi sillar ciwon hawan jinin ta ya tashi ta suma musu a wurin nan a take, nan
da aka Kira nurses aka kai ta wani d'aki ita ma tare da bata treatment.

Tun a lokacin ne suke son k'iran Husna amma babu hali domin babu layin ta, a
lokacin ne kuma y'an sanda sun kawo kayan Aliyu, wato wayarsa jakar tafiyar sa da
kuma mukullen motar. Sai a lokacin wata idea ta fad'a ma Habib na cire SIM d'in
aliyu ya saka a nashi domin wayar Aliyun tayi condemn, farkon k'ira da suka mata
layin na shiga amma bata d'aga ba, daga baya kuma baya shiga gaba d'aya to tun
ranar suke ta gwada wa ko Allah zai yi ya shiga ta d'aga su fad'a mata dan wannan
hak'in ta ne ta sani amma baya shiga.

Tsakin da ya kuma yi ne yasa Hajjiya duban shi tare da tambayar shi ya k'i shiga
ne. "Eh Hajjiya ya k'i shiga." "Uhm yayi kyau." Kawai ta fad'a dan a yanda take nan
bata da k'arfin magana sosai yanzu kawai burin ta su je ya jikin d'an nata ne tunda
yau kwana biyu kenan da faruwar abun kuma ya kamata ya tashi a cewar likitocin amma
har yanzu shuru babu labari.

"Hmm wallahi ku kuke wani damuwa da sai kun sanar da ita, tun fa shakaran jiya muke
ta faman k'iran ta amma bata d'aga ba yanzu kuma wai bata shiga wato dai an dame ta
shi yasa ta rufe wayar ma gaba d'aya. To an fad'a mata muma muna son k'iran nata
ne, dan dai kawai ya zama dole ne amma da Wallahi ba zamu K'ira ba." Cewar Hamida
da gaba d'aya haushin Husna ya rufe ta." "Ke ma da abun magana Hamida ki ka sani ko
fad'a su kayi kafin rabuwar su?" K'ila sun samu sab'ani shi yasa ta k'i d'agawa ta
d'auka shi ke k'iran ta." Zarah da ke ba y'ar ta nono ta fad'a." "Haba Aunty dan
sunyi fad'a shi kenan sai ta k'i d'aga wayarsa saboda rashin hankali ai ko
mahaukaci ne yaga k'iran da a ka mata ranar ya san ba lafiya bane, shine ita rashin
hankalin na bai fad'a mata ba maimakon ta k'ira daga baya in ma tace bata kusa da
wayar ai sai ta k'ira ba wai ta kulle ta ba." Duk abun nan da suke Balkisu bata
saka musu baki ba Wanda ba d'abiyar ta bane dan da ne tuni ta sa baki tana zagi da
kuma zugi amma yanzu kamar bata wurin gaba d'aya ta zama shuru-shuru.
"Ya isa haka nan ku dai na k'ira min sunan ta ma ni, dama na ce a k'ira ta saboda a
fad'a mata ne amma tunda haka ne Habibu Ka cire SIM d'in Kar a k'ara k'iran ta. Ni
yanzu ba ta ita nake ba ta Yaro na nake kuma ko an fad'a mata me zata zo ta mishi
dan na san ba kulla da shi zata yi ba, tunda ko lokacin da yana da lafiyan shi bata
yi ba balle yanzu, dan haka daga yau Kar wanda ya kuma gwada k'iran ta. In ta gama
yawon gantalin ta ta zo." "In sha Allah ba zamu k'ira ba." Suka fad'a a tare."

"Allah sarki Aunty Aisha tana jin labarin hatsarin ta zo duba shi, duk da ba sa
tare hakan bai hana ta zuwa duba shi ba kuma a ranar d'auren auren ta." Cewar
Hamida. "Eh fa kuma bayan haka ma har sau biyu ta zo duba shi bayan ranar kuma har
da abinci ta kawo mana." Balkisu da tun d'azu bata yi magana ba ta fad'a. "Ai ranar
da ta zo nan bata fad'awa kowa ba ta zo, sai da na maida ita gida Baban ta ya ke
fad'a min an neme ta an rasa dan ba wanda ma ya ga fitar ta." Habib ya fad'a." "Ai
mahaifiyar ta ta fad'a min jiya da suka zo suma, mutane kirki masu tattaku." "Eh fa
duk da ba sa tare da Yaya hakan bai hana su zuwa ba daga ita har y'an uwan ta amma
wancan kuma da ita ya kamata ta kasance da damu a nan tana can tana shagali." Cewar
Hamida.

********

B'angaren Husna kuwa duk wannan wainar da ake damawa bata sani ba,

Tunda suka iso Kaduna ba su zauna wuri d'aya ba daga zuwa gyaran jikin sai zuwa
kitso da kuma lalle, gaba d'aya tunda ta dawo ta manta da tana da wani miji da ta
bari dan koda suka isa hankalin ta bai fad'a mata ta k'ira shi ba.

Suna cikin hada-hadan zuwa dinner party ne ta ga k'iran shi, a lokacin ana mata
makeup ne dan haka bata d'aga ba ta bari sai an gama mata tukun. Amma kuma ba'a
dena k'iran ba, ganin zai dame ta ne yasa ta kashe wayar gaba d'aya da nufin in sun
dawo daga dinner zata k'ira shi a lokacin zata samu lokaci amma yanzu baza ta iya
d'aga ba dan zai b'ata mata lokaci ne a banza da surutun shi da baya k'arewa. Daga
haka ta fara shirye-shiryen zuwa dinner d'in ba tare da damuwar komai ba,suna ina
wurin event ta bud'e wayar tare da blocking d'in numbern shi dan Kar ya kuma k'ira
ya dame ta.

*******HOSPITAL******

A hankali d'an yatsan shi ya fara motse, a hankali a hankali idanunshi suka fara
motse suma, wasu siraran hawaye ne suka gangaro daga gefin idanunshi, kamar an
danna remote haka komai ya fara haskawa a idanuwan sa. Nan da nan numfashin sa ya
soma yin sama kamar wanda zai shek'a lahira. Hajjiya ce da ke zaune a can k'asa
gefi tana lazimi ne ta yi saurin tashi wa sakamokon jin k'aran tititti da bata san
daga ina ya ke ba amma tasan babu lafiya, tana juyawa ga Ali ta ga numfashin sai
sama yake, ko kafin ya k'ira Drs ta ga sun shigo su biyu tare da wasu nurses a
bayan su.

"Congratulations, ya farka alhamdulilah komai is normal yanzu yana bacci nan da


d'an awanni zai farka." Likitan da ya fito daga d'akin Aliyu ya fad'a.
"Alhamdulilah! Allah mun gode maka, zamu iya ganin sa yanzu?" " Eh za ku iya ganin
sa amma yanzu yana bacci dan haka karku yi hayaniya da zai tayar dashi yana
buk'atar baccin so that zai yi digesting d'in komai."
**********

Aisha tun tana d'an d'ari-d'ari da Abbu kan matakin da zai d'auka a kan ta har ta
saki ranta ta cigaba da tsabgogin ta, dan ba wanda ya kuma kawo maganar. Kawai
abunda ke damun ta shine bata gane ma Lukman gaba d'aya ya canja mata ba kamar da
ba, baya k'iran ta baya tura mata text massage's kamar da kuma ko da ita ta k'ira
shi daga gaisuwa shi kenan zai kashe wayar, akasin da ita ke gajiya da surutun shi.
Amma yanzu babu wani hira ko kalaman soyayya da ya ke mata baya yi, sosai abun ke
damun ta dan har tambayar shi ta yi kan ko ta mishi wani abu ne ya ke mata haka
amma zancen d'aya ne. "Babu komai kawai aiki ne yayi min yawa." Sosai ta shiga
damuwa sai take ganin killa har yanzu bai yafe mata bane, dan bata b'oye mishi
komai ba kan fitar ta na ranar.

Sai kuma rashin lafiyar Aliyu wanda Alhamdulilah yanzu yana samun lafiya dan ta je
duba shi har sau uku kuma Ummi bata mata fad'a ba kai ita ce ma ke bata umarnin
zuwa Wanda sosai hakan ke bata mamaki duba da irin alak'ar su ta yanzu musamman ma
irin fad'an ta ta mata ranar.

B'angaren gyaran ki da ake mata kuwa sai abunda ya aka k'ara domin Abbu ya ce nan
da kwana biyu zata tare dan haka sosai take shan gyara ciki da waje sosai tayi kyau
jikinta sai shek'i yake fatar ta sai glowing take, amma abunda ya d'aure mata kai
shine tare ake musu gyaran jikin da Eeman. Ba ita kad'ai abun ya ba wa mamaki ba
har ita Eeman ma dan har tambayar Inna Hasiya ta yi amma ba ta bata amasa ba, da
haka aka cigaba da yi musu gyaran jikin tare.

Ana gobe tarewar ta ne da daddare tana cikin had'a wasu kayan da ba a tafi da su
lokacin da aka je jera ba.

"Shi kenan daga gobe zaki tafi ki bar ni ni kad'a." Cewar Eeman da take taya ta
had'a kaya. "Yeah daga gobe shi kenan bana nan, sai dai in zo ziyara kamar yanda
nake da." "Gaskiya za mu yi kewar ki sosai amma kuma ba sosai ba tunda ba Zaria zai
aje ki ba a nan za ku zauna, so anytime mu kayi missing d'in ki zaki gan mu ko kuma
ki zo mana. Amma fa kuma ina murna da tafiyar ki, kin ga zaki bar min d'akin ni
kad'ai na yi yanda na ke so da d'aki na dama ai nawa ne tunda ki kayi aure ya zama
nawa da kika dawo ne na d'an ji tausayen ki na bar ki dan kar ace na hana y'ar
k'anwata zama da ni. So am so much happy da zaki bar min d'aki na yanzu na yi yanda
Naga dama." Ta k'are maganar da yar dariya. "Hahaha, kin d'auka ke ma zaki zauna a
nan ne har abada, ina tafiya ke ma za'a zo kanki yarinya dan haka gwara ma ki yi ki
fitar da miji mu miki auren nan ki huta. "Eh naji d'in za'a zo kai na amma bayan
kin tafi ba, dan haka sai na more d'akin tukun."

"Y'an matan Ummi, zo Baban ku na son magana da ku." Cewar Ummi da shigar ta d'akin
kenan. "To muna zuwa Ummi." Daga haka suka aje abunda suka tare da bin bayan ta.

D'an jara murya Abbu yayi tare da d'an zuba mu su ido na d'an wani lokaci kana ya
ce. "Abunda yasa na sa a k'ira min ku nan shine akwai maganar da na ke son yi da
ku, Lukman ya zo ya same ni da wata magana a ranar d'auren auren. Yazo min da
maganar ba zai iya auren ki ba, ya rok'e ne da na maida ki wurin tsohon mijinki dan
ba zai iya zama sillan rabuwar Ku ba dan har yanzu kina son shi dan haka ba zai iya
auren ki ba zuciyarki kuma tana wurin tsohon mijinki. Dan haka ne ya rok'e ne da a
maida auren Ku da Aliyu wanda kuma hakan aka yi ba'a d'aura auren da Lukman da
Aliyu aka daura.
*****FLASHBACK.

Abbu yana cikin jama'a ne Lukman ya same shi da yana son magana da shi kuma me
muhimmanci ne, da jin maganar me mahimmanci ne yasa shi barin wurin da Lukam. Falon
shi ya shiga da shi tare da nuna mishi wurin zama kana ya tambaye shi lafiya ko
akwai abunda ke faruwa. "Amm.. dan Allah Baba kayi hak'uri da abunda na zo maka da
shi cikin k'ank'anin lokaci." "Ina Jin ka Lukman me ya faru ne?" Fad'a min kar kaji
komai ai Nima kamar mahaifi nake a gurin Ka dan haka fad'a min me ke faruwa?"

"Dan Allah Baba ina buk'atar alfarma a wurin Ka dan Allah kayi hak'uri da abunda
zan ce amma a gaskiya bazan iya auren Aisha ba." "Me ka ce?" Ba zaka iya auren ta
ba?" Wani abu ya faru ne ko kuma an fad'a maka wani abu a kanta ne da ya canja maka
ra'ayi a kanta?" "Kayi hak'uri Baba amma ba wanda ya fad'a min komai a kanta kuma
ma ni koda an fad'a min ba abunda zai canja ra'ayi na a kanta saboda na yarda da
ita kuma ina son." "To me ya saka ks fad'an baza Ka iya auren ta?" "A gaskiya Baba
bazan iya b'oye maka ba, tabbas ina son Aisha kuma har yanzu ina son amma ita bata
sona har yanzu tsohon mijin ta take so. Bazan iya auren ta ba zuciyarta kuma ta
kasance ga wani a waje, duk da bata fad'a min ba amma na sani ta amince da auren
nan ne saboda yi muku biyayya bata son watsa muku k'asa a ido shi yasa ta yarda
amma na sani babu sona a ranta. A da na d'auka zan iya sa mata sona a ranta amma
hakan bai yu ba saboda har yanzu tana son shi, duk da ban san me ya raba su ba amma
na tabbata har yanzu suna son junan su dan haka why zan shiga tsakanin su. Shi yasa
na yanke wannan shawarar da dan Allah ka amince da a d'aura auren da shi this is
the least I can do for her, koda anyi auren nan ba zata tab'a yin farinciki ba
saboda zuciyarta bata nan tana wani wurin. Dan Allah kayi hak'uri ka yafe mishi
abunda yayi maka duk da ban san me yayi ba da yasa ka irin wannan fushin ba amma
Baba d'an adam ajizi ne no one is above mistake yayi kuskure dan Allah Ka yafe
mishi a maida mishi matar shi kar ka bar fushin nan da kake da shi ya ɗauki maka
hankali da har Ka kasa sanin farincikin y'arka, in har ita zata iya yafe mishi to
banga dalilin kai ka kasa ba. Dan haka ne na zo rok'an alfarma a wurin ka da dan
Allah a d'aura auren nan da shi ni zan biya kud'in sadakin kuma kar damu da mutanen
mu da suka zo d'auren auren zan musu bayani zasu fahimta, bana son auren wace bata
sona duk da tana iya k'ok'rin ta na nuna min komai lafiya amma ni within myself
nasan ba haka bane. In dai har son da nake mata na gaskiya ne, to bazan k'wace mata
farinciki ta. baza ta tab'a yin farinciki da ni ba dan haka ne nake son a yafe
mishi duk abinda yayi maka ka bari a maida auren nan kuma ma ba musan me Allah ya
k'addara mu su ba a nan gaba."

Shuru Abbu yayi yana sauraran maganganun shi ba tare da ta koda cewa komai ba,
tabbas ko shi ma yasan har yanzu da akwai soyayyar Aliyu a ranta, amma bai d'auka
abun ya kai haka ba da har Lukman ma zai gane ba. Ya d'auka kawai na d'an wani
lokaci ne da zarar an yi auren komai zai dai-dai ta ashe-she ba haka bane. Kuma
gaskiyan shi duk da yana jin haushin da zafin abunda Ali yayi ma y'ar shi bai kai
zafin da ita take ji ba, idan har ita za ta iya yafe mishi to shi me nashi, kawai
dai yana son y'ar shi ta yi farinciki in Lukman ba zai sa ta farinciki ba ya ai
dole ya amince ko Dan farinciki ta, tunda ita ma domin farinciki sa ta yarda da
auren ba tare da gardama ba.

"A hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da duban Lukman da ya sunkuyar da Kai k'asa
yana me jiran amsar shi. "To shi kenan Lukman tunda Kai da Bakin ka ka zo da
maganar babu damuwa za'a yi yanda Ka ce d'in, amma kafin nan ina buk'atar magana da
mahaifin ka." Abbu ya fad'a da wani Tunani da yazo Kan shi yanzu, tabbas Lukman
mutumin kirki ne wanda kuma duk uba na gari zai so ya zama sirkin shi.

"To Baba ina gode, na gode da fahimta da kayi. Zan mishi magana yanzu in na fita."
"A'a babu komai Allah yayi maka albarka." Abbu ya fad'a.

"Amin ina godeya." Daga haka ya fita daga falon tare da barin Abbu cikin tunanin
abunda ya ke son aiwatar wa.
A hankali ya zaka hannun shi cikin aljihunsa tare da cire wayarsa kana yayi dialing
numbern Baban Eeman, bugu biyu ya d'aga da sallama Baki.

Bayan sun gaisa ne Abbu ya fad'a mishi komai da kuma k'udinrin shi da ya ke son
aiwatar wa. "Ai babu damuwa Alhaji Muhammad ai Eeman y'ar Ka ce dan haka ba sai ka
tambaye ni ba ko kayi shawara ba, na baka wik'a da nama. "Na gode da wannan girman
da Ka bani, ina fad'a maka Yaron kirki ne kuma daga d'an babban gida, manyan mutane
ne masu tattaku ba zata tab'a da na sani ba in sha Allah." "To Baban amare kayi duk
abunda ya kamata ba sai ka k'ira ni ba, yanzu ina d'an wani aiki ne zamu magana
daga baya." "To shi kenan babu damuwa sai anjuma." Daga haka ya katse k'iran tare
da tabbatar wa kanshi yes abunda yake shirrin yi dai-dai ne dan haka da k'arfin
guiwa ya tunkari Baban Lukman zancen. Bayan yayi mishi bayanin komai da Lukman yayi
mishi kana ya d'aura mishi da na shi kud'rin.

"Kai ma sha Allah hakan ya yi ai duk d'aya ne da wannan da wancan duk d'aya ne ai
babu damuwa, ai yazo min da maganar amma na ce mishi hakan ba me yuwa bane dan ba
zai maida mu k'ananan mutane ba, ashe ya zo ya same ka." "A'a babu komai ai gwara
da ya fad'a tun da wuri, yanzu tunda ka amince sai a fad'a mishi shima ko dan ba mu
san na shi ra'ayin ba."

"Wani irin ra'ayin shi ai bashi da ra'ayi a nan kawai a d'aura daga baya ya sani mu
ne manya dan haka magana ta zauna." "To shi kenan tunda ka ce haka, yanzu bari in
k'ira shi kyawun shi d'ayan Yaron sai a yi abunda ya kamata." "Eh ya kamata Ka
k'ira shi." Daga haka Abbu ya sa layin kyawun Aliyu wato kawu Bala nan ya fad'a
mishi komai da tare da fad'a mishi nan da awa d'aya za'a d'aura auren bayan sallhn
jumma'a dan haka ko zai samu damar zuwa kafin lokacin. "Ai babu damuwa Alhaji koda
bana nan ma ai zaka iya yin komai tunda an zma d'aya tun ba yau ma amma duk da haka
in sha Allah zamu zo kafin lokacin." Abbu jin maganar sa sai gaba d'aya yaji kunyar
Kan sa, kan irin abunda ya dinga yi ma Aliyun. "To sai kun iso." Ya ce daga haka ya
sauke wayar tare da furta. "za su zo dan haka muna buk'atar d'an d'aga lokacin har
sai sun zo." "Ai babu damuwa sai sun zo d'in."

To wannan ne silar mai da auren Aisha da Aliyu banyan zuwan su Kawu Bala da y'an
uwan sa aka d'aura auren Aisha Muhammad da Aliyu Abubakar matawale kan sadaki Naira
dubu d'are Wanda kuma Lukman ne ya biya kamar yanda ya ce din. Kana aka zo aka
d'aura auren Lukaman mustapha da kuma amaryar sa Fatima jibrin kan sadaki naira
duba d'are.

Sosai Lukman ya kad'u da jin wai an d'aura auren shi da Eeman, da farko ya d'auka
bai ji sosai bane sai da Baban shi ya kuma mai-maita mishi kuma da fad'a mishi ya
musu biyayya da ba zai dana sani ba.

Bayan d'auren auren ne sak'on hatsarin motar Aliyu ya iso su, hakan ne yasa su Baba
Bala barin Wajan domin zuwa asibiti. Suma Abbu bayan mutane sun Watse sun je sun
duba shi kafin suka koma, bayan ya koma gida ne ya ke sanar da Ummi Wanda kuma a
lokacin Aisha ta ji har ta bar gidan ba tare da sanin su ba.

Da ya bari sai bayan Aliyu ya warke gaba d'aya tukun za'a yi maganar tarewar ta
amma abunda Aisha ta yi ranar ne yasa shi canja ra'ayi Kan gwara ta tare kawai in
ya so daga can ta yi jinyar mijin ta zai fi.

Jin haka ne Inna Hasiya ma tace kawai ita ma Eeman d'in in mijinta ya shirya kawai
ta tare zai fi a yi gaba d'aya, hakan ne yasa a ka fara yi ma Eeman ma jaran jikin
tare da Aisha. Ita ma Eeman a nan Kano za su zauna da mijin ta Lukman ya ce gwara
su fara zama a nan d'in kafin su koma Zaria gwara ta d'an zauna a nan d'in kusa da
y'an uwan ta kafin su saba zai fi. Dan haka ita ma jibi zata tare dan har jere an
yi kawai amarya kawai za a kai.
*****END OF FLASHBACK.

"To Kun ji abunda ya faru fatan za ku min biyayya." Abbu ya fad'a tare da duban su.

Eeman mamaki tsoro fargaba ne ya kamata lokacin guda, abu kamar a farki. Da ace ba
Abbu ne ya fad'a mu su wannan maganar ba za ta k'aryatar amma fa abbu ne fa?" Ina
ba zai tab'a mu su wasa irin wannan, yanzu ita ya ma zata iya kallon Lukman a
matsayin mijinta bayan ya so y'ar uwar ta?" Duk da ba tun yau ba ta ke crushing a
kan shi amma kuma tun ranar da ya nuna mata yana son Aisha ta yi iya k'ok'rin ta
wurin ta ga ta fitar da shi daga zuciyarta amma yanzu kuma lokacin da bata shirya
ba all of a sudden a ce wai ya za ma mijin ta. Kai wannan ai taci amanar y'ar uwar
ta, kuma ba za tab'a iya fad'a ma Abbu bata son zab'in shi. Tana cikin tsaka me
wuya ya za ta yi.

B'angaren Aisha kuwa ba hakan bane a wurin ta akasin Eeman ita farinciki ne da kuma
gode wa Lukman da ta ke a ranta, sai yanzu ta gane Dalilin shi na treating d'in
haka. Ita kam da wani irin baki za ta gode mishi ga irin hallaci da ya yi mata.

"Zabi na bai mu Ku ba kenan?"

"A'a yayi kuma in sha Allah za mu ma Ka biyayya ba zamu baka kunya ba." Eeman ta
fad'a. "In sha Allah Abbu duk abunda ka yanke mu masu yi maka biyayya ne a koda
yaushe." Cewar Aisha. "Na gode da k'arban zab'i na da Ku Ka yi, Allah ya yi mu ku
albarka. Ke Eeman na san abunda ki ke tunanin, bana son kiyi tunanin cewar wai dan
ko Lukman ya ce yana son Aisha shi kenan ba za ki mishi biyayya ba. Ba wanda ya ke
auren matar wani haka ba wace ke auren mijin wata, Allah bai k'addarar Aisha matar
shi ba ce dan haka ki cire wannan tunanin ki rik'e mijinki ki yi mishi biyayya dan
aljanar ki na k'arkashin tafin k'afar shi. Daga nan yayi mu su fad'a tare da nasiha
kana yace za su iya tafiya.

Koda suka koma cikin gida ma Ummi da Inna Hasiya da har yanzu bata koma Kaduna ba
saboda tarewar Aisha da kuma Eeman sai kuma Baba fatsme ma da ta zo domin tarewar
su, duk ba wani za'a yi ba kawai dai tarewa za'a yi duba da irin yanda komai ya
faru d'in kawai y'an uwa da abokan arziki za su raka ka wace gidan ta.

Sosai a ka musu fad'a musamman Eeman da ta ke ganin kamar taci amanar Aisha ne, sai
da Aisha ta zauna ta yi mata bayanin ita fa koda can ba son Lukman ta ke ba kawai
biyayya da kuma irin nacewar ta ne yasa ta amince da auren shi amma in dai sone kam
Aliyu take so.

Jin hakan ne yasa Eeman Jin d'an saukin abunda ta ke ji tare da d'aure damaran
shawo kanshi zuwa gare ta, tunda haka k'addara ta so, duk da tana fargaban ko zai
amshe ta?

Aisha ma sosai a ka mata fad'a da nasiha da kuma iya zama da Husna tunda ta zama
abunda da ta zama

**********

B'angaren Hajjiya ma kawu Bala ya yi mata bayani komai dan haka tasan da tarewar
Aisha ma kuma ta fad'a ma Zarah da balki kawai da Hamida ne kawai ba'a fad'a ma ba
sai ana gobe tarewar ta sani kuma taji dad'in Jin an mai da auren yayan ta da Aisha
dan a yanzu ba wanda take son ta zama matar yayan ta kamar Aisha dan haka jin koma
war ta ga yayan ta sosai ya faran ta mata.

B'angaren Aliyu da jiki Alhamdulilah dan a gaskiya yana samun lafiya dan ya farka
yanzu har magana yana duk da ba sosai ba ana samun improvement. Duk da Hajjiya ta
hana Kar a fad'a mishi mai da auren shi da Aisha da aka yi Hamida sai da ta fad'a
mishi tare da gaya mishi kar ya ce ita ta fad'a mishi. Hakan ne yasa shi shima
shuru da bakin shi kamar bai san komai ba amma a k'asan ranshi Allah kad'ai ya san
irin farin cikin da yake ciki, wanda shi yasa ya ke samun lafiya.

Hamida ganin d'an uwan ta baya magana kullum tunani-tunani ya ke ne yasa ta yi


mishi wannan albishir d'in dan ba za ta iya ganin shi cikin wannan halin ba.

Koda ya tashi ya tambaye Husna amma an ce mishi bata zo ba sosai bai ji dad'i ba
duk da ya san koda da ta zo ba wani abunda za ta tsinana ba amma zai ji dad'in
hakan, koda ya ke ma ko da lafiyar shi ma me ta yi mishi balle yanzu. Sai yaji gaba
d'aya ma ta fitar mishi a ranshi baya ko son jin muryar ta ne balle ganin ta.

Jin Aisha tana jin hatsarin shi ta bar komai ta zo duba shi ba k'aramin dad'i ya yi
mishi ba sai yaji ya k'ara son ta, barin ma da yaji cewa yanzu ta zama matar shi ta
sunah. Shi kam me zai yi banda gode wa Allah da ya mai da mishi matar shi, yanzu
Allah-Allah ya ke ya samu sauki a sallame su ya koma gida wurin matar shi rabin
ransh.

P.39

Washe gari sun tashi da shirye–shiryen tarewar Aisha, tunda safe suka tashi ake ta
hada–hada. Duk da sun ce ba za'a yi taro ba hakan bai hana y'an uwa na kusa da
mak'ota zuwa ba Anci ansha anyi hani'an abun sai son barka. yanma nayi kowa ya
watse a ka bar sai su Baba fatsme, Domin Abbu ya ce ba sai an yi rakiya ba dan shi
da kanshi zai sada ta da gidan ta. Dan bai ga anfanin duk wannan abun ba ita da
mijinta bashi da lafiya yana kwance a godon asibiti mai ya kai ta da duk irin
wannan abun, ita da zata je jinya me ya kawo wannan. Dan shi bai san wa ya fad'a mu
su da har suka zo dan shi ya so a yi abun cikin sirri zai fi duba da irin halin da
mijin ma ya ke ciki, dan yasan ba komai bane ya kawo su sai sa ido da gulma da son
jin me ke faruwa da ya a kayi za ta koma. Hakan ne ma yasa shi cewa babu y'an
rakiya shi zai kai ta da kanshi, kamar yanda ya yi a farkon auren ta.

Da jin haka kowa ya watse, a ka bar su Inna Hasiya da su Baba fatsme. Da daddare
suka shirya ta cikin riga da zanin wata koriyar atamfa me ratsin fari, sai a ka
d'aura mata farar laffaya a kai. Fad'in irin kyawun da ta yi b'ata lokaci ne.

Ganin komai take kamar sabo, yanda suke da ita da kuma yanda su ke mata fad'a kamar
wacce bata tab'a yin auren ba. Ita abun har ya so bata dariya ma, ko sun manta
aurenta shakara goma kenan wanda ya ci ace ta wuce wannan wurin tunda in dad'in
auren ne ta gani haka rashin dad'in sa.Yanzu kam ai ta san komai sai dai ta ba wa
su labari balle ita da still mutumin nan dai wada take aure kuma ta yi zama da shi
har na tsawon lokaci shi yanzu zata koma mai.

Duk da tasan me yasa suke hakan, su iyaye ne kuma duk yanda kake ganin ka girman
kasan me kake a wajan iyayen ka kai kamar jariri ne a wurin su. Balle kuma ita da
na ta situation da bane, barin ma in ta tuna da Husna da kuma irin zaman da za su
fara yanzu. Abunda ta sani shine yanzu ba kamar da bane da zata zauna tayi ta
hak'uri, ba zata yi magana ba. Abinda ta jure da yanzu ba zata jure ba. Duk abunda
suka yi mata daga ita har shi d'in zata yi maganin su ne cikin ruwan sanyi, barin
ma Husna da take cike da ita. Dan Aishar yanzu ba ta da ba ce da zata taka ta yanda
ta ga dama, duk renen hankalin da take kawo mata da tana kyale ta to yanzu ba zata
bari ba.

"ko ya zata yi in ta ganta?"

Horn d'in mota da ta ji ne yasa ta dawowa daga duniyar tunani da ta Lula, ashe har
sun iso gidan bata sani ba ta fad'a duniyar tunani.

Da sauri mai gadi ya wangale musu gate motar su ta danno kai, Abbu ne ya fara
fitowa daga motar kafin Baba fatsme sai kuma Khadija ita ma y'ar uwar su Aisha ce
tukun ita Aisha ma ta fita.

Suna fita Abbu ya kama hannunta kana suka nufi part d'in ta.

Zarah da Hamida dake jiran zuwan su tun d'azu ne suka tashi tare da nufan su tare
da yi musu lale da zuwa.

Har d'aki abbu ya raka Aisha tare da zaunar da ita kan gado kana ya rik'e kanta
tare da yi mata addu'a kana ya koma dan su Baba fatsme sai gobe, Zarah ma ba su
d'ade ba suka koma a ka bar Aisha da fatsme da khadija.

~~~~~~~~HOSPITAL~~~~~~~~

ALIYU.

hankali ya bud'e k'ofar toilet tare da tsayawa a bakin k'ofa ba tare da ya cigaba
da tafiya ba, da sauri Habib ya tashi tare da kama shi. Da taimakon Habib ya iya
takawa har zuwa bakin gadon, dama wanka ya shiga yi dan baya jin dad'in jikin na
shi saboda tunda a ka kawo shi bai yi wanka ba sai dai a goge mishi jiki. Ganin ya
fara samun sauk'i ne dan har yana iya tsayawa da kanshi ne yasa suka yarda da yayi
wankan, amma kar ruwan ya tab'a bandage d'in da a ka lullub'e kanshi da kuma d'ayar
k'afar ta shi.
"Sannu har yanzu kana jin zafin ta ne?" "Yeah! Ina jin zafin amma ba sosai ba yanzu
ma ina ga ruwan da ya tab'a ta ne yasa nake jin zafin haka." Ya fad'i hakan ne tare
da mik'e k'afar. "Sorry, kai ne baka ji wallahi ka nace sai kayi wakan nan yanzu
gashi ka ja ma kanka ciwo. Bari na k'ira nurse a zo a canja maka bandage d'in
k'afar dan baza ka zauna da shi haka ba, na tabbata kaji ma k'afar ciwo ne dan
gashi har jini take gwara su zo su duba zai fi. Ya k'are maganar ne tare da danna
wani button kusan da gadon,,ko minti biyu ba suyi ba sai ga nurse ta shiga tare da
tambayar ko lafiya? Nuna mata k'afar yayi tare da cewa. "K'afar ce ke fitar da jini
ina ga d'an takawa da yayi ne ya jawo hakan." "Kai kawai ta kad'a mishi kana ta
soma canja ma Aliyu bandage d'in tare da yi mishi allura kana ta dubi Habib tare da
cewa. "Ba abun tada hankali bane, ya d'ade bai motsa ba shi yasa yanzu da ya d'an
taka veins d'in wurin sun mik'e jini yayi circulating wanda kuma abu ne me kyau,
amma ya dena sa pressure sosai dan zai iya zama matsala." "To mun gode nurse." "Ba
komai Allah ya ba shi lafiya." Daga haka ta bar ward d'in.

"Ka dai ji me tace sai ka kiyaye duk abunda suka ce domin samun lafiya da wuri dan
zuwa wurin amaryar ka." "In sha Allah zan kiyaye ko dan zuwa wurin ta ma, ni da ma
zasu tausaye min su sallame ni na koma gida zai fi dan na samu sauk'i yanzu." "Ya
da sauri haka eh?" Ai ba kai babu sallama sai Ka samu lafiya sosai tukun, dan haka
ka ma cire tunanin sallama yanzu dan ba inda zaka je. Kuma ma kai da ko ka kuma
gidan me zaka tsinana ma in banda ba ta wahala kawai dan ba k'arfe ne da kai da har
za'a ce zaka yi noma ba. Ya k'are maganar da dariyar shak'iyanci. "Wa ya ce maka
bazan iya noma ba?" Ko a yanzu ma haka na fi Ka k'arfin noma Yaro don't
underestimate me." "Ah lallai lafiya ta fara samuwa tunda har kake tunanin haka,
amma serious ka tsaya kan treatment kar ka je kaja mana aiki baya ko in ce aikin
likitoci baya dan na san ka ba k'aramin aikin ka bane Ka danne y'ar mutane in ta
zo. Ka daure ka yi hak'uri har ka samu lafiya, in ya so kwai ci kanku bai dame mu
ba amma yanzu you have to focus." "Kai banza ne wallahi, ni na ce maka zan yi wani
abu ne?" In ma zanyi sai a nan?" "Ai na san ka ne Ali, kuma ko na rantse bazan yi
kaffara ba ka rantse babu wannan tunanin a kanka?" Tell me you don't intend to do
so?"

"Ban sani ba d'an sa ido kawai." Ya fad'a tare da juya kanshi gefe. "I knew it! Na
fad'a maka fa ba abunda zaka iya b'oye min." "Na ji d'an sa ido kawai."

Daga haka suka canja hirar ta su zuwa daban, cikin hirar ne Habib ke tambayar shi
ko Husna ta k'ira shi? Dan tun ranar da Hajjiya ta ce musu kar wanda ya k'ira ta ba
wanda ya sake yin attempt d'in k'iran ta, shi yasa ya tambaye shi ko ta k'ira shi
saboda tun ranar da ya tashi ya samu waya ya saka SIM card d'in shi a ciki saboda
ma su neman shi musamman ma wurin aikin shi.

"Eh ta k'ira d'azu, wai kud'in hannunta sun k'are tana buk'atan wasu dan ko kud'in
mota bata dashi." "Ba ka fad'a mata rashin lafiyar ka bane?" "Na fad'a mata mana,
ai shi yasa ta ce wai na tura mata kud'in mota." "To me ka ce mata zaka tura mata
Kenan?" "Wa zai tura mata?" "Sisi bazan tura mata ba Allah ya sa kar ta dawo d'in
dama ba son zuwan take ba, kuma bata tashi nema na ba sai da buk'atar ta tashi
tukun?" Koda na fad'a mata rashin lafiyar tawa bata nuna damuwar komai ba sai ma
maganar kud'i da ta min ma." "Uhmm! Allah ya kyauta kawai zan iya ce maka dan duk
kai Ka ja wa kanka, ba yanda ban ja ma kunne a kanta ba amma ba ka ji ba." "Wallahi
k'addara ce, k'addara ce ta sa ni in ba haka ba me ya kai ni da Husna, k'arya,
sata, rashin kunya, da kuma k'azanta duk a kanta ya kare." "Hahaha daga baya kenen,
amma bai kamata ka ce ba zaka tura mata kud'in ba. Tunda matar ka ce, nawin ta a
kanka ya ke in ba ka yi mata ba wa kake son yayi mata. Duk da bata da hali me kyau
hakan ba shi zai hana ka sauke hak'in ta da ke kanka ba." "Ka d'auka ban bata kud'i
bane, na fa bata kud'i kuma lokacin da ta tashi tafiyar sai da na bata extra ta
rik'e. Tunda ta tafi nan ko sau d'aya ne ta tab'a k'ira dan jin ya nake ne ko kuma
da a ke k'iran ta ta d'aga wato ga shasha da bai san me ya ke KO?" Koda na fad'a
mata hatsarin da na yi bata nuna damuwar komai ba kawai dai ita burin ta kud'i. To
bazan tura ba dan har na rantse, ni yanzu tunanin yanda zan rabu da ita ma nake dan
ba matar zama ba ce." Habib zai yi magana kenan ya dakatar shi. "Please ka bar
manager nan haka ya isa." "To shi kenan Allah ya kyauta amma duk abunda ke faruwa
kai kaja ma kanka, daga haka ya ɗauki pillow tare da kwanciya kan cushin. Aliyu
kuwa wayarsa ya d'auka tare da dailing d'in numbern Aisha amma baya shiga.

~~~~~~~~~~~~~~

Washe gari ba su koma gida ba sai da suka ta ya ta y'an gyare-gyare tukun, ba yanda
bata yi da su da su tsaya da yanma driver sai kai su amma sun ce suna da aikin yi
dan haka ba za su tsaya ba. Haka ba dan ta so ba ta raka su har compound d'in gidan
tare da sa Hamza driver ya kai su gida, sai da taga fitar su kafin ta koma part
d'in ta.

BABA MARIYA HOUSE.

"to yanzu ya za'a yi?" Tunda ya ce bashi da shi." Baba Mariya ta fad'i tare da
duban Husna dake zaune kan kujerar tsakar gida. "Yana da shi fa, kawai baya son
bayar wa ne kuma sai na cire daga jikin shi." "Gaskiya dai kam, kiyi ki samu kud'in
nan da wuri dan a fara aikin nan." "Ai karki damu Baba zai ba da kud'in, in ma bai
babda ba ni zan d'auka." "Yawwa y'ar albarka na san zaki samu ai, kin ga kina bani
kud'in zan kai ma malam zai fara aikin, duk wannan taurin kan nan na shi za ki ga
ya sauka sai yanda kika yi da shi. To amma ya yanzu ya za'a yi ki koma gidan?"
Bayan kin ce mishi baki da kud'in motar zuwa kuma yanzu ya ganki me zaki ce mishi?"
Y'ar dariya tayi kafin ta ce. "Gaskiya zan fad'a mishi, zan ce mishi na bi Lubna ne
ita ta biya min kud'in motar. Amma ba zan fad'a mishi cewa tun jiya muka dawo ba
kawai zan yi kamar yau muka dawo. Kuma ma bana tunanin yana gida yanzu dan ya ce
min zai tafi Abuja to ban san ko ya dawo ba amma kuma ya ce min wai yayi hatsari."
"Hatsari kuma?" "Eh haka ya ce wai yayi hatsari amma bana tunanin babban abu bane,
tunda in wani abu ya same shi za'a neme ni kuma muryar shi bata yi kama da mara
lafiya ba kawai dai ya fad'i hakan ne domin gujewa ba da kud'in." "Amma baki da
hankali wallahi, to taya ma kike tunanin za'a same ki bayan wayar ki ma a rufe
take, ai koda ba babban hatsari bane ya kamata ki shiga damuwa tunda mijin ki ne
yanzu in wani abu ya same shi fa?" Shine zai fad'a miki magana irin wannan kuma ki
banzatar eh?" To taya ma kike son ya baki kud'in bayan kin nuna mishi baki da damu
da shi ba. Yanzu ki k'ira shi ki ji ya yake." "Tabbas gaskiyan ki ne Baba, bari na
gwada k'iran shi." Daga haka ta d'auki wayarta tare da dailing d'in numbern sa sai
dai kuma har k'ira biyar tayi mishi bai d'aga ba.

"Hmmm Bai d'aga ba." "Taya zai d'aga bayan kin yi rashin hankali eh, tashi ki koma
gida yanzu duk yanda ake ciki sai ki sanar da ni a waya. Daga nan kuma zamu san
abun yi, dan ba za mu yi sake ba har ya je ya ga wata a waje. Dan haka ne ma gobe
zan je wurin Malam a fara aikin kafin ki kawo raguwar kud'in."

"To Baba bari na yi wanka tukun." "To kiyi sauri dai." "To!daga haka ta shiga bayi
domin wanka, sharp-sharp ta yi ta gama tare da fita tsakar gida inda ta bar Baba
Mariya zaune. "To Baba ni zan wuce sai na k'ira ki, in su Kausar sun dawo ki gaida
min su." "To za su ji, sai na ji ki." Daga haka ta taja trolley d'in ta tare da
barin gidan, tana fita ta samu napep ta shiga kana ya ja.

~~~~~~~~

AISHA.

Bayan ta dawo daga rakiyar su Fatsme direct kitchen ta shiga tare da d'aura abinci
kan wuta, tuwon semo da miyar kub'ewa wanda taji nama da kuma Ganda, sai kuma
ferfesun kifi da tasan yana bala'in so, sai ta soya dankali ta had'a da kuma kunun
gyad'a da tasan yana so shima. Babu b'ata lokaci ta gama ta sa a warmers kana ta
gyara kitchen d'in tare da had'a wanke-wanke, lokacin da ta gama har k'arfe biyar
ta yi. Dan haka direct d'aki ta shiga tare da yin wanka kana ta shirya cikin jar
atanfa fitted gown wanda ba k'aramin karb'an ta rigar ta yi ba, powder da lipgloss
kawai ta shafa sai kuma kwalli da ta sa idonta. Fad'in irin kyawun da tayi bata
lokaci ne, ta fito a amarya ta. Wardrobe ta bud'e tare da d'auko sabon hijab tare
da d'an fesa mishi turare amma ba sosai ba dan kad'an tasa kana ta sa hijabin wanda
ya kai mata har k'asa.saka hannun hijabin ta yi kana ta d'auki jakar tare da saka
wayar ta a ciki kana ta bar d'akin ta koma kitchen, abincin mai gadi ta d'auka ta
kai mishi kana ta koma Kan basket da ta jera warmers a ciki kana ta fita. Sai da ta
kulle k'ofar part d'in ta tukunna ta nufi parking lot.

"Ina wuni Hajjiya?" Hamza dake ba wa flowers ruwa ya fad'a. "Lafiya Hamza, ya
kake?" Ya su Mama kana jin labarin su?" "Lafiya alhamdulilah, eh muna waya da su."
"Ma sha Allah haka mu ke so, d'an bani mukullin mota dan Allah." "To Hajjiya." Daga
haka ya saka hannunshi cikin aljihunsa tare da mik'a mata mukullen." "A'a Hamza ban
ce ka bani duka ba, kawai Ka bani d'aya zan je asibiti ne wurin Alhaji." "Eh kiyi
hak'uri dama ina shirin ka miki su in na gama." "A'a Hamza ai bani na baka su ba
dan haka Ka jira in ya dawo sai ka mai da mishi da su amma ni yanzu bani d'aya zan
fita kar dare yayi." "To Hajjiya amma da kin karb'a, dama d'ayar motar ne ta samu
matsala na kai ta gyara sai kuma biyun ya bar su ko wai ko Hajjiya k'arama zata je
anguwa. Amma tunda kin dawo sai ki karb'a." Ya k'are maganar cikin girmamawa. "To
Hamza tunda ka ce haka sai ka bani mukullin motar alhaji da da nawa d'ayar kuma sai
ka bar ta in zaka wani aike." To Hajjiya, Allah ya ba Alhaji lafiya." "Amin Hamza,
amma dan Allah ka dena k'ira na da Hajjiya nan na sha fad'a maka sunana Aisha ka
k'ira ni da Aisha." "To Aunty Aisha, ga mukullin." "Yawwa tace tare da bud'e booth
ta saka basket d'in kana ta shiga gaba ta tayar da motar ta ja ta fice daga gidan
bayan mai gadi ya wangale mata gate.

P.40

Husna dake d'aki tana mai gyara kayan ta a wardrobe ne ta ji k'arar fitar mota,
wanda yasa ta aje kayan tare da fita waje domin a tunanin ta Aliyu ne. Sai dai koda
ta fita motar har ta tafi, bata san yana nan ba ta d'auka baya garin ma gaba d'aya
duba da irin yanda ta samu gidan. Yanda ta tafi tabar shi haka ta zo ta same shi,
ko ina a wargaje hatta wanke-wanke da ta bari kafin tafiyar ta yana nan har ya fara
tsusa sakamokon raguwar abinci da ke ciki. "To amma in har yana gidan me ya sa bata
gan shi ba?" To kodai shima yau ya dawo daga Abujan tunda dama ya ce sai bayan
kwana biyu zai dawo to k'illa shima yau ya dawo. Da tunanin haka ta juya da nufin
komawa ciki amma sai ta hange Hamza da ke ba flowers ruwa, sai da ta mishi kallon
sama da k'asa kana ta ja dogon tsaki. "Kai Hamza zo nan." Ta fad'a cikin tsantsan
rashin tarbiyya. Ganin bai ji bane yasa ta k'ara jan tsaki tare da cewa. "d'an
wahala sai jiji da kai. "Hamza ta k'ara kiran sunan shi tare da zuwa wurin sa. "Wai
baka ji ne nake ta kwalla maka k'ira amma ka yi banza da ni?" Hamza da ya gama waya
kenan ya juya gare ta tare da cewa. "Ina waya ne shi yasa, kuma ma ni ban jiki ba."
Ya k'are maganar cikin had'a fuskar dan shi dama tun fil azal baya son yarinya nan
tun kafin ma ta aure ogan shi saboda rashin kunyar ta da kuma kallon k'askanci da
take mutane. "Har za ta gaya mishi bak'ar magana kamar yanda ta ta sa ba amma ganin
yanda ya had'e fuskar shi kamar wanda bai tab'a yin dariya bane yasa ta d'an jin
shakkar sa.

"na ji k'arar mota, Alhaji ne ya fita yanzu?" "Alhaji kuma?" Alhaji ai yana asibiti
ba a sallame shi ba tukun." "What! Yana asibiti kuma?" Tun yaushe ya ke asibitin
kuma me faru da shi haka ne?" "Alhaji yayi hatsari mota cikin hanyar shi ta tafiya,
yanzu haka yana asibiti ba'a sallame shi ba."D'an shuru ta yi tare da tunanin ashe
da gaskiye ne bashi da lafiya, to amma in shi yana asibiti waya fita yanzu,?"

"Am...amma kamar naji k'arar mota yanzu nan da nake ciki, to waya fita ne?"
"Hajjiya ce." "Hajjiya kuma?" "Eh Hajjiya." Ya ba ta amsa cikin k'osawa da
tambayoyin ta. "To me yasa bata shiga ciki ba ta koma, ko dai ta d'auka ban dawo
bane." Ta fad'a, dan ita gaba d'aya tunanin ta Hajjiya mahaifiyar Aliyu ce ta zo.

"Ba Hajjiya Mahaifiyar Alhaji ba ce, Hajjiya Babba matar Alhaji ce." "M...me..me ka
ce?" Dama yana da mata bayan ni ne ban sani ba?" "Aisha nake nufi, uwar gidan
Alhaji." Daga haka ya aje pipe d'in ruwan dake hannun shi kana ya nufi d'akin shi
da a ka bashi cikin gidan.

Husna sabon rud'u daskarewa ta yi wurin ba tare sanin abun yi ko fad'a ba, sabon
maganar ta buge ta har bata san lokacin da ya bar wurin ba. Sai da ta d'auki minti
uku kafin ta dawo haiyacin ta, za ta k'ara magana ne ta ga wayam babu Hamza. Har za
ta k'walla mishi k'ira sai idon ta ya kai part d'in Aisha da ya sha sabon fenti sai
kyali yake, nan zuciyarta ta fara yarda da abunda Hamza ya fad'a mata dan a gaskiya
bata yarda da abunda ya ce ba duk da a can k'asan zuciyarta, tana mai tantama a kan
haka amma ganin sabon fenti da kuma yanda ko ina na wurin tsab-tsab babu datti ko
daya ya sa fara yards da maganar sa. Nan da nan ta fara gumi zuciyarta sai bugawa
take, addu'a take Allah yasa ba haka bane Allah yasa ba Aisha ba ce ta dawo. Dan
kuwa idan Aisha ce ta dawo ta sani kashin ta ya bushe. Tunanin yanda asirin ta zai
tonu da kuma abunda Aliyu zai iya yi mata ne ya fad'o mata, da sauri ta kau da
tunanin tare da nufan part d'in da sauri domin gani ma idonta dan an ce gani ya
kore ji.

Bata tashi shiga tashin hankali ba sai da ta isa part d'in ta tarar da k'ofar a
kulle dan haka glass d'in window ta d'an bud'e tare da d'an lek'a cikin falon, ido
ta zero waje sakamokon ganin hotonan Aisha da Aliyu dake manne a bangon falo wato
frame picture da a ka manna a bangon falon. Ai da sauri ta bar wurin cikin sarsarfa
ta isa part d'in ta tare da d'aukan wayarta ta danna wa Lubna k'ira ba gaugautawa,
dan ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta gan ta a gaban Lubna dan a yanzu haka ba me
iya taimakon ta sai ita.

Lubna na d'agawa bata bari ta yi magana ba ta katse ta ta hanyar cewa. "Lubna na


shiga uku asire na ya tonu, komai ya lalace shi kenan komai ya b'ace." Ta fad'a
cikin tsantsan tsoro da kuma fargaba da ke lullub'e da ita.

"Wait! tsaya ki kwantar da hankalin ki, ki kwantar da hankalin ki. Me ya faru?" Ki


yi min bayani." Lubna ta fad'a ta d'ayan b'angaren. "Sai da taja dogon numfashi
tare da sita Kanta tukan ta soma labarta mata komai da ke faru.

~~~~~~~

Aisha kuwa tuk'e take cikin farinciki da annushuwa, sai zabga murmushi take wanda
ita kanta bata san tana yi ba. Haka kawai take jin farinciki da kuma zumud'i,
Allah-Allah take ta isa asibitin dan gani take kamar ma motar bata gudu. Ta d'ayan
b'angaren kuma tana addu'ar Allah ya ba mijinta lafiya ya dawo gida su zauna lafiya
cikin farinciki da kuma son juna har abada.

Tana cikin tuk'e ne ta hango masu sai da fruit dan haka ta tsayar da motar ta gefin
titi kafin ta sauka ta siya fruit d'in, a bayan mota ta aje kafin ta shiga gaba ta
tada motar.

Tana isa asibitin ta nemi wuri ta yi parking kana ta sauka tare da fito da basket
d'in abincin da kuma ledar kayan fruit d'in, tana k'ok'rin d'auko jakar ta da ta
manta a motar ne ta ji muryar Habib a bayan ta.

"A'a amarya ke ce a nan?" Kai ta sauki k'asa cikin kunyar sa ta ce. "Eh ni ce, na
samu ku lafiya?" "Lafiyan mu k'alau, an zo duba ango kenan?" "Y'ar dariya ta yi
kafin ta ce. "Eh ba dole ba." "Ah gaskiya ne, kawo wannan na taya ki." Daga haka ya
karb'i basket da fruit d'in gaba d'aya. "Zan iya d'auka fa." "Na sani amma ki bari
zan d'auka, amma yanzu ke amarya ce kuma bak'uwar mu dan haka ba zan bar ki da su
ba in ogan ki ya gani zai iya hallaka ni." Ya fad'a cikin barkwanci wanda yasa ta
dariya. "Ok tunda ka ce haka." Daga haka suka nufi cikin asibitin yana gaba tana
biye da shi a baya har suka iso ward d'in.

Shi ya fara tura k'ofar ya shiga kafin ita ma ta shiga da sallama a bakin ta, gaba
d'aya suka amsa mata. Aisha har gaban Hajjiya ta tsuguna ta gaishe ta kafin ta
gashi da sauran mutanen davke cikin d'akin.

Hajjiya ce da k'anwar ta wato Balkisu takorar Balkisu sai kuma ita Balkisun da
Zarah, can kan gado kuma Aliyu ne zaune an jingina mishi pillow a bayan shi domin
supporting d'in shi. Sai kuma Hamida da ke zaune kusa da shi, da gani suna tau-
tauana Abu ne.

Tana jin yanda idanuwan sa na kanta, amma bata ko kalli in da yake ba saboda kunyar
Hajjiya da take ji, kuma ma tunda ta shiga idon Hajjiya da Balkisu Babba na kanta
dan haka jinta take a ta kure.

Sama-sama take sa musu baki a cikin hirar su dan har yanzu tana ganin abun wani
iri, rabon da ta zauna da su Hajjiya haka ba gori da hantara tun tana amarya. Dan
haka yanzu sai take jin ta a takure dan bata saba ba, ita mamaki ma hakan ya bata
dan tun lokacin auren Balkisu take ganin y'an canji daga wurin su amma na yanzu kam
ya wuce ya sha ban-ban.
Ganin dare na yi ne yasa Hajjiya fara maganar koma wa gida, tunda dare ya yi kuma
ma ga Aisha ma ta zo dan haka ba sai sun tsaya sai dare ba kamar yanda suka saba
tunda ga matar shi ta zo gwara su koma gida su ma su huta da zaman nan. Duk da dama
Hajjiya ita ke nacewa kan zuwa kullum dan gani take Yaron ta ba zai samu kulawar da
zata bashi ba, shi yasa take zuwa tun safe sai dare take komawa gida. Amma yanzu da
Aisha ta dawo za ta samu kwanciyar hankali da kuma tabbacin cewa d'an ta na hannu
na gari, zai samu kulawar da ya ke buk'ata.

Jin za su koma gida ne yasa Aisha

tashi wa tare da bud'e basket d'in ta fara cire warmers d'in kana ta dubi Balkisu
da ke kusa da ita ta ce. "Balkisu abinci ne nan, ko za ki zuba muku?" Dan dama ta
yi tuwon domin Hajjiya ne dan ta san tana son tuwon fiya da shinkafa ko taliya, shi
yasa ma da ta tashi girkin tuwon ta yi ba shinkafa ba.

"Kai abincin nan zai ci yo kuwa?" Dan ba mu d'ade da cin abincin ba fa." "Ki dai
tambaye su ko zasu ci d'in." "Hajjiya ga abincin fa, matar Yaya ta kawo." "Abincin
nan ba zai ci yo ba yanzu ba dan ba mu d'ade da cin abincin ba." Hajjiya ta fad'a.
"Ba na fad'a miki ba." "Eh to sai ku tafi da shi gida kwa ci shi a matsayin na
dare." "Sai dai haka, dan yanzu kam kowa a k'oshe yake." Cire na Aliyu ta yi ta aje
a gefe kafin ta mai da sauran cikin basket d'in kana ta mik'a ma ta ga shi nan ku
tafi da shi, wannan kuma na Yayan ku ne." Ta fad'a tare nuna da yatsa.

Suna cikin haka ne suka ji an tura k'ofar a ka shigo ba tare da k'onk'sa wa balle
sallama wanda shi ya ja dukan su d'aga kai domin duba waye, baki bud'e su ke kallon
ta dan ba wanda ya yi tsammanin zuwan ta barin ma shi Aliyu. Dan the last time da
suka yi magana jiya ne kuma ta ce bata da kud'in mota dan haka bai kawo zuwan ta
ba, dama gobe yake shirin tura mata kud'in mota dan duk yanda ya ce ba zai tura ba
he can not. Matar shi ce kuma akwai hakk'in ta a kan shi, duk da ita ta kasa zama
ta sauki na shi hakk'in da ke Kanta hakan ba zai hana shi cika na shi ba.

Husna kuwa, kwantar mata da hankali Lubna ta yi tare da bata shawarar ta je


asibitin ta duba shi tare da ba shi hak'urin rashin ta a wurin, daga nan kuma za su
k'ara tabbatar da zargin su kan koma war Aisha gidan. Daga nan kuma za su yi
tunanin abun yi a kanta, amma yanzu shawo kanshi ne a gaba.

Tana sauke wayar ta nemi hijabi ta saka tare da fita compound d'in gidan ta sa
Hamza ya kawo ta asibitin.

Kanta ta sauke k'asa ganin irin kallon da suke mata, da kyar ta iya aro jarimta ta
gaida Hajjiya. tab'e baki Hajjiya ta yi tare da kawar da kanta gefe kana tace. Kai
ku tashi mu tafi dare na yi." To suka ce daga haka duk suka tashi had'a kayan su ba
tare ko kallon in da Husna ta ke ba. Husna kam gaba d'aya jikin ta ya yi sanyi can
gefe ta tsaya kamar gunki.

Hajjiya kam ta na tashi ta nufi k'ofar fita kafin ta juya kan Aisha da ke mik'a ma
Aliyu Banana yana ci. "To zamu wuce, sai jibi in mun sake zuwa." Balkisu Babba ma
ta ce. "Gaskiya kam gobe dai kam za mu zauna a gida sai jibi in Allah ya kai mu
zamu zo duba shi, tunda kun dawo sai Ku k'arasa ladan kulla da mijin ku." "Gaskiya
ne Inna yanzu ya kamata ku huta da zuwa asibiti nan musamman Hajjiya da tunda
wannan abun ya faru bata ma samun baccin kirki kullum cikin damuwa, amma yanzu
komai yana tafiya dai-dai in sha Allah nan kusan za'a sallame shi kuma ma ga Aisha
nan. Ba sai kin dawo gobe ba mu zamu zo amma ki huta ke ma da wannan zirga-zirgan."
Zarah ta k'are maganar ne tare da sab'a y'ar ta a baya. "Eh Hajjiya ba sai kin zo
gobe, ki zauna a gida ke ma ba lafiya ce ta ishe ki ba, kuma kin ga nima ina samun
lafiya dan haka ki dena damuwar nan." A hankali ta taka har zuwa in da ya ke tare
da d'aura hannunta bisa kanshi, kana ta mishi addu'a. "Allah ya ba ka lafiya, ya yi
ma rayuwarku albarka gaba d'ayan ku." "Amin! Suka fad'a a tare, daga haka suka mu
su sallama.
Husna tana ganin sun fita ta sauki ajiyar zuciyar da bata san tana rik'e da ba, da
sauri ta matsa kusa da Aliyu har tana d'an ture Aisha dan gane ta ba su wuri, amma
Aisha ko kallon in da ta ke bata yi ba Sai ma zama kusa da shi da ta yi tare da
b'are mishi banana tana ba shi.

P.41

Aliyu ne ya dubi Husna kana ya ce. "yaushe ki ka dawo?" Ba kin ce baki da kud'in
mota ba?" "Eh Baby bani da shi, yanzu ma bashi na karb'a na samu na dawo. Kana
fad'a min kana asibiti hankalina ya tashi har na kasa hak'uri na aro kud'i na zo,
ina isa na ce ma driver ya kawo ni nan ko gida ban shiga ba sabon tashin hankalin
da nake ciki." Ta k'ara sa maganar ne da share hawayen k'arya.

"Kin kyauta." "Kamar ya na kyauta Baby?" Ko dan baka san irin tashin hankalin da na
shiga bane shi ya sa kake magana haka, kuma ma Baby ba wanda ya d'aga waya ya k'ira
dan sanar da ni. To ta ya kake tunanin zan sani har na zo na kula da kai, amma
yanzu komai ya wuce tun da na dawo ba Ka buk'atar kowa."

Rolled d'in idanunta Aisha ta yi jin ƙarashen maganar ta, kai kawai ta girgiza tare
da cigaba da ba shi bananar da ke hannunta. Ta tabbata da gayya ta ke wannan
maganar dan abun ya mata ciwo ne bata san ita ko a collar rigar ta.

Husna kuwa sai zuba ta ke, shi ko kai kawai ya ke kad'a mata. Jin hirar su ta ishe
ta ne yasa ta jan d'an guntun tsaki tare da mik'ewa tsaye, rik'e hannunta ya yi
tare da tambayar ta. "Ina zaki je?" Sai da ta d'an harare shi kafin ta bashi amsa a
dak'ile. "Toilet zan shiga." Ta k'are da murgud'a mishi baki wanda kuma hakan bai
wuce shi ba tun d'azu ya ke lura da yanayen ta, yana ganin yanda ta ke rolling
idanuwan ta in Husna ta yi magana da kuma harar da ta ke jefan shi da.

Ba ta jira me zai ce ba ta k'wace hannunta ta shiga toilet tare da banko k'ofar da


k'arfe, murmushi ya yi tare da girgiza kanshi kafin ya juya ga Husna. Cikin d'aure
fuska kamar wanda bai tab'a dariya ba ya ce. "Ke ba ki iya gaisuwa bane?" "D'an
had'a rai ita ma ta yi kafin ta ce. "Kamar ya ban iya gaisuwa ba?" "To me ya sa ni
ban gani ba?" "Ina fa shigowa na gaida Hajjiya amma bata amsa ba." "Aisha fa kin
gaishe ta?" "Nan da nan ta had'e rai. "Me kake nufi da na gaishe ta?" Ba na yi
gaisuwa ba da na shigo?" To me sai na k'ara gaishe da ita kuma ma ni ai ba dan ita
na zo nan d'in ba. In ni ban gaishe ta ita ba za ta gaishe ni bane tunda ni ce
babba yanzu." Me kake nufi?" "Eh abunda kaji na ce, yaushe ka dawo ta ita ban sani
ba?" Shine zaka dawo da ita ba ka fad'a min ba, yanzu ka yi min adalci Kenan?"

"Me kike nufi da na maida ta?" Na tab'a ce miki mun rabo da Aisha?" Tambayar ki na
ke?" na tab'a fad'a miki mun rabo ne?" Kuma ko da rabuwar muka yi ke har kin isa in
nema shawara ki kafin in dawo da matata?" Look, don't cross your limit, kar ki sa
na fad'i abunda ban yi niyya ba. Respect your yourself, kar ki ce ban san duk
abunda kike ba.

Ke in banda ma butulu bace har kina da bakin magana a nan?" Har kina da bakin cewa
sai an fad'a miki tukun. Ko kin manta a gidan kika zo kika same ta?" In akwai wanda
zai yi wannan k'orafin to Aisha ce ba ke, kar ki manta da ba dan Aisha ba da yanzu
ba ki kai haka ba a rayuwa. Dan haka ki kiyaye, dan ba ki da wannan right. Kuma da
a ka k'iran ki a waya kin d'aga ne?" Sau nawa a ka k'ira ki amma kin k'i d'aga
ƙarashe ma kashe wayar ki ka yi. Kuma kar ki d'auka ban san cewa ba yau ku ka dawo
ba, saboda naji maganar k'ananan ki a baground jiya da kika k'ira ni. Ace tun jiya
kike garin amma ki ka kasa zuwa duba ni sai yanzu, dan haka ki san matsayin ki
don't push me na yi abunda za mu yi dana sani."

"Eh ba ka fad'a min ba amma hakan ba shi ke nufin ban san rabuwar ku ba, kuma
wallahi ba zan yarda ba. Kar ka manta fa ita ce ta yi sandin zubewar cikin mu, in
kai ka manta to ni ban manta ba. Kuma ni ban ce ta taimaka min ba, ko da ita ko ba
ita zan kai haka. Dan haka ka dena fad'an ta yi min wani abu, in tana tunanin kai
mijinta ne to nima haka. Tana kai wa nan ta juya fita daga d'akin.

Duk ta ji maganar da suke kawai bata fito bane, dama ta basu wurin ne ba wai dan za
ta yi anfani da toilet ba. Jin shuru ba'a sake yin magana bane ya sa ta bud'e
k'ofar ta fita dan ta tabbata Husna tafiya ta yi shi ya sa ta ji shuru.

Ilai kuwa tana fita bata ganta ba sai Aliyu da ya d'aura hannun a kanshi da gani
ciwo yake mishi, d'an wannan maganar da ya yi da Husna har kanshi ya soma ciwo.

A hankali ta taka zuwa in da yake tare da d'aura hannunta a kanshi, jin kanshi ya
yi zafi sosai ne yasa ta sauki hannunta ba tare da ta ce mishi komai ba ta juya ta
d'auki basket d'in abincin da ta zo da shi.

Shi kuwa yana jin hannunta a kanshi ya bud'e idanunshi, ido ya zuba mata da kuma
karantar yanayen ta. Ya sani ko bata fad'a ba ya tabbata ta ji maganar su, wanda
kuma ba k'aramin kunyar ta ya ke ji ba. His so ashamed of himself, ya tabbata da
bai je ya auro Husna ba da duk ba su kai haka ba. Da duk wannan matsalolin ba su
tashi ba, da Husna ba za ta tsaya a gaban shi tana fada mishi magana a kan matarshi
ba. Da kuma ba abunda zai raba shi da matarsa matar son sa, komai ya lalace komai
ya b'ace. Amma in sha Allah ya yi alk'awari zai gyara kuskuren sa duk da ya san ba
zai tab'a goge wannan fentin bak'in cikin da ya shafa mata, amma zai yi k'ok'rin ya
ga ya gyara.

Sabon ya fad'a duniyar tunanin, har bai san lokacin da ta gama serving ta ja
kujerar da ke d'akin ta daura abincin a kai. Sai da ta yi tapping d'in shi tukan ya
dawo haiyacin shi.

"Me kake tunani ne haka?" Ta tambaye shi cikin muryar damuwa. Bai bata amsa ba sai
ma kanshi da ya sauke k'asa dan ba zai iya had'a ido da ita ba. "Ok! Tunda ba za ka
fad'a min ba gwara na tashi na koma gida dare na yi." Ta k'are da mik'ewa tsaye.

Da sauri ya rik'e hannunta tare da cewa. "Please kar ki tafi dan Allah." "In baka
son na tafi sai ka fad'a min tunanin me kake haka da har baka san mutum na kusa da
kai?"

"Sorry kawai ina tuna laifin da na miki ne, ina tunanin yanda zan nemi gafarar ki
ki manta da komai. Dan Allah Aisha ki yi hak'uri na mike alk'awarin hakan ba zai
tab'a faruwa ba, wannan ma tsautsayi ni da kuma kaddara.

Ko baki fad'a ba na sani bakya sona yanzu, kawai tilas ta miki a ka yi amma ba dan
kina Sona bane. Na sani koda baki fad'a ba ban canci yafiyar ki ba, shi ya sa ma ba
zan tilas ta miki sai kin yafe min ba. Duk hukuncin da kika ga ya yi miki ki d'auka
a kai na in har zaki huci haushin da kika ji a kai na."

"Please ka dai na irin wannan maganganun, kana karye min zuciya in kana fad'an
haka. Na yafe maka, na yafe maka Aliyu. Nima Ka yafe min duk abunda na maka a baya,
dan Allah na sani ba laifin ka bane. Haka k'addarar mu take kuma ba mu isa mu guje
mata ba, auren ka da Husna k'addarar mu ce. Rabo ya rantse a tsakanin ku wanda ko
da ba ta hanyar aure bace sai an samu wannan cikin dan haka me ya sa zan rik'e ka a
rai na?" Yes! Na yi k'arya in na ce ban ji ciwon abun ba, na ji zafi na ji ciwo Ali
wanda har na kusa kamuwa da ciwon zuciya. Amma Ka san abunda yafi min ciwo?" Kai ya
girgsa mata, sai da ta goge hawayen da suka wanke fuskar ta kafin ta dubi shi ido
cikin ido suke kallon juna kafin ta ce. "Abunda yafi min ciwo shi ne, duk zaman da
muka yi da kai, duk irin tsawon lokaci da muka zauna da kai Aliyu ace har zaka nemi
aure ka kasa gaya min har sai biki saura kwana biyu. "Kwana biyu ka fad'a min wai
zaka k'ara aure?" Ni zan hana ka aure ne in ka fad'a min?" A bar zan cen ba ka
fad'a min za ka k'ara aure a lokacin da ya kamata ba, me ya hana haka sanar dani
wanda za ka kamin a matsayin kishiya ba?" bani da wannan k'imar da darajar a
idanunka da sai washe garin biki, kuma ka rasa wa zaka kamin Aliyu sai k'anwata?"
Sai k'anwata Aliyu?" Yarinya da nake ganin ta kamar y'ata?" Duk wannan bai ishe ka
ba ka iya Bud'e baki ka k'ira ni da juya?" Dan kawai Allah bai bani haihu ba ka
k'ira ni da juya, abun bai tsaya a nan ba Ka dubi tsabar idonna ka ce ina maka
bak'in ciki har da cewa ni na zubar ma matarka ciki?"

Tana kaiwa nan ta fashe da kuka, bai hana ta kukun ba sai ma d'aura kanta a kirjin
shi da yayi yana bubbuga bayan ta. Ya san kukan da take nan shi zai sa ta huce, shi
zai ba zuciyarta sallama. Tunda ta amayra da dukan abunda me zuciyarta zata ji
sauk'i.

"Am sorry! Ban san da wani irin baki zan baki hak'uri ba, amma na san ni me laifi
ne a gurin ki Aisha. I promise you hakan ba zai sake faruwa ba, lallai ni me lafine
a gare ki. But amma ya na iya ba zan tab'a iya gujewa k'addarar da Allah ya rubuta
min."

"Ka bar maganar komai ya wuce, bana son kana kawo zancen, forget about the past let
focus on the present and think of the future."

"To na dai na tunda Gimbiya bata so." Kai ta kad'a mishi alamar ya yi kana ta
d'auki boil d'in ferfesun ta soma ba shi, sai da ta tabbatar ya ya k'oshe kafin ta
barshi haka nan.

Bud'e magun-gunan shi ta yi ta bashi ya sha kafin ta gyara mishi pillown bayan shi
kana ta gyara mishi kwanciya.

~~~~~~~~~~

Husna tana barin asibitin direct gidan lubna ta nufa domin tana buk'atar shawarar
ta dan ta san yanzu ita kad'ai zata iya shawo matsalar nan da ta taso mata, shi ya
sa ma ta zo da kanta dan zai fi a kan su yi maganar ta waya.

Amma sai dai koda ta isa gidan mai gadin gidan ya ce mata bata nan ta fita, koda ta
k'ira numbern ta bata d'aga ba ƙarashe dai baya ma shiga. Tsaki taja tare da
harararn mai gadi da ya hana ta shiga tayi kana ta nuna shi da yatsa ta ce. "Zaka
gani ai ba ni ka hana shiga ba?" Sai na sa ta kore ka daga aikin ma gaba d'aya sai
na ga ta tsiya." Ta k'are da jan kwafa kana ta juya ta koma cikin mota driver ya ja
suka bar wurin.

Lubna kuwa suna cikin aikata masha'ar su da sabon suger Daddy d'in ta da ta samu,
shi ya sa ma ta ba mai gadi umarnin duk wanda ya zo neman ta ya ce bata nan. Dan
bata son a b'ata mata shiri, fitar ta daga wanka kenan ta na mai goge ruwan kanta
da towel ta ji ringing d'in wayarta. Banza ta yi da wayar ta ci gaba da goge kanta
kafin ta nemi k'ananan Kaya ta sa , tana cikin fesa turare wayarta ta sake ringing,
idanuwan ta ta juya irin an dame ta d'in nan kafin ta taka zuwa bakin gado.

Guntun tsaki ta ja tare da kallon screen d'in wayar ba tare da ta d'aga ba, har
k'iran ya tsinke wani k'iran ya k'ara shigo wa amma bata d'aga ba. Zata aje wayar
kenan ta ji an fisgi wayar ta baya, da sauri ta juya tare da fuskantar sa.

"Kai dear, har ka tsorata ni." "Da wa kike waya?" wani dattijo Wanda a k'alla zai
kai shakara hamsin ya fad'a cikin had'a rai. "Kai baby, wai kishi kake?" To ba kawo
bani k'awata ta ce, ita ma bata san kana nan ba da ba zata k'ira ni a wannan
lokacin ba." Ta k'are maganar ne tare d'an harar shi wanda bai luru da ba.

Zai yi magana kenan wayar ta sake ringing,kashe wayar ya yi tare da d'aura ta a kan
bedside drawer kana ya ce. "Na sha fad'a miki, in muna tare bana son disturbance?"
"Na sani ka yi hak'uri yanzu ma na manta ne ban sa wayar a fly mode."
~~~~~~~~~~~~>

HUSNA.

Suna isa ta bud'e mota ta fita ba tare da ko kallon driver da ya ke magana ta wuce
ciki, tana shiga falo ta yi wulli da jakarta da hijabin ta. Sai faman zirya ta ke
cikin d'akin, gaba d'aya komai ya tushe mata. Tun a yanzu ya fara canja mata ina ga
in asirin ta ya tuno?" kuma a ce duk aikin da suka yi a kanshi da dan raba su amma
ace tun ba'a je ko ina ba aiki ya lalace?" Gashi wacce tasan zata iya taimakon ta
ma bata nan, dole ne ta yi duk yanda zata yi ta ga Aisha ta bar gidan a wannan
karon ma kuma na har abada. Da sauri ta d'auki wayarta, jiki na rawa ta soma k'iran
Baba Mariya. Bugu biyu ta d'aga bata tsaya wata gaisuwa ba soma mata bayanin abunda
ke faruwa.

Cikin tashin hankali ita ma Baba ta ce. "Shine baki fad'a min ba tun d'azu?" Ina ai
ba zai yu ba, gobe-goben nan zan tafi wurin malam a soma aiki kafin mu samu sauran
kud'in. Yanzu abunda nake so dake ki kwantar da hankalin ki, yanda ta fita ta bar
miki gidan, to haka wannan karon ma zata bar gidan." "Ni Wallahi Baba na fasa kar a
kore ta daga gidan, kawai dai ni bana son ya san ina da sa hannu cikin dukan abunda
ya faru." "Ke dalla shashasha me kika sani da zaki ce ba sai an fitar da ita ba,
kin d'auka zai baki muhimmanci ne in tana nan?" Ba za mu tab'a samun abunda muke so
ba in tana nan, da bata nan ma ya kike fama da shi?" Balle yanzu da ta dawo. Kuma
ke kin d'auka ta zo haka nan?" To bari ki ji, in har ke baki cire ta ba to ita zata
cire ki. Gashi dai kin gani da idonki, tun a yanzun ma ke nan." Dan haka gobe da
safe zan je wurin malam a san abun yi tun wuri."

P.42

Kamar yanda Baba Mariya ta ce d'in ne, safiya na yi ita da k'awarta Delu dallaliya
su ka tafi wurin Malamin ba su ko tsaya sun ci abincin safe ba suka tafi. Ba su
suka dawo ba sai Kusan k'arfe biyu na rana, domin wurin Malam d'in akwai nisa a can
wajan gari ya ke.

Suna isa babu b'ata lokaci suka samu ganin shi domin yau mutanen shi kad'an ne,
suna shiga ta zube gaban Malam ta fara koro mishi buk'atar ta.

Tana son a raba Aliyu da Aisha, tana son kuma su mallaki shi ta yanda sai abunda
suka ce mishi. Tana son a fitar da Aisha daga rayuwar sa gaba d'aya, ta yanda ko da
mai sunan ta ya ji zai tsani ta. Kuma a sa mishi tsoran Husna a ranshi ta yanda ko
kara ta a je to ba zai tsallake ba, hatta mahaifiyar shi ma tana son a yi aiki a
kanta ita ma so that ba za ta ba su matsala ba.

Sai da ta gama karo mishi buk'atar ta tas yana sauraron ta, kai ya kad'a tare da
buga k'asa sau uku, jim kad'an kuma ya goge ya sake wani. Sau hudu ya ke hakan amma
abu d'aya ya ke gani, shine auren ba mai iya raba auren nan. Kai karshe ma in sun
na ci sai sun ciri ta, to kuwa tsotsayi ne zai koma kan ma shek'iya. Domin kuwa a
yanda ya allon duban shi ya nuna mishi, taurari biyu ni had'e wurin d'aya ya yanda
ba mai raba su. Bayan su kuma k'ananan taurari ne ke zagaye da su, wanda kuma su ke
kare wadannan taurarin guda biyu. Ba wanda ya isa ya raba wadannan taurarin guda
biyu domin kuwa duk wanda ya yi k'ok'rin haka zai iya rasa rayuwar sa, dan wa anan
taurarin ba za su bar komai ya rab'e su saboda irin k'arfin da taurarin suke da.

Ganin in ya fad'a musu abunda ya gani da ba za su tab'a samun biyan buk'atar nan ta
su ba ƙarashe in ba su hak'ura da k'udinrin nan na su ba to kuwa tsotsayi ne zai
koma kan ma shek'iya, dan kuwa burin su na cire wannan agidan ba zai yu ba. Amma
kuma in har ya fito fili ya fad'a musu shi ne da hasara dan ya tabbata ko sun bar
nan d'in wani wurin za su je domin a yanda suke d'in nan ba za su hak'ura ba, hakan
ne ya yi na'am da shawarar da ya yanke. Tunda dai ko shi bai ci kud'in su ba wani
zai ci, dan haka mai hana shi tunda ga dama ta samu.

Kai ya kad'ai kafin ya dubi su ya ce."Tabas akwai aiki babba a gaban ku, sai kun
mik'e tsaye dan kuwa yarinyar nan ba haka nan ta koma gidan ba. Da shirin ta tazo
wannan Karon da kuwa asiri ta mishi shi ya sa ya maida ita babu shiri, kuma yanzu
haka shiri take babba kan y'ar ki. In ba'a gaugauta tsayar da aikin ta ba to y'ar
ki ce za ta fita daga gidan, yanzu haka ta riga da ta mallake shi saura kad'an
aikin ta ya cika ta cire y'ar ki a hoton."

"Ka yi hak'uri Malam, zan ba da ko nawa ne domin buk'ata ta ta biya, ka yi duk


yanda za ka yi ka rushe aikinta. Yanzu ga wannan ka rik'e sauran ma zan kawo kafin
Ka gama aikin, amma ina son a yi yanda zaka yi na ganin ta bar gidan."

"Kar ki damu yau d'in nan zan fara aiki a kanta duk da bokan ta babba ne amma bai
fi k'arfin mu ba, yanzu ga wannan ki ba y'ar ki ta zuba a ruwa ta bari sai ya yi
sati kafin ta yi wanka da shi. Wannan garin kuma turaren wuta za ta yi dashi a
d'akin ta, duk sanda ta san zai shigo b'angaren ta sai ta turare dak'inta.

Karb'a ta yi tare da yi mishi godeya kana suka bar wajan sa, koda ta isa gida ta
tarar da Husna har tazo tana jiran zuwan ta. Nan ta yi mata bayanin komai da Malam
ya yi mata kana ta d'aura da ce wa. "Sai ki yi hankali da komai kar ki je ki yi
shiririta da har aikin ya b'ace.

~~~~~~~~~~

For the next three weeks, Aisha stayed at the hospital caring for Aliyu.

Sosai Aisha take kula da shi, a asibiti ta ke kwana da safe kuma ta koma gida ta
had'a abinci duk da a na ka musu daga gidan Hajjiya hakan bai hana ta yi girka ta
kawo mishi ba, haka b'angaren kula da cin sa wankan sa da kuma shan maganinsa.

Husna ma ta kan lek'awa wani lokacin, a duk randa tazo asibitin sai sun yi fad'a da
shi shi ya sa ma bata cika zuwa asibitin ba. A d'ayan b'angaren kuma tana jiran
lokacin da aikin su zai ci ta rama dukkan abubuwan da ya ke mata, Baba Mariya tazo
ta duba shi, haka ma su Ummi ma sun zo.

Hajjiya ma ta zo sau biyu duba shi daga nan kuma bata sake zuwa ba domin Aisha na
iya k'ok'rin ta na kula da shi dan haka bata ga dalilin zuwa ba tunda yana samun
kulawa, haka Hamida da Balkisu ma na shigowa lokaci zuwa lokaci. Ganin komai ya
fara dai-daita ya fara samun lafiya yasa Zarah ma tattara kayan ta ta koma gida
saboda ta bar Yara su kad'ai da Baban su gashi za'a koma makaranta huta ya k'are.

=====Hospital=====

Night.

Bud'e k'ofar toilet ta yi tare da fito wa, d'aure take da d'an k'aramin towel da
bai wuce guiwar ta ba. Da gani daga wanka ta fito, domin jikin ta sai d'igan ruwa
ya ke. Hannunta kuma rik'e da d'an k'aramin towel da take goge kanta da shi, wurin
jakar kayan ta nufa tare da d'auko sleeping dress ta a je bakin godan kafin ta
cigaba da goge kan na ta.

"Let me help you with this." "Aliyu da shima fitar shi kenan daga toilet ya fad'a.
Zata yi magana ya k'wace towel d'in daga hannunta ya fara goge mata kan. "I can do
it myself." "Eh na san zaki iya ai, but I want to do it. Beside ni na caza miki
wanka da ruwan sanyi cikin daren nan." "Thank God da ka san haka." "Yeah na sani
amma ai ke kika jawo hakan, you are the one who seduce me with your body har na
kasa hak'uri. So ta ina ya zama laifi na dan Allah?" daga zuwa jinya kika sa d'an
mutane yin abunda bai shirya ba." "Innalillahi, ni na yi saducing d'in ka?" Ko kuma
kai ne baka da hak'uri. Da tuntuni ka samu lafiyar nan an sallame mu amma sai fama
ciwon kake kana maida aiki baya." "To ni na ce you should be sexy?" How do you
expect me to control myself dan Allah, nifa shi ya warkar da ni da wuri haka. Da
har yanzu ina kwanciye ba'a san ranar tashi wa ta ba, but don't lie oo. I know you
enjoyed it too, na san yanzu haka ma ba za ki k'i second round ba." Ya fad'a tare
da hura mata iska kunne. Ture shi ta yi tare da mik'ewa tsaye kana ta dube shi ta
ce. "Ba wani second round, na gaji dama kai nasan ba gajiya kake ba ko da kuwa za'a
kwana a na abu d'aya." "Dama a na gajiya da yi ne?" Don't talk like baky... Da
sauri ta d'aura hannunta a bakin shi kana tace. "Lokaci ya k'ure yanzu kusan k'arfe
biyu da wani abu fa." Daga haka ta d'auki kayan baccin ta ta rab'a daga gefen shi
ta shiga toilet, kai ya girgiza kafin ya ɗauki kayan shi ya sa kana ya haura kan
gado. Jim kad'an ta fito all dressed cikin kayan baccin ta, kan gadon ta hau ta
kwanta itama. Rungume ta baya ya yi tare da rik'e kungun ta gam kana ya ce. "Good
night."

Washe gari bayan sun idar da sallahr asuba bacci suka koma, ba su suka tashi ba sai
kusan k'arfe tara. Shima Dalilin zuwan Balkisu ne, ta ka mu su breakfast. Shi ya
fara tashi wa kafin ita ma ta tashi, da sauri ta dire daga kan ta nufi toilet da
gudu. Sai da ya ga shigar ta toilet tukun ya gyara rigar shi da gaba d'aya ta yi
squeezing kafin ya bud'e baki ya ce. "Yes come in."

Sai da ta ji ya bata damar shiga tukun ta turu k'ofa ta shiga. "Yaya ina kwana?" Ya
jikin?" "Lafiya, jiki ma alhamdulilah ina samu sauk'i. In sha Allah ma yau zamu
karb'i takardar sallama domin na samu lafiya." "Ma sha Allah haka muke so Allah ya
k'ara maka lafiya, eh batun sallama jiya Aunty Aisha ta fad'a min yau za'a sallame
ku. Come to think of it, ina take ban ganta ba?" Ko ta je d'auko wani abu ne a
gida?" Ta fad'a tare da raba idanuwan ta a d'akin.

Zai yi magana kenan ta bud'e k'ofar toilet ta fito. "Oh! Ashe kina nan na d'auka
kin koma gida ne?" "A'a na shiga toilet ne, yaushe kika zo?" "Ban d'ade da zuwa ba,
dama breakfast na kawo muku. Da ban gan ki ba na d'auka kin je kawo muku shi ne
ai." "A'a ban tafi ba, brush na shiga yi." "Ok! "So ya Hajjiya tana lafiya?"
"Lafiyan ta lau, yanzu ma ita ta yi urging d'ina na kawo muku breakfast d'in."
"Eyyah ki gaishe min da ita, sai mun zo gaishe ta."

"To! Ta ce daga haka suka yi shuru ba mai magana, Aliyu ne ya mik'e tsaye. "Kana
buk'atar wani abu ne?" Aisha ta tambaya. "No ina son na yi wanka ne." "Ok, tsaya
bari na had'a maka ruwan wanka sai ka shiga." Daga haka ta shiga toilet jim kad'an
ta fito. "You can go Know." "Ok thank you." Ya ce.

Shuru d'akin ya yi bayan shigar shi toilet, kowa da abunda ya ke tunani. tana lura
da yanayen Balkisun, tana ganin yanda ta ke yin attempt na yin magana sai kuma ta
fasa. Sau uku take take k'ok'rin bud'e baki ta yi magana sai kuma ta fasa, dan bata
san ya zata fara ta ina ma zata fara. Gashi in har bata amayar da da maganar ta
nemi yafe a wurin Aisha, bata tunanin zata samu kwanciyar hankali. Dan ta tabbata
duk wannan matsalolin gidan auren ta ta san alhak'i ne ke bibiyar ta in har bata
nemi yafer Aisha ta yafe mata ba, ba za ta ga farin ciki a gidan auren ta.

"Na'am Balkisu kina son wani abu ne?" Aisha ta tambaye ta ganin tana son magana
amma sai kuma ta yi shuru.

"Am..um..." "Me ya faru ne Balkisu?"


"Ki yi hak'uri ki yafe min dukan abinda nake miki a baya, nasan alhak'in ki ne ke
bibiya ta." "Me kike cewa ne Balkisu me kike min da har alhak'i na ke bibiyar ki?"

=====flashed back=====

"Kai hajara kin yi sa'ar sirka, a zamanin mu na yanzu nan da wuya ki samu sirka
kamar Aisha." Hajiya maimuna k'awar Hajjiya ta fad'a. "Gaskiyan ne maimuna, a
gaskiya na yi sa'ar sirka. Kin ga yarinya nan haka duk bayan kwana biyu sai tazo ta
gaishe da ni, bata zuwa haka nan, sai ta rik'e abu. Haka fa in tazo d'in nan bata
zama wuri d'aya sai ta nemi aiki ta yi,

Bari ma ki ga kayan da ta kamin."

Tsaki Balkisu taja tare rolling d'in idanuwan ta, ta tsani a ta ga a na yabon Aisha
tun ma ba Hajjiya. "Ke Balkisu je ki kawo kayan yana cikin wardrobe." Ba tare da
ta amsa mata ba ta nufi d'akin domin kawo kayan.

Ko da ta kawo aje wa ta yi tare da juya ta bar falon amma Hajjiya ta tsayar da ita.
"Ki bud'e mana." Haka nan ba dab ta so ba ta zauna ta kunce ledar tare da fitar da
atanfofi biyu sai kuma shadda ma d'aya.

"Kai ma sha Allah Hajara, kina nufin ita ka duk miki wadannan?" Cikin pride Hajjiya
ta ce. "Eh ita kamin su, nan gaba zan kai a min d'inki da ya da ce su." "Gaskiya
kam, kuma da gani ma ma su tsada ne ma." "Eh mana ai ke da gani kin san ma su tsada
ne."

*** *** ***

"Hamida k'ira min Aisha mu je ko tana Lafiya kwana biyu shuru ko tana lafiya?" "To
Hajjiya, gaskiya dai kam kwana biyu shuru bata zo ba. Da wai gobe zamu je mu duba
ta ma, amma bari na k'ira ta mu ji to." Hamida Ta fad'a tare da dailing numbern
Aisha. "Sorry Hajjiya ya k'i shiga bani kati, Auntie billy ina wayarki mu k'ira ta
na san kina da kati." Hararar ta Balkisu ta yi kafin ta ce. "Bani da waya." Dan
Allah mana Hajjiya ce ta ke son magana da ita ba ni ba." Sai da ta sake Harararn
ta da jan tsaki kafin ta yi layin Aisha, bugu biyu Aisha ta d'aga amma ko kafin ta
yi magana ta sauki wayar tare da saka ta a silence ta yanda ko da ta k'ira ba za su
sani ba. "Kin sa na k'ira ta a banza gashi ta kashe." "Ta kashe kuma?" Ya zata
kashe k'ara dai k'ira ta k'ila a rashin sani ne." "Hajjiya na fa fad'a miki, bata
kirki kawai tana nuna miki ita k'ware ce dan kawai ta gama da ke kamar yanda ta yi
da Yaya."

====Two days letter===

"Dan Allah Hajjiya ki bari in Hamida ta dawo daga makaranta ta je." "Bana son
shashanci fah Balkisu, tashi dan Allah ki je ki dubu mana ita. Ga wannan ki kai
mata." Ba dan ta so ba ta karb'i ledan da Hajjiya ke mik'o mata.

Har ta isa gidan sai zagin Aisha take a zuciyarta, ta rasa wani irin asiri ta yi wa
Hajjiya da sam bata ganin bak'in ta. Yanda Hajjiya ke nuna mata soyayya ko ita da
take y'ar ta bata nuna mata, ta gama da yayan ta yanzu kuma ta koma kan mahaifiyar
su. Da wannan sake-saken ta isa gidan, zata yi knocking kenan ta ji muryoyin su.

"Na d'auka ciki ne ma wallahi Batool, amma muna zuwa asibiti sun ce malaria and
typos ne. Baki ga irin farin cikin da muka shiga kafin mu tafi asibiti dan gaba
d'aya tunanin mu ciki ne, duk wannan rashin lafiyar nan na d'auka k'ila laulaye ne
irin na mata da ake fad'a. I wonder if I will ever get pregnant." "Kar ki ce haka
Aisha, haihuwar nan ta Allah ce fa. In lokaci ya yi za ki ga kin samu ciki kema so
kar ki sa damuwar rashin haihuwar nan."

Bata tsaya jin ƙarashen hirar su ba ta bar wurin, jiki na b'are ta shiga falon tana
mai k'walla wa Hajjiya k'ira.

"Hajjiya! Hajjiya!! Hajjiya!!!

"Ke lafiya kike k'walla min k'ira haka?" Me ya faru?" Ya na ga kin dawo da wuri
Aisha bata nan." "Ba dole ki gan ni da wuri ba." "Bata nan Kenan?" "Tana nan, amma
ba zaki yarda da abunda naji da kunnen na ba. Hajjiya ashe wai juya ce suka b'oye
miki, shi ya sa har yanzu bata samu ciki ba. Wai ashe har shi Yaya ya san da hakan
amma bai tab'a fad'a miki ba saboda an mallake shi." "Ke Balkisu bana son k'arya
fa, ina kika ji wannan maganar?" "Da kunne na na ji tana fad'a ma k'awarta, kuma
Hajjiya baki san wani abu ba. Kuma har zagin ki ta yi dan kawai dan na tambaye ta
dalilin ta na b'oye mana wannan babban abu, koda na aje mata ledar da kika ce na
kai mata. Cewa ta yi na zo na ɗauki tsiyar mu bata so." Nan ta dinga zigar Hajjiya
a kan Aisha tun bata yarda har ta fara gaskata maganar Balkisu, amma bata bar
shaidan ya rinjaye ta ba sai da ta fara ganin canji wurin Aisha. Ta dai na zuwa
gaishe ta kamar da, kuma koda tazo bata d'adewa. Nan Hajjiya ta fara zama kan
abunda Balkisu ke d'aura ta a kai, sai kuma na maganar mutune.

=====END Of FALSHED BACK====

"Dan Allah ki yi hak'uri, na san I wrong you. Wallahi sharrin shaidan ne da kuma
kishin ki da nake, bana jin dad'in yanda Hajjiya ki nuna miki soyayya. Na gane
kuskuren na dan Allah ki yafe min."

"Shuru Aisha ta yi ba tare da sanin me ta ce mata b, sai ido ta zuba mata ba tare
da cewa komai. "Ya wuce Balkisu na yafe miki, Allah ya yafe mana gaba d'aya."

P.43

"Na yafe miki Allah ya yafe mana gaba d'aya." Aisha ta fad'a. "Am so sorry, wallahi
na gane kuskure na. Am so ashamed of myself, indeed karma is real. Gashi tun ba'a
je ko ina ba ina ganin sakayya, ban san ya zan yi facing d'in Hajjiya ba if she
comes to know about this." "Kar ki damu Balkisu ba sai Hajjiya taji ba, ya wuce so
a barshi a hakan ko Yayan ki ba sai yaji." "Thank you."

Daga haka d'akin ya sake d'aukan shuru, can dai Balkisu ta mik'e tsaye."Zan wuce
sai mun sake zuwa duban shi." "Har zaki tafi?" Ki jira ya fita sai ki tafi ko?"
"A'a gwara na tafi, akwai inda nake son zuwa." "To shi kenan tunda kika ce haka,
amma tsaya bari na baki kwanikan jiya da a ka kawo abinci a ciki ki tafi da su.
Anjuma za'a sallame mu, so ba sai an kawo abinci ba." "To kawo su, yau dai za ku
koma gida, hai ku huta da zaman asibiti." "Ke dai bari, hai zamu huta da zaman
asibitin sai dai mu zo a sake duba shi lokaci zuwa lokaci kamar yanda suka ce.
Gashi ki gaida Hajjiya sai mun zo duba ta ita ma da gajiya, ki fad'a mata yau za'a
sallame." " To in sha Allah zata ji kuma zan fad'a mata." "Yawwa na gode a gaisa
gida."

Da haka suka yi sallama da Balkisu ta tafi Aisha kuma ta soma had'a kayan su. Ko
bayan da Aliyu ya fita suka yi breakfast Dr ya shigo ya sake duba shi kafin ya ba
su takardar sallama, sun yi murna sosai da kuma gode wa Allah subhanahu wa ta'ala
da ya bashi lafiya. Dan duk cikin su ba wanda ya sa ran zai rayu har ya samu lafiya
amma da ikon uban giji gashi ya warke har an sallame shi, su ko me za su yi in ban
da godeya ma Allah.

Da taimakon Habib suka cika sauran formalities kafin suka bar asibiti, jin shi ya
ke so free like a bird. After so many days a asibiti finally his been discharged
know, jin sa yake kamar kowa yanzu unlike da.

Habib ke tuk'e while Aliyu ke zaune a kujerar zaman banza Aisha kuma a baya, hira
suke jefi-jefi a tsakanin su wanda yawan hirar ma a kan aikin office ne da yake
Habib da Aliyu wurin aikin so d'aya.

Habib yana sauke su a gida ya juya ya wuce office ba tare da ya shiga ciki da su
ba, dalilin k'iran da a ka mishi na gaggawa amma ya yi alk'awarin zai shigo zuwa
anjuma ko gobe.

Suna shiga Aisha ta wuce part d'in ta direct ba tare da ko kallon part d'in Husna
ba ta shiga b'angaren ta, ta d'auka Aliyu part d'in Husna zai shiga amma sai ta ga
bai ko kalli hanyar part d'in ba. Da kamar zata yi magana amma sai ta yi shuru,
gwara ta yi minding business d'in ta.

Tana shiga bata zauna ba ta soma gyare-gyare domin a y'an kwanakin nan da bata gida
ko ina ya yi dust, sai da ta gyara ko ina sai kyali yake da kuma k'amshin turaren
wuta. Lokacin da ta gama har k'arfe d'aya ma ta yi dan haka ba ta zauna ba ta shiga
kitchen ta d'aura mu su abincin rana, ba wani abu mai nawi ta dafa ba kawai jalof
d'in taliya da ta ji kifi da kayan Had'i.

Ganin lokacin sallahn azahar har ya yi ne yasa ta rage wutar gas tare da koma d'aki
ta tashe shi daga bacci, kana ita ma ta shiga toilet ta d'auro alwalla.

Lokacin da ta fita bata tarar da shi a d'akin ba hakan ya tabbatar mata da yaje
masalaci, kitchen ta nufa tare da kashe gas d'in kana ta juya abincin a cooler tare
da d'auko drinks da cups ta aje a tire kana ta kai falo ta jera a dining table.

D'aki ta shiga ta bud'e wardrobe tare da d'auko hijabi ta sa kafin ta shinfid'a


darduma ta kabbara sallah, bayan idar da sallah fatiha ta shafa kafin ta mik'e ta
cire hijabin ta nannad'e ta maida shi wurin shi haka dardmar ma kafin ta Shiga
toilet domin watsa ruwa.

Cikin black and gold lashe ta shirya da a ka mishi d'inkin bubu wanda ba k'aramin
kyau ya yi mata ba, powder da lipstick ta shafa kana ta sa kwali a idonta. Ture ka
ga tsiya ta d'aura kana ta fesa turare da saka d'an kunne da sark'a, wayarta ta
d'auka tare da nufan falo ta zauna tana jiran zuwan sha.

**** ****

Aliyu kuwa yana dawo daga masalaci part d'in Husna ya nufa domin duba lafiyar ta,
ganin tun d'azu suka dawo amma bata lek'a ba. Da sallama a bakin shi ya turo k'ofa
ya shigo, zaune take kan kujera. Kallo take hankali kwanciye gaban ta kuma snacks
ne da TV remote, tana jin muryar shi ta suke fuska da harare-harare.

Sarai ya ga abunda take amma sai ya yi kamar bai gani ba dan in ya ce zai biye mata
to baza su wanye lafiya ba, yanzu ma ya zo ne dan sauki hakk'in da ke kanshi da ba
haka ba ba abunda zai kawo shi nan.

"Sannu ya kike fatan na same ki lafiya?" Aliyu da ya yi k'ok'rin kai zuciyarsa nesa
ya fad'a. Bata amsa gaisuwar da ya yi mata ba sai ma k'orafin da ta fara yi mishi
kamar koda yaushe. "Yanzu an min adalci kenan eh?" An min adalci kenan?" Ko dan an
ga ni yarinya ce shi ya sa za'a yi ta zalinta ta?" dan an gan ni k'arama sai a yi
ta min abinda a ka ga dama." "Me kike cewa ne Husna?" Waya zalince ki?" Me a ka yi
miki?"

"An min mana, an min komai ma. Dan Allah yanzu fisabililah an min adalci dan kawai
ka ga ni yarinya shi ya sa ka ke treating d'in na haka?" tunda ka yi rashin lafiyar
nan kullun-kullun Aisha ce ke zaune da kai a asibiti dare da rana. Yanzu ma da ka
dawo sai ka tafi part d'in ta while nan ya kamata ka zo."

"Wai ke Husna me yake damun ki ne?" Ke komai abun magana ne a wurin ki?"

Akwai wanda ya hana ki zama a asibiti ne, ko kuwa akwai wanda ya hana ki zuwa
tarbata da zaki ce ba'a miki adalci ba. Ke yanzu har kina da bakin cewa ba'a miki
adalci ba, fad'a min me kika tab'a yi a gidan nan mai kyau. Be it for me or aikin
gida, ina fad'a miki karki sa hak'uri na ya k'are, ke dai ko yaya ne sai kin san
yanda zaki b'ata ma mutum rai. Ban fa dade da zuwa daga asibiti ba baki zo kin
gaishe ne ba baki zo kin duba ni ba, duk ban yi k'orafi a kan hakan ba na zo da kai
na dan ganin lafiyar. Maimakon ki tambaye ni ya nake da jiki sai ma k'orafi da ki
ke min, in an yi magana ki ce ba'a miki adalci."

"Ni dama na sani ai duk abunda nake so ba za'a min ba, komai na yi ban yi dai-dai
ba dan kawai an ga ni k'arama ce."

Hannunshi ya d'aura Kan goshin shi tare da murzawa, d'an maganar nan da ya yi da
ita har kanshi ya fara ciwo. Ya rasa me yasa take haka, gaba d'aya wahalar ta bata
k'are wa.

"To yanzu me kike son a yi?"

"Me anfanin fad'a tunda ko na fad'i abinda nake so ba yi mishi za'a yi ba." "Husna
fad'i abinda zaki fad'a in kuma baki da shi to ni zan koma."

"Ok! In dai har kana son a zauna lafiya cikin gidan nan, to ka siya min mota nima
kamar yanda ita ma tana ke da Tata motar. And abu na ƙarashe tunda yanzu ni ce
babba to a yi changen part, ta dawo nan nima kuma in koma part d'in ta. Ni ta zo ta
samu a gidan dan haka ni ya kamata ta na zauna a wacan part d'in ba ita ba."

Sabon shock d'in da ya shiga ya ma kasa magana, lallai yau ya tabbata Husna bata da
hankali. Da kyar ya iya danne zuciyarsa wajan bai yi abinda zai kai shi da na sani.

"First of all ina son ki san bani da kud'in da zan siya miki mota, Kuma koda ina da
shi ba zan siya ba. Na biyu kuma ina son ki tashi daga mafarkin da kike na zaki
koma d'aya part d'in. Kuma da kike cewa zaki koma d'aya part d'in da wani kayan?"
Kina da kayan da zai d'auki part d'in?" Ko kin d'auka zaki d'auki way'an nan?" Ko
kin manta baki zo da kaya bane?" A gidan kika same ta dan haka ki kiyaye duk abunda
ya shafi matata, kar na sake jin wanna daga bakin ki in ba haka ba." Yana kai wa
nan ya bar falon cikin b'acin rai.

Lallai akwai matsala, akwai babbar matsala ma kuwa. Aikin malam Bai ci, dole ne ta
nemi wata hanya da ban tunda aikin Malam bai ci ba. Ina ba zata zauna haka nan ba
har komai ya bace, gashi tun ba'a je ko ina ba ya fara mata gorin kayan d'aki ina
ga nan gaba.

"Ina bazai yauwa ba." Ta fad'a da k'arfi tare da lalub'o wayarta.

**** ****

Aliyu koda ya fita ba direct ya nufi part d'in Aisha ba sai da ya tsaya ya sauko
daga b'acin ran da Husna ta k'unsa masa tukan, tun kafin ma ya shiga part d'in yaji
b'acin ransa ya kau. Yana shiga farin ciki ya mamaye zuciyarsa.

Tana ganin sa ta gane an b'ata mishi rai, duk da bai nuna ko a fuska ba hakan bai
hana ta fahimtar halin da yake ciki ba. Kama hannunshi ta yi tare da jawo shi zuwa
dining area, kujera ta ja ya zauna kafin ita ma ta zauna. Ruwa ta fara bashi ya sha
ya kwantar da hankalin shi kafin ta yi serving d'in su a plate d'aya suka fara
ci,suna ci suna hira da haka ta mantar da shi b'acin randa ya shigo da.
Da haka suka gama cin abincin ta tattara kwanikan ta maida kitchen kafin ta koma
falo, maganin shi ta fara bashi kafin ta zauna suka cigaba da hirara su ta ma
aurata.

Sai da lokacin sallah ya yi suka tashi, shi ya tafi masalaci ita kuma ta yi tata a
gida. Ta na idar wa ta shiga kitchen ta soma wanke-wanke kafin ta d'aura abinci
dare.

Ba shi ya shigo ba sai bayan sallahn Isha ya shigo, lokacin Aisha ta gama komai har
ta idar da sallah Isha. Abinci ya fara ci kafin ya yi wanka kana suka zauna suna
d'an hira har lokacin bacci ya yi dan haka suka koma d'aki domin bacci.

Washe gari ya shirya zuwa aiki, ba yanda Aisha ba ta yi da shi ya bari in ya d'an
samu k'arfen jikin shi sai ya koma amma ya ce ya gaji da zama wuri d'aya. Haka nan
ba dan ta so ya tafi aiki, haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya da dad'i da ba
dad'i. Zuwa lokacin Aliyu ya warke kamar bai tab'a jinya ba, ya koma aliyun shi na
da. Tsakanin shi da Husna kuma sai abunda ya cigaba, kullun-kullun sai anji kan su
kawai hak'uri yake da ita.

**** ****

Husna da lubna ne cikin garden d'in gidan lubna suna hira, hirar yanda za su fitar
da Aisha daga gidan suke.

"Na fad'a miki wannan Malam cutar mu ya yi aikin shi bai yi aiki ba, kawai kud'in
mu ya ce ya damfare mu. Amma Baba bata yarda ba wai Aisha ce ta b'ata mana aiki,
shi ya sa ma na zo wurin ki na san ba zan rasa ma fita ba?" Kina gani fa yanda
komai ya sauya daga zuwan ta, gaba d'aya ya canja min komai na yi ko na ce ban yi
dai-dai ba a wurin shi. Na fara yarda da maganar Baba a kan tana bin Boka, da ban
yar da ba A

amma yanzu na yarda. Kuma da gani bokan ta babban boka ne da ya iya aiki, ki ga
yanda take controling d'in shi. Ina son tun kafin ta fitar da ni daga gidan ni in
fitar da ita."

P.44

"calm down sweetheart, in dai wannan ne me sauk'i ne. But akwai risk, dan kuwa
babban abu ne wannan ba kamar wan can plan d'in ba. Kai let think about something
else, dan wannan is too risky. Amma kuma is the best plan, dan kuwa ba saki ba zata
fita daga zuciyarsa ne zai tsane ta, duk sanda ya ganta to da wannan bak'in fenti
zai ganta. Kuma kin ce yana da masifaffen kishi, so why not mu yi anfani da wannan
masifaffen kishi na shi to our own advantage."

"Nifa ban fahimce ki ba, me ya kawo kishi shi cikin wannan maganar?" Nifa kawai na
ce miki I want her out of the house at any cost, amma kina min maganar kishi a
nan."

"Fool! Har yanzu baki gane ba?" Sometimes I wonder ma ya a ka yi har nake k'awance
da ke ba kanki baya ja wallahi. Look! Kin ce yana da bala'in kishi, Just imagine,
ya zo ya samu wani k'ato da matarshi kuma a gidan shi, me kike tunanin zai faru?"

"Wow!wow! What a great idea, but ta ya kike tunanin zamu tafiyar da plan d'in?" I
mean, ina zamu samu wanda zai yi aikin?" Kuma taya kike tunanin Aisha zata kula shi
bayan ita ba kamar way'an nan matan bane da suke kula mazan waje?"

Tsaki Lubna taja tare da hararar Husna, ita fa wallahi ta fara gajiya da ita. Ace
mutum kwata-kwata kwakwalwarsa bata ja? Ji wani zance wai zata kula shi?" Bata
tab'a ganin dak'ik'iyar yarinya ba irin ta, komai sai an koya mata.

"Kamar ya zata kula shi?" Wai ke komai sai an fassara miki ne?" Abinda nake nufi a
nan shine, zamu nemi wanda zai shigo gidan a sirrin ce." Nan ta suma fad'a mata
yanda za su had'a plan d'in.

"Gaskiya wannan plan d'in ya yi babu k'arya, dana sani da tuntuni na zo wurin ki.
Gashi cikin sauk'i kin magance min matsala ta, babu Malam balle boka. Amma ina zamu
samu wanda zai mana aikin ba tare da an samu matsala ba?" Kuma kina ganin zamu iya
trusting d'in shi da plan d'in mu?" Kar fa ya je ya kobsa mana aiki ko kuma daga
baya ya zo yana blackmailing d'in mu." "Relax! Duk hakan ba zai faru ba, za mu
tsara komai ne kamar da gaskiye. Ko kina tantama ne?" Kar ki manta fa ko wancan
karon ma ni na kawo plan d'in kuma dai kin gani da idonki yanda komai ya tafi yanda
muke tsara, to wannan karon ma haka just trust me on this. Akwai wani aboki na haka
a na ce mishi Usman, na san zai yi aikin. Muna bashi d'an kud'in wiwi zai mana
aikin, kuma na yarda da shi koda aikin bai tafi dai-dai ba zai fad'i sunan mu ba."

"I trust you, kuma kar ki damu da kud'in da za'a bashi ni kawai buri na plan d'in
mu ya yi aiki." Nan suka cigaba da tsara plan d'in su.

**** ****

AISHA.

A hankali ta mik'e daga kan gado tare da nufan toilet, amma tana taku d'aya biyu ta
soma jin Jira na d'aukan ta. Da sauri ta suk'una k'asa ta zauna tare da rik'e kanta
da ke faman sara mata, ta rasa gane me yake damun ta cikin kwanakin nan. Jin ta
take wani iri, ga kuma wasu abubuwa da ta ke wanda da ba haka bane. Yawan jiri da
take ji da kuma yawan bacci musamman baccin rana, sai kuma Aman safiya. Kullum da
safe sai ta yi mai, ya zama mata kamar morning routine.

Da kyar ta iya mik'ewa tsaye rik'e da kanta, ruwa take son watsa a jiki amma jin
yanda cikin ta ke kukan yunwa yasa ta barin wakan sai ta cika cikin ta tukun. Tea
ta had'a tare da d'auko raguwar biredi da ya saura ta dawo falo, k'asan carpet ta
zauna ta soma ci. Ko gama shan tea d'in bata yi ba ta soma jin tashi war zuciya
kamar zata yi amai, da sauri ta d'aura hannu a baki da gudu ta shiga toilet ta soma
amai kamar zata fitar da hanjin cikin ta.

Kusan minti biyar take wuri d'aya bata motsa ba, a hankali ta kai hannu ta bud'e
tape ta soma watsa ma fuskar ta ruwa wanda ya taimaka mata sosai wurin dawowa dai-
dai. Jin abu mai d'umi ya sauka a pant d'in ta ne yasa ta dubawa, sosai ta yi
mamakin ganin period d'in ta ne ya zo bayan jinkirin kwana goma da ya yi. Ba ma
wannan ba, jinin d'an kad'an ne kuma ba normal jinin period bane. Is much lighter
than usual, kuma colourn shi ba ja ba shi ba fari ba hakan ya nuna is not normal.

Tsoro ne ya mamaye zuciyarta tunanin ko ta kamu da wata cutar, nan da nan ta had'a
gumi ta ko ina. No wonder take jin jiri da kuma yawan amai, hakan na nufin cutar
har ta yi nesa a jikin ta bata sani ba?" Da sauri ta nemo wayarta tare da danna wa
Aliyu k'ira amma bai d'aga ba, ganin bai d'aga ba yasa ta tura mishi sak'o kan zata
tafi asibiti bata da lafiya. Gwara taje ta san wace iriyar cuta ce ta kamata, cikin
mota ma ba irin tunanin da bata yi ba. Ta kawo cancer, HIV har ma da Corona, sabon
tsoron hannayen ta sai shaking suke.

Bayan kusan 1hour da ta yi na jiran layi finally ya zo kanta, in banda bugu ba


abunda zuciyarta ke yi. Tsoron shiga take, tsoron sanin me ke damun ta take. Sai da
ta ja dogon numfashi shi ta sauki tare da gyara nutsuwar da kuma shirya wa abinda
ke tunkaro ta kafin ta turo k'ofa ta shiga, the attending d'in mace ce da ba zata
haura shakara arbain ba.
After listening to Aisha symptoms, rubutu ta yi a farar takardar tare da mik'ewa
mata. "First, go get a urine test."

Karb'an takardar ta yi tare da tafiya yin test tare da zama jiran results d'in, 15
minutes letter ta shiga office d'in Dr bayan ta bata izinin zama. Duba results d'in
Dr ta yi kafin ta kad'ai ta ce. "Congratulations, kina da juna biyu." Shuru Aisha
ta yi tare da zuba wa bakin Dr dake magana ido na d'an lokaci sai kuma tafashe da
dariya. "Ina ga baki gani dai-dai bane ko kuma an yi mistake d'in result." "Aisha
Ali ko ba haka bane?" "Eh..eh... Aisha Ali." Ta fad'a cikin rawar murya dan yanzu
kam ta fara yarda da maganar Dr. "To kina da juna biyu, kuma har na tsawon sati
16." Cak ta mik'e tsaye tare da d'aura hannu a baki domin hana kukan da ke son
kub'uce mata, kallon Dr take ba ko kiftawa kamar wanda a ka ce ma ta nemi wata
mak'usa a tattare da ita. "K..ki..kina nufin ina da ciki?" Kai Dr ta kad'ai mata
tare da cewa. "Abinda ya sa baki gane ba saboda period da kike yi wanda hakan na
faruwa, zaki ga mace tana da ciki amma ba zata gane ba dalilin tana ganin period
wanda sai cikin ya fara girma wasu ke gane wa. Same thing with you, kawai dai baki
gane bane amma duk symptoms na ciki kina gani baki aje hankali bane ko kuma baki
kawo shi d'in bane."

Hannu ta d'aga sama ta soma godeya wa Allah da ya bata wannan babbar kyautar da
babu kamar ta, kyautar da ta dade take rok'an Allah ya bata. Kyautar da ta cire
tsammanin samu sai gashi Allah ya bata ita a lokacin da bata yi tsammani ba,
kyautar da dalilin rashin ta tasha gori daga mutane dayawa. Ciki har da mijinta da
kuma dangin shi, kyautar da dan bata da ita a ka yi mata sharrin ta yi bak'in ciki
da wacce ta samu har ta yi sana diyyar zubewar ta. Kyautar da sai dai ta ganta daga
nesa tana Sha'awar ta, sai gashi ita ma yau an wayi gari da samuwar wannan kyautar.
Sai kawai ta fashe da kuka, tabbas komai lokaci ne. Ita wai?" Ita ce ke da ciki?"
Gani take kamar a mafarki, da ba dan ciwon ciki da take ji da tace mafarki take.
Mafarkin da bata son tashi wa daga ba, mafarkin da zata so ta dauwama a ciki.

A hanyar ta ta dawo ne ta ga wasu yara da suka tashi daga islamiyya suka yi ma me


yoghurt caa a kai, wuri ta samu ta yi parking tare da sauki glass d'in mota ta zuba
wa yaran ido cikin farin ciki da annushuwa. Tunani ta fad'a ko ya nata yaron ko
yarinya will look like idan suka girma, k'ila su yi kama da ita, ko kuma mahaifin
su.

Tana ganin yanda wasu yaran ke siyan yoghurt wasu kuma sun tsaya gefi suna kallon
way'an da suke siya, jakarta ta d'auka tare da fita daga motar. Wurin mai sai da
yoghurt d'in ta nufa tare da tambayar shi nawa yoghurt d'in. "Akwai na hamsin da
y'an dari, wanne za'a baki Hajjiya?" Kai ta kad'ai mishi tare da tambayar shi nawa
ne gaba d'aya zata siya." Da sauri ya ce. "Na dubu uku da dari biyu ne." "Ok! Ta ce
tare da bud'e jakarta, dubu hudu ta mik'a mishi tare da cewa. "A rabawa yara sauran
canjin kuma na ka ne." "Godiya muke Hajjiya Allah ya saka ya cika miki burin ki na
alkhaire." "Amin! Ta ce tare da koma wa motar ta ta zauna, tana ganin yanda yaran
ki tsalle da ihun murna.

Bata tafi ba sai da ta ga duk yaran sun samu tukun, lokacin da ta isa gida magrib
har ta gabato.

Tun kafin ta shiga ciki ta gane Aliyu ya dawo dalilin motar shi da ta gani, Allah
Allah take ta shiga ta sanar da shi wannan daddad'an labarin. Gani take kamar bata
sauri dan ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gaban shi, tana shiga ta soma
baza ido, Can ta hango shi wurin dining table da gani abinci yake ci.

Aliyu kuwa suna cikin meeting ne lokacin da k'iran ta ya shigo wayarsa, kuma bai ga
sak'on da ta tura mishi da wuri ba. Bayan sun gama meeting ya koma office d'in shi
tukun ya bud'e wayar nan ya ga sak'on, ganin bashi da wani aiki da ya rage mishi
yau d'in yasa shi tattara kayan shi ya bar office ya kama hanyar gida. Sau biyu
yake k'iran layin ta bata d'aga ba, lokacin Aisha ta bar wayarta a mota ta fita
wurin mai sai da yoghurt.

Hakan ne ya tabbatar mishi da ta tafi asibitin, koda ya isa gida part d'in ta ya
fara zuwa ya ga bata nan.

Kitchen ya shiga domin sama wa kanshi abunda zai ci dan wata uban yunwa yake ji,
rabon shi da abinci tun da safe shi ma tea ne dama ya saba duk ranar girkin Husna
kullum cikin yunwa yake. Shi ya sa duk sanda girkin ta yazo Allah-Allah yake girkin
Aisha yazo, ganin babu abinci ga kuma yunwar da ke addabar shi ne ya sa shi d'auko
indomie.

Sabon yunwa taci k'arfin shi haka ya dafa ta babu albasa balle targu, d'auko plate
ya yi ya juya ta a ciki ya dawo falo dining area ya soma ci.

Yana cikin ci ne yaji an turo k'ofa a ka shigo, ko ba'a fad'a mishi ba ya san Aisha
ce ta dawo dan haka tura abincin ya yi gefi tare da mik'ewa tsaye yana tambayar ta
ya jikin ta kuma me likita ya ce yana damun ta?

Rungume shi ta yi tare da fashewa da kuka, kamo kafad'un ta ya yi tare da rik'e


hab'arta ya zuba fuskarta da gaba d'aya ta b'ace da ruwan hawaye ido. hankali ya
kai hannu ya soma goge mata fuskar tare da kad'ai mata kai alamun ta dai kuka. "Me
ya faru?" Wani abu a ka ce yake damun ki?" Me ya sa baki jira mun tafi tare ba?" Ya
soma jifa mata tambayoyi.

"Relax ba abinda ya same ni sai ma abun alkhaire da ya same mu." " Ya same mu?" Me
ya same mu?" Ya tambaya cikin rud'u Dan gaba d'aya bai gane ina maganar ta ta dusa
ba. "Yes alkhaire ne ya same mu abunda muka dade muke nema." Ganin har yanzu bai
gane bane ya sa ta jawo shi falo tare da zaunar da shi kan kujera kana ta mik'e
mishi takardar result, "takardar me wannan?" "Ka karanta mana." "Na karanta ai,
takardar waye?" Waye ya ke da ciki?" "Kai baka gane wa wallahi ka duba sunan ka
gani mana." Ta fad'a cikin k'osawa.

"No way!no way! You mean...?" "Yes abinda idon ka ya nuna maka haka ne ina da juna
biyu."

"Alhamdulilah! Alhamdulilah alhamdulilah, Allah mun gode ma." Ya fad'a tare da yin
sujjadar shukur.

Fad'in irin farin ciki da yake ciki ba zai musaltu ba, gaba d'aya ya cire ran zai
samu haihuwar nan amma sai gashi Allah ya bashi lokacin da bai yi tsammani ba.
Rungume ta ya yi ta baya tare da kai hannunshi kan cikin yana shafa a hankali.
"Thank you very much, thank you for making me a father. Thank you for everything
that you did for me, thank you for accepting me again. Na miki alk'awari I will
never disappoint you again, thank you for putting your trust in me again. Thank you
for being my baby's mama, Allah kawo su lafiya." "Amin King! Ta fad'a tare da
juyawa ta fuskance shi. "You know, just like you I wasn't expecting it. Na d'auka
ma wani ciwo gare ni ashe-ashe babyn ka ne, wai fa har na tsawon 16 weeks ba mu
sani ba." "16 weeks?" Kwana nawa Kenan?" "Kai ba fa kwana bane kai ma, kamar 4
months ko?" "Eh wata hudu ne, can't believe it. Shine wai ba wanda ya gane, yanzu
saura mana wata shida ki haifa min baby na?" "In sha Allah, ni yanzu ba abinda nake
zumud'in kamar na ga na fara zuwa antenatal Nima na ji yanda a ke ji." "Kar ki damu
in sha Allah ke ma zaki ji yanda a ke ji, ba antenatal ba harta labor room zaki
shiga ki fito lafiya ki bani labari." "Wai! Ina ruwan Aisha cikin labor room." Gaba
d'aya suka fashe dariya, nan dai suka cigaba da murnan samuwar cikin. Aliyu sai
tarairaiyar ta yake ko abincin dare ranar ya hana ta girki wa restaurant suka tafi,
dan ya san ko ya ce da Husna ta yi girkin ba yi zata yi ba ƙarashe ta b'ata mishi
rai a banza. Daren ranar ba su yi bacci ba, raba dare suke suna nafila da godiya wa
ma'aiki.
P.45

Washe gari ma haka ya hana ta shiga kitchen shi ya had'a musu breakfast da kuma
taya ta aikin gida, bai so zuwa aiki ba ranar dan so ya yi ya zauna da ita amma ba
ba yanda ya iya haka ya tafi aiki ranshi babu dad'i.

Hakan nan yake fita aiki da safe bayan ya taya ta da wasu aiyukan gida, yana gama
aiki da yanma zai dawo gida a cigaba daga inda a ka tsaya. Da haka kwanakin girkin
ta suka k'are girki ya koma hannun Husna, wanda ita ma tun safe yau take cikin
farin cikin dan kuwa yau za su yi maganin Aisha ta huta.

Dan haka yau da wuri ta tashi ta d'aura sanwar dare da kuma wasu aiyukan, tana gama
wa ta shiga bathroom ta yi wanka tare da yin gayu kana ta dawo falo zaman jiran
dawowar shi.

Shuru-shuru aliyu bai dawo ba har sallar magrib, hakan ya bata tabbacin yaje gidan
Hajjiya. Da da ne da sai hakan ya zamar musu abin magana, dan cewa zata yi dan
ranar girkin ta ne shi ya sa ya k'i zuwa ya tafi gidan Hajjiya. Amma da yake yau
akwai abunda take k'ulla wa bata yi wannan tunanin ba sai ma gode wa Allah da bai
zo da wurin ba ta yanda komai zai tafi dai-dai kamar yanda suka tsara, dan ta san
ba zai zo yanzu ba sai bayan sallan Isha wanda a lokacin sun gama tsara abunsu.

Ganin lokacin sallah ya yi ne ya sa ta tashi wa ta d'auro alwalla ta yi sallah,


tana idar wa ta cire hijabin ta nad'e dardumar ta aje a gefe. Wayarta ta d'auka
tare kunna data, nan ta ga sak'on Lubna da ta tura mata through WhatsApp.

[Hi husyy komai ya kammala na tura miki numbern shi, yana anguwar yanzu haka]

Tana karanta sak'on ta fara typing ita ma cikin sauri ta tura mata.

[No! Ki ce mishi ya tsaya sai na k'ira shi tukun, Aliyu bai dawo ba har yanzu. Ya
bari sai an shiga sallar Isha tukun, yanzu mai gadi yana bakin gate. Ya bari sai an
shiga sallah lokacin ba wanda zai ga shigowar shi]

[Kar ki damu ba zai shigo yanzu ba sai ya ji daga gare ki tukun shi ya sa na tura
miki numbern shi ai, yanzu dai ni na gama nawa aikin saura naki da na shi, in sha
Allah gobe da safe zamu tashi da labari mai dad'i] Lubna ta tura tare da sak'on
emoji a ƙarashe.

[In sha Allah, ni Wallahi ban san me ya sa ba nake jin tsoro. What if the plan
backfired?]

[Kin fara ko? Wai ke baki yarda dani bane? Kar ki manta fa ko wancan karon ma ni na
kawo a zubar da cikin, kuma dai kin gani da idon ki yanda komai ya waka na. To
wannan karon ma kamar yanda muka zubar da cikin muka lak'a mata shirri ita ta
zubar, haka yanzun ma komai zai tafi ne kamar yanda muka tsara. Karki damu ba zai
gane cewa muna da sa hannu a ciki ba kamar wancan karon]

[I trust you mana, kawai dai ina jin wani iri. Amma da kika yi wannan maganar sai
naji duk tsorona ya kau]

[Ke dai just relax ki ga magic]

Jin k'iraye-k'irayen sallahn Isha ne ya sa ta kashe data tare mik'ewa tsaya ta sa


hijabi ta fita compound d'in gidan, kamar yanda ta yi tunanin ne ta ga Baba mai
gadi yana d'auro alwalla zai tafi masalaci. Can nesa inda ba zai ganta ba ta tsaya
tare da jira ya gama ya fita, shi ko Baba mai gadi ba wai bai ganta ba ya ganta
sarai kawai dai bai mata magana bane dan ya san halin ta sarai dan ba k'aramin
aikin ta bane ta mishi rashin kunya yanzun nan.
Dan haka cigaba da d'aura alwalla shi ya yi, koda ya ya gama d'aura alwalla ya d'an
tsaya wai ko tana buk'atar wani abu ne a kawo mata. Amma ganin kamar akwai wanda
take jira ne ya sa shi fita dan har an kabbara sallah ma, tana ganin fitar shi ta
danna wa numbern da Lubna ta tura mata k'ira.

"Ka shigo babu kawo." Daga haka ta sauke wayar tare jiran zuwan shi, jim kad'an sai
ga knocking. Da sauri ta nufi gate ta bud'e mishi tare da nuna mishi part d'in
Aisha da yatsa kana tace. "Ga part d'in can, ka san me zaka yi ai?" "Eh kar ki damu
na san aiki na." "Good! Yanzu sai ka yi sauri mu je na nuna maka d'ayar k'ofar."
"Ok! Ya ce tare da bin bayan ta.

K'ofar kitchen baya inda dama ta nan Aisha ke fitar da dattin shara ta kawo shi dan
ta san ba inda zai shiga part d'in in ba ta wannan k'ofar, kamar yanda ta yi tunani
ne k'ofar a rufe take amma ba a sa sakata ba. "Zauna a nan da ka ga k'ira na ka san
mai zaka yi?" "Karki damu fa Hajiya na san aiki na." "Good sai ka ji ni." Tana
fad'an haka ta bar wurin ba tare da kowa ya gan ta ba,nan wurin shima ya zauna tare
da jiran k'iran ta.

Abunda ba su sani ba tun fitar Husna compound d'in gidan har zuwa lokacin da ta
bud'e ma mutumin k'ofar da kuma kai Shi part d'in Aisha duk a idon Hamza driver,
dan ya shiga bayi ne ya fita kenan zai d'auro alwalla ya ga abunda ke wakana.

~~~~~~~~~~

Aliyu ba shi ya dawo ba sai kusan k'arfe tara, part d'in Husna ya fara shiga. Koda
ya shiga bai ganta ba kuma bai damu da ya neme ta ba dan ya san baza ta wuce tana
d'aki ba, d'akinsa ya shiga ya watsa ruwa tare da saka kayan baccin kana ya fito
falo. Zama ya yi kan kujera kana ya k'walla mata k'ira, yana k'ok'rin sake k'iran
ta sai ga ta ta fito daga kitchen hannunta rik'e da tire d'in abinci.

Hankali ta taka har zuwa gaban shi ta aje abincin. "Me wannan?" "Kamar ya me
wannan?" Abinci ni mana, abincin da kafi so na dafa ma yau tuwo miyar kuka." "Toh!
Me kuma ya faru yau?" Dan na san haka kawai ba zaki yi tuwo ba sai da dalili, in ma
kud'i kike buk'ata to bani da su dan akwai abunda ke gaba." "Wato dai ni ba zan yi
abin kirki ba sai ina buk'atar wani abu a wurin ka?" "Na san ki ne ai, sai dai ki
yi hak'uri bani da kud'in da zan baki." Ya fad'a tare da mik'ewa tsaye. "Ya kuma ka
tashi baza ka ci bane?" "A'a a k'oshe nake yanzu haka amma ki bari zuwa anjuma zan
ci, ina zuwa bari na d'an lek'a Auntyn ki." Yana fad'an haka ya bar falon ba tare
da ya ji me zata ce ba, dariyar mugunta ta yi tare da tafa hannayen ta kana ta
d'auki wayarta da sauri ta tura ma Usman sak'o [his coming, sai ka yi shiri] tana
aika sak'on ta zauna Kan kujera tare da jiran abinda zai faru, duk da tana da
tabbacin plan d'in su zai tafi dai-dai amma ba tasan me ya sa ba zuciyarta sai
faman bugu take kamar wani abu zai faru da ita.

ALIYU.

Aliyu kuwa yana fita hanyar part d'in Aisha ya nufa, ya isa kenan zai tura k'ofa ya
ji muryar Hamza na k'iran shi wanda hakan ya saka shi tsayawa tare da fuskantar
shi. Shuru Hamza ya yi ba tare da ya san ya zai fad'a ma ogan shi abinda ya gani
d'azu ba.

"Na'am Hamza ya ka yi shuru kuma?" Akwai abinda ya faru ne da bana nan?" Ya


tambaya, d'an sosa kai ya yi kafin ya gyara muryar kana ya soma magana. "Dama
Alhaji akwai abinda na gani d'azu kuma ya tada min hankali shi ya sa na ce bara na
fad'a maka ban san ko ka sani ba." "Ina jin ka Hamza fad'a min me ya faru?" D'an
jim kad'an ya yi kafin ya ce. "Dama d'azu ne da ake shiga sallah na ga wani abu."
Sai kuma ya yi shuru dan tsoron abinda ka iya faruwa. "Ina sauraran ka Hamza fad'a
min me ya faru karka ji tsoro ba abunda zai faru." Aliyu da kamar ya shiga
zuciyarshi ya fad'a. Ajiyar zuciya ya sauke kana ya soma koro mishi bayanin abunda
ya gani d'azu.

"Ka tabbata abunda Ka fad'a min haka ne?" "E...eh yallabai." Ya fad'a cikin rawar
murya dan sosai ya tsorata da canja war ogan shi cikin lokaci guda, kai Aliyu ya
kad'ai tare da yi ma Hamza godiya kana ya tunkari part d'in cikin zafin nama.

Har zai tura handle d'in k'ofa ya tsaya cakk sai kuma ya juya ga Hamza dake bayan
shi ya ce. "Je ka tsaya ta k'ofar baya so ba zai samu hanyar guduwa ba." Sai da
yaga wuce warsa kana ya tura k'ofar amma yaji ta a kark'ame, hakan ya bashi
tabbacin k'ofar a kulle take ta ciki. Zagaya wa ya yi ta k'ofar baya nan ya ga
Hamza tsaye yana gadin k'ofar, da sauri ya matsa ya bashi hanya ya wuce ciki shi
kuma ya tsaya bakin k'ofar.

~~~~~~~

Yana ganin sak'on da ta tura mishi ya tashi da sauri ya tura k'ofar kitchen d'in a
hankali, sai da ya lek'a bai ga kowa ba tukun ya tura ya shiga ciki. Sai da ya
shiga ma ya tuna ashe bata fad'a mishi d'akin da zai shiga ba, tsaki yaja tare da
dana sanin karb'an aikin ma da ya yi. Ganin yana b'ata lokaci kuma bai gane d'akin
da zai shiga ba ya sa shi kawai cire rigar shi da wandon shi ya rage daga shi sai
boxer and singlet, wurge ya yi da kayan shi cikin falon kana ya hau saman staircase
kana ya zauna jiran me shigo wa.

ALIYU.

Yana shiga ya soma scanning d'in falo dan ganin d'an iskan da ya iya shigo mishi
gida gidan ma har muhallin iyalin shi, ganin baya nan ne yasa shi haura sama cikin
zafin nama. Tun kafin ya gama haurawa ya soma jin murya k'asa-k'asa wanda haka ya
ba shi tabbacin ya haura mishi sama, Aliyu bai gama shiga b'acin rai ba sai da yaga
guye d'in tsaye a bakin k'ofar d'akin Aisha kuma da gani ciki ya ke son shiga.

Hoton guy d'in babu kaya a jiki da ga shi sai boxer a d'akin matar shi ne ya yi
mishi flashing a idanu wanda ya k'ara ruruta wutar kishi da ke zuciyar shi, sabon
bak'in ciki da kuma b'acin rai da ya had'u mishi idon shi har ruwa-ruwa suke sai
kayi tunanin hawaye ne.

Cikin b'acin rai da kuma bak'ar zuciya ya soma takawa zuwa wurin guy d'in, ja da
baya guy d'in ya soma yi tare da neman wajan tserewa dan sosai ya tsorata da Aliyu
kuma in bai yi reacting da wuri ba to zai iya mutuwa a hannunshi. Aliyu bai bashi
wannan damar ba ya damk'i wuyar shi tare da had'a shi da bangon wuri tare da kai
mishi punch ta ko ina, so yake ya k'wace kansa ya gudu amma Aliyu bai bashi wannan
damar ba sai k'ara tightening shakar da ya yi mishi.

Hamza jin shuru tunda ogan shi ya shiga bai fito ba kuma bai ji wani motsi ba ya sa
shi yin shahada tare da shiga ciki dan ganin me ke faruwa, shigar shi kenan ya ga
abinda ke faruwa. Ai da sauri ya yi wurin tare da k'ok'rin b'anbare ogan shi daga
guy d'in kar yavje ya yi kisan kai amma Aliyu ko gizau sai ma hankad'e shi da ya yi
gefi.

"Oga Dan Allah kayi hak'uri a bi komai a hankali." Hamza da gaba d'aya ya rud'e bai
san me zai yi ba in ba rok'o, da kyar da rok'o magiya tukun Aliyu ya sau-sauta
rik'on da ya yi wa guyen tare da wurgi da shi. K'ara kamoshi Aliyu ya yi tare da
kai mishi wani naushin a fuska kafin ya ja shi kamar kayan wanki zuwa compound d'in
gidan, bai tsaya wata-wata ba ya soma kai mishi naushi ta ko ina tare da tambayar
shi wanda ya aiko shi. Duk da ya san Wanda ya turo shi, yana son ji daga bakin shi.
"Zan fad'a zan fad'a." Ya fad'a cikin wahalaliyar murya.

HUSNA.
Tun fitar Aliyu ta ke zaune cikin falon ba tare da ta iya taboka komai ba, sai safa
da marwa take cikin falon ba tare da ta san abunda ke faruwa a d'ayan part d'in ba.
Tsaki ta ja tare da kama handle d'in k'ofa a karo na barkate, so take ta je ta ga
abunda ke faru amma kuma tana tsoron abinda zata je ta tarar.

Tana cikin haka taji kamar muryar Aliyu a tsakar gidan, ai da sauri ta d'aga
labulen window tare da ganin abinda ke faruwa. K'irnjin ta dafa da k'arfi tare da
furta. "Inna lillahi wa Inna ilayhi raji'un, na shiga uku ni Husna me na ja wa
kaina." Da sauri ta saki labulen tare da nemo wayarta ta danna wa Lubna k'ira, bugu
biyu Lubna ta d'aga tare da cewa.

"Hello matar ali ya ake ci... Bata bari ta gama ba ta soma magana cikin tashin
hankali. "Lubna mun shiga uku komai ya b'ace, komai ya b'ace ya kobsa mana. Ga shi
can yana hannun Aliyu shi kenan asiri na ya tonu na shiga uku dan Allah ki taimake
ni." "Kamar ya ya kobsa mana?" Yanzu ina busy ina da bak'i ne zamu yi magana gobe."
Daga haka ta kashe wayar. "Hello! hello! Lubna!Lubna! Fashe wa da kuka tayi tare da
d'aura hannu a kai. "Na shiga uku kashi na ya bushe."

"Bai bushe ba nan gaba zai bushe." Ta ji muryarsa ta bayan ta, da sauri ta juya
tare da fuskantar shi. "Wallahi wallahi Allah sharrin shaidan ne." Ta fad'a cikin
muryar kuka, bai kulla ta ba sai ma hannu da ya mik'a mata da ta bashi wayar. B'oye
wayar ta yi a bayan ta tare girgiza mishi kai. "Dan Allah kiyi hak'uri ba zan sake
ba." Bai kulla ta ba sai ma k'wace wayar da ya yi daga hannunta ya shiga wurin
number's da massage's bai ga komai sai wata number da babu suna, Kai ya kad'a tare
da shiga WhatsApp wanda nan ya ga gaba d'aya chatting d'in da suka yi da Lubna
d'azu.

"Dan Allah kayi hak'uri wallahi bazan sake ba." " Ni me kika min da kike bani
hakuri?" Kanki kika yi wa dan haka ki daina bani hak'uri. Kin bani mamaki, kin bani
mamaki Husna ban tab'a zaton haka daga gare ki ba amma na gode wa Allah da ya nuna
min the kind person you are. Ashe dama haka kike?" Lallai baki cika y'ar halak ba,
da ace wani ne ya fad'a min zaki iya aikata abu irin haka da ba zan tab'a yarda ba
amma yau kin tabbatar min da cewa zaki iya yin fiya da haka ma. Wallahi na yi dana
sanin sanin ki a rayuwata, na yi dana sanin auren ki da na yi Husna. Na yi dana
sanin rik'e ki, na yi dana sanin sonki. Kin cuce ni kin kuma cuci kanki, ban tab'a
sanin haka kike ba. Ashe zaki iya yin kisa?" Eh mana kisa, zubar da ciki ai kisa
ne. Sanin kanki ne yanda nake son haihu amma haka kike rufe ido kika zubar da cikin
ba tare da tunanin halin da zan shiga ba, baki tsaya a nan ba kika lak'a ma matata
sharrin wai ita ta zubar miki da ciki. Har kuna ikirarin wai zaku d'aure ta, anya
Husna kina da zuciya a k'irnjin ki?" Bayan dukan wad'an nan abubuwan da kike yi bai
ishe ki ba kike son lak'a mata wani sharrin. To albishirin ki, kanki ki yi wa dan
likita ya tabbatar min da cewa ba za ki tab'a d'aukan ciki ba balle har ki haihu."
Zunmur ta mik'e tsaye tare da d'aura hannayen ta a kirji kafin ta bud'e baki cikin
rawar murya tace. "M..me..me kake nufi?" "Eh abinda kunnuwan ki suka ji ye miki ne,
Dr ya tabbatar min mahaifar ki ta lalace dan haka ba zaki iya d'aukan ciki ba kuma
ko kin d'auka ba zai zauna ba. Ban fad'a miki bane domin tausayen ki da nake je
wanda shi ya sa nake tolerating d'in ki har zuwa wannan lokacin, Amma yanzu komai
ya zo ƙarashe dan bazan iya zama dake ba Husna ki je gida na sake ki saki uku. Ki
tattara ina ki ina ki ki bar min gidana, kuma ina mai baki albishirin din matata
Aisha na d'auke da juna biyu nan da y'an watanni zata haifa min baby. Dama k'addara
ce ta had'a mu kuma ita ta rab'a mu, dan haka ki tattara ki bar min gida kar ki
Bari na sake ganin ko da inuwar ki ce kusa da gidan nan. Kuma in sha Allah zaki
gani, sai kin girbi abinda kika shuka." Yana kai wa nan ya wuce d'akinsa ya bar ta
nan wurin sai kuka take.

Tun a daren ta soma had'a kayan ta, daren ranar ko bacci ba ta yi ba sai tunani-
tunanin abubuwan da ya fad'a mata take. Duk cikin su ba wanda ya tayar mata da
hankali na kamar kalmar shi ta wai mahaifar ta ta lalace ba zata k'ara samun ciki
har ta haihu ba, abu na biyu kuma da ya tsaya mata a rai shine wai Aisha na da ciki
abinda ba zata tab'a yarda da shi ba. Amma kuma ta san Aliyu fa ba zai tab'a yi
mata k'arya ba balle ma irin wannan, shi kenan yanzu ta tashi a tutar babu? Babu
mijin babu mahaifa gashi wacce take son ganin ta fita ta bar mata gidan tana nan
sai ma ita ce ta zata bar mata gidan, bari ma na har abada tunda saki uku ya mata
ba maganar koma wa.

Yanzu shi kenan komai ya k'are? Shi kenan ita tashi a tutar babu? Yanzu me zata je
ta fad'a ma Baba Mariya? Lallai Lubna ta cuce ta, dama ta san maganin lalata
mahaifa ne ta bata? Allah-Allah take gare ya waye ta je gidan lubna a yi ta k'are,
dama ashe mak'iyiyar tace bata sani ba? Lallai gaskiyan mutune ne da suka ce duk
abunda babba ya hango yaro ko ya hau kan tirmi ba zai gani ba, gashi kuwa ta gani
da idonta. Ta bijire wa maganar mahaifiyar ta gashi ta biye wa k'awa ga inda ta
kawo ta, ta lalata mata mahaifar da kuma kashe mata aure. Ji take ina ma Lubna na
gaban ta yanzu da mai raba ta da ita sai Allah, sabon b'acen rai da haushi da kuma
tsoro ji take kamar zuciyarta zata faso k'irnjin ta fito. Shi kenan Lubna ta nakasa
ta, na kasa ma ta har abada. Yanzu ita waya zai sake auren ta, ta san ma Baba sai
ta kusan tsine mata in taji Aliyu ya sake ta. Sai kawai ta d'aura hannu a kai ta
fashe da kuka. Daren ranar bacci b'arawo ne ya kwashe ta...

P.46

Washe gari ta makara bata tashi da wuri ba sai kusan k'arfe tara da wani abu tukun
ta tashi, koda ta tashi bata tsaya yin sallah ba kawai fuskar ta wanke tare da
d'auko hijab ta bar gidan. Bakin hanya ta je ta taro mai napep ta dawo, ta lura da
irin kallon da mai gadi da Hamza ke jifan ta dashi tunda ta fito. Wanda ko ba'a
fad'a mata ba ta san sun san abinda ke faruwa, shi ya sa ma bata bi ta kan su ba
dan matsalar da ke gaban ta fi ta kallon da suke mata dan haka bata kula su ba ta
wuce cikin domin fito da akwatinan ta.

Akwatinan ta ringa janyowa tana fitowa da su ta loda wa mai napep da ta a je a


waje, duk abinda ta ke su Hamza na kallon ta amma ba wanda ya taimaka mata, Suna
kallon yanda take fito da kayan tana tirkar ninshi.

Saida ta gama loda komai a napep d'in kafin ta juya ta dubi su Hamza ta ce. "Sai me
dan baku taimaka min ba, an gaya muku ba zan iya bane?" Gashi ban da taimakon ku ma
na fitar da kayan, sai kuyi ta yi y'an wahala kawai a haka zaku k'are." Daga haka
ta juya ta shiga napep d'in da k'udirin za su zo da akori kura su kwashe kayan
kitchen, duk da kayan kitchen d'in ma Aisha ce tayi mata amma hakan ba zai hana su
kwashe wa ba. Kai har ma kayan d'akin sai sun kwashe dan ba za ta bari ba, in ya so
Aliyu ya d'aure su amma ba za su bari ba ko siyar wa sa yi suyi anfani da kud'in.

Muryar mai napep ne da yake tambayar ta inda za su ne ya dawo da ita daga duniyar
tunanin da ta fad'a. "Birget zamu fara zuwa zan karb'i sak'o ne sai mu wuce." Gwara
ta fara zuwa gidan lubna a yi ta ta k'are, dole ne ta fad'a mata dalilin ta na bata
maganin lalata mahaifa kan na zubar da ciki da ta fad'a.

Suna isa ta sauka tare da duban mai napep d'in kana tace." "Ka jira ni yanzu zan
dawo." "A'a Hajiya gaskiya ba zan iya jiran ki ba kawai ki bani kud'i na zan wuce."
"Haba mana kayi hak'uri yanzu zan fita ba zan dade ba kuma ba zan gudun maka da
kud'i ba ai tunda ga kayana a napep d'in ka." Tana fad'an haka ta dunfari gate d'in
gidan Lubna ta soma yi musu knocking na tashin hankali, da sauri mai gadi da ya
fito yana tambayar waye.

"Kai dalla Malam ka bud'e min k'ofa tun kafin ranka ya b'ace." Ta fad'a cikin
b'acin rai dan so kawai ya bud'e mata k'ofar ta je ta shak'i wuyar Lubna ko zata ji
sanyi a ranta. "Za ka bud'e k'ofar ko sai na karya ta?" Husna ta fad'a tare da kai
wa k'ofar wani bugun da ya sa mai gadi bud'e k'ofar babu shiri, bata tsaya ya gama
bud'e k'ofar ba ta tura da k'arfe ta shiga ba tare da ko kulla mai gadin da ta buge
mishi k'afa da k'ofar ba.

"Lubna! Lubna!! Lubna!!! Ki fito nan shegiya maciya amana y'ar iska, Allah sai ya
saka min karuwa kawai. Husna ta fad'a tare da dunfarar Lubna dake zaune a gardin
gaban ta kuma kayan fruit tana ci d'ayan hannunta kuma wayarta ce tana chatting ba
tare ta damu da ihun da Husna ke mata a kai ba.

"Wato kin mai da ni mahaukaciya ma ko?" ba dole ki maida ni mahaukaciya ba tunda


kin riga da kin cuce ne Allah sai ya saka min muguwa kawai azzaluma." Tsaki Lubna
taja tare da yi ma Husna kallon sama da k'asa kafin kuma ta k'ara jan wani tsaki.

"Wai me ya faru ne da ki ka zo kina wani damun safiya ta?" So sai me dan ya sake
ki?" Ai ba shine ƙarashen rayuwar ki ba, ki kwantar da hankalin ki ki zo na had'a
ki da alhazai da suka fishi kud'i da kuma mik'amai. Ke fa full option ce, kina da
kyaun ki kuma alhamdulilah diri ma Allah ya baki babu laifi so just come zan had'a
ki da manya-manyan ma su kud'i ke ma ki yagi rabon ki yarinya I don't know why kike
wani tada jijiyar wuya ba. Shima Aliyun da kike wani hayagaga a kai dan kud'in shi
kika aure shi, dan haka indai kud'i ne zaki sa.... Tassss,,,,tasss,,,,tasss Husna
ta d'auke ta da maroka da yasa ta yin taga-taga ta kusa fad'i.

"Ni kike cewa na zo ki had'a ni da alhazai?" Na ce ni kike cewa na zo zaki had'a ni


da alhazai na samu kud'i?" Ki kalle ni da kyau na miki kama da karuwa?" Na miki
kama da karuwa da zaki ce min na zo ki had'a da maza?" To bari ki ji na fad'a miki,
ni Husna ba karuwa bace kuma koda zan yi yawo tsirara ba zan tab'a aikata zina ba.
Na zo nan ni na ji dalilin ki na bani maganin lalata mahaifa kan na zubar da ciki
da ki ka fad'a, me na miki da zaki saka min da irin wannan muguntar?" Ina zaman-
zamana kike zo min da shawarar na zubar da cikin ashe dama kina da wata manufa a
kaina maciya amana kawai."

"Wait tsaya-tsaya ban gane kina zaman-zaman ki ba?" Da na baki shawarar bindiga na
d'aura a kanki da sai kin bi shawara ta?" Kuma maganin ma da na baki ban fad'a miki
illar sa in an sha overdose ba?" amma baki ji kin je kinyi abinda kanki ya gaya
miki. Sai yanzu da komai ya lalace zaki zo min da wata banzar magana?" Lokacin da
aikin ya tafi dai-dai Aisha ta bar gidan me ya sa ba ki zo kin gaya min magana ba
sai yanzu da kika lalata komai da kanki?" Kuma da kike kice min maciya amana akwai
maciya amana da ta kai ki ne?" Na ce akwai maciya amana da ta kai ki?" Ai in ana
neman maciya amana a zo wurin ki tunda har kika iya auren mijin yayar ki, kuma har
kike da mind d'in wai ki fitar da ita daga gidan mijinta. Ke ba'a ce miki maciya
amana ba sai ni?" Kin d'auka Allah zai barki haka ne?" To bara ki ji, yanzu kika
fara ganin sakayya. Kuma da kike cewa ni karuwa ce eh ni karuwa ce kuma am proud of
it tunda ban ci amanar yayata ba, ban aure mijin y'ar uwar ta ba. Ke yanzu ko kunya
bakya ji?" Matar da ta taimake ki da y'an uwan ki, ta rik'e ki kamar y'arta ta baki
yarda kamar k'anwarta da suka fito ciki d'aya. Ta kula da ke ta saka ki a makaranta
ta yi miki komai a rayuwar nan amma da me kuka saka mata ke da mahaifiyar ki?"
Auren mijinta, ke koda maza sun k'are wallahi ni Lubna bazan tab'a auren mijinta ba
balle har na soma bin bokaye dan cire ta daga gidan. Ai gashi yanzu kun gani da
idonku, maimakon ki rik'e maraicin ki ki kama mijin da a ka bi bokaye tukun a ka
samu ki rufa wa kanki asiri ku zauna lafiya amma a'a ke da mahaifiyar ki da yake
babu tsoron Allah a zuciyar ku ko in ce rashin godiyar Allah kun rantse sai kun
fitar da ita ai gashi Allah ya nuna muku ikon sa. Sai aje gida a cigaba da cin
tuwon dawa da miyar kuka, in kuma zaki zo a d'an taimaka miki ni ma to in kuma kin
raina sai a je a cigaba da talla." Ta k'are maganar ne da dariyar shek'iyanci.

Tabbas ta san maganganun Lubna gaskiya ne amma kuma bashi ke nufin ta ci banza ba,
dan ba zata ta yarda ba. Ta lalata mata mahaifa da kuma kashe mata aure yanzu kuma
take fad'a mata way'an nan maganganun? Ta d'auka by just saying that zata yi sanyi
ta bar ta ne bayan ta gama cutar ta? Ina ba zai yu ba "yau ko ni ko ita." Ta fad'a
tare da cakumo wuyar rigar Lubna suka soma kokawa, abu kamar wasa ya zama babba.
Sai da suka ka yi wa juna lilis ko wace ta ji jiki tukun suka rabo dan kansu, gaba
d'ayan su sun yi laushi dan ba laifi sun dambatu.

Shi ko mai gadi yana can bakin gate yana kallon dukkan abinda ke faruwa amma bai je
ya raba su ba, dan ya san ko ya sa baki ba rabuwar za su yi ba su ne d'aya yanzu
nan za su iya juyowa kanshi su juya mishi kwandon rashin mutunci dan ba tarbiyya ne
da su. Gashi bugun da Husna ta yi mishi a k'afa ma har yanzu zugi yake mishi, dan
haka zama kan benci ya yi tare da kallon live wrestling.

Husna nuna Lubna da yatsa ta yi kafin tace. "Wallahi zaki gani, yanda kika ci amana
ta kika cuce ni kema sai an miki. Karuwa munafuka mai fuska biyu kawai ƙarashen ki
ba zai yi kyau Lubna, ba dai karuwanci kika sa a gaba ba?" You will see."

"Eh karuwanci na sa a gaba, duk karuwanci na ina da d'an da ke k'ira na Mama ke


fa?" Har abada sai dai kiji a mak'ota, banza shashasha kawai. Ki fitar min daga
gida kar na sake ganin k'afar ki koda bakin gate ne tunda ba Baballe bani ya siya
min ba."

Sai kuma ta juya ga mai gadi tace. "Wallahi ka kuskura na ganta a gidan nan to a
bakin aikin." Daga haka ta d'auki wayarta da kuma plate d'in fruit d'in ta wuce
cikin gida ta bar Husna tsaye a wurin, goge hawayen fuskar ta yi kafin ta nemo
takalman ta da suka fito daga k'afar ta lokacin fad'a ta sa kana ta juya ta nufi
gate.

Koda ta fita taga wayam babu mai napep ba alamar shi, kai ta fara juya tana dube-
dube ko zata ganshi amma shuru layin yake ba alamar mai napep. Hannu ta d'aura kai
tare da fasa ihu da ya sa mai gadi bud'e k'ofar da sauri domin duba abinda ya same
ta, tsaki ya ja lokacin da yaga lafiyar ta k'alau ba abinda ya same ta. Har zai
rufe k'ofar ta tsayar da shi da cewa.

"Dan Allah Baba baka ga mai napep da muka zo tare ba?" Sai da ya yi mata kallon
kyama da kuma tsana kafin ya bud'e baki ya ce. "Ya je koyan tarbiyya." Daga haka ya
banko k'ofar da k'arfi tare da sa sakata.

Zaman dirshen ta yi a wurin tare da fashe wa da kuku, abu goma da ashirin da wani
zata ji? Gaba ki d'aya suturar ta ya tattara ya yi gaba ita, k'aryar ta da mutuncin
ta tana shiga cikin k'awaye duk silar kayan ce. Kayan da take son ta lallab'a su
tana shiga mai kyau har zuwa lokacin da zata samu wani mijin da yafi Aliyu kyau da
kud'i amma tsinannan mai napep d'in ya gudun mata da su.

P.47

Ba zata ce ga iya adadin lokacin da ta d'auka a k'ofar gidan ba, zafin ranar da a
ke kwalla wa ne ya sa ta tashiwa tare da kakkabe kayan ta kana ta soma takawa zuwa
bakin hanya ta tari wani napep zuwa gidan su. Lokaci zuwa lokaci ta ke sa hannu
tana goge kwallar da ke zubo mata, sai yanzu wani tsoro da fargaban abinda zata je
ta tarar a gidan su ya dirar mata.

Dari biyar ta ba mai napep ta wuce ciki da sallamar ta da Kausar ta amsa mata, tana
zaune a bakin k'ofar d'aki tana tsintar shinkafa. Ganin halin da Husna ta shigo
ciki ne ya sa ta aje farantin shinkafar tare da mik'ewa tsaye. "Auntie?" Ya na
ganki haka?" Me ya faru?" Kunyi fad'a da Auntie Aisha ne na ganki haka?" Dubi jikin
ki duk yakushi ga kuma yagaggen hijabi." Kausar ta jero mata way'an nan tambayoyin
da ya sa Baba Mariya fitowa daga d'aki tare da tambayar ta abinda ke faruwa? wuri
Husna ta samu ta zauna ba tare da ta amsa tambayoyin da su ke mata ba. To me zata
ce musu? Auren ta kaso ko lalata mahaifar a ka yi? ko kuma kayan ta da wannan
tsinannan mai napep ya gudun mata da su?

"Ya sake ni Baba, Aliyu ya sake ni." Ta fad'a tare da share hawayen dake zubo
mata." Hannu Baba ta d'aura a k'irji tare da ambaton "Innalillahi wa inna ilayhi
raji'un, Husna me na ke ji haka?" Me ya faru?" Me kika mishi da zafi haka da har ya
kai da saki?" Shuru Husna ta yi ba tare da sanin ta ina zata fara amsa tambayoyin
ta ba, abinda ta sani shine komai ya k'are musu. Duk wata tak'amar ta da jiji da
kai da take duk dalilin auren Aliyu da ke kanta ne, yanzu kuma da ya sake ta, komai
ya k'are tunda ba maganar koma wa.

Kai koda ba saki uku ya mata ba, ta tabbata Aliyu ba zai maida ita ba saboda
Hajiyarsa ba zata bari ba. Sai yanzu take danasanin duk abubuwan da ta aikata, ina
ma zata iya maida agogo baya. Da ta gyara dukkan kura-kuran ta, Ina ma lokaci zai
koma baya ta gyara alak'ar ta da Aisha, ina ma lokaci zai koma baya lokacin da ta
had'u da Lubna a saloon. Ina ma lokaci zai koma baya ta gyara kuskuren da ta yi na
biye ma Lubna har ta zubar da kyautar da Allah ya yi mata, ina ma lokaci zai koma
bayan da take zaune da Aisha.

Lokacin da take cikin kwanciyar hankali, lokacin da take zaune da y'ar uwar ta
Lafiya. Lokacin da bata da tension d'in a san ta aure mijin y'ar uwar ta, lokacin
da bata da tension d'in asirin ta zai iya tunowa. Lokacin da bata da wani guilt
d'in ta kashe rai balle har ta san wannan mummunar labarin wai ba zata tab'a iya
zama uwa ba, lokacin da bata da wani buri da ya wuce ta yi karatu ta zama wani abu
a rayuwar ta yanda zata taimaka wa mahaifiyar ta da kuma y'an uwan ta.

Shin me auren Aliyu ya tsinana mata? Ba abinda auren shi ya tsinana mata banda
fargaba da tashin hankali da kusan kullun take ciki, sai kuma kan family da yaraba.
Tabbas auren Aliyu ba alkhairi bane, duk abinda ta hango zata samu kafin auren ba
shi ta tarar ba. Banda cin amana da kuma butulci da ta yi har da sab'awa Allah, ta
yi shirka, ta kashe rai, ta kuma shiga tsakanin ma'aurata.

Ma aurantan da suka yi mata komai a rayuwar nan, da ba dan su ba da yanzu wani


zancan a ke.

Shin ina zata kai duk wannan zunubin da ke wuyar ta? Anya Allah zai yafe mata?
Lallai ta aikata abubuwa da dama da sai yanzu take ganin illar su, shin ya a ka yi
ta biye wa son zuciya har ta aikata way'an nan abubuwan? Tabbas auren ta da Aliyu
yana cikin k'addarar su ne amma kuma har da son zuciya, son duniya ya rufe musu ido
da har suka manta irin alkairin Aisha gare su.

Lallai gaskiyan Hausawa ne da suka ce d'an Adam ba abun yarda bane, wai taya a ka
yi har ta yarda a ka yi way'an nan abubuwan da ita? Anya Aisha zata iya yafe mata?
Yanzu ta ina ma zata fara neman yafiyar ta? lallai bata ciki y'ar halak ba. Dan
d'an halak baya manta alkairi komai k'ank'antar sa, sai yanzu komai yake replaying
a kwakwalwar.

Kuku take sosai, kukun da ke fitowa daga can k'asan zuciyarta. Kukun da ba zai
anfani da ta da komai ba a yanzu, kukun da ke da ma'anoni dayawa. Kukun da a
k'arkashin sa akwai, nadama,danasani,da kuma tuba. Ji take gaba d'aya ta tsani
rayuwar ta, ina ma ba'a haife ta ba. Da duk haka bata faru ba, da bata ga wannan
bak'ar ranar ba.

"Husna!Husna!! Husna!!! Baba ta k'ira sunan ta cikin tashin hankali tare da


jijjigata. "Dan Allah aunty ki dai na wannan kukun komai ya yi zafi maganin sa
Allah, haka Allah ya k'addara dan haka ba yanda muka iya. Ki yi hak'uri in sha
Allah everything will be alright, ai bashi ne ƙarashen maza ba dan ya sake ki hakan
ba yana nufin ba zaki samu wani mijin ki yi aure ba." Kausar ta fad'a cikin muryar
kuku ganin Husna cikin wannan halin ba k'aramin tayar mata da hankali ya yi ba,
rungume ta ta yi tare da bubbuga bayan ta.

"Kiyi hak'uri Auntie ki dai na wannan kukun nan haka kina k'ara tayar mana da
hankali ne." Zuwa lokacin ta daina kukun sai ajiyar zuciya da take faman sauke wa,
goge hawayen da ke fuskar ta yi tare da fuskantar Baba da tun d'azu ta kasa magana
saboda damuwa. Kana ta soma ba su labarin komai da ya faru, tun daga zubewar cikin
da kuma irin tsiyar da ta dinga tsulawa a gidan da kuma dalilin sakin da Aliyu ya
yi mata bata b'oye musu komai. K'ara fashe da kuka ta yi tare da duba Mariya tana
cewa. "Duk ke ce sila, ke ce silar komai da ke faruwa. Kin cuce ni kin cuce
rayuwarta Baba." Ta k'are zancen da tashiwa ta shiga d'aki tare da banko k'ofar ta
sa sakata, tashiwa Baba Mariya ta yi cikin tashin hankalin abinda Husna ta fad'a
mata da nufin bin bayan ta amma Kausar ta dagatar da ita da cewa. "Ki barta tana
buk'atar lokaci, karki d'auki magana ta da zafi."

~~~~ ~~~~

B'angaren Aliyu kuwa gari na waye wa ya bar gidan gaba d'aya ji yake his
suffocating so kawai ya clearing mind d'in shi, dan haka tun da ya fita sallar
asuba bai koma gida ba. Strolling ya shiga yi da tunani kala-kala, tunanin abubawan
da suka faru cikin shakara d'aya da rabin nan yake.

Bai tab'a tsammanin haka abubuwa za su kasance ba, bai tab'a kawo rabuwar shi da
Husna nan kusa ba. But everything happened for the best, finally zasu yi rayuwa
cikin kwanciyar hankali kamar da babu fitina da munafunci. Auren Husna kaddarar sa
ce ko ya ce kaddarar su ce gaba d'aya, haka Allah ya k'addara sai sun zauna tare a
matsayin ma'aurata na d'an wani lokaci. Yanzu burin shi shine Allah ya sauke matar
shi lafiya kuma su kasance cikin farin ciki da kuma k'oshin lafiya, everything that
happens is in the past. Zai yi iya k'ok'arin shi na ganin ya manta da abubuwan da
suka faru haka ma Aisha, things have changed nan ba da jimawa ba za su zama iyaye.
Dan haka, they need to forget their past and focus on their future.

~~~~~~

Koda ya koma gida darect part d'in Aisha ya nufa da tunani kala-kala a kanshi, bai
same ta a falo ba dan haka ya haura sama d'akin ta. Koda ya shiga bai ganta a
d'akin ba amma ya ji k'arar zuban ruwa a bathroom hakan ya bashi tabbacin tana
wanka, wuri ya samu a bakin gado ya zaune tare da jiran fitowar ta.

"A'a Babe yaushe ka shigo ban sani ba?" Aisha da fitowar ta daga bathroom kenan ta
tambaya. "Sorry kina wanka lokacin da na shigo, shi ya sa na zaune jiran fitar ki
na gana da little bundle dan na yi missing d'in shi." "Hmmm kamar da gaskiye." Ta
fad'a tare da zama kusa da shi. "Ke ma kin san ba zan iya yin awa d'aya ba tare da
naji lafiyan sa da ta mummyn sa ba ko?" "Ba wani nan ba ma son dad'in baki, haka
jiya da daddare mu ka yi ta zaman jiran ka ba ka zo ba." "Eyyah am so sorry for
that amma ai na zo kuna bacci." Ya fad'a cikin d'acin murya.

"Yauwa ka tuna min, ban san me ya sa ba amma kamar b'arayi sun shigo mana jiya.
Saboda da na tashi da safe na tarar da falon duk a wargaje everything is scattered,
amma kuma da na duba nothing is missing. Ko ka san me ya faru?" Ta jefo mishi
tambayar unexpected tare da kura mishi ido, in-ina ya soma yi dan bai san ya zai
fad'a mata wannan bak'in labarin ba dan gaba d'aya he feels ashamed.

"N..no.. ban.. san komai ba." Ya fad'a a da burje wanda hakan ya sa ta fara
suspecting wani abu ya faru amma baya son fad'a mata. "Na san dai k'arya ba halin
ka bane Aliyu, dan haka gaya min me ke faru?" Ta fad'a with serious tons, ido ya
zuba mata ba tare da sanin ta ina ma zai fara ba, abun ya yi nawi amma kuma dole ne
ta sani dan ko ba yanzu ba taza sani wata rana.

Shuru ya yi na d'an wani lokaci kafin ya d'an gyara muryar kana ya fara bata
labarin komai, shuru ya yi lokacin da ya gama bata labarin tare zuba mata ido dan
ganin reaction d'in ta. Ya sani koda bata fad'a ba she's hurt, and his ready to
accept ko wani irin hukunci da zata yanke tunda shi ne sila. Da bai aure Husna ba
da hakan bata faru ba, dan haka he will take responsibility for it. Ya sani k'ila
ma ba zata tab'a yafe mishi ba, bai tab'a kawo rashin hankalin Husna har ya kai
haka ba. Shuru yayi tare da sunkuyar da kanshi yana me jiran hukuncin da zata yanka
a kanshi, amma kuma sai da maganar ta ta bashi mamaki.

"Thank you very much, na gode da ceto na da ka yi. Am so grateful to you, ban san
me zai faru ba da baka zo da wuri ba." Ta fad'a with shaky voice, da sauri ya
d'aura hannun shi a bakin ta tare da girgiza mata kai. "no ki dai na min godiya ni
ya kamata na miki godiya Aisha, am the cause roth of everything. Da ban aure ta ba
da hakan bata faru ba kiyi hak'uri ki yafe min." "No ba laifin ka bane haka Allah
ya so, komai ya wuce."

Ta yi k'arya in ta ce bata ji zafin abun da Husna ta yi kokarin yi mata ba, ko a


mafarki a ka fad'a mata Husna zata iya yi mata haka ba zata yarda ba, amma sai
gashi an wayi gari ta yi k'ok'arin haka. Ta d'auka bayan auren mijinta da kuma
kulla mata sharrin ta zubar mata da ciki ta gama sanin ta ashe-ashe ta wuce wurin,
da ba dan Hamza da kuma shi Aliyun ba bata san abunda zai faru. Thinking of it
kad'ai ma is terrifying her, amma kuma duk da hakan bata ji dad'in sakin da ya yi
mata ba. Duk da tana jin zafin ta da kuma haushin ta amma kuma y'ar uwar tace,
Husna har yanzu yarinya ce akwai yarinya a tattare da ita. Shi ya sa ma wani lokaci
bata biye mata dan ta san yarinya ce komai ya zo kanta ko an fad'a mata yi zata yi
ba tare da ta yi tunani ba, kuma ta tabbata wannan ba aikin ta bane wani ke d'aura
ta a kai da yake y'ar fari ce babu wayo sai take biye musu.

Yanzu dai aikin gama ya gama tunda saki uku ya yi balle ace zata sa baki a mai da
ita, addu'ar ta d'aya gare ta shine Allah ya shirye ta yasa ta gane gaskiya. "Allah
ya shirye ki yasa kin gane gaskiya, ya kuma baki miji na gari." Ta furta can k'asan
mok'oshin ta.

Months Letter~~~~

Haka suka cigaba da rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, fad'in irin
soyayya da kulawar da Aisha ke samu wurin Aliyu da mahaifiyar shi b'ata baki ne.
Tunda Hajjiya taji labarin cikin Aisha ta soma nuna mata kulawa ta musamman, haka
nan zata yi abubuwan kwadayi irin na masu ciki ta aika mata.

Zuwa yanzu alak'ar su ta gyaru, domin yanda Hajjiya ke nuna mata kulawa ba zaka
tab'a cewa sun tab'a samun sab'ani ba.

Dan bayan girki da take aika mata, kusan kullun sai ta k'ira taji lafiyar ta, wanda
hakan ba k'aramin dad'i yake ma Aisha ba. Dama burin ta kenan ta zauna da dangin
mijinta lafiya musamman mahaifiyar shi, kuma alhamdulilah burin ta ya cika domin
kuwa Hajjiya sosai take nuna mata k'auna kamar y'ar cikin ta.

Haka k'annensa ma su Hamida ba'a bar su a baya, sosai suka gyara halayen su tare da
karb'an ta hannu biyu musamman Balkisu da yanzu sun zama k'awaye da Aisha. Wanda a
yanzu ta koma gidan mijinta bayan sintirin biko da yayi, da ta ce ba za ta koma ba
amma da nasiha da kuma shawarar Aisha da ta dinga yi mata ya sa ta koma ba dan
komai ba sai dan har yanzu tana son mijinta kawai matsalar kishiyoyin ta ne bata
so. Amma ya yi alk'awarin hakan ba zai sake faruwa ba kuma alhamdulilah ya cika
alk'awari dan suna zaune lafiya da abokan zaman ta.

B'angaren Aisha da Husna ma sun dai-daita domin Husna da Baba Mariya sun zo har
gida suka nemi gafarar ta, kuma alhamdulilah ta yafe musu dan da ma can bata rik'e
su a ranta ba. "Allah ma muna mishi laifi ya yafe mana balle mu d'an Adam Baba."
Abinda ta fad'a wa Baba Mariya wanda hakan ba k'aramin sake sa Baba jin kunyar ta
ba, a tak'aici dai sun shirya kuma they moved on duk ba hakan take da Husna ba dan
har yanzu tana jin nawin Aisha.

~~~~~~~

HUSNA.

B'angaren Husna kuwa sosai ta shiga damuwa da kuma depression, gaba d'aya ta hana
kanta farin ciki da walwala. bata fita ko ina kullum tana d'aki bata fita ko nan da
tsakar gida ne, in an ga ta fita alwalla za ta yi ko wani uzurin. Tun Baba Mariya
na d'aukan abu wasa har ya soma fin k'arfin ta, sosai suka yi k'ok'ari dan ganin
sun jawo ta jiki amma abun ya faskara. Da addu'a da rik'on Allah ya soma d'an fita
waje, shima bata magana sai dai ta kurawa waje d'aya ido ta soma hawaye.

Sosai fa hankalin su Baba ya kuma tashi, nan a ka kai ta asibiti a nan ne ma suka
san da ciwon depression ke damun ta. Magani a ka ba su da kuma shawarwarin kan samu
war lafiyar ta, da rok'an Allah sadaka da kuma nasiha da ake Husna ta soma samun
lafiya. yanzu har tana fita a na hira da ita ta kan taya da wasu aiyukan gida ma,
zuwa lokacin Baba Mariya ta gani gaskiya. Sosai ta gane irin kuskuren da ta tapka,
cin amana da ta yi da kuma butulci.

Ranar da ta yi realizing abinda ta yi ta yi kuku har ta gode wa Allah, gaba d'aya


taji ta muzanta a gaban y'ay'an ta da kuma family. Wani irin son zuciya ne ya rufe
mata ido da har ta b'ata wa y'arta rayuwa ba ta sani ba, tabbas gaskiyan Husna ne
da tace ta b'ata mata rayuwar. Garin kwadayi da kuma neman abun duniya ta yi wa
y'arta lahanin da har duniya ta nad'e ba zai gogo ba, ta yi nadama, ta yi nadamar
da ba za ta anfane ta da komai ba. Wannan shi ne garin neman gira a ka rasa ido,
gaba d'aya jin kunyar kanta da kanta take. Yanzu ya za ta nemi gafarar y'ar uwar
ta, mutunen da su suka zame musu garkuwa lokacin da kowa ya guje su.

**** ****

AISHA.

Haka suka cigaba da rayuwa har Aisha ta shiga watan haihuwar ta, zuwa lokacin sun
gama siyayyar kayan baby unisex. Dan ba su yarda da maganar scan ba, su dai duk
wanda Allah ya su suna farin ciki da shi dan haka ba su damu da sanin sex d'in
babyn ba kawai burin su Allah ya kawo shi ko ita lafiya.

Ganin watan haihuwar ta ya shiga kuma Aliyu bai amince ta koma gida haihuwa ba ya
sa a ka yanke shawarar Baba fatsme ta zauna da ita, haihuwar fari ce dan haka ba
za'a bar ta ita kad'ai ba domin in ya fita office da safe baya dawowa sai yamma dan
haka komai zai iya faruwa kafin zuwan shi.

Wata safiyar alhamis bayan sun idar da sallah asuba ba ta koma bacci ba ta soma
gyare-gyare da kuma had'a musu breakfast, tana gama wa ta shiga d'aki tare da shiga
bathroom ta had'a ma aliyu ruwan wanka kana ta tashe shi. Kayan da zai sa ta cire
mishi tare da aje mishi kan gado kana ta koma kitchen d'in tare da fito da abincin
dining, lokacin da ta gama Aliyu har ya fito dan haka serving d'in shi ta yi tare
da zama kan d'aya daga kujeran dining ta soma jan shi da hira duk da irin ciwon
cikin da take ji. Wanda yau kusan sati kenan take fama da shi koda suka tafi
asibiti cewa suka yi tukunna lokaci bai yi ba, koda ta raka shi waje sai da ya
tambaye ta ko su tafi asibitin ne dan ya lura da yanayen ta kamar ciwon ne ya tashi
amma tace a'a ya yi tafiyar sa bata jin haihuwar ce.

Hakan nan ya tafi ba dan ya so ba ita ma ta koma ciki, d'akin bak'i ta shiga wanda
a yanzu ya zama na Baba fatsme. Samu ta yi ta farka ma har ta yi wanka. "Ah Baba
ashe kin tashi, ina kwana kin tashi lafiya?" "Lafiya Aisha fatan kun tashi lafiya?"
Ya kuma nawin jiki?" "Lafiya lau Baba, ke ma ya gajiyar hidima da mu. Ai yau da na
fito ban ganki a kitchen ba na ce kin makara kenan yau baki tashi da wuri ba, da
har zan tashe ki amma kuma na ce yau dai kam ke ma ki huta." Kin ji ki da magana to
waya fad'a miki a gajiye nake?" Kawai dai jiya ban yi bacci ba sakamokon tashiwa da
nayi sallar dare, kuma ban koma bacci sai bayan sallar asuba shi ya sa na makara.
Lokacin da na fito kuma na ga har kin gama aiyukan shi ya sa na koma ciki dan na
baku wuri."

"Kai Baba wani irin ki ba mu wurin?" Da kin shigo kun gaisa ai, ya tambeki na ce
yau kin makara." "Haka kawai na shigo muku sai kace mara Tunani?" Ni zaman nan ma
ba dan dan dole bane ba za'a yi da ni ba, haba abun da kunya ai gidan sirkin?"
Dariya Aisha ta fashe da, ita kam wannan abun na su Ummi na bata mamaki?" Komai wai
su gidan sirki ba za su yi wannan ba dasu iya yin wannan.

"Okay na ji to yanzu sai ki tashi mu tafi kiyi breakfast." "Ke ba zaki ci bane?"
"A'a ba na jin cin komai, kawai bacci nake son yi." "To kije ki yi bacci mana ba na
san kitchen ba in ina buk'ata zan zubo ai." "To shi kenan Baba ni zan je na yi
bacci." Ta fad'a tare da barin d'akin ta koma d'akin ta kwanta dan sosai take jin
baccin, cikin bacci ta soma jin ciwon baya kad'an-kad'an amma bata tashi ba domin
ji take kamar a mafarki.

Can dai taji wani azababban ciwo da tunda uwar ta ta haife ta bata ji irin sa ba, a
zabure ta farka da addu'a a bakin ta. Safa da marwa ta soma tare da yarfa hannu dan
azaba, wani juya taji cikin ta ya yi tare da wani azababban ciwo da ya sata soma
takawa a hankali har ta bar d'akin ta nufi d'akin Baba fatsme.

Turo k'ofar d'akin tayi da k'arfi tare da kwallawa Baba fatsme k'ira da k'arfi, da
sauri Baba ta fito daga bayi babu shiri dan dama alwalla ta shigo d'aurawa dan idar
da walha. "Aisha?" Me ya faru cikin ne?" Baba fatsme ta soma jefo mata tambayoyi,
kai kawai Aisha ta iya kad'ai mata domin ta ma kasa magana sai addu'a da take.
"Innalillahi, sannu Aisha sannu. Ki daure in sha Allah zaki sauka lafiya da izinin
Allah, bari na k'ira mai gadi ya zo a kai mu asibiti." Ta fad'a cikin tashin
hankali dan gaba d'aya ta rude, kama hannunta Aisha ta yi tare da cewa. "Baya na
Baba, baya na sai karya ciwo yake min." "Daurewa zaki yi Aisha, ciwon na d'an
lokaci ne." Ta fad'a tare da k'ok'arin fita domin d'auko kayan haihuwa su tafi
asibitin amma Aisha ta rik'e ta gam ta hana ta fita. "ina kuma zaki tafi ki bar
ni?" Dan Allah ki zauna dani zan mutu in kika tafi, kuma ni ba zan iya tafiya ba
kafafuna sun rik'e." "Sannu ba abinda zai same ki da izinin Allah ke dai kiyi
addu'a nima kuma ina taya ki da ita, ki kwantar da hankalin ki ba inda zan je kayan
haihuwar zan d'auka mu tafi asibiti... Shuru ta yi ba tare ta k'arasa abinda take
fad'a ba sakamokon fashewar faya, ai da sauri Baba ta rik'e ta tare da zaunar ita
kana ta wuce da'kin Aisha ta d'auko jakar kayan haihuwar.

Cire zanin dake jikin ta ta yi tare umartarta ta cire panta d'in ta kana ta zaunar
da ita kan ledan haihuwa da shima yana cikin kayan haihuwa da suka siya, a na haka
babu jimawa sai ga santalelen bouncing baby boy. A tak'aice dai Baba fatsme ce ta
karb'i haihuwar dan dama ungozoma ce tana karb'an haihuwa, within 2 hours ta gama
yi ma mai jego da babyn ta komai ta gyara wurin har da saka turaren wuta kamar ba'a
yi haihuwa cikin gidan ba.

Sai da ta tabbatar uwar da baby suna cikin k'oshin lafiya sun ci sun k'oshi tukun
ta k'ira Aliyu da layin Aisha kana ta mik'a mata wayar, lokacin da Aisha ta sanar
da shi haihuwar bai yarda ba sai da Baba fatsme ta karb'i wayar ta k'ara tabbatar
mishi da gaskiye ne Aisha ta haihu.

Fad'in irin farin cikin da wannan a halin suka shiga ranar bata baki ne, kan ka ce
me gida ga ciki da y'an uwa da abokan arziki a na ta mai-maita yanda haihuwar ta
kansace kowa ya jinjina ma Aisha na irin mijin k'ok'arin da ta yi. Haihuwar fari
kuma a gida gaskiya wannan babban risks ne amma da taimakon Baba fatsme komai ya
tafi dai-dai.

washe gari suka tafi asibiti a ka ba babyn vaccination ita ma Aisha sai da a ka
duba ta tukun suka koma gida. Fad'in irin soyayya da kulawar da da Aisha da babyn
ta ke samu wurin family da mijinta ba'a magana, zaman jefo me kyau da tsabta a ke.

Ranar suna baby ya ci sunan kakan shi wato mahaifin Baban shi Abubakar amma za su
na dinga k'iran shi da Arish, an yi shagali anci an sha dangi sun taka rawar gani
sosai dan hidima babu kama hannun yaro. Sosai a ka tashe kamar ba gobe, cikin
mutunen da suka halatta har da Baba Mariya da Kausar. Husna dai bata zo ba dan har
yanzu tana jin kunyar Aisha da kuma dangi amma kuma ta zo barka, kowa sai tambayar
ta suke daga masu tambayar lafiyar ta sai kuma yan gulma da ya mididi. Haka dai
ranar ta k'are kowa ya watse ba dan sun son ba, a ka bar d'ad'akun mutune wanda
suma washe garin ranar suka tattara suka koma. A ka bar Baba fatsme da ta cigaba da
kula da me jego wato ummu Arish, bayan arba'in Baba fatsme ta koma gidan ta da
kyautar sha tara ta arziki.

Sosai Aisha suka yi missing d'in ta dan gaba d'aya gidan ya zamar musu wani iri,
haka nan kullun sai take k'iran Baba da rok'an ta zo sun yi missing d'in. Rayuwar
juyi-juyi tun suna kiwa har suka saba da rashin Baba, suka cigaba da rayuwa a kwana
a tashi baby Arish yayi wayo dan zuwa yanzu an fara zamar da shi. Soyayya wurin
Hajiya kam ba'a magana, dan sosai take nuna ma yaron so. Soyayyar da take mishi har
tafi ta uban sa, dama an ce abun cikin kwan yafi kwan dad'i.

SOME YEAR'S LETTER.

Kwanaki sun rikid'e sun zama satuttuka,watanni,shakaru. Rayuwar juyi-juyi, yau ga


Aisha da yara uku, Arish, Amnah takorar Ummi sai kuma last born wato Basmah. Ya
yinda Eeman ma yaran ta hudu, Aisha da suke k'iran ta shanty sai Hasan da Hussain
da sa'ani suke da Amnah sai kuma last born Afifah takorar mahaifiyar Lukman. Zuwa
yanzu ba abunda za su ce sai godiyar Allah domin alhamdulilah bud'e ya zo suna
rayuwa cikin farin kwanciyar hankali da kuma aminci.

B'angaren Husna ma za'a ce alhamdulilah domin bayan zaman shakara biyu da ta yi a


gida Allah ya had'a ta da Usman, da fari bata kula shi dan gani take ko ta amince
da shi tare da bashi dama zai guje ta ne kamar yanda sauran mazan da suke zuwa
kuma da zarar suka ji bak'in tarihin ta suka tafiya ba tare da sake dawowa ba. Amma
Usman ya canja mata tunani, dan bayan ta sanar da shi rayuwar ta baya bai guje ta
ba sai ma tausayen ta da yaji ya kuma samu k'arfin guiwar auren ta.

Ba irin maganganun da ba'a fad'a mishi a kan ta ba amma haka nan ya rufe ido ya
aure ta, Usman ba mai kud'i bane amma yana da rufin asiri kuma yana da zuciyar
nema. Tun tana baya-baya da shi har ta zo ta fad'a soyayyar shi, tare a ka had'a
bikin da na Kausar wanda ita ma ta samu wani soja d'an Zaria amma bayan aure can
port Harcourt a ka kai ta dan nan ne wurin aikin shi. Haka Husna bayan auren su da
wata uku suka tattara da mijinta suka koma Maiduguri dan dama d'an can ne iyayen
shi a can suke dama ziyara ya zo Kano wurin kawun shi wanda a nan ne ya ga Husna
kuma ya fad'a da son ta. Dai dai k'arfin sa Usman ke yi mata hidama, matsalar ta
d'aya ce da take damuna ta ita ce rashin haihuwa amma ban da haka ba abinda ta nema
ta rasa dan Usman na iya k'ok'arin shi.
Lubna ma alhamdulilah ta shiryu ta koma gida tare da neman gafarar iyayen ta kuma
sun yafe mata, dan suma sun gane irin kuskuren da suka tabka na korar ta daga gidan
da suka yi. maimakon su zaunar da ita suyi mata nasiha da fad'a sai zuciya ta debe
su suka kore ta daga gida ba tare da tunanin d'ad'a lalacewa zata yi ba.

END

ALHAMDULILAH

Ina wa Allah godiya da ya bani iKON kammala wannan littafin lafiya, ina kuma k'ara
mik'o d'unbin godiya ta gare ku masoyan wannan littafi.Da fatan zaku cigaba da
kasancewa da ni Dan kawo muku wani sabon littafi na da zai zo muku da sabon salo.

You might also like